Showing 96001 words to 99000 words out of 170719 words
daidaita da Umma, shi yasa ya nace zai gyara mu'amalar shi
Aisha amma dake bakin wayo ne da ita, sam taki yarda su zauna lafiya. Dan haka ya biyo ni hanyar d'akina, baki daya sai na rud'e, kawai na fada dakin shi. Sake baki nayi ina kallon duniyar da aka zuba a cikin
ɗ
akin har ya shigo.
A hankali nake
takawa tare da nufar inda wani babban kofar glass yake, na janye labulen, yar karamar gurin shan iska ne, ga can ruwa, gwanin ban sha'awa, ga wasu irin kujera masu kyau, an Kawata gurin har da newspapers.
A hankali na fito naga karamar kofar da zata
kaika har gurin ruwan, a hankali na ji motsin shi.
"Gurin ya baki sha'awa ne?"
"Hm"
"Gashi nan ai! Don Allah"
Juyawa nayi tare da nad'e hannu a Kirjina,
"Ahmad idan ka ci maita zaka kai mutum lahira babu makawa. Don Allah ka kyale ni"
"Aishaf
areeda! Taimakawa zaki yi, nasan kece kawai umma take masifar kaunar zaman mu, amma ba zan kuma rokonki ba, iya yau na gama."
"Alhamdulillahi! Ubangiji Nagode maka da ka kawo min sauki, Allah ka rabani da chewgum" na fada ina kallon shi zan fita.
"Nagode
" na saka kai na fita abuna, na koma dakin Umma.
Duk da yace ba zai kuma min dole ba, amma bai fasa idan muka zauna ya shiga marairaice fuska ba, wato tunda Uwata ta haife ni ban tab'a ganin mutum me bakin naci irin Ahmad ba, ni kuma naki karban shi
sam naki amsar bukatar shi.
Bayan kwanaki jikin Umma yayi sauki sosai, dan haka muna hira tace mishi.
"Malam Ahmad! Zamu koma gida fa"
"Toh amma ke da Khadijah ko?" Ya tambaye ta, kamar a razane,
"Har da Fareedah, tunda babu wani abinda zata y
i maka."
Jin kafar shi nayi yana min tafiyar tsutsa, ban san lokacin da na zabura ba.
"Umma!" Cikin kulawa ya kalle ni, sosa kaina nayi tare da cewa.
"Hmm!"
"Ba zaki bi Ni ba?"
"A'a ban ce haka ba,"
"A'a Humairah idan kina son zama da mijinki ai ki
n rage min wani nauyi ne, Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba."
Ina har ta yanke hukuncin, shi kuma yayi ta min dariya, karshe hirar da ba a karasa dani ba kenan, na mike tare da barin gurin.
Dakin ya biyo ni, ina kwance, ya shigo ya k
unna wutar
ɗ
akin, ganin yadda nake zubda kwalla yasa jikin shi sanyi. Hannuna da yake saman duvet din ya riko.
"Nasan na cutar dake, amma ina kara baki hakuri da abinda ya faru sharrin shaidan ne"
Janye hannuna cikin nashi nayi sannan nace mishi
.
"Sharrin shaidan ko sharrin mutum? Don Allah ka rabu dani, na ka sani na zauna ba. Toh idan kasan darajar Ubangiji karka shiga harkana, ni kuma ba zan shiga na ka ba, idan ka shiga harkana xan fita na bar maka gidan ka."
Kwalla ne ya cika min ida
nuna, haka na juya mishi baya ina shashekar kuka, mik'ewa yayi ya bar d'akin.
Washi gari.
Umma suka bar abuja ko dakin ban leko ba, haka ya gama gulmar shi ya shigo tare da kawo min abin karyawa. Da gaske shiri yake son muyi haka kawai zai saka ni a
gaba sai na shirya mu fita unguwa, tun bana so har ba saba, duk abokan aikin shi, ya gaya musu nice matar shi.
Lokacin da Saimah surukar Shugaban kasa ta haihu ranar sunan da kanshi ya kai ni har gidan Shugaban kasa, tare da gabatar musu dani, ai mat
ar sa ce ni second choice din shi.
Tabbas nasan Ahmad yana bukatar shiri, sai dai yadda yake nuna min shirin yana saka ni jin tsoron Allah da tsoron shi. Domin baki daya, yake kara kusanto ni, duk da ina kare kaina, amma yanzun na fara sarewa, bay
a ganin wulakancin da nake mishi baya damuwa da abinda nake mishi, abu daya kawai ya sani ya sani a jikin shi.
.... Ta bangare shi yayi kokarin b'oye yanayin shi akan yarinyar duk wannan abinda ta aikata a bayan ya dauke shi ya binne shi a kasar
ranshi, kamar bai tab'a faruwa ba, so yake su gina rayuwar su, cikin tsarin da yarda da juna, ya kuma kokarin dauke kanshi yana zaman biye mata ne dan a zauna lafiya.
Bawai son ta yake ba, a'a yana Bin tane sabida ya fahimci itace farin cikin Mahaifiy
ar shi, idan ya nace sai ya rabu da ita zai iya fuskarta rashin albarka a rayuwar shi,shi yasa ya yanke hukuncin zama da ita duk da ta mishi illa ba zai hakura da ita ba, ta kuma kyautatta mishi ta samu fannin domin ta saka mahaifiyar shi alfahari dashi. M
urmushi yayi domin yana son ganinta cikin farin ciki, shi yasa yake ta addabar ta dason a zauna lafiya.
Amma baiwar Allah nan bata gani ba, ba mamaki sai yayi nisar kiwo zai saka ta Fahimci abinda yake son su gina ne. Sabida Farin cikin umma ya zama hak
a,gashi bata da kirki. Domin ko ya sameta su yi maganar gaskiya zata nuna mishi bata so!
Da yamma ina zaune a falon, baki suka shigo daukar mayafina nayi tare da kallon su.
"Barkan ku da zuwa"
"Yawwa! Muna niman Halima ce?"
"Allah Sarki, bata
nan idan ta dawo zan gaya mata."
"Toh mun gode" suna gaya min, tare da barin falon, suna fita yana shigowa.
"Meye ya had'a ki da su, wai sun zo gurin matar gidan ne"
"Ni daya ce Matarkaa? Toh ni ban sansu ba, dan haka. A bar had'a Ni da wasu c
an mrasa kan gado."
"Toh Allah ya baki hakuri"
Ya fada tare da zama yana kallona.
"Ayagi"
Daure fuska nayi irin bana son wasan da yake min, amma baya ganewa, dan haka yana cigaba da wasan.
Mikewa nayi tare da barin shi a gurin zaune, dakina ta biyo
ni yaji a rufe kuma dama nasan zai biyo ni, bikini na saka tare da daura babban hijab a jikina, sannan na fito daga dakin na fita ta kofar baya da yake kitchen na bi.
A hankali na nufi gurin ruwan da yake kwance, na saka kafana ina wasa da ruwan. Cik
in wani irin yanayi, murmushi nayi a karo na biyu, ina kara son ruwan a raina. Cire hijab din nayi tare da warware gashin kaina na rike karfen jikin ruwan me matakala, na shiga a hankali ina jin yadda ruwan yaƙe, wani irin dad'i ya kamani, na fad'a ruwan t
a baya, kawai ya wani bada fanjamm. Sai da na nutse na minti uku kafin na d'ago daga ruwan ina eyo.
Baki daya na zama yar ruwa. Haka na yi ta wanka na, ina jin wani dadi a raina, daga wannan kusurwan zuwa wancan kusurwan.
.....
Haka yayi ta nime
na tare da jin tashin hankali, ba dai yarinyar nan tafiya tayi ba, baki daya ya fita bakin get ya kai sai biyar yana tambayar su Fareedah ta fito suka ce a'a. A matukar gajiye ya dawo dakin shi zai dauki wayar shi, kamar ance ya d'aga kanshi, ya hango hann
u yana yawo a sama, bai san lokacin da yayi wurgi da wayar hannun shi ba, gaban shi ya fadi.
"Ba dai kashe kanta tazo yi ba?"
Bai da me bashi amsa ya fita da kofar dakin shi ya nufe ta da mugun gudu, yana zuwa bai nutsu ya ga abinda take ba ya fad'a r
uwan, tare da niman ta duk da ruwan garau ne zaka iya hango kome, yana shiga ya ganta zaune tayi zaman yogo, ta daka hannun ta a saman gwiwar ta, bata san ya shigo ba, cike da al'ajabi yake kallon yadda ta rike numfashinta
Rigar jikin ta ya kall
a wanda suka bayyana tsakiyar kirjinta, rigar ta bayyana kan nonuwar ta, cikin wani irin fisga ya sake numfashinsa bayan ya shaki ruwa, kallon gashin kanta yayi da yake yawo cikin ruwa, sake shaƙar ruwa yayi bai san lokacin da ta haura mishi kai ba, tare d
a shan ruwan babu shiri. Yana ƙoƙarin kamo abinda zai rike.
Na bude idanuna, ganin yadda yake kokuwa da numfashin sa ya sani maza na mik'ewa tare da fita a ruwan na cafke wuyar shi ta baya na d'ago shi bakin pool
ɗ
in, wani irin numfashi yaja. Tare da ju
yawa yana kallona.
Yana son min magana amma har lokacin ruwa na hancin shi.
"Malam ka kula da lafiyar ka, ka zauna inda Allah yayi ka, karka ce zaka saka rawan wani domin zaka iya rasa turmin daka taka." Na juya tare da fita daga cikin ruwan.
Kallon k'ugunta yake da suke motsewa,. Musamman rubber bom
ɗ
inta, had'iye yawu yayi tare da dauke kanshi. Wannan yarinyar zata kashe shi sam bata da kunya, gaba gadi take kome.
Tunda na fito na shiga goge gashina ina daura towel na juya na barshi
a gurin bayan na saka hijab, fita yayi a gajiye abubuwa yawa yake ji a ranshi, dan haka ya wuce dakin shi ya sauya kayansa. Karar wayar shi yasa shi dubawa, Ummana. Ya gani,
A hankali ya
ɗ
auka. Tare da sallama.
"Ahmad mun kira Fareedah bata dauka tana
ina ne?"
"Kai Umma wato sai kin rasa Fareedah zaki kirani, toh bari na bata tunda ni yanzun an daina yayina."
"Can da shirmenka" ta fa
ɗ
a mishi.
Fita yayi tare da kashe wayar, ya nufi dakin kai tsaye. Yana shiga cikin dakin ya same ta, da sauri ya ja k
ofar.
"Sorry! Wallahi ban san zan ganki haka ba."
Tab'e baki nayi tare da cewa.
"Meye ya kawo ka d'akina?"
"Umma ta kira ki baki dauka ba, shine ta kirani."
"Ok" na fada ina saka bra
ɗ
ina, Iskancin banza nonuwa ta ya gani fa,(
😒😏
) shine sai k
ace wanda yau ya fara ganin su, tsaki nayi tare da Cigaba da saka kayana.
3qurts na saka da wata riga iya cibiya na, na nufi kitchen bayan na kira Umma mun yi magana akan Umar ne da ya tura manyan mu gurin Baffan su Ahmad.
Mun gama maganar aji
yewa wayar kawai na shiga dafa abinda zan ci, domin tun bayan Tafiyar Umma me girkin gidan iya Ahmad yake dafawa ni kuma nake dafa nawa, haka na had'a kayan lambu da kifi, sai namar rago, na had'a na dafa brown macaroni, da yaji kayan lambu.
Na fit
a na dawo na samu Ahmad ya juyr rabin abincin a filet, yana ganina ya kama murmushi da d'age min gira. Daure fuska na nayi, sannan na juye sauran dan ba zai ishe ni ba.
"Nagode sosai! Wannan abincin." Ban kula shi ba dan nasan abincin ba isata
zai yi ba, na hada har da Golden morn, na juye a cup na nufi waje yana bina.
"Baki hada min nawa ba"
Cikin fushi na dangwara abincin na juya tare da cewa.
"Ba sai ka gaya min abincin gidanka ne ba, ba zan ci ba, hada ka cinye Baba rodo" na nufi dakina
tare da
ɗ
aukar side bag dina na saka kudi zan fita.
"Kiyi hakuri da nasan baki son wasa ba da bazan tab'a miki abincin ki ba."
Ya fada tare da ajiye filet din shi.
"Ina zaka tafi ka barni min wanda ka fara ci? Dalla malam zoka dauki abincin ka"
"A
t least ni mijinki ne. Ina bukatar mutunttawa koda ba zaki iya girmama ni ba, karki na min abu kamar dan karamin yaro"
"Ahmad! Ni bani da miji! Tun tuni narasa mijin, wallahi bana kaunar ka, bana kaunar zama da kai, don Allah ka rabu dani, idan da kansa
n yadda na tsane ka ba zaka nace min ba kamar kasaka ba."
"Ok Nagode"
Ya fada na zata zai yi zuciya da abincin ne sai gani nayi ya
ɗ
auka tare da gyara zama ya shiga cikin abincin shi, kamar ban gaya mishi magana ba.
🤷🏽
♀
️
Kishi a tsakanin zubda
jini isn't free, if you need chat me.
300
₿
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank!
+2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
9/4/21, 9:27 PM - Buhainat
😝
: 48.
"Amma baka da zuciya!" Na fada ina hade rai.
"Eh Kawata yar ruwa"
Banza nayi dashi tare da Cigaba da cin abincina.
"A'isha!"
"Hmm" zan tafi taro akan man fetur, a kasar Qatar zaki rakani?" Yadda yayi maganar akwai wani abu a kasar tambayar.
"Babu inda zani, ka kira Halimah ka tafi da ita"
"Don Allah"
"Ka ga ina da abinda ya zame min dole na duba, ba zan bika Qatar ba"
"Ok" ya fada tare da cigaba da abinda yake, wallahi na zata yayi zuciya ne sai da na gama cin abincin ina shan morn kawai yace min.
"Don Allah!"
"Ahmad!" Na fada kamar x
an yi kuka.
"Don Allah"
Wallahi ban tab'a ganin mutum me masifar roko irin Ahmad ba, kamar zanyi kuka nace mishi.
"Idan kana kaunar Allah ka barni ba zan je ba"
"Please Fareedah" ban san lokacin da ba fashe da kuka ba, na tsani naci a rayuwata shi ku
ma abinda na Fahimta dangane dashi yana da naci kamar bashi, dan haka na sha kuka na har na tashi na koma daki na kwanta.
Biyo ni d'akina yayi tare da zama ya sani a gaba da naci,.ban san lokacin da na fasa ihu ba, ina. Ture shi tare da kuka ha
ɗ
a n
i yi da bango. Ban san lokacin da na kama dukan kirjin shi ba, yana kallona. A hankali ya saka kanshi a ƙafadana.
"Kin tsane ni ko? Toh nima haka nake ji akanki da can baya, a yanzun kuma ina jin zan yi abota dake ne, amma tunda baki bukatar sakinki shi
kenan!" Ya janye jikin shi da yayi matukar sanyi da buqatar abokiyar rayuwa.
Rike hannun shi nayi tare da cewa.
"Da gaske zaka sake ni?" Na tambaye shi idanuna cike da kwalla.
"Eh zan sake ki" ya fada da kyar tare da fidda numfashi.
"Ahmad karka cut
ar dani, da gaske zaka sake ni?"
"Baki yarda dani bane" kwalla ne ya zubo min.
"Dama zaka sake ni? A'a ina nufin yaushe daka sake ni?"
"Ok idan kin bani damar zama dake na wasu lokuta, zaki rakani ko ina, sannan zaki yarda mu zauna guri daya. Muyi ab
ota. Muyi kome tare!"
"Amma ban da!" Kura min ido yayi sannan yace.
"Nayi miki alƙawarin ko sex ba zan yi dake ba, ince shine kike tsoron?"
Gyada mishi kai nayi sannan ya cigaba da cewa.
"Zamu yi sharing abubuwa da ya shafe mu. Sannan zaki sama a
bokiyata, karki yi tunanin zamu ci amanar juna, sannan zaki tsaya min nima zan tsaya miki, babu rashin kunya ki maganar banza, bana son fada ko rigima.
Between me And You zamu zama kamar lover"
"Ahmad! Meye na maganar Lover?" Na tambaye shi ina ka
llon shi kamar zanyi kuka.
"Kinga sabida zamu je bikin Umar da Khadijah ne, idan muka tafi muna wannan rashin jituwa zasu Fahimci bamu shirya ba. Dan haka idan muka kika dauki haka kowa zai na mana kallon zaman lafiya."
Haka Ahmad yayi ta ts
ara Aishafareeda, ba dan kome ba sai dan wani magana da Umma tayi mishi akan rashin haihuwar su, da tace mishi.
"Idan kai ne baka haihuwa ja sawwake musu, idan kuka daya ne a cikin su, sai ka zauna lafiya da ita daya daya kuma ka sallame ta. Domin babu am
fanin riketa a rayuwarka, koda Aishafareeda ce ban fadi haka ba dan wani dalili sai dan nasan akwai mutane dayawa da rabon su yana wani gurin amma idan zaka iya zama dasu babu matsala, amma ka fara daukar su zuwa ganin likita tukun."
Shi yasa zai tafi d
a ita Aishafareeda tunda baya tare da Ishrah, amma da Ishrah tana nan da da ita zai tafi domin ita ta dace ya nima mata magani, toh dake yana son haihuwar shi yasa yayi maza ya mai da hankali akan hakuri da abinda take mishi, bawai son ta yake ba. Kawai za
i magance tasa matsalar ce kuma Umma ta fa
ɗ
a mishi haka ne bawai dan ya tozarta matan shi ba, shi kuma zai yi haka ne domin ya tozarta Aishafareeda. Sam ya manta da akwai Allah kuma baya barci.
Shi yasa koda suka dawo bawai dan tun a can da ta mishi mag
anar yake kara bibiyar Aishafareeda din.
Murmushi yayi sannan ya shafa kanshi yana kara tabbatarwa kanshi Tabbas tarkon shi idan ya kama kurciya za ayi ta ta ƙarshe. Dan haka zai cigaba da lallab'a ta, har ta sake jiki dashi.
**
Kanta a s
unkuye tana shashekar kuka, domin kuwa ya kuma tuntubar Bagauda yace wallahi yayiwa Ahmad magana, dan haka ta tafi gurin Umma shima zai zo da kanshi.
Tana durkushe ban da kuka babu abinda Ishrah take.
"Hakika Allah yayi gaskiya da yace masu hakuri s
una tare da shi, dan haka Ishrah ban tab'a kawowa Ahmad zai zalince shi sai dai ke, domin duk wani soyayyar gaskiya yayi miki. Dan haka kije zan mishi magana idan ya gadama ya mai dake, idan bai gadama ba, toh babu dole domin wallahi ina mishi soyayyar da
ba zan iya mishi dole akan ki ba."
Daga haka ta mike tare da cewa.
"Ki gaida Mahaifiyarki"
"Umma don Allah kiyi hakuri! Karki manta kema Uwacr kuma kina da yaran nan don Allah ki yafe min na koma dakina."