Showing 3001 words to 6000 words out of 170719 words

Chapter 2 - KISHI COMPLETE

30 Sep 2026

1142

Umman shi ya dawo da baya yana sosa kanshi.

"Umma tay

a kika sani?"

"Hmm,.jiya kake bawa su Hadiza labarin budurwan ka"

"Umma na zata kina barci ne?"

"Idanuna biyu."

Ta fa

ɗ

a mishi tana Cigaba da aikinta.

"Sai na dawo" "Allah yasa"

Ahmad Bala Raees,

Su din yan asalin garin tira ne dake karamar hukum

ar takansh dake garin, Fulanin Tira ne su. Ahmad yana da kane hudu mata biyu da namiji daya.

Azeema ita take bin bayan shi, sai Salim wanda yake bin Azeema sai Khadijah yar autar su.

Idan ana niman Jarumar Uwa aka samu Umma an gama, domin babu sana'a

r da bata yi ba sabida Ahmad yayi karatun shi. Ta sayar da kosai ta sayar da awara babu sana'ar da bata yi ba har da kasuwan ƙauyuka ta shiga.

Umma Ramlat Allah yayi mata sanyin hali da na kyauta, tana da Alkhairi sosai. Kuma har yau baki daya unguwar s

u babu wanda bai san ta ba. Mutanen unguwar kuka suna matukar mutuntatta.

     Yanzun Ahmad ya gama karatun shi na Psychology.  matsayin master, yana ta faffutikar niman aiki ne amma yanayin kasar mu sai a hankali, duk wannan fadi tashin da yake Umma ce

ta tsaya mishi domin Malam Adamu ya rasu ya barta da yara hu

ɗ

u. Dangin Uban su kuwa ba wani karfi ne dasu ba, Umma ta saka rai akan Yaronta shi yasa tayi ta niman kudi ya tafi har jami'a, da sana'ar kamu da koko.  kuma tana kosai. Khadijah tana sayar da k

ayan koli, salim shima yana zama a kofar gidan da yar karamar shagon shi yana sayar da bakin mai dama sana'ar Ahmad din ne, yanzun ma da ya gama jami'ar abinda yake faffutikar yi kenan.

    Nuhu abokin shi ne tun yaranta, abokin shi da suka yi gwagwarma

yyar rayuwa, amma shi yana aiki da babban Asibitin rauta. Shi yake auren Azeema, har da yaran su biyu.

       Da wannan sana'ar Allah ya taimaka ta aurar da Azeema, yanzun dashi yake biyan kudin Makarantar Salim, kasancewa yana Poly.

     ----

Da ve

spa din shi ya isa kofar gidan su Ishrat Sadeeq Kakari. Su din yan garin Kakari ne, Alhaji Abubakar Sadeeq Kakari attajiri ne kuma dan kasuwa, yana da Yara Maza biyu sune manyan sai Yan mata hu

ɗ

u.

Yayun Ishrat, wacce asalin sunanta Halimatu. Tana da Yay

arta da take auren wani dan Majilisar dattawan, me suna Raliya, sai Hibbatu wacce take auren Sojar ruwa tana aure a Lagos. Sai Hishmah tana auren wani Commissioner na lafiya tana nan Rauta. Sai dai ita tunda Allah ya had'ata da Ra'is ta haukace.

    Ga

manyan mutane da attajirai da yan siyasa amma bata ta

ɓ

a d'aga ido ta kalle su ba, duk da mahaifin su bai da damuwa duk wanda Yar shi ta kawo an gama magana. Mai matsalar mahaifiyar su ce, sai dai dake Allah ya daura mata son Yar autar ta yasa bata iya lank

wasa ta.

       Yana isa ya hango ta, ta juyawa wani Alhaji baya, dan ba son shi take ba, abokin mijin Raliya ne, shi kuma ya nace da sonta. Tana ganin Ahmad bata sallame mutumin ba, ta nufi gurin Ahmad.

"Kaga dauke ni mu bar unguwar nan" ta fa

ɗ

a tana

hawa bayan mashin dinshi. Babu musu ya dauke ta, suka bar unguwar.

    Basu yi nisa ba, ya tsaya a gefen wani gida.

"Yau shekaran mu hudu me yasa ba zaka shigo gidan mu ba, Abban mu bai da matsala, Hajiya kuwa abinda nake so zata bani. Don Allah Ra'is

ka shigo gidan mu mana."

     Murmushi yayi sannan yace mata.

"Ba wai bana son ki bane, Ishrat bani da hanyar da zan aure ki ne, bani da dukiyar da zan kashe miki ne, Ishrat ke kin saba da ganin kome an ajiye miki idan kika aure ni kome sai kin tambaya

bani da arzikin da zan iya baki don haka ina."

"Ba arziki nake nima ba, domin ina da masu arzikin kai nake so! Kuma yau insha Allah zan gabatar da sunanka, don Allah karka watsa min kasa a idanu."

   Gyada kai yayi domin baya jin zai iya kin Ishrat

sai dai bai da halin da zai iya bajintar auren ba. Suka sha soyayyar su, sannan ya maida ita gidan su, inda suka ha

ɗ

u da Yayanta Yusuf. Bai wani damu can da tsawalawa ba, sai Habibu ne ma yake da matsalar saka ido, bayan sun gaisa da Raees ya juya yayi taf

iyar shi.

    Tunda Ishrat ta shiga gidan ake tashin hankali da ita, domin ta hautsuna gidan da tashin hankali, har sai da aka tafi kasuwa aka gayawa Alhaji Abubakar Dan Kamusho, yazo da kanshi, yana jin abinda take so, bai d'aga hankalin shi ba. Sai ma

tambayar da yayi mata.

   "Kina son Ahmad? Kuma Meye sana'ar shi?" Cikin kuka tace mishi.

"Abba ya gama master din shi, sannan yana kasuwancin sayar da bakin mai, Abba wallahi talaka ne amma mai zuciya, don Allah Abba karka ce a'a"

       "Shikenan

Halimatu ince ba zaki dawo kiyi kuka da shi ba, domin bai da abinda zai iya rike ki? Bai da motar da zai baki kyauta, talaka ne sosai. Halima ba zan miki auren dole ba, tunda nasan ke ba ma Kinga mutanen da suka yi ta niman soyayyarki. Dan haka ba zan kar

a ba ya turo nan da wata biyu kacal ayi bikin ku."

    Haka ta amince dukda Hajiyar su bata so ba, amma ba zata iya hana yar autar su abinda take so na.

Da dare da Ahmad yazo ta gaya mishi hankalin shi ya tashi, bayan ya koma gida ya samu umma da maga

nar, shiru tayi bata ce kala ba, har ya tafi dakin shi.

Washi gari da sassafe ta nufi sabuwar unguwar Joni, ta gayawa Baffan Ahmad, tare da gaya mishi tana da karsananta guda biyu, sai awakai wanda take kiwon su a gidanta, sai akwai shsshin da ta gyara

wa Ahmad din ko zai yi aure. Baffan yaji dad'i, tare da yaba mata irin kokarin ta.

     Kwana biyu tsakani dangin mahaifin Ahmad suka nufi gidan su Ishrat kuma ikon Allah an bashi aurenta, aka yanke kome.

   Mahaifinta dattijon arziki, yace ya yafe k

ayan lefe, amma haka Umma ta hada kayan lefe na ban mamaki, ta bada aka kai gidan bayan an kai sadaki dubu ashirin lokacin kudi na da daraja.

     Wata biyun da aka yanke kafin lokacin Umma ta gyara shashin sa,.an fidda mishi kofa ta waje, sai daya ta c

ikin gidan ta ja musu pampo ta gyara gidan yadda duk wanda yaga gidan zai gane ba karamin kokari tayi ba.

     Haka kafin a fara bikin sai da addana kudin da zasu nima bayan bikin, ga kayan abincin da ta saya ta ajiye musu. Dama geron kunu da waken kosa

i buhu buhu take dauka.

    ..... Haka akayi bikin Cikin rufin asiri da kwanciyar hankali, aka kawo mata Surukarta har d'akinta, itama iyayen ta sun mata shatara na arziki.

     Bayan bikin kowa ya watse umma ta cigaba da kula da harkokin ta, da na Y

aranta, gashi lokacin Ahmad yayi hidimar biki da kudin hannun shi na bakin mai, dole ita ta kuma cire kudi a jikinta aka sake zuba sabon jari.

    Umma tana da nata hidimar haka take ajiyewa tana yiwa Ahmad da matar shi, bata tab'a b'ata rai ko sau Daya

, asalima kamar gani take babu kome dan tayiwa Danta hidima,

  Tsakanin Amarya da Ango love ake bugawa, musamman da ya fahimci shine ya fara ta'adin matar shi ya kara haukace mata, hidima sosai yake mata, idan Yan uwanta suka zo basu tab'a barin gidan s

ai ya nima musu kudin abin hawa. Haka ya kara musu kwarin gwiwar son Kanwar su ta zauna dashi yana da kirki da kyautattawa mutanen da suke zagaye dashi musamman dangin Ishrat.

Itama a duniyar ta bata da na Biyun mahaifiyar shi, kamar ta kwanta Umma ta b

i kanta.. itama kuma Umma babu ruwan ta da harkan su, domin bata son reni, bata shiga harkan su. kullum da safe zata shigo ta gaida Umma, tayi hira sannan ta koma shashinta tayi musu girki tana sakawa Umman.

          Duk da suma suna da nasu kayan abin

cin, haka bai hana ta saka musu ba.

        Yan uwan shi basu da gurin hira sai part din su, kuma itama bata da matsala, gata da hankali da sanin Ya kamata.....

#Mai_Dambu

#PaidBook

#Freepage

300

₿

katin mtn ko shaida ta wannan Numbers

👇🏽

0472282

105 Ramlat abdulrahman manga GT bank! +2347035133148 or 08130269641

8/24/21, 12:07 PM - Buhainat

😝

:

⚪

🖤

KISHI..!!

🖤

⚿

       ~_A Tsakanin Zubda Jini

🩸

_~

       Mai_Dambu

*Sadaukarwa ga Halimatu kangiwa (haliloss). Mrs J Moon. A'isha Fareedah Ya'u Nus

aiba Sulaiman Ayuba jikalle na*

                  *03*

Aishafareeda.

2007-December-04

Yar matashiyar yarinya da bazata wuce shekara takwas ne rike da kofar dakin da Mahaifiyar ta take ciki, jama'ar gidan suna kuka.

"Aishafareeda" a ka kira sunan

ta suka riko hannunta, zuwa dakin Hajja Aliyah. Rungume ta cikin kika da ban tausayi.

"Allah Sarki, Sannun Fareeda kin zama mareniya babu uwa babu Uba. Allah ka jikan Fatimah."

     Duk da bani da hankali a cikin jikina amma ina tsoron kar dai Ummi na

ce ta rasu, dan haka na d'ago kai na kalli hajja Aliyah.

"Mama meye ya samu Ummina?"

Ina kallon fuskarta,

"Allah ya amshi rayuwarta."

Kwanciya nayi a jikin ta, domin na tuna Ummi tana yawan gaya min cewa.

"Aishafareeda Abbinki kashe shi aka yi sabida

hidimar siyasa, kuma Allah ba zai bar su ba, domin ban yafe musu ba, dake namiji ce Tabbas sai na saka kin zama mai daukar fansa, sai na saka kin bi hakkin Mahaifinki Amma babu kome Allah zai bi mana hakkin mu"

    Haka tayi ta gaya min abubuwan da ya f

aru, duk da ba daukar wasu nake ba amma ina matukar kaunar Mahaifiyata.

  Ana gama mata sutura suka fita da ita. Kukan gidan ne ya karu dan haka na fito ina kallon su, haka na koma dakin na kwanta a gadon da muke kwana da Ummina.

      Babu wanda ya

lura ina dakin, sai daga baya suka zo rufe dakin aka ganni kwance a gadon, daukata Aunty Neena tayi tare da cewa.

"Muje kisha magani jikinki babu dad'i."

Domin zazza

ɓ

i ne ya rufe ni sosai, tana kai ni dakin ta bani magana na sha, sannan na kwanta. Ban yi

kuka ba amma kuma a cikin kwanaki nima kamar zan bi mamana, domin rashin lafiya nayi sosai kamar zan mutu, haka suka yi ta daura min ruwa da jini, kafin kwana uku kakata Hajiya Turai tazo daga Nigeria, ganin yadda na koma yasa ta rokon arzikin su bata ni,

idan na ji sauki zata dawo dani.

    Babu yadda suka yi domin kuwa sun san dole wata rana zan koma gurin ta, tunda wa'adin da aka diba idan da nisan kwana shekara goma ne zan yi, dan haka suka amince, ta tawo dani bayan anyi addu'ar bakwai, akan zata d

awo dani addu'ar arba'in.

   Tunda muka shiga garin  ya burge ni, na kuma ji a raina kamar na shigo cikin dangina ne, Hajiya da kanta ta ware min daki me kyau aka zuba min kayan kawa ne yara. Ko ina gwanin ban sha'awa.

      Tunda na shigo gidan kome

na gidan ya sauya, idan gari ya waye babu wanda ya isa yayi kwaranniya da kaya, sai na tashi a barci, kuma babu surutu. Domin kwana na daya da zuwa na fito tsakar gidan na rike ƙatuwar teddy bear na ce musu.

"Hajja Kaka, ni bana son hayaniya idan ina b

arci, kuma bana son surutu duk wanda ba zai yi kome a hankali ba ya tafi ya bar gidan."

Na fada ina zaro kananun idanuna.

"Toh dai kun ji? Toh a kiyayye a zauna lafiya."  Ta fa

ɗ

a tare da kallon su, sanin cewa gidan Hajiya yana daga cikin gidajen da ake k

yautatawa dan haya duk da kasancewar ta mafadaciya yasa suka yi mubaya'a.

       Haka na cigaba da daura mulkina bana fita ko ina, sai ranar da Umar ya shigo da mugun gudu, yana haki.

      "Hajja Kaka waye wannan?" Na tambaye ta Umar,

"Lusarin dan

uwanki ne, bai da zuciya yanzun zaki samu koro shi suka yi."

Mik'ewa nayi tare da cewa.

"Muje" na riko hannun shi muka fito waje, wasu yara ne da basu wuce shi ba.

"Kai meye yayi muku?"

"Laaa! Babangida kaga baturiyan cikin tv nan da muke gani"

"

Kai dalla can, meye zaki yi idan muka gaya miki"

"Zanci Ubanku ne a sanyayye." Na fada ina kallon su.

  

Cikin jin haushi suka hada baki tare da cewa.

"Ke yarinya karama har kin iya zagin mutane yau sai mun zane ki"

"Dauko min wancan kananun duwa

tsun."

    A hankali ya dauko min nace musu.

"Zaku tafi ko sai na fasa muku kanku?"

"Dukar ki zamu yi kuma mu daki dan uwanki."

Wato da na dauki dutsen na cab'e cab'e sama, na saita shi akan su na shiga jifar su, da gudu suka bar kofar gidan mu, ju

yawa nayi tare da cewa.

"Ka zama banza wallahi" na shiga cikin gidan. Shi ya bawa Hajiya labarin abinda nayi musu, bana hayaniya bana magana sosai. Ina son a rayuwata na ga ana min fadanci dan haka ina zaune Umar ya shiga min fadanci.

          ----

G

idan su Umar muka je na gaida Mamar shi, a hanyar dawowa muka tsaya a wani shago zamu sayi alawa. Wata yarinya ce tazo ta bangaje ni, juyawa nayi na daki kirjinta.

"Ke baki da hankali ne?"

"Kutt yar karama dake kin iya gayawa mutum maganar banza"

Mika

wa Umar kudin nayi ina cewa.

"Bari na koya miki hankali." Na cire takalmi na, na kwala mata a fuskar ta.

Yana zuwa bai bi ba'asi ba ya kore mu a shagon, ni kuwa nace a bani kudi na ko alawata.

"Ba zaki tafi ba sai na zane ki"

Dauke kai nayi tare da m

ikawa me shagon hannuna.

"Zo mu tafi mana babu lokaci fa"

        Amsar al'awar yayi ya watsa min. Na kalle shi da sauri na dauka nima na watsa mishi ina kallon shi. Abun mamaki bai tab'a ganin yarinya mara kunya irin wannan yarinyar ba. Sauka yayi a m

ashin din tare da karyo bulalar maina. Ina kallon shi.

"Raees karka janyo mana masifar Hajiya Turai, barta bakuwa ce ba yar gari bace"

         Kura mata ido yayi ya ga itama shi take kallo.

"Ba dan ina sauri ba sai na zane ki sai dai kakarki tayi abi

nda zata yi mara kunya kawai."

Murguda mishi baki nayi tare da dauke kaina ina kallon Umar na ja hannun shi muka bar gurin.

  "Nuhu kasan yarinyar ne haka?"  Ya tambaye abokin shi.

"Eh mana, mahaifinta yana kai kaya Chad a can ya auri mahaifiyarta w

allahi mutumin kirki itama matar shi haka, kashe su aka yi akan bangan siyasa. Ka tuna Hassan da Hussaini nan? Wanda dayan yake yawo kullum da kayan Jami'ayyar GDP?"

"Eh na tuna shi wani dogo baki, yar shi ce?"

"A'a yar Hassan din shi ce, itama yarinya

r bata jima da zuwa ba sai dai kuma mahaifiyarta  ta rasu ne tazo nan kwana biyu. Abinda yasa na gaya maka ma sabida Rabe abokin Jamil ne yake gaya musu, kyan yarinyar shi yasa da naganta da Umar na Fahimci haka, ai shi Umar din mahaifiyar shi tana aure a

bayan layin mu ne."

     Shiru yayi suna tafiya har  suka tsaya inda zasu  zo kusa da gidan Hajiya Turai, domin duk unguwar kuka suke matsalar layi ne ya rabasu,  yana tsaye suna magana da wani mutum.

   Da uwar harara na bi bayan su, sannan na saka

Umar a gaba ina masifa ina gaya mishi magana, har muka isa  na ganshi a kusa da gidan mu, dauke kai nayi.

Shima kuma yana ta uzurin shi haka ya d'ago dai dai zan shiga gidan.

*Ai Nan ne gidan Hajiya Turai?* Ya tambayi kan shi.

    Yana gama abinda y

a kawo su, suka yi tafiyar su ya manta da ita baki daya a tarihin shi niman aikin shi kawai yasaka a gaba.

   ---- Ana jibi arba'in Ummina Hajja kaka ta maida ni Chad, sai da aka yi addu'a sannan ta dawo, ta barni da kewar ta.

Alhaji Mustapha Nasir Ma

i turare . Shine cikakken sunan Kakana, sana'ar shi kenan turare wanda ya gada tun daga iyayen shi da kakanin shi, gidan su Ummina ana kiran shi gidan turare, ko ya ka shiga gidan sai ka fita da kamshin.

   Sannan Kakata da sauran yan gidan suna aikin g

yaran amare,dilke hatta sabulun wanka na, idan zaka dauka sai ka rantse dilke ne. Na taso inda ake mutuntta kamshi ake daraja kamshi.

   Ummina itace ya ta kusan goma a cikin gidan, kuma wani abin mamaki rabo ya ha

ɗ

a auren, domin idan ba haka ba babu ab

inda zai saka su bashi auren Ummina.

   Familyn su Ummi sun fi yin auren dangi sama da na bare, shi yasa da Abbana yazo aka yi ta mamaki, gidan zagaye yake da yan uwa  Hajja Aliyah kakar su Ummina Hajja Nusaiba kuma kakana wacce ta haifi su Ummina, gida

n babban gida ne me dauke da mutane sama da talatin.

     Hajja Nusaiba tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login