Showing 63001 words to 66000 words out of 170719 words

Chapter 22 - KISHI COMPLETE

30 Sep 2026

1168

ya dauke nauyin iyalin Zakaria, ta hanyar daurawa Salim nauyi

.

   Sannan ya kuma saka a bincike yan fashin da suka kashe Zakaria, tun da aka yi addu'ar bakwai, Mahaifiyarta Zakaria ta kira Raees ta mika mishi katin bankin. Nan ya sha jinin jikin shi akan wannan katin aka kashe Zakaria! Dan haka ya dauki katin ya

dawo da ita, gida.

   Ya samu rashin mutuncin Ishrah, tun daga ranar sai yanayin shi yayi mugun sauya, baya magana inda ba a majalisa ba, baya shiga harkan kowa. Kullum mood din shi kamar wanda aka zage shi. Ita kanta Ishrah bata tsoro yake yi. Domin za

i iya kafta mata rashin daraja kafin kuma ya dawo yana bata hakuri.

     Dan haka babu shiri ta nufi hanyar gidan wani boka da yake mata aiki anan wani kauyen zuba, kallon ta yayi sannan yace mata.

"Mutuwar abokin shi yana jijjiga shi, karki matsa daya

wa. Kin ja lokacin ki fa, sai dai kadan ya rage mijinki ya dawo daga barcin da kika saka shi, taurarin biyu suna dab da haduwa da juna."

"Yanzun ya zanyi?"  Ta fada muryanta na rawa,

"Yadda zaki yi kenan karki bari ya koma komawa garin matukar ya koma

toh akwai aiki a gabanki. Sai dai idan lokacin zaben shi yayi baki isa hana shi ba."

    "Toh fushin fa? Tsoro yake bani"  ta fa

ɗ

a.

"Zai daina, amma bai zama dole ba, domin abu ne da Umar cikin ranshi da zuciyar shi."

Haka ya bata magani tare da yad

da zata yi amfani dashi.

***

Raees yana cikin yan majalisun da talakawa suke so, ga iya turanci ko a gaban shugaban kasa ne yana magana, haka yasa aka shiga nad'a shi a wasu kwamitin ma musamman.

       Ga iya wanka da

ɗ

aukar kayan, idan ya saka kay

a kamar wani wanda aka kera kayan a jikin shi ne, sai da ta kai Raees ya amshi lambar yabo sabida ya gwada shi dan kasa ne, duk abinda yasan zai isa gurin talaka bawan Allah nan yana tsaye akan shi, mazabun da suka zabe shi sun fi kowa moran shi.

  Duk

yan unguwar su ya taimaka musu ban da Adamu, domin sau biyu yana yunkurin taimaka mishi, yana mafarkin Zakaria cikin zubar jini,  na farko rike hannun shi yayi yana girgiza mishi kai, na biyu kuwa jini na zuba a jikin shi yana kallon shi cikin kuka tare da

girgiza mishi kai akan kyautar da zai bawa Adamu, ganin anyi daya anyi biyu, yace ina ba zai yi na uku ba..

Idan Ahmad ya tsaya yana jawabi, sai dai ka ga Igbo da Yoroba sun zuba mishi ido. Sabida yadda yake magana da fidda hakkin kowacce harafi yasa suk

e masifar tsoron shi, dama ga mutumin Giant ne, a tsaye yake ko irin tumbin nan bayi dashi.

Akwai wani award din da ya samu na sanatan da yafi sauran iya kwalliya, gashi idan Yasaka ko Suit ne, sai hankalin yan mata ya tashi.

      Wannan matsayin da

ya samu ya kara habbaka kishinsa da kaunar shi a zuciyar Ishrah. Dan haka take kaf kaf dashi, gani take kamar matan waje zasu cinye mata mijinta, ga wani irin azazzaben dokokin da ta daura mishi.

   *

Kowace rayuwa akwai jarabawa, matar Salim ta haih

u, inda ta samu d'a namiji, aka sami shi sunan babansu Muhammad, suna cikin jego aka mai da Salim Lagos, da farko ya tafi sai da yayi wata biyu sannan ya dawo, anan yake son tafiya da matar shi, amma ya rasa yadda zai gayawa Umma.

   Karshe ita ta fahim

ci yana son tafiya da matar shi bata hana ba domin Umma adalar mace ce, bata riko, bata kuma gaba. Dan haka ya ce ya tafi dasu, domin tasan halin shi, idan bata barshi ya tafi da matar shi ba, zai iya fadawa mugun abu, ai babu amfanin badi ba rai. Ta boye

damuwar ta, dan haka suka tafi bayan ya sauke duk wasu abubuwan da suke kan shi, sannan suka tafi.

Baya bata kad'an, tun bayan tafiyar su, Khadijah ta kwanta babu lafiya.  Musamman ciwon ciki, haka suka yi ta jigilar asibiti, kudin hannunta ya kare.

     Haka idan taje niman aro akan idan salim ya turo zata kawo musu, an hanata.  Wasa wasa sai da ya kai Umma fara jin gidan mutane rokon abinda zata ci, ana bata wasu suna wulakantatta.

     Domin shi Salim da ya tafi kamar an dauke hanaklin shi daga

kan Umma.

    A hankali rayuwar tayi Tafiyar bazata.

   Domin bayan na samu lafiya na tafi gurin dangin Mahaifiyata. Amma ina isa can kaka na yace min.

"Sha rubutu, ina jin a jikina mijinki ya kusan bayyana"

"Allah mai turare ka raba Ni da batun aure

n nan, ina da mijin karfe irin ka me zanyi da katako?" Na fada mishi.

"Sha rubutu zaki yaudare ni ne? Ni zaki cewa karfe bayan nayi imani da Allah kina samun miji zaki manta da ni"

"Kai Mai turare na? Mijin Hajiya Hajjo da Meramu yar kunama, mijin Haww

a! Ina da miji irinka ai sai godiya kawai miko min yan canjin aljuhun ka"

"Aashir, Elyakub, Annur. Alhaji" duk ya kwalawa Iyayena kira.

"Kun ganta! Zata cuce ni"  ya nuna musu ni, zama suka yi suna dariya.

"Babee! Amma ai sharubutun dai takace, kuma"

"Aiwo! Toh wato gani nan mara gaskiya ke gaya musu abinda muka yi" cikin harshen shuwa na gaya musu abinda ya faru, dariya suka saka na cigaba da cewa.

"Mai turare kawai ka bani yan canjin aljuhun ka, sai a wuce gurin. Kasan ina sonka"

"Karya kike kina

son kudina, ku fitar min da yar damfarar nan, bata tashi abin arziki zai ta fahimci ina da kudi a jikina, tun daga zuwan ta nake rasa yan canji na."

"Toh me turare na, Ayya bani da Angon da yafika, ina sonka".na fada kamar zanyi kuka,

"Ni kuma bana son

ki Matana nake so" haka muka yi ta rigima dashi sai da ya cire kudin domin kawunaina sun yi kokarin bani nace na mai turare ne so. Yana bani yana min gori. Haka na tafi ina murna.

     "Ina ji a jikina ta kusan aure! Kuma zata nutsu sosai, sai dai ranar

da tazo na fahimci akwai masu bibiyar rayuwar ta, domin tunda tazo nake istahara a kanta, sai dai kuma kanta yana da karfi da kwari, tana daga cikin mutanen da ake kira yan baiwa, an yi anyi a tab'a ta haka bai damu ba, da gaske sha rubutunka ce Babee"

Murmushi yayi sannan yace musu.

"Tun daga ranar da aka dawo da Uwarta, na fahimci akwai haske, an haife ta bayan mutuwar iyayenta maza, lokacin da na dauke ta na mata addu'o'in, dai naga kwayar idanun ta, yana fitar da wani irin ruwa, fari kamar madara,

na kaiwa Malam ita ya ganta, abinda ya gaya min ne ya bani mamaki.

"Yarinyar dai haife ta a lokacin mafi girma da muni,, sanyi ya fidda zafi. lallai dabi'ar kowani mutum yana jinin shi, tatta

ɗ

abi'ar daban ne, ban sani ba ko zan yi nisan kwana. Amma tab

bas jinin da yake yawo a jikinta na musamman ne, domin zata iya raba kowane a muhallin shi." Koda ya gaya min wannan yayi min magana na kula da lafiyar ta, domin kar a samu matsalar gurbatacciyar dabi'a ta bayyana a jikinta, sannan ya gaya min mutane dayaw

a zasu nime ta, domin ita din ba kasafai ake samun irin su ba.

         Shi yasa na maida hankali kafin ta bar kasar nan sai da ta ha

ɗ

a Alqur'ani. Sha rubutu tana da

ɗ

abi'ar mutane uku, domin bayan komawarta kasar mahaifinta Sha'aban ya Cigaba da kawo m

in bayani kanta, anan na fahimci, tana da kirki irin na mahaifinta, tana da hakuri irin na mahaiyarta, sai dai tana da zafin rai ina na Hussain din Ubanta, haka yasa take shiga cikin bangar siyasa.

    Ban kuma sarewa ba, sai da naji labarin tana bin y

an siyasa har ana zargin tana bin maza, sai naga duk cikin ya'yan babu mazinaci, balle nace hakki ne. Mahaifin da Mahaifiyar ta ba halin su bane, haka kanin mahaifinta, sai na cigaba da mata addu'o'in, nasan san Allah yana amsar addu'ar bayin shi. Sha rubu

tu ba irin yaran nan bane, domin bata da kawaye sai maza, kamar yadda muke nan muna niman kudi sharubutu itama haka take tana da manyan shaguna yana da motar Safa, yarinya ce qarama amma Allah ya bud'a mata, kuma Alhamdulillahi tana cikin masu kyakyawan na

saba. Da niyya shi yasa Allah ya kare mana ita, ko yanzun kudin da ta karb'a ba ita zata yi amfani dashi ba, d'azun ina dawowa masalaci, naji suna hira da malam Haliru, take cewa ya ajiye aikin ya huta, shine yace yana da iyali da yara, ba zai iya ajiyar a

ikin ba. Saboda yaran shi duk mata ne, shine tace mishi bari ya ciro kudin ai dole ya hakura sai da lafiya ake kome, shine ta fita ta bashi na b'atarwa. Kunji yadda ake rayuwa, tausayi halin mahaifiyar ta ce, idan ta ga wani na nima zata bashi ta hakura, t

oh gashi Humairah ta dauka, har ya fi na Uwarta, domin ita nata domin al'umma ce"

       Jinjina kai yaran suka yi, sannan suka ce.

"Gata nan dai kamar bata magana, amma kuma tana yi da kai da Aashir, kune abokan hiranta sai, irfan." Gyada kai yayi Alh

aji yayi Babban yayan su, shine baban irfan.

"Ai jiya ina jin shi yana ce mata, Hajiya Fareedah me zakiyi da kudin account dinki haka,. Taimaka ki bani mana!"

Ta ce Mishi.

"Ko zaka mutu ba zan baka kwandala ba, ina da ma'aikata sama da dari biyar, kuma

ni ke biyan su, kuma ina son na bude makaranta karkashin sunan iyayena, amma kudin bai kai ba, domin baki dayan shi, miliyan Talatin da biyar, toh sai naga iyayena bari na gina musu masallatai, Akwai Kabir jijjiya, Musa dan kani, sai Tasi'u loto. Yarana ne

da aka kashe shi, a shekarar da ta wuce, ina son bude makarantar da sunan su, shi yasa ba zan baka kwandala ba."

Ya bude baki zai mata magana na fito ina ce mishi.

"Amma kai kan da maganar kudi kamar jimina, karki bashi Ubangiji ya idda nufi." Yarinya

r zuciyarta na da laushi da taushi, amma bayan haka sai da ya gaya min ta bashi kudin amma ta mai dashi Dalar Amirka, ta tura mishi, ita mutum ce da bata damu da kanta ba, sai wasu. Allah ya bata mijin da zai damu da ita, domin kuwa idan ta samu wanda bai

damu da ita ba, zata wahala ita zatayi ta bauta mishi yana kwance baya kome"

   Haka suka yi ta hiran su akan ta, har zuwa lokacin sallah la'asar suka watse.

   Satina uku a can na shiga shirin dawowa gida, babban abinda ya dame ni, mafarkin da na ta

b'a yi a asibitin nan ne ya kuma d'aga min hankali, dan haka naji sam zaman garin ya ishe ni, kamar da wacce ake ingizo ni gida.

        Dan haka babu shiri na dawo, sai da nayi kwana uku. Ina kallon madubi naga uban kibar da nayi,.na dauko Tap na gwada

. Ji nayi kamar zuciyata zata buga babu shiri na dauko kayan motsa jiki na fito.

   Unguwar babu kowa haka na wuce, Allah sarki yarana suna gani na suka shiga take min baya, domin a kofar gidan mu suke ajiye ababben hawan su, dan haka suka biyo Ni a nap

ep suna hira.

    Karfe shida da wani bi, bakwai saura kadan na dawo muna tafiya dasu muna hira akan zasu yi aure ne ma.

"Toh na dauki nauyin kayan lefe"

Ihu suka saka suna murna, mun zo daidai kofar gidan da na tab'a ajiye Maman Khadeeja naga tana ku

ka tare da cewa.

"Ku taimake wallahi zata mutu, don Allah ku taimake ni"

"Waye zai taimaka miki, bayan yaranki babu kananun masu kudi!"

"Adamu karka manta akwai Allah ta fa

ɗ

a cikin kuka tana kokarin d'aga yarinyar."

"Kai dan durun uwar mutum ya bar nan

kunga yan kutumar Uban can, Uwar Daba mu kaddamar mishi ne? Kaga dan iska mara rabo a duniya."

"Goga maza jeka Umar ya baka mota na ka kawo, kace Hajiya ta baka jakata ka kawo min don Allah Karka bata lokaci."

8/30/21, 1:07 PM - Buhainat

😝

: 32

"Dun

a kaci min mutuncin wannan gayen, tun ina yarinya na tashi da wasu abubuwan guda uku. Idan kayi min bana kallon shi a matsayin laifi, idan na maka laifi zan baka hakuri, idan kuka ka tab'a babba, zan kuntatta maka ku gyara mishi zama a Unguwar nan"

    

"Don Allah ki kyale shi." Ta fa

ɗ

a cikin sanyin tare da da kuka.

"Duna kyale shi, amma."

"An gama Uwar Daba" jikin shi rawa yake, Sabida amma din yana nufin idan muka bar gurin, goga na kawo motar muka d'aga yarinyar muka saka ta, sannan na na shiga guri

n tukin tana baya.

"Kai ku gurja min takalmina, sannan ku goge min kayana, ina nan tafe, ku kai gida ku ajiye min"

   Sannan na fisge motar da gudun bala'i, ina jin zuciyata tana bugawa, dake ni dai matuƙar ina da mara lafiya, toh asibitin kudi baya zuwa

min sai na gwamnatin, muna isa suka shiga gaya min magana ba zasu dubata ba, Ni kuwa na fita gurin motana na dauko addata tsiraranta, na saka a ƙafadana.

"Zaku dubata ko na kaddamar muku da aikin sa kai?"

"Ke zamu kira miki yan sanda!"

"Zai fi kyau k

u gaya musu Uwar Daba bace tafito mission." Na kame, akan lokaci aka shiga da ita tiyata.

"Mama karki damu zata ji sauki, bana son kina kuka. Ba gani ba, kukan me zaki yi? Ai mu an haife mu ne domin ku, yau kina kuka sai naji babu dad'i, kawai kwantar da

hankalinki, zata ji sauki"

      Baki daya tausayin yarinyar take ji, ga mace har mace amma baki daya rayuwarta a dunkule,

"Allah yayi miki albarka"

"Amin Mama na!"

"Su waye suka kawo Khadijah Muhammad?"

Mikewa nayi tare da saka hannu a cikin aljuhu

n wandon jikina nace mata.

"Gamu nan"

"Ana buƙatar jini ne? Kuma akan lokaci!"

"Baki da damuwa" hannu na saka a aljuhun wando na, na ciro wayata. Sai da na gama latsa wayar na saka a kunne.

"Yarinya taya zamu sami jinin?"

"Mama Suna na Aishafareeda, k

awai kirani Uwar Daba ma"

   "Hello don Allah ka zo asibiti,maza"

Zai min magana nace mishi.

"Naji ciwo ne jini ya zuba ana niman jini" na kashe wayar, can ya kirani.

"Wani asibiti"

"Medical center"

Can kuwa sai gashi nan, gani ina tsaye da kafana,

yana zuwa na nunawa Nurse din shi, nace mata.

"Jinin shi grp O ne, kuma bai da matsalar kome, baya shan ta

ɓ

a. Baya bin mata, bai da typooh, bai da maleria. Kai ki duba shi sosai."

   Sannan na zauna, can sai gashi sun fito da jinin.

"Ina yaƙe?"

"Ya

na hutawa"

"Toh yayi kyau"

Na nufi dakin, yayi shar alamar an kwashi jinin shi.

"Ya haka kamar tsuntsun da ruwa yayi mishi duka? Toh sannu huta sai mu tafi gidan."

   Haka na fito na same ta, ta zabga tagumi.

"Mama babu kyau tagumi, gani meye zak

i damu, Allah na tuba ko me kika ce kina so a yanzun sai inda karfina ya kare,"

     "Haka ko? Da gaske idan nace ina son ki min abu zaki yi?" Ta tambaye ni idanunta cike da kwalla.

"Wallahi billahi Azim, matukar bai fi karfina ba, kai ko yafi karfina

zan yi, koda shine abu na karshe da zanyi  a rayuwata! Zan miki mama da ina da iyayen a raye ba zan barsu, suyi kuka ba. Da na ganki sai naji kamar na sami uwar da na rasa ina da shekara takwas, dan haka ki gaya min Insha Allah zan yi"

          "Alhamd

ulillahi! Insha ALLAH zan zo niman Alfarmar ki, amma sai yar uwar ki taji sauki." A hankali na mike tare da cewa.

"Toh Allah ya bata lafiya. Zamu wuce amma zan kawo abin karyawa, idan zan wuce aiki"

     Komawa nayi gurin Umar muka tawo gida,tun a hany

a yake ja min Allah ya isa, magana da cin mutuncin yayi min, amma ban damu ba, muna zuwa gida na rike shi ya shiga cikin gidan, Hajiya na ganin mu ta shiga salati, kunshe dariya nayi na Barsu tare, sannan na kira Basira ba bata aiki ta fara min, yar Gwaggo

na ce, tana dariya tare da cewa.

"Wallahi kaji kunya, Umar jini aka diba kamar an kwashi rayuwar ka."

"Hajiya kin gansu ko? Wai dariya suka min, ina nasan wannan ta'addancin kika shirya min ai da ban je ba,muguwa me bakin hali"

   "Nagode sosai"

Ha

ka yayi ta gaya min magana naki kula shi, sanan na samu Hajiya na gaya mata abinda yake faruwa kafin karfe goma, na saka doguwar gown dina, na nufi asibitin, ina zuwa naga tana boye takardan da aka rubuta magani.

"Mama bani takardan."

"Wai zan tafi nim

an taimako ne, kar na daura miki nauyin da yawa!"

"Kinsan yadda na samu kudin da suke gurina? Dan haka bani, a banza ki fita garin niman taimako wani dan iska ya gaya miki magana, sai naci uban mutum wallahi" na ajiye mata abun karyawa na kuma naje na biy

a kudin dakin a aminiti, aka zo aka wuce dasu. Muka bi bayan su,sai da na gama kome sannan da zan fita na ciro dubu sha biyar na ajiye mata.

"Idan an rubuta magani, ga Number na don Allah ki kirani, idan kin dauke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login