Showing 87001 words to 90000 words out of 170719 words
dai ba gori zaku min na Umma ta haife ku ni karere ce uwar yan shishigi."
"Allah ya baki sa'a, Ubangiji ya tabbatar da alkhairi, mun gode da kulawar da kike da Mahaifiyar mu."
"No need! Ni dai Allah ya bamu ni
san kwana ku taimaka min akan nawa rayuwar!"
"Kiyi hakuri" Nuhu yace min,
"Kinga baban Inteesar ya ajiye mishi aikin shi ya koma bakin aikin shi da yake, don Allah ki taimaka min karki juya baya dayawa."
Murmushi nayi sannan na fita, sai da
muka kwashe kwana biyar kafin na had'a mana ko, sannan tare da Khadijah muka tafi.
Zan iya cewa Alhamdulillahi, mun iso da kwana uku, baiwar Allah nan ta motsa, kafin saka shiga aiki akan ta. Tsawon Wata Daya ana Abu daya. Kafin ta fara motsi baki
daya.
Sai dai haka kawai idan kuka mata brush zata shanye ruwan, idan kuma kuka bata tea zata zubda shi, suna ganin haka suka shiga da ita aiki. Amfanar mun cire rai da ita, domin bayan an fita da ita, Umma kamar ba zata rayu ba. Haka muka
kwana a tsaye akanta, wannan karon Khadijah ta kira Rukayyah da Salim, ta gaya musu. Babu shiri Nuhu ya tafi har Abuja.
....
Kasancewar an sanshi tare da Minista, yasa koda baya nan ta tafi majalisar zartarwa na shugaban kasa, yana zaune har ta s
higo wani cin magani yaƙe kamar yaga kashi.
"Ba sai ka wulknata Ni ba fa? A'a ko daya, baka isa ba, magana nazo maka dashi akan Umma, mun idan ka gadama ka tafi Germany idan ka gadama ka zauna ka rike Ishrah, tafi uwar da ta haifaka. Wallahi ina tsoron
fushin Allah akanka."
"Nuhu! Umma nace ba lafiya?"
"Bani da lokacin ka" ya gaya mishi tare da barin Office din, ya barshi cikin tashin hankali, ya ajiye duk wani aikin da yake gaban shi ya dauki hutu. Koda ya iso gida. Ya samu Ishrah bata gida wa
i ta tafi dauko uwarta bata da lafiya,kuma dama kwana biyu da suka wuce ta gaya mishi Hajiyarta bata da lafiya kafarta yana ciwo, kamar wanda aka mishi wani abu ya farka daga barci ne ko ya fara tuno abinda yake faruwa dashi, kamar ya fasa ihu haka ya zaun
a yayi shiru.
Yayi rasa me yake damun shi, a hankali ya mike ya shiga had'a kayan shi, a daren ya bar ƙasar.
**
"Ba zaki kuma samun damar da kika samu ba, sai dai na ce miki kika sake a wannan tsarin idan kika nace zaki iya hauka ko k
i mutu. Domin suna gabbar da duk wanda ya kuma shiga tsakanin su zai fadi gaskiyar shi."
"Malam kayi wani abu! Don Allah" Ishrah ta roke shi kamar zata yi kuka,
"Babu hanya, sai kace ba mace ba? Ke zaki iya rike shi da kirsa da kisisina, dan haka k
i rike haka"
"Toh" ta fa
ɗ
a a dakile,
"Hajiya Halimah idan kika tafi wani gurin, abu biyu zaki tashi zaki iya samun wanda yafiki shu'umancin, domin zai kwanta dake yayi miki aikin da koda kin samu nasara zaki yi hauka tuburan, sannan kuma idan baki
yi da gaske ba zaki kunshi bakin cikin da har ki mutu ba zaki manta dashi ba"
Haka ta mike tare da barin d'akin,a ranta tana fadin mugun nufinsa ya koma kan shi, sai ga bayan Umma da Aishafareeda.
**
Lokacin da ya iso, muna zaune ya iso
. Lokacin har su Salim sun iso, sannan ya zo. Babu laifi naga yana bina da kallo, musamman dake Allah yayi ni bana son kananan kaya, shi nake sakawa tare da jacket har gwiwa ta, nake Salim bayani, cikin murmushi Salim yace.
"Sannun Yar Umma Allah ya baki
lada."
Sosa kai nayi, tare da cewa.
"Kai wannan meye a ciki, kamar Uwata umma take."
Baki daya haka muka kwana a asibitin, babu wanda ya rintsa,sai gurin Asuba likitocin suka tabbatar ta fita daga yanayi me hatsari,zamu iya tafi. Dama
mun gaji, dan haka masaukin mu. duk muka nufa.
Safiyar suka kuma kama masauki Salim da matar shi, ni dama da Khadijah daki daya muke, sai oga Ahmad. Da yake wani cin magani, ko yana tunanin zan Nime wani abu ne, ganin na shiga dakin na kwanta, ban bi
ta kanshi ba yasa shi jin babu dad'i.
Dake tun a asibitin muka yi sallah, barci muka wuni yi.
Ji nayi ana zunguri na , na bude idanuna. Tsaye yake da wayar shi.
"Lafiya?"
"Karb'a Alhaji Mai turare yake son magana dake"
Amsa nayi tare
da kallon wayar sannan na latsa wayar tare da sakawa a kunne na.
"Angona!"
"Na'am"
Nan muka shiga hira, sam na manta dashi, a dakin yana kallon yadda nake hira, tab'e baki yayi tare da cewa.
"Kome na yan duniya kin iya"
Ban kula shi ba, na cigab
a da wayana, sai da na gaji sannan na mishi sallama, na ajiye mishi wayar shi ka juya baya, tare da Cigaba da barcina.
Kwanan mu bakwai Allah da ikon shi Umma ta farka da nutsuwar ta, nice na mata wanka da alola, na shafa mata mai sannan na saka mat
a kayanta, sannan na gyara mata zama tana kallon alkibla, ta jima tana ibada.
Tana idarwa ta kalle ni sannan tace min.
"Kwana nawa ina kwance"
"Umma kusan sati Uku ne"
"Toh Allah ya bani ikon sauke salolli kaina."
"Amin Ya Allah"
A hankali ta
fara gabatar da sallar, ina kirgawa. Har suka zo baki daya, suka zauna sun zo da abincin Afrika, tana idarwa aka saka mata abincin.
"Waye ya sayi?" Ya bude baki zai magana nace mata.
"Nice na bawa Salim kudi ya sayo mana"
Shafa kaina tayi tana fa
ɗ
in.
"
Ubangiji ya baki tsawon rayuwa, domin ki mori aikin Alkhairin ki"
Murmushi nayi tare da cewa.
"Amin Ya Allah, Umma baki dayan mu"
"Dukkan nayi muku addu'ar"
Kowa ya gaisheta amma taki amsa na Ahmad, ban tab'a ganin ta cikin fushi da b'acin
rai ba sai a wannan lokacin. Koda likitocin suka dubata cewa suka yi.
"Anya kuna son matar nan kuwa? Me yasa kike b'ata mata rai? Yanzun baka zuciyarta yana harbawa sama da yadda yake a da, don Allah ku kula da lafiyar ta,"
"Mun gode"
Shiru dakin ya
dauka suna ta kallon yadda Umma take amsar abincin da nake bata..
"Aishafareeda! Allah ya baki abokin rayuwa na gari, kiyi hakuri na lalata miki rayuwa, kuma baki samu yadda ya dace ba, nasani jarabawar mu ce. Aishafareeda kice ya fita bana son ganin shi.
"
D'ago kai nayi ina kallon shi, yayi bala'in firgita, tunda taki amsar gaisuwar shi ya fahimci haka.
"Idan ba zai fita ba, Ni zan fita"
Sake d'ago kai muka yi muna kallon juna. A hankali ya juya tare da fita.
"Umma!"
"Bishi" tacewa Salim, tsuru tsu
ru Khadijah tayi.
"Kema bisu"
"Umma ita"
"Kyale ni Nanah Aisha, su fita Allah ya bani yara Bama su share min kuka ba."
"Umma ki daina gaya musu haka,. Kamar zata yi kuka tace min.
"Ya zanyi? Ina son su dukkan su, nasha wahala akan su, bayan mutuwar
mahaifin su. Babu wanda ya taimaka min sai Allah ashe ba zan huta yanzun a jikin su ba?"
"Umma zaki huta, Insha Allah lokaci na zuwa."
"Idan na mutu? Ko idan na nakasa? Aishafareeda bani da yancin ni da Yarana? Babu wanda xan kalla nace ina jin sauki a
tare dashi sai ya'ya mata?"
Rike hannunta nayi cikin nawa, ina kallonta kafin nace mata.
"Duk gwagwarmayar da kika sha Umma baki sare ba sai yanzun? Umma na zata zaki Cigaba da faffutikar nasarar yaranki ne? Umma sai kuma naji kina cewa kin gaji! Karki
gaji dasu, idan har Allah da ya halicce mu bai gaji damu ba, Umma ba zaki gaji da su ba, umma ina can ina kazaman rayuwa kika kawo ni nan fa, kika inganta min rayuwa, Umma baki kyamace ni ba, sai ma nuna min da kika yi zaki iya zama dani. Umma hannunka ba
ya rubewa ka yanke ka yasar, sai dai ka nima mishi magani, Umma kiyi hakuri, Insha Allah daga rana irin ta yau, na shirya domin baki farin cikin sosai. Amma ki yafe masu"
Murmushi tayi sannan tace min.
"Ina kaunarki dan kaifin basirarki, kin iya sa
rrafa harshenki, kin san darajar kanki da na iyayenki, har da na wanda ya rab'eki. Ina sonki sosai domin yakanarki, ina sonki domin hakurinki. Ina sonki domin mai da kome ba kome ba, Aishafareeda wallahi na yarda dake sama da yadda baki dauka ba. Allah yay
i miki albarka, ya kuma baki Zuri'ar dayyiba."
Dakyar na iya cewa.
"Amin" sabida ta bani kunya, umma har yau kunyata take ji, dan haka nima nake jin kunyarsa.
....
"Yanzun sabida Fareedah ta kore mu? Me yasa umma ta zab'e ta,akan mu? Wallah
i nayi matukar jin haushin yarinyar."
Inji Ahmad,
"Duk haushin da zaka ji tayi nisa, Yarinyar kamar bata san ciwon kanta ba!" Inji Salim,
"Wai ya akayi ma kuka tawo nan?" Ahmad ya tambayi Khadijah,
"Aunty Fareedah ta biya kome har jinyar umma, kuma k
udin tana gina wani makaranta ne fa? Amma baiwar Allah nan ta saka shi a kudin jinyar Umma, ta tsayar da aikinta. Wallahi idan kace zaka wulakantatta, Umma zata iya maka baki, domin tana son Aunty Fareedah sosai."
"Akan Fareedah zata min baki?"
Ya tambayi Kanwar shi cike da mamaki.
"Baka yarda ba kenan? Toh shi Kenan"
Shi mamaki abin ya Bashir kuma ya zata karya take, kawai taga ai umma ta dauke mishi wuta baki daya.
Gashi aka kiran shi a gurin aiki, kuma nan ya kasa samun kan Umma, ma da
wo gyara jikina sabida al'adar data zo min, ashe ya biyo ni, ban sani ba, ina shiga yana turo kofar a razane na juya.
"Meye haka?"
"Abu nazo nima a gurinki"
A matukar razane na kalle shi ina kallon jikina. Shafa wuyar shi yayi tare da jingina da k
ofar d'akin. Kallon bakin shi nayi tare da dauke kai na. Sabida bakin cikin abinda yake bukatar nayi mishi...
"Sai nayi nazari"
"Kinga!"
"Excuse me!" Na wuce ban daki na barshi tsaye, ni Ahmad zai renawa hankali. Yana takalata da magana.....
🤷🏽
♀
️
Kis
hi a tsakanin zubda jini isn't free, if you need chat me.
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank!
+2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
9/3/21, 11:11 AM - Buhainat
😝
: 44.
Bai bar dakin ba har na fi
to, ina gyara zaman pant dina.
"Malama ki tsaya mu yi maganar gaskiya"
"Bani da lokacin ka" ya zata da wasa nake, sai da yaga da gaske nake, naki bashi koda kashin lokaci ne balle ya fahimci zan hakura, haka nayi ta gara shi. Sake kwana hudu nake h
ailata, kamar yana sane da kwanakin, yau na dawo da wuri, kasancewar ranar talata ne, na shiga nayi wanka.
Ya biyo ni dakin, zama yayi tare da marairaice fuska. Ina fitowa na ganshi a zaune. Dauke kai nayi tare da shimfid'a abin sallah, na saka do
gon riga xan yi sallah ya tsaya a gabana.
"Ki saurare ni mana! Kasan kin mallake Umma, amma bani da wacce zata iya min wannan aikin sai ke, dan haka ko gaya min nawa zan biyaki?"
Cike da takaici nake kallon shi.
"Don Allah ka bani guri nayi Ib
adana"
"Don Allah mana! Aishafareeda ki taimaka min mana"
"Dama karuwa tana da rana ce? Na zata karuwa bata da amfani, sai dai shishigi da karere. Kasan Allah ka fita ka bani guri"
"Fareedah ina binki ne saboda na san kece kawai zaki iya sassantani da
Umma, kuma ai ba wani abu bane, zamu kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin mu, zamu kuma zama abu daya a gaban jama'a."
Nad'e hannu nayi a kirjina nace mishi.
"Ni fa karuwa ce!"
"Ki bar wannan maganar, anan nima na a gurin aiki, kuma bana son na tafi
babu albarkan ta,"
"Zanyi sallah" na fada mishi, Ba musu ya bani gurin na cigaba da sallah ina kallona.
'dama haka take da sani akan ibada? Dubi yadda take bawa kowani abu hakkin shi' ya shiga zancen zuci yana kallon Fareedah. Ina idarwa n
a fara addu'o'in, har na gama. Na tashi zan saka kaya nace mishi.
"Don Allah zan saka kaya"
"Ki saka abinci babu wani abu, fatana ki amince min da abinda nake bukata, please"
"Kai da kake da Halimah"
Ganin zai b'ata min lokaci na shiga ban da
ki na saka kayana na fito, tare muka fito dashi. Ya wuce dani gurin cin abincin, baki daya naki sakewa naci.
"Please kici wani abu"
Dauke kai nayi sannan na fara cin abincin, kamar zanyi kuka.
"Hmm! Nasan nayi laifi gashi nan na zo baki hakuri"
"Kasan me? Ni ba zan maka aikin ba, sabida abu daya ya zauna da ni a jikin Umma shine takardan sakin da zaka.."
"Fareedah! Kinga halin da take ciki,.idan na sake ki wallahi tsine min albarka zata yi, don Allah ki taimaka min mana"
"Raees!
Nifa karuwa ce!" Hannun shi naji a saman nawa, yana kallon cikin idanuna.
"I know! Amma haka na yana nufin cewa ba zaki taimaka min bane, kowani mutum yana da nashi kaddaran gashi nazo gurinki niman taimako! Please"
"Ba zan taimaka maka ba, kawai
ka sake ni" na fada tare da mik'ewa.
Abinda ya faru kuwa kwanakin Salim da Khadijah suna bashi shawara. Akan ya samu Fareedah su shirya, koda baya so haka zai saka umma ta sauko mishi,wallahi tunda taki amsar gaisuwar shi ko barci baya yi, sai ya
ki amsar shawaran su. Idan ya shiga dakin sai yaga yadda sauran yan uwan shi, suke nan-nan da Fareedah haka Umma take nan-nan da su, da ya kira Nuhu ya gaya mishi, yace kar ya dame shi, yayi duk abinda yayi mishi, dakyar dai ya samo kan Nuhu, ya kara hadin
kai tare da kwarin gwiwa.
Shine yake bin Aishafareeda a kan ta amince su shirya da shi yadda Umma zata yafe mishi.
... Biyan kudin yayi tare da biyo bayana.
"Nasan nayi kuskuren, amma na Kuma baki hakuri."
"Ka addabi rayuwata! Ka gal
labe ni, ka takura min yadda ban tab'a jin ko ganin takura irin naka ba, Ahmad Ni fa sake ni zaka yi"
Riko hannuna yayi duka biyu ya daura a kirjin shi. Wani irin yarrr naji a jikina ba iya ni ba hatta shi sai da yaji haka,kallon shi nayi tare da dauke ka
i na kwace hannuna daga kirjin shi.
"Ki min uzuri, idan na samu ta yafe min zan duba haka, amma yanxun ki bani ha
ɗ
in kai mana"
Sake riko hannuna yayi na kwace hannu nayi tare,juyawa na tari motar na shiga shima kuma ya bini.
Zama yayi kamar z
ai shige jikina, na matsa ya kuma matsowa.
"Raees! Ina ganin mutuncinka karka min abinda xan kai karan ka gurin Umma" da mugun sauri ya matsa. Yana kallon wayar shi tana haske. Dauka yayi tare a cewa.
"Yallabai! Kayi hakuri Mahaifiyata har yanzun bata ji
n dadi amma da sauki, kuma ina son dawowa amma mun sami matsala da mai d'akina, idan na daidaita tsakanin mu Insha Allah zan dawo"
Murmushi yayi yana shafa kanshi idan an gaya mishi magana me dad'i.
*
"Wai ina Fareedah ne? Ina Aishafareeda ne?"
Inji Umma tana jiro musu tambayoyin rashin ganinta.
"Umma ai sun Fita da Ya Ahmad cin abinci" tsuke fuska tayi, sannan tace musu.
"Kan me? Akan wani hujja zai fita da ita?"
"Umma matar shi"
"Ni zaka gayawa matar shi ce?"
"Allah ya huci zuciyar ki
"
Fa
ɗ
a take kamar zata dake su, kuma dama sun shirya haka, da zaran ta nemi Fareedah zasu sun fita da Ahmad ko haka zai saka ta farin ciki. Sai suka ga akasin haka.
"Assalamu alaikum!" Kura min ido tayi, sanan ta sake min murmushi. Tana mika
min hannun. A hankali ta taka tare da isa gurinta.
"Kina da daraja, akan me zaki yi watsi dashi? Kin manta cewa yayi matar shi yake so? Ko kin manta a kan idanun ki yace shi ya aure ki ne dan ya yi biyayya? Anya kin tuna lokacin da kika rike hannuna domin
ki boye hawayen da yake shirin sauka a idanunki sabida kiranki matar shi tayi karuwa? Idan kin manta toh zan tuna miki har abada ba zai daina zubda kwalla akan abin da Ahmad"
"Na yafe mishi" na fada mata tare da sunkuyar da kaina kasa, a hankali na zube
gwiwa ta, a kasa. Wani irin kukan bakin ciki nake yi tare da rike hannun ta.
"Muna yiwa Allah laifi ya yafe mana, akan me shi yayi kuskuren ba zamu yafe Mishi ba? Umma wallahi ban tab'a rike shi a raina ba, don Allah ki yafe mishi ki amshi gaisuwar shi,ya
nzun haka niman shi ake yi a gurin aiki, ya watsar da Amanar kasa ya tawo domin ke, Umma kiyi hakuri! Idan har y'ace kika dauke ni"
Tun haduwa na da Ahmad nake kuka,tun haduwa na dashi nake jin b'acin rai, yau ina nima mishi yafiya ne sabida irin rokon
da yayi min, akan na shiga tsakanin su da Umma.
Amma Billahi azim sai na rama abinda yayi min,