Showing 159001 words to 162000 words out of 170719 words

Chapter 54 - KISHI COMPLETE

30 Sep 2026

1167

da hankali akan karatu, sai gashi idan abin ya fito a Office din ake kashe muraba, suna tura yaran su.

       Abun mamaki take yasa aka yi wuf da mutanen da suke da hannun abin haushi koda aka shiga kotu a take aka wanke su saboda

rashin hujjojin da za a gabatar a gaban Alkali shi kuma ya wanke su, tare da nuna musu basu da laifi.

Rai a b'ace ya shigo min tare da cillar da wayar shi. Ina rungume da Zaheer, sai huci yake, dan haka na dauko mishi ruwa ina kallon shi ya sha kadan ya

ajiye, kasa magana nayi ina kallon. Domin nasan abinda ya faru, kuma na ji labarin.

         "Toh meye na wani jin babu dad'i? Naga dai ai ba wani abu bane Allah na tuba, kuma ai gwara da aka watsar da shara'ar domin idan ka dage allura zata tono garma

"

"Me yasa kika ce haka?"

Ya tambaye ni, share shi nayi tare da cewa.

"Yana da kyau mutum ya san abinda zai yi kafin ya yanke hukuncin mai bi abin zai zo maka da sauki"

     "Taya? Taya zan yi yazo min da sauki" a hankali na kwantar da yaron nace m

ishi.

"Sai ka zuba ido, wasu abubuwan ana kyale su ne sabida siyasa, ba wai dan an fi karfin abu ba ko dan Alfarmar da wani ya nima."

    Daga haka na barshi a gurin, ban ce mishi kala ba, dakin shi ya shiga ya janyo kayan shi ya fara bincike abinda ya

ke Nima.

Dawowa yayi ya kunna Laptop din shi, dan haka ya shiga bincike.

   *Barka dai sir ga wani abu na Turo maka ko zaka duba*

Shiru yayi yana kallon PDF din da aka turo mishi, a hankali ya bude ya fara kokarin dubawa aka kira shi dauka yayi tare

da cewa.

"Eh! Ok"

   Mik'ewa yayi Tare Da kashe Laptop din, ya bar dakin. Kan sakon da bai kuma bi ba kenan,  Ni ina can ina tattara mishi duk wani bayani da abubuwan da yake bukata mutumin nan yana nan yana baza ikon shi. Wata na shida na gama hutun

da nake, dan haka na koma bakin aikin da nake.

.....

Muka shiga taimakawa mata da matasa, tare da bude wasu giduniyyar tallafawa al'umma, sai da ta kai nayi matukar Busy bani da lokacin kaina sai na mutane, Yarana bani da lokacin su.  Ban tab'a sanin h

aka hidimar al'umma yake ba sai Yanzun.

  Kuma Alhamdulillahi domin na dauka da muhimmanci, kafin shekara daya mun fara daidaita al'amuran rayuwar talakawan mu,.kuma duk da haka yan adawa suna sukar gwamnatin mu.

     Ranar da aka yi bikin cika sheka

ra daya da hawa mulkin mu, ranar aka fara fuskarta matsala da ba a fatan haka ta kuma faruwa.

    Domin dai Ahmad yayi kokarin talaka ya more roman domakaradiyya, amma abin takaici da bakin ciki sai gashi sun  tura mishi katin gayyata, da dare ya shirya

zai tafi, dan haka ya nime nazo na taimaka mishi ya shirya ni kuma dana fishi rashin arziki ina zuwa na shiga ban daki na had'a mishi ruwan wanka, riko ni na b'ata rai ina fa

ɗ

in.

  "Sake ni zan dawo zan cire maka kayan ka ne"

     Fita nayi tare da

barin shi ya gama abinda zai yi, sannan na dawo na cire mishi kayan da zai saka hatta turare sai da na ajiye mishi  na koma ban dakin muka yi wankan tare, sannan muka fito tare, bayan mun fito na taimaka mishi ya saka kayan, sannna ya tafi.

           H

ar ya fita sai gashi ya dawo.

"Don Allah ki duba yaran nan jiya Naeem ya kawo min kar'ar baƙi duba su ba, so please a duba su."

         Haka aka yi yana fita na shiga dakin su, muka fara hira da su, muna tab'awa da Umma, sai matar Salim naja'atu da ta

zo gaida Umma. Dake yanzun Umma bata gidan su, shi yasa bata sati biyu bata zo ba, kuma kunsan halin dan Adam, shi yasa ban cika damuwa da ita ba, yaranta dasu Naeem suke wasa.

Mijinta ma yanzun bai cika zama ba, idan yana gari toh yana tare da dan uwan

shi, idan baya gari. Matar zata zo.

            Tashi nayi na koma dakina sannan na shiga binciken Abinda Ya dace har muka shiga tattaunawa da Mr Jonathan dasu Baba Tanimu, nan muka nutsu sosai ina tura musu wasu bayanai na musamman da nake samu a loka

cin, sannan na gaya musu su tattara duk abinda yake akwai zamu fara yakar Bagauda.

    Kuma naji dadin da suka bani goyan bayan sannan suka nuna min lallai na tsaya a bayan Ahmad, domin anytime kome zai iya faruwa.

   Na amince kuma na yarda, dan hak

a bai shigo gidan ba sai tsakiyar dare, kamar wanda aka mishi duka haka ya shigo, har d'akina ya shigo ya same ni kan abin Sallah, a hankali ya fita daga dakin.

   Zan iya cewa tun daga ranar ban kuma gane kanshi ba, sai dai bai fasa abinda yake ba, kum

a bai gaya min meke damun shi ba, asalima sai cewa yake.

"Ku sani a sujadar ku."

  Umma ya kalle shi sannan tace mishi.

"Wannan ba sai ka tuna min ba ina gayawa Allah kullum damuwarku."

        Ban amsa mishi ba, sai da na shiga daki ina gyara d'ak

ina ya shigo tare da kallona.

"Meye kika sani akan siyasa?"

"Abinda na sani dayawa, ana iya sayo ka a baka damar zama za

ɓ

a

ɓɓ

en gwamnati amma ba zaka iya kome sai abinda ka zab'a maka."

        "Ina cikin bala'i;"

"Baka cikin bala'i, domin kuwa ida

n kana cikin bala'i baka isa zama ka fada ba, idan talakawan ka ne a cikin masifa zaka iya shiga amma idan ba su bane babu abinda zai dame ka"

     Kura min ido yayi sannan yace min.

" Ba zaki gane ba, idan kin san halin da nake ciki ba zaki fahimta ba

, kawai kina kallona ne amma Tabbas ina cikin tashin hankalin da damuwa, na rasa yadda zan yi da rayuwata, talakawa nake dubawa"

"Eh toh Allah ya kyauta" na fada mishi ina kallon shi, daga haka bai kuma ce min ba, sai dai yadda ya shigo da nashi kudirin

ne ban juya mishi baya ba, na amshi tayin shi kuma mun gurje juna tare da kallon yadda nayi laushi.

"Yau kam kece zaki taimaka min na muyi wanka bani da karfin jiki" haka na nufi ban daki na had'a ruwanka, fito ya shiga muka yi a tare, sannan muka fito.

      Suma sun san cewa bai basu amsa ba, kuma bai musu magana ba, sai ma kara tunzira shi da suna fara ta hanyar amfani da wasu matasa suna fita sara suka, kamar da wasa aka maida kwace waya a cikin garin mafi muni a kasa da sati daya, ana ƙoƙarin tatt

aunawa da jami'an tsaron akan wannan lamarin domin dab abu kadan ya samu talakawa basu da inda zasu kai kuka sai ga gwamnati. Dan haka aka saka hukumar yan sintiri a cikin gari suna yawo.

   Sai da aka fara kokarin magance wannan matsalar kawai aka fito

da wani mugun abu, na haka kawai idan ka shiga keke napep za a yanke ka, idan kayi nisan kwana toh idan ba kayi nisan kwana ba shikenan. Nan ma talakawa suka yi caaa, a hankali rashin tsaro ya fara kokarin zama abu mafi illa. Cikin Garin.

Ana cikin wan

nan yanayin kawai aka fara kaiwa manoma, hari, mutanen kauyinka lokaci guda aka tashe kauyi biyar, wannan abin ya tab'a Ahmad, domin sai da ya kwanta zazza

ɓ

i.

Ya rasa yadda zai yi, lokacin da aka tura jami'an tsaron sun dawo akan kafar su, tare da bada

labarin ba zasu iya zuwa ba, domin yan ta'addan suna da manyan rokoki, haka ba karamin d'aga hankalin mutane yayi ba, dan haka ya zauna da duk masu ruwa da tsaki a harkan tsaro, amma babu mafita, dan haka ga na cikin gari ga na kauyika, dole hankalin shi y

a kasu gida biyu.

   Ya mai da hankalin shi sosai kan tsaro, abin takaici sai gashi ko wata biyu ba ayi ba, harkan tsaron ya kara tabarbarewa, har an fara zagin gwamnatin shi, a lokacin ne na kuma tura mishi sakon amma bai duba ba, asalima sai dauke kai

yayi akan abin.

Kamar yadda suka bukata haka ya fara kokarin mai da musu ragamar shugabancin shi a hannun su, kuma lokacin rayuwar talaka ta kuma lalacewa, dan haka babu ta inda talaka zai huta.

      **

"Sir da alamun zai mika musu mulkin su cigab

a da juya talaka babu abinda ya isa yayi!"

  Buga kallon golf din Mr Jonathan yayi tare da cewa.

"Shi yasa muka bukace ki anan, dole salon su zamu koya, domin kare rayuwar talaka, dole zamu shiga cikin su, gashi ki duba abinda yake rubuce anan"

   

Kowani

ɓ

angare na samu har da inda ban tab'a sanin ba.

"Sir taya zamu yi haka?"

   "Idan suka tab'a talaka zamu saka ido muga me gwamnatin zata ce, idan kuma suka tab'a gwamnatin zamu tab'a su daidai price din su."

"Toh meye makomar talakawa?" Na ta

mbaya,

"Basu da alkibla, kome aka musu basu da hakuri, mu fara kare gwamnatin kafin mu shigar da kome"

    **

Damuwa tayi mishi yawa dan haka abinda ya fara ya nufi gidan Kuli.

Inda bayan sun gaisa yace mishi.

"Yallabai a shekarun baya, ka tab'a min

magana akan shigana siyasa, yallabai me ka sani akan siyasar garin? Na rasa inda zan dafa"

     Murmushi yayi sannan yace mishi.

"Baka san kome da kake sune suka bukaci haka ba? Ai duk abinda zaka yi ko zaka tsaya, kome zaka yi, kana under control

ɗ

in

sune, kuma koda baka tsaya musu ba, zasu iya kawar da kai, dan haka ka rufe idanunka kai musu gyaran ban mamaki, idan ta kama domin talaka a kashe rai zaka iya, amma kafin nan ka samu ma'aikata na musamman da suka kware gurin aikin sirri su maka wani aiki

. Su fara binciko..

🤷🏽

‍♀

️

Kishi a tsakanin zubda jini isn't free, if you need chat me.

0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank!

+2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76

9/18/21, 2:32 PM - Buhainat

😝

:

*##*

"Wa

ɗ

anda zasu iya maka aiki babu wanda zai sani, batun rashin tsaron gari kuma, ka saka dokar duk wanda aka kama a harbe shi, babu maganar tausayawa sannan ka saka doka da oda a cikin garin, ka rufe idanun ka, ka yake su da karfin tsiya. Karka sake

ka bari a gano lakarka, idan da hali ka koyi makirci irin na siyasa.

   Amma dole sai ka koyi karya da yaudara domin baka san su ba, shi yasa haka ta faru. Da ka iya kuma ba zaka tab'a fadawa wannan yanayin ba. And kayi ƙoƙarin gano su waye keda nasaba

da abubuwan da suke faruwa."

     "Nagode sosai"

Yana zuwa gida ya fara nazarin abinda suka tattauna a kai, washi gari ya tara jami'an tsaron ya saka musu dokar duk wanda aka kama shi da wani abu makami ko wani a kashe shi a gurin.  Sannan ya saka a

ka kirkiro wata kungiyar tsaro na musamman, tare da basu kariya na hakika, sannan aka basu kayan aiki.

           Yadda a cikin kankanin lokaci suka hautsina hankalin b'ata gari, ana cikin haka yan adawa suka fito tare da cewa ana kashe talakawa, ba abi

takan su ba.

    ***

"Me Raees yake nufi? Mu da muka ce ya koma gefe ya barmu muyi abinda muke so"

       "Eh mana! Taya zai bamu guri ana taimaka mishi ta kowani fuska, abinda zamu yi mu fara mishi barazana da iyalin shi." Inji professor Ibrahim C

hindo.

      Dan haka suka had'a yadda zasu razana Ahmad,  kamar da wasa kawai.

      Suka sako Ahmad a gaba, shi kuma yayi kunnenn uwar shegu dasu, lokacin da suka gaya mishi ai akwai mutanen shi da suke gefe baya da kawazuci ne akan su? Anan ne ya

dan dakatar da abinda yake, bai ce musu kome ba.

Duk yadda Ahmad yaso tattara wasu abubuwan munafikai sun tare gaba sun tare baya, kuma sun hana shi yayi magana ko wani abu.

       Sabida dangin shi ya sashi komawa gefe, ya kasa cewa kome, ana lima C

igaba da cin Uban talakawa, gefe suma suna tsine mishi kamar me.

  Lokacin da muka samu bayanin abinda suka mishi.

A lokacin ne muka so mu taimaka mishi Baba Sani yace mana.

"Kuna tab'a wani daga cikin su, zasu farmaki talaka ko Ahmad, ki nutsu haka b

a zai tab'a yiwa ba, ai ya riga da ya shiga game din  sai yabiya abinda ya ci, ta hanyar da baki zata ba. Sannan akwai na jikin Ahmad da yake tare dasu, shi yasa suka mishi barazana da zasu iya dira akan shi."

*Halimah*

Kirjina ya buga lokacin da na tu

na da ita da Adamu sune suke ha'intar Ahmad, shiru nayi ina kallon Baba Tanimu.

"Kuma idan har kika yi wani kuskuren yaranki sune zasu biya kudin da baban su ya ci"

   Zaro idanu nayi tare da cewa.

"Kamar Ya? Ban gane ba"

"Nutsu! Idan muka yi wani

abu zasu sauke akan yaranki ne, domin sun fi kusanci da su a yanzun. Ina da yakinin har cikin gidan ku akwai mutanen su, sannan idan ma babu akwai me tattara musu duk wani bayani naku.

          Idan har zamu samu damar toh mu fara kame yan iska, tare d

a fitar da hotunan da labarai muna raye,.hankalin su zai kasu gida biyu, zasu bar Ahmad zasu fara niman mu domin su kashe mu."

Sauke ajiyar zuciya nayi tare da kallon shi, tare da jinjina al'amarin sannan nace mishi.

"Toh ya za ayi kenan"

"Jeki zamu y

i magana"

     **

Dake akwai wani tallafin da muke badawa na lokaci zuwa lokaci, gaskiya wannan karon ban samu damar zuwa gurin ba, sai na tura wakilai. 

   Aikuwa garin bada tallafin ko nace yadda aka shirya abin kawai sai gashi an tashi gurin da

karamar nakiyar fasa dutse.

   Yana Office Halimah ta kira shi.

"Ka kunna tv kaga abinda yake faruwa!"

   "A yau abin tashin hankali da ya faru, a garin nan shine abinda talaka ba zai tab'a Mantawa ba, yadda me dakin gwamna First lady, ta shirya wa

ni taron tallafi na musamman, koda yake wasu majiyar na cewa bata so taron ba, dake ana rade radin gwamnatin ta yan shan jini ce ga dai talakawa a cikin jini na zuba. Wannan abin ya bamu tsoro da tashin hankali.

  Tun hawa gwamantin Ahmad Bala Raees bam

u more kome ba sai bakin ciki, daga wannan..."

Kashe tv aka yi Nuhu yace mishi.

"Fareedah ba zata aikata haka ba, anyi amfani da sawunta ne don Allah.."

"Amma meye ya hanata zuwa gurin? Meye zance ga hukumar kare hakkin dan Adam? Zasu bincike ta."

Daga ko ina ya fara amsar kiran wayar jama'a, a take ya shirya tawaga na musamman, suka tafi Unguwar, sai dai abin bakin ciki yadda talakawa sukayi ta jifar motar gwamna yayi masifar mishi ciwo.

Haka ya koma gida tare da zubawa Fareedah idanu da itama n

ata suke cike da kwalla.

   Dan haka ta mike tare da barin gurin.

Bayan awa ashirin da hudu.

  Sai ga lauyoyi daga abuja, aka turo har da jami'an tsaron. Zasu tafi da ita domin amsa tambayoyin karkashin Hukumar yaki da ta'addanci na duniya, reshe

n Nijeriya.

Hankalin Raees ya tashi lokacin da yaga zata shiga cikin motar su.

"Fareedah! Ki nutsu zan nima miki lauyoyi Insha Allah zan zo"

"Bana bukata, ka kula da Umma da Yarana, don Allah karka sake wani abu da a faru dasu."

   Sannan muka tafi

, dake ta jirgi zamu bi, bamu dauki lokaci ba muka bar garin.

   Hankalin Raees yayi masifar tashi. Duk inda yake da damar yayi magana abin ya faskara, dan dole aka ma daina jin labarin Fareedah domin babu ita babu labarinta.

Har sai da ya had'a da s

hugaban kasa, sannan ya kwantar mishi da hankali, kafin aka gaya mishi inda Fareedah take, sun dauke ta daga Abuja sun kaita Lagos,  hankalin shi a tashe ya nufi Lagos.

   Anan ya ganta lafiya lau.

"Fareedah babu abinda aka miki?"

"Babu Ahmad, sai da

i ina bukatar addu'o'in ku, sannan akwai hujjojin da suke bukata, kuma" kasa gaya mishi nayi na fashe da kuka.

"Ahmad! Yarana, ka bincika sosai akwai hujjojin da suke tare da kai, laifin ba na iya wannan abun bane."

Ina kuka sabida gurin bana cikin tak

uri sai dai sun ki bani damar na kare kaina, ko na kawo musu wasu hujja. Babu abinda yafi basu takaici kamar yadda suka san ina cikin jami'an tsaron da basu sani ba.

     Bayan tafiyar shi.

Aka Cigaba da fitar da sakamakon abinda na aikata, a lokacin d

a suke binciken basu samu wani bayani ba sai dai sun. Fada na musu kutse a cikin ma'aikatan tsaro, ana fitar da labarin aka turo musu bayanai na musamman da yadda aka yi na samu horon.

***

  "Ai na sha gaya maka yarinyar nan ta shiga jikin mu, ashe yar

iska hukumar tsaro ma tayiwa kutse." Inji Qarib yana gayawa Bagauda.

Shigowa Alhaji Wali yayi tare da kunna tv.

     "A yau muka samu labarin Manyan jigoggon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login