Showing 33001 words to 36000 words out of 170719 words
/>
Ahmad karka manta wata rana kai ubane, abinda kayiwa
dan wani shi zaa maka,, ba fata nake maka ba, karka yarda damar da ka samu Yasaka ka ji a ranka zaka iya cutar da wani, idan baka manta ba, Allah ya dubi zucuyarka ne ya had'a ka da abokin arziki irin Bagauda, Ahmad idan har ofishin da aka baka zai zame ma
ka tashin hankali don Allah ka hakura ka zauna a sana'ar bakin man ka, wallahi Allah yasan dalilin da ya Barka a wannan yanayin.
Ahmad ina maka nasiha ce domin inda zaka shiga na tab'a zama a matsayin dalibi, yau kuma zaka je a matsayin malami. Ina
laifin kayi ƙoƙarin inganta rayuwar wasu? Jami'a ce kuma dole duk wata tabargaza zaka samu akwai a can, ni dai don Allah karka tab'a abinda zai tab'a haular mu baki daya, idan su basu dauki mugun abu illa ba, ka nuna musu kai kasan illar shi, Raees ka duba
kanwarka tana da yara mata biyu namiji daya, Akwai Ramlat, akwai Bintu Fatima ga Rukayya, iya kan su kawai sun isa kare hakkin wasu, karka manta kai ba kowa bane, ba dan mafi su iya Sallah bane,ba wai kafi su iya kome bane Allah ya zab'e ka, sai dan ya gw
ada imanin ka, idan har ka tsalleke abubuw dayawa, sabida kimarka. Nayi Imani da Allah babu abinda zai same ka. Mutuncin mu,kimar mu, walwalar mu. Tana hannun Allah tana hannun ka, idan ka kare kimar wani, Allah ya kare naka, idan ka ci Mutuncin kimar wan
i Allah zai ci naka, muna hannun Allah muna Hannun ka, karka yarda a had'a kai da kai a cutar da bayin Allah, wannan shine nasihar da zan maka."
Sosai jikin shi yayi sanyi, tare da cewa.
"Umma Insha Allah zan yi aiki da Abinda kika gaya min, In
sha Allah zan kiyayye duk wani abinda zai zubda mana kimar mu, Umma Insha ALLAH zan yi aiki da duk wata kalmarki"
Haka ya mike tare da mata sallama, sannan ya shiga yayiwa Ishrah sallama..sannan yayi tafiyar shi.
Koda ya fito kofar gidan, kal
lon Abokansa yayi sannan ya ce musu.
"Zakaria zan tafi aiki amma yau shagon mai na ya koma naka, bawai dan na rena ka bane, a'a kawai naga dacewar ka tsaya a gurin kai ma kayi alfahari da kanka. Don Allah karka rena shi ba karamin sana'a bace."
"Ahmad
Bala Raees, ka bar min shagon man ka? Kai Nagode sosai, Insha Allah zan nimo kudi na kara har da Fetur zan na sayarwa."
Kamar zai fasa ihu, ya rasa inda zai shiga dan farin ciki, godiya kuwa kamar bakin shi zai zai tsinke, haka Nuhu da Raees suka
bar shi a gurin, yana godiya.
A hanya Nuhu yace mishi.
"Ahmad, Allah yayi maka sauyi cikin ruwan sanyi ba tare da ka sha wahala ba!, Kasan Meye ya kawo haka? Uwa! Kyautatawa mahaifiya wani arziki ne, gashi kaga yadda Allah ya maida al'amarin ka
"
"Kwarai kuwa na yarda da haka,"
Har ya sauki Nuhu a gurin aiki sannan ya wuce gurin aikin shi,
A hankali rayuwar Raees ya sauya, tare da Cigaba na musamman gashi duk abinda Bagauda zai yi sai ya sako Ahmad, duk wani mataki na rayuwa sai
ya sako Ahmad,.wasa wasa ya nunawa Mutane Ahmad magajin shine a kowani
ɓ
angare,
Alkhairi da Ahmad yake samu a gurin mutanen da suke tare da Bagauda babu iyaka, duk da wannan abin da ya samu, Bagauda yasa shi ajiye aikin makarantar ya saka aka bashi
aikin gwamnati a garin Abuja, a fadar shugaban kasa.
Inda a cikin wata shida kawai, duk zuwan Ahmad garin sai kofar gidan su ta cika da mutane, abin karyawa kuwa manyan kulolin bikin nan haka ake fito dashi, yayi wani irin kiba wanda ya bi jik
in shi, sake baya son tumbi sai gashi kibar ta saka saka shi ya zama Giant. Anan hankalin Ishrah ya kuma tashi mijinta ya zama handsome, dan haka idan zai tafi zai ajiyewa Umma duk wani abin bukata, ya tafi. Haka ma itama Ishrah tana son bin shi amma yaki
, bawai bai da inda zata zauna bane, mahaifiyar shi yake tunawa, shi yasa baya son ya tafi da ita.
***
Abuja.
Zama yayi tare da kallon office din Ahmad din, sanan tace mishi.
"Yarona hankalina ya kwanta da naga inda kake, kuma nasa ba za ayi dana
sani da kai ba. Zaka raka ni fadar shugaban kasa da magarib."
Cikin girmamawa da ya ke risine a gaban shi yace mishi.
"Insha Allah, Abba zan raka ka"
"Toh ya aikin dai da fatan babu matsala" cikin sosa kai yace masa.
"Abba babu kome wallahi"
"Me
yasa ba zaka tawo da ishrah ba?"
"Abba, bana son mahaifiyata ta zama babu wani da zai na gaya mata ina lafiya ne, duk da tana da wayarta amma ina son a kalla Ishrah ta saba da zama da ita,
koda nan gaba wani dalili zai taso ba sai nace ta zauna ba, kuma k
a ga umma bata lafiya, Salim ya tafi bautar ƙasa, idan aka watse Dijeemah ba zata iya daukar nauyin kome ban amma idan da ishrah Tabbas hankalina zai kwanta."
"Na fahimce ka, amma ko sau daya ne ka daukota ta maka sati biyu, Umma zata fahimce ka.
Kai magidanci ne da ya saba matar shi anan kuwa zaka na shiga hakkin kanka, sabida kai ba waliyi bane, muma da girman mu tsofai tsofai, haka bai hana mu niman iyalin mu ba, balle kai me niman arba'in da wani abu, dan haka ka dauko ta tayi maka sati biyu, i
dan yaso sai kana tsallaken zuwa. Idan tana nan kai dai ka je kayiwa Umma weekend. Idan ta gama kwanakin da zatayi sai ka mai da ita, ka kuma Cigaba da yadda ka saba.."
"Insha Allah haka za ayi, yadda kace." Inji Raees,
"A'a kawai kayi yadda kake so
, kar na sauya maka ra'ayinka."
Cikin hanzari yace mishi.
"Haba Abba babu kome wallahi, duk yadda ka fada haka za ayi."
"Toh Allah yayi maka Albarka." Inji Bagauda, ya mike da sandar shi da yake dogarawa da ita, sannan ya ce mishi.
"Ina hilton
hotel in room 340, ka tawo akan lokaci ina jiranka"
"Insha Allah Abba zan tawo."
Har gurin motar shi, ya raka shi sai da ya bar ma'aikatan kafin Raees ya koma, yana girmama irin kaunar da yake mishi, mutumin kirki. Mutane sun gaza fahimtar waye sh
i? Sun kasa gane yadda Allah yayi mishi kirki da mutuncin.
Ban da dattijon arziki waye zai iya wannan lamari, amma mutumin baki daya ya nuna shi mutumin kirki ne, dubi da Yadda ya rasa kafar shi daya, kuma yake amfani da na roba, bai tab'a gajiya da
taimakon talakawa ba, wannan yanayin yasa shi, shima jin a ranshi zai iya zama kamar Bagauda gurin kyautawa al'umma da wasu manyan abubuwan da zai kawo musu Cigaba a cikin Unguwar su, Insha Allah wannan alƙawari ke da ya dauka.....
Mai_Dambu
#PaidBook
#
Freepage
300
₿
katin mtn ko shaida ta wannan Numbers
👇🏽
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank! +2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
8/25/21, 8:02 AM - Buhainat
😝
: HAKKIN MALLAKATA
#Tue-Aug-2021
KISHI..
!!
~_A Tsakanin Zubda Jini
🩸
_~
Mai_Dambu
*Sadaukarwa ga Halimatu kangiwa (haliloss). Mrs J Moon. A'isha Fareedah Ya'u Nusaiba Sulaiman Ayuba jikalle na*
*16*
_Ina kuke matan ina kuke matan alfarma! Ina matar da ta yarda da kanta toh m
u marmatso nesa tazo kusa! A yau wannan kamfanin nan dai ta kuma dawo da karfin ta! Wato oriflame ta dawo muku da kaya masu aminci nagarta uwa Uban kyau ga sauki. A ƙarƙashin jagorancin feedy b collection ba iya kayan gare mu ba, akwai lashe masu kyau da t
sada akwai atamfoffin zamani masu kyau da k'awa uwargida ko amarya ina Kawayen amarya domin fidda anko ko wani shagali zaku iya tuntube,feedy b collection_
Mayukan gyaran jiki
Turaruka
Kayan kwalliya
Infection
~*Hmm garin garin mu da nisa, amma wannan
kina dakinki zai kayanki zai iso gare ki! Ga masu bukatar kayan zasu tuntube wannan Number:+234 808 663 9163 feedy b collection.... Sai kun zo sayan nagari mai da kudi gida*~
Wannan alƙawari ne da ya dauka a bisa kudirar Ubangiji, kuma zai yi kokari c
ika shi da yardan Ubangiji, ba zai yi kasa a gwiwa ba.
A hankali yake zaga ofishin tare da kallon ko ina, sanyin a.c yana kara ratsa shi ga kamshin room freshness, yana kara tabbatar mishi da yana cikin ni'imommin rayuwa, a hankali ya zauna ta
re da nazartar Bagauda kuma gaskiya ya gaya mishi,
Bayan magarib, ya shirya tsaf cikin wata material na maza tayi mishi kyau, sannan ya nufi hotel din da Bagauda yake ya nufa har dakin da y sauka, sai da ya buga kofar yace mishi.
"Ka shigo na gama shir
yawa ina saka kafar roba na ne"
Idanun shi ne suka cika da kwalla.
Tura kofar yayi, tare da sallama.
"Sannun da hutawa Abba."
"Yawwa Raees, bari mu tafi ko?"
"Toh Abba" haka ya mike tare da kafar robar, suka nufi hanyar waje suna hira cikin nutsuwa
, har waje,da taimakon kwatancen da yake mishi suka isa har gidan shugaban kasa.
Taro ne na manyan kasar baki daya, masu dirka-dirkan gashin baki, yan mata ne suka yi ta kawo musu abin sha, yana kallon wata shaidaniyar yarinya ta mika mishi lemo
a kwalba. Murmushi yayi sannan yace mata.
"Am ok"
Yana zaune sai ga Shugaban kasa, ya tawo har inda yake, ya mika mishi hannu.
"Dr Abdul Hamid Jamil,yace min kai yaron shine! Inda kake aiki babu matsala? Idan akwai matsala ka gaya min. A sauya m
aka da NNPC,ina ganin kamar gurin zai wadacce ka"
Mikewa yayi cikin girmamawa, yace mishi.
"A'a wallahi ya wadatar dani, ai Nagode sosai"
"Dr Abdul Hamid Jamil, baka gayawa Yaronka cewa nan gidan su bane, ina da yara kyawawa idan kana so ka shigo."
"A'a yallabai, Halima ta ishe ni. Ta zauna dani tun ban zama kome ba, dan na zama wani abu kamata yayi na gina mata rayuwarta da Goben ta a zuciyata. Ba na mata kyautar bakin ciki da kishiya ba, ni mijin mace daya ce Nagode."
Murmushi Bagauda yayi
sannan yace mishi.
"Nima ina bayan surukata, duk ranar da kace zaka mata kishiya sai na maka bulala da sanda ta."
Dariya duk suka saka tare da gayawa sauran abokan shi, anan din ma ya samu kyaututtukan, anan ya hadu da wani Dan jahar Tura, inda lo
kaci guda. Suka ji sun yarda da juna. A take mutumin ya bawa Raees fara gwada bude hannun jari mara ruwa a cikin sa. Kuma ya amince da shawarar shi, tare da gaya mishi idan har aka samu abinda ya dace toh yana son su bude kamfani koda a kasar waje ce,yadda
zasu ci gajiyar abin su. Kuma Raees ya amince da haka, a gurin shagalin ya samu kyautar mota sabuwa dal, da kyautar zunzurutun kudi masu mahaukatar yawa, a take suka ajiye magana daya da abokin shi zasu hadu.
Haka suka yi taron har suka gama, sannan ya
kai Bagauda hotel,shi kuma ya wuce gida.
Bayan kwana biyu, suka ha
ɗ
u da mutumin me suna Harees Abul Aswad, nan suka tattara kome suka zuba hannun jari a kamfanonin kasar da suke kusancin kasar,
***
A hankali rayuwa ta cigaba da tafi ha
r zuwa lokacin zab'e, gashi cigaba ta ina Raees yana samu, duk da baya ra'ayin siyasa amma Bagauda ya janyo shi yaga yadda ake dambarwan siyasa, abun bai birge shi ba, kawai yana amsa gayyatar Abba ne dan kar Bagauda ya ji haushi.
Tsaye yake gaban
Madubi, kanshi yana digar ruwa, hannun shi dauke da karamin towel yana goge jikin shi, Ishrah ta shigo dakin kallon shi tayi, tace mishi.
"Baby you look sexy" ta fa
ɗ
a in normal sound, murmushi yayi yace mata.
"Come on" ya bude mata hannu. Da sauri ta
fa
ɗ
a jikin shi.
"Ina fatan Allah ya azurta mu da yara na gari, amma zo na gurje ki"
"Amin Ya Allah, amma ai ni ba abinci bane da za a gurje ni, ma dai gurji juna" ta fa
ɗ
a tana shafa Jikin shi. Juyar da ita yayi suna fada gadon, ita kanta tasan Ahmad Bala
Raees, ne a saman ta, dan haka ya koyar da ita labarin shi da shi kanshi. Sannan ya mike a hankali wayar shi tana kara.
Dauka yayi tare da cewa.
"Ina zuwa" ya kashe wayar, ban daki ya shiga yayi wanka a gurguje ya fito ya shirya cikin wata d
ankarerriyar shadda fara kyal wacce aka mata aikin surfani da jar zare da blue, sannan ya ya murza jar hula irinta Jam'iyyar su, an rubuta GDP. Takalmin shi baki ce half Cover, yayi kyau sai wani daukar ido yake, ya dauki agogon shi ta Roxy, ya saka a ha
nkali ya ya fesa turaren Emergency, take gurin ya dauki wani shu'umin kamshi.
"Baby inda zaka fa akwai yan mata da yan iskan mata, kake wannan uban kwalliyar!" Juyawa yayi tare da cewa.
"Ahmad Bala Raees, bai da burin wata mace, idan ba Ishrah ba, ko
kina son na gaya miki gaskiyar abinda yake zuciyata tace?" Fari tayi da ido, sannan ta gyara zaman ta bayan ta sake mayafin gadon yana kallon kirjinta, hannun shi ya kai ya shafa kafin yace mata.
"Insha Allah kece matar Raees har abada, Insha Allah ba
zan tab'a son wata mace bayan ke ba, Na miki alqawarin babu macen da zan kalla da sunan mace koma yar uban waye ce, Ki yarda ko kar ki yarda ba zan taba kallon mace da sunan soyayya ba.
Wallahi na rena duk wata mace da zan ganta, bana jin akwai
cikakkun mara a duniya, Ishrah wallahi bana jin akwai macen da zan kusance ta kamar yadda na kusance ki naji dadi, Halimah na miki alƙawari bayan ke ba zan kuma ajiye mace da sunan mata ba, har ba mutu. Ki yarda dani" ya mike tare da nufar wardrob din shi
tare da ciro wani dan karamin box, mai fadi ya kawo gaban ta, ya ajiye mata akan cinyarta, a hankali ya bude mata, wata dankarerriyar dham ya ciro mata, tare da saka mata sannan ya ciro awarwaron ya saka mata su, Kafin ya sumbaci goshinta.
"Wannan naki
ne, Umma itama na bata nata kwana biyu da suka wuce, sai Khadeeja itama na bata nata, na turawa Maman Inteesar nata. Salim ya saya mishi mashin dan haka ki yarda dani bayan Umma ta, sai ke sannan kanena."
Sake baki tayi tana kallon shi, bayan ya sum
baci goshinta a karo na biyu, ya mike tare da kallonta yace mata.
"Ki rufe bakin ki, bari na nufi ungurin rally da za ayi da fatan ba wata matsala?". Murmushin yake tayi mishi tare da cewa.
"Nagode sosai mijina a dawo lafiya.". A hankali ya sakar mata mu
rmushi sannan ya fita. Cire dham din tayi bata san lokacin da kuka ya kwace mata ba, ta nutsu tasha kukanta zunzurutun bakin ciki. (
🤓😂
) Kiran Yayarta Tayi me suna mai suna Rumaisa. Cikin kuka take gaya mata.
"Aunty kwana biyu da ya saya yan kunnen bai
gaya min ba, kawai ashe sai d ya gama zabarwa Mahaifiyar shi da kanen shi har da Rukayyah da mijinta yake tatsar shi, Aunty duk zaman da nayi dashi cikin talauci da matsi lambar rayuwa bai gani ba, sai yau dan yaji dadina shine ya dauki daham din ya bani,
yana gaya min ya bawa uwar shi da kanen shi, wani irin abu ne baya musu, kwanaki sai da ya canzawa Maman shi furnitures da Kanwar shi, sannan ya zo ya saya min da nakina. Tsofin ya saka a dakin shi, Aunty ko zani zai yi saya mana kawai sai dai na ga Supe
r wax a jikin Umma ni kuma ya barni da kananun zani.
Wancan zuwa abuja ne ya kaini sahad store shine na zab'i Holand daya, Super wax biyu. Sai swiss. Wallahi yana can yana jidarwa Uwar shi da Kanen shi sai da ya kawo kayan na rena wanda na zab'e, in
a tsaye ya biya dubu dari uku, wa uwarsa kawai dari da tamanin ya kashewa, kanen shi kuka dari da wani abu.
Wallahi nayi danasanin zama a gidan da surika take, karfi da yaji an hanani moran mijina"
(Wallahi bamu kyautawa, meye a cikin dan yayiwa
Uwar shi da Kanen shi hidima? Meye a ciki dan ya kyautatta musu. Ina ruwanki? Lokacin da ta dauki
cikin shi kina ina? Iskancin wofi wasu surukan dama can haka suke fitannun amma ki samu mace dan ta, baki da hurumin saka ido akan su.)
Nan Yayarta ta sh
iga zugata, tare da gaya mata karta bar umma taci mata mutunci kuma daga yau mutunci ya kare, tayi ta zabga musu tijara.
Yadda ta daurata haka kuwa ta dauka, domin tayi imani da shawaran da Yayarta ta bata.
***
Yana fita gidan Umma ya shiga
ya gaishe ta, sannan ya ce mata.
"Umma zamu tafi yawon niman zab'e, nazo a saka min albarka"
.tana kan sallaya ne, amma ta sake murmushi tana fa
ɗ
in.
"Ya rabbil alamina ya tsare ku gaban ku da bayan ku, Allah yayi muku jagora, Ubangiji ya bada abinda ak
a fita nima,