Showing 18001 words to 21000 words out of 170719 words
/>
"Kayi hakuri Dr Bagauda, wallahi nima saka ni aka yi amma yanzun haka zan
tafi na dauko yarinyar."
Mikewa yayi tare da saka hannun shi a aljuhun wandon shi, yana fa
ɗ
in.
"Aikin dan sanda ba iya kare shuwagabannin bane, aikinshi domin ya kare rayukan al'umma ne, sannan idan aka duba yanayin yarinyar tayi kankantar da fuskarta wa
nnan yanayin, don Allah a daina bin muradin yan siyasa, basu ne suka baki damar da kike kai ba Allah ne ya baki sai ki gode Mishi ta hanyar kyautata alaƙar ki da kowa."
Sara Mishi tayi sannan tace mishi.
"Zan kiyayye yallabai, Nagode ina sanye da k
ayan dan sanda ne saboda kai ba dan kai ba da na zama babu amma ka nima min aiki ka bani ka bani kome zan kiyayye abinda zai saka ka kuma dawo dani nan din nan"
Sannan ya nuna mata hanya, ta fita.
Jingina yayi da jikin tagar shi, yana kallon tashin mot
ar mataimakiyar Kwamishina yan sanda. Bai da wani kazamin buri akan al'umma, kuma bai tab'a jin ya zalinci kowa ba, dan ko da PA ya gaya mishi abinda ya faru ya sha mamaki, dan haka yayi fatar su kyale yarinyar da bata san kome ba. Yana fatan haka ya zama
izina a gare su.
***
A hankali nake tafiya rataye da jakar makaranta na, duk inda na wuce ni ake nunawa kamar nayi wani abu, ban kula su ba, na isa gida na samu Kawu Sha'aban da Hajiya hankalin su a tashe, d'akina na wuce, tare da ajiye jakar. Sa
nnan na cire kayana na sauya, kafin na fito.
"Lafiya suka kai ki ofishin jami'ayyar PLP?" Kawu Sha'aban ya tambaye ni, Baba Sallau yana gefe, ga Gwaggo karima. Zama nayi kafin na kura mishi ido.
"Lafiyar kenan,." Sannan na dauki madaran Hajiya na fara
sha.
"Aishafareeda kin san inda kika je?" D'ago kai nayi tare da kallon Baba Sallau da yayi min tambayar murmushi nayi sannan nace mishi.
"Baba ban cika son tambaya ba."
"Kyaleta karku d'aga mata hankali" inji Hajiya, haka na gama tare da cewa.
"Kawu
Sha'aban, idan kaje ka gaida su Hajja da kawu Aashir, sannan ka basu wannan sakon zasu baka sako kawo min, Nagode kace musu ina kewar su, sannan bai zama dole abinda idanun mu ya gani zuciyar mu ta zama alkalin ta
ba, kowani dan adam yana nashi mulkin kans
hi, dan haka iya adadin nisar tafiyar bai kai wanda zai zama abin yayatawa ba"
Sannan na shige dakina, kafin ya kalli hajiya.
"Insha Allah ba zaki tab'a samu na a cikin mutane masu kai wa da komowa ba, na miki alƙawarin haka."
Sannan yayi musu
sallama, ya fita.
--
Ina kwance naji Hajiya na salati, da sauri na fito.
"Lafiya?"
"Wai an Sara suka sun kaiwa makarantar ku shara, sannan sun fitar da Umar suna gana mishi azaba" gyada kai nayi tare da jin wani irin abu yana hawa kaina, dakin na shiga
na cire doguwar rigar jikina, na saka riga da wando, sannan na daura After dress akan shi da mayafi na fita bayan na saka boot, na fita.
"Don Allah Karku barta ta fita."
Kafin wani ya rike Ni na fita ina zan kulata, da gudu nake ratsa unguwar makarant
ar mu. A bakin get na tsaya bayan na shiga . Yana kwance a filin makarantar, numfashi nake saukewa tare da nufar cikin makarantar, zuciyana yana tafasa. Ina zuwa na d'ago shi ina kallon su, suka taso.
"Ke yar iska ke muke nima," taka dutse nayi tare da mu
rza shi.
Kafin na durkusa cikin zafin nama na saita gwiwar shi na hagu, na kai mishi wani.irin jifa sai da ya fadi.
Cikin sauri Umar yake miko min dutse ina fashe musu kai. Sai gashi da iya duwatsu na Kore su a cikin makarantar. Da sauri shugaban mak
arantar yazo tare da cewa.
"Mun gode! Ba dan ke ba, bamu san me zasu mishi ba, mun gode." A hankali na kamo hannun shi, na zaunar dashi. Kafin na nufi ajin su na dauko jakar shi zan fita, wani yaro yace min.
"Yar daba kawai" juyawa nayi na kifa mishi mar
i! Sai da ajin ya amsa.
"Kul ka kirani da sunan nan?" Bai iya magana ba, sai bayan na fita wani a cikin ajin yace mishi.
"Deen hancinka yana jini" shafawa yai tare da kallon yadda na riko hannun Umar.
"Shegiyar yarinya wallahi zaka dauka ko kera mata ha
nnun aka yi kamar ba na mace ba"
Muna fitowa Hajiya suna isowa da mai kawo mu, saka shi nayi muka nufi asibitin. Anan aka mishi duk abinda zasu iya mishi suka sallame mu zuwa gida.
**
Hajiya fada tai min bayan ta gama ta buge da rarrashina, tun dag
a ranar muka sami hutu da matsalar yan iska a unguwar mu. Sai dai karfi da yaji ana niman manna min hauka a cikin unguwar mu, ba dan kome ba sai dan yadda suka zuba min ido. Kowa da abinda yake fada a kaina da na Alkhairi da na sharri.
Irin haka ya fada k
unnen Hajiya bata wani damu ba, musamman da ake yawan yabon Aishafareeda, sai dai haka ya tab'a rayuwar yarinyar sabida yadda ake yawan magana akan kyanta da kuma karfin halinta.
***
A cikin wannan yanayin zab'e ya karato, aka fara zazzabar kamfen,
abinda ya tab'a rayuwar al'umma kenan, a cikin su har dani domin ina kaunar naga an fita rally, har kin zuwa makarantar nake, na fara bin madam Ruth, idan zan tafi makarantar sai na wuce gidanta.
Koda aka ganni aka gayawa Hajiya bata Zafaffa ba, ita
babban damuwar ta, kar na zubda mutuncina da kuma darajata, sai karatuna. Domin lokacin da ta sami labarin ta min fa
ɗ
a kuka na saka tare da cewa.
"Idan Abbana yana raye ba zai takura min ba amma ke duk abinda aka dauko aka gaya miki dauka kike, shi kenan
zan koma chad" jin haka yasa ta shiga rarrashina tare da gaya min wanda ya kawo gulmar, ni kuwa nace ya gama zaman gidan haya a gidan baki daya.
"Ayya Sharubutun mai turaren, ayi haka? Koyi hakuri a barshi Insha Allah ba zan Kuma ba, na miki alƙawar
in bani kuma
ɗ
aukar maganar wani." Ta fada min, a hankali naga yana share kwalla tare da rike hannuna.
"Wallahi ba zan hanaki abinda kike so ba" kwalla suka ci-gaba da zuba a idanun ta.
"Kinsan ke mace ce, kuma duk abinda zaki yi karki rasa mutuncin k
i, idan kika min haka wallahi wallahi kin gama min kome, ba zan kuma
ɗ
aukar maganar mutane ba, amma ki kammala karatun ki sai kiyi duk abinda zaki yi"
Ta bani tausayi domin nasan da iyayena suna raye ba zasu Barta tayi kuka haka ba. Gashi Ni karama d
ani na sata kuka.
"Hajiyana Insha Allah, ba zan tab'a zubda darajar gidan nan ba."
Tun daga ranar rashin mutunci ya kafu a gidan mu, tare da dokoki kala kala, ba a kunna radio idan ina barci, ba a wasa ko hayaniya, haka yasa wasu zagina tare d
a gulmata.
Akwai wata mata da suke haya, mai sunan Sugura, matar bata da mutunci, haka ta ishe mu ita da Yaranta Yan mata. Sai na dawo daga yawo na zasu kama min habaici. Ban cika kula su ba, domin ina jin hajiyayye tana musu magana da uwar Yaran.
"Wallahi Maman Jamilah ki daina abinda kike aikatawa, gidan nan da kike zaune kakar Yarinyar nan ne take dashi, idan wani abu yarinyar ta miki sai ki gayawa kakar balle kuma ita kanta Yarinyar bata da matsala matukar ka fahimci halinta, ba ki zauna ki
ta zaginta da mata habaici ba, kina da yara mata uku Jamila ta girme ta, Nana sa'arta ga kuma Zakiya, itama basu wuce kai
ɗ
aya ba.
Idan kika sake Hajiya Turai taji ranki zai b'aci, wallahi kuma ai uwa ta gari bata da bakin zagin dan wani"
"To
h a karanbana, Uwar Muminai na gidan Hajiya Turai, ban da son zuciya ya kina da budurwa a gabanki Na'ilah, kuma nema kin san yarinyar nan ko da iya kyanta aka bar su, babu mashin shin da zai zo gurin yaran mu, shegiyar yarinyar
sai kace aljana ko wani irin
kwalliya tayi sai ya karbe ta, Insha Allah a yawon ta zubar zata kare rayuwar ta. Abin kunya kuwa idan da nisan kwana sai ta ajiyewa Hajiya shi"
Ta fada tare da buga hannunta, idan na saka aka kore ta, ban burge ba. Amma idan na barta ta zauna taga
yadda Ubangiji yake ikon shi yafi sauki. Dan haka nayi kamar ban ji ba, daga Chad ana min aika kuma ina kaiwa Makarantar mu, Mama ma tana sayarwa,
Lokacin da Umar ya gama karatun shi, Hajiya ta shiga niman Kawu Sha'aban shi ya yi mish
i kome aka tura shi, Sudan.
Dama sabida takurani da yake yi ne da magana yasa bana son fito da halina, yana barin kasar. Na yanke zuwa makaranta, hatta sana'ar sayar da turaren a yawon bangan siyasa na ke yin shi. Gani yarinya me karamin shekaru, am
ma wallahi ko barkono ya sallama mini, kuma haka ya kara min daraja a gurin Madam Ruth.
Ita da kanta ta kaini Office din Alhaji Sani Musa, shugaban jam'iyyar PLP, ya kare min kallo sannan ya ce ta fita. Tana fita ya dawo gabana ya zauna.
"Maraba d
a zuwa sashen mu, lokacin da nasaka aka kawo ki baki ce kome ba, gashi nan kin kuma dawowa nan."
Mikewa nayi tare da cewa.
"Kai baka da matsala ne? Dan haka sai an jima" na juya tare da barin shi a tsaye, zuciyar shi cike da farin cikin. Abinda ya
ke dako ya zo har gidan shi, nasarar shi zata bayyana.
*
Ahmad Bala Raees.
"Kai ABR! Kasan wannan karon siyasar garin nan zata yi zafi? Domin kuwa bayan shekaru goma sha shida wannan karon kowani
ɓ
angare zasu bada wuta."
"Allah ya taimaka!"
Ya Cigaba da lissafin shi,
"Kai fa baka da mutunci;"
"Haka kuke manne dani"
"Dan iska kawai"
"Kaho ne a kaina"
"Banza Bakwai"
"Nagode shima arziki ne"
Ya zuba kudin shi a aljuhun wandon shi, sallamar Zakaria yasa su amsawa. Zama yayi ranshi a dagule
.
"Toh lafiya?"
"Babu kome" ya sauke ajiyar zuciya,
"Ko Matarka ta haihu ne?"
"Eh wallahi"
Daga haka basu kuma cewa kome ba, sai Ahmad ne ya mike tare da shiga ta kofar Umma, ko kafin ya dawo Zakaria ya tafi.
"Assalamu alaikum! Umma Sannun da huta
wa, don Allah auna min gero mudu goma, da masara mudu Ashirin shinkafa.sha biyu, sannan zan dauki wancan ragonki Insha Allah sai ki hada min kudin su, an jima zan shiga Barka gidan Zakaria "
"Toh babu damuwa" ta kira Khadijah, ta auna kome, sannan suka a
jiye mishi. Koda ya fita ya samu baya nan.
"Ina Zakaria?"
"Yanzun yaro yazo kiran shi."
Bai zauna ba ya nufi gidan Zakaria ba iya shi ba, har da su Nuhu da Adamu, suna zuwa suka samu ana fito da matar shi za a kaita asibiti, zuwa gurin shi Ahmad yayi
tare da riko hannun shi, ya cusa mishi abu a cikin hannun.
"Idan ana bukatar wani abu ka min magana, kamar yadda muke lokacin muna makaranta, ka min magana kamar haka, nauyin ka nauyi na ne, karka damu da cewa Ni din daban ne dukkan mu daya ne"
Ajiyar
zuciya ya sauke tare da cewa.
"Kai kamar waliyi ne! Kuma kamar Uba kake min nagode sosai"
"Kuje Allah ya bata lafiya" haka suka bar gurin bayan motar ya tashi, koda suka koma, shiga cikin gidan Ahmad yayi tare da dauko kayan abincin ya kai musu har da ra
gon, yayi sallama matar Zakaria ta fito ya bata har da kudin cefane, godiya tayi ta mishi, barin kofar gidan yayi.
Koda ya dawo shagon shi, ya samu ana ta hiran Zakaria.
"A lokacin da muke hana shi kara aure ai bai yarda ba, yanzun don Allah meye
amfanin haka? Ka tara iyali amma ba zaka iya sauke musu nauyin su ba, haba don Allah mata uku...
Mai_Dambu
#PaidBook
#Freepage
300
₿
katin mtn ko shaida ta wannan Numbers
👇🏽
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank! +2347035133148 or 08130269641
*Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza
garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na ama
re da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya ta
ɓ
a Ni ta wannan Number:08130269641 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza -
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina
ya rikice
Zazzogau
Ha
ɗ
in gigita shi
Maƙale mata
8/24/21, 8:26 PM - Buhainat
😝
: https://www.wattpad.com/1118720695?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=wo4D5qpkmJsA214
Z469a6z6IiCB%2FpXTp47ivt2phjUEr8TZvaoetVy248dKP8EEwnXWTD2S9T%2B2AATJjeGLKX6DtNdg6goMx55LuHJWY1xykQpWUTeMIDFYbeVgYOquF
HAKKIN MALLAKATA
#SaturAug-2021
KISHI..!!
~_A Tsakanin Zubda Jini
🩸
_~
Mai_Dambu
*Sadaukarwa ga Halimatu kangiwa (haliloss). Mr
s J Moon. A'isha Fareedah Ya'u Nusaiba Sulaiman Ayuba jikalle na*
*10*
"Gani yake a lokacin bamu da hankali, sannan bamu san me muke ba, kullum shine mai lafiyar da zai kwanta da mace sau uku zuwa hudu a dare guda, shi wannan al'amarin ba
haka yake ba, idan har kana da macen da kake so! Kana kaunarta toh dole ka bukace ta, musamman kayi dace da wacce zata iya daukar nauyin ka, ta kuma san darajar ka, toh ba makawa zaka iya biyar da ita sau bakwai ma a dare guda, ba wai dan kawai kana samun
yan canji zaka dauko mata ka aura ba, ai abinda ya kashe na gidan shi zai kashe wacce zaka aura, shi yasa nake tattalin iyalina" inji Adamu.
"Amma ku munafukai ne? Duk cikinku babu wanda ya tab'a zaunar da Zakaria ya gaya mishi gaskiya abinda yake faru
wa da shi ba, amma kun zauna kuna gulmar shi, wallahi yayi kokari da ya tara mata, kuma yake zaune lafiya dasu, kuma wallahi da yana da Wadata babu wanda ya isa yayi gulmar shi, ku daina haka haramun ne, zaman tare ya wuce haka, duk inda zaka zauna da muta
ne ka zauna dasu da gaskiya da amana."
Kamar wanda ruwa yayi musu duka haka suka sunkuyar da kai, sannan ya Cigaba da abinda yake domin shi dai bai da matsala dasu. Wata yarinya ce tazo ta wuce da wasu irin kananun kaya, zunzurutun ya matse ta, har k
ana iya hango mazauninta, kiran sunan Allah yake, kafin yaji ina ba zai iya zama ba, kawai ya nufi gidan shi, dariya suka saka mishi.
"Za'a tafi ban ruwa ne" banza yayi dasu ya shige a hankali bai damu da dariyar shu'umancin da suke mishi ba, shi baya cik
in jerin mutanen da suke da mugun bukata, amma idan da zai ga koda sumbata ce, a Film take jinin shi yake harbawa, balle kuma taga mace ta wuce ta gaban shi, da guda yake barin shafin shi.
Yana shiga ya samu Ishrat ta fito da wanki tana yi, sai lokacin ya
tuna da ashe sun yi fa
ɗ
a kafin ya fita. Kuma idan suka samu irin wannan sab'ani hana shi hakkin shi take, dan haka yana shiga bai tsaya rokonta ba, daukarta yayi suka wuce cikin falo, zata mishi tijara, ya had'e bakin su guri guda, kafin ya shiga aika mat
a da makaman nukiliyar shi.. Kafin kace me, tayi laushi jikin shi yana rawa ya rufe kofar falon, ya dawo sannan ya shiga shafeta. Tare da tsutseta, duk ta cika mishi kune da Moaning, a hankali ya zauna bayan ya d'agota ya direta a saman raees din shi, ciki
n wani irin kara ta sake ajiyar zuciya, shima kuma haka, tare da rungumar ta, yana jin saukar Ni'imarta, a saman raees din shi, wayyo a zauce yake binta kamar zai cinye ta danye, bai samu kanshi ba, sai da yayi bayin shi son ranshi, kuma ya lura da ita ida
n ba irin wannan abun ya mata ba, sai ya gama bata kawo kai ba. Matsa kirjinta yayi yana kallon ta, yadda take sauke numfashin ta.
"Tashi muyi wanka"
Haka ya d'ago ta, sannan ya nufi hanyar ban daki da ita.
***
"Tabbas akwai abubuwa masu tsada a cik
in wannan yanayin, mafi alkhairi da girman shi, ka mallaki abinda ya zartas su. Karka sake ayi zaben nan baka makamar iko, ka zartas su iko da fadar aji. Dole sai ka mallaki shafukan da babu rubutu a cikin su, dama na gaya maka zaka dawo, toh wannan shine
tafiyar farko da wancan da wannan sune karfin ka, karka yarda wani ya tsaya maka ba tare da ka samu wadannan taurari biyun ba.
Saura wata guda, kuma al'amari ne kara rincabewa, dan haka kayi maza ka samo min yadda za ayi."
"Toh sai"
"Tashi ka ta
fi, a fara niman Almajirai makafi maza bakwai mata bakwai, a binne su bayan an musu yankan rago, a nimo min budurwan karya, sannan a kawo min matashin zaki a kawo min shi nan akwai aikin da zan yi dashi"
Gyada kai yayi sannan ya mike tare da ajiye jakar
kudin ya fita abin shi.
**
Cikin lokaci