Showing 75001 words to 78000 words out of 170719 words
ta wayar ta ne take karatun Alkur'an.
Addu'o'in take ajikin dabino, tana murmushi. Koda aljanun suka shiga gidan karfin tasirin addu'o'in ta, ya kona su baki daya.
***
"Ni Raees zai wa kishiya da yar bariki? Yarinyar da ta
na tafiya jikinta yana rawa? Tun bai zama haka ba take tare dashi. Yanzun kuma Allah ka dai yasan me zai faru."
Ta fada tana kuka, shigowa yayi jikin shi a sake, ya zauna kusa da ita.
"Idan kana son zama dani, ka je ka sake ta."
"Kiyi hakuri, wannan
karon ba zan iya ja da Umma na ba, na dai san ba zan tab'a yarda nayi wani abu da ita ba, wallahi na miki alƙawarin haka."
Ya fada cikin ban tausayi, yana kara rike hannunta.
"Fita bana son ganinka" babu musu ya tashi ya bar dakin.
"Toh tunda ki
nji abinda ya fada dole ki amince a zauna lafiya, idan ya so sai ki Cigaba da abinda za yi domin fitar da ita, tunda nasan ba zai taba yarda yayi mu'amalar aure da ita ba.
Shu'umin murmushi ta tana fa
ɗ
in.
"Tabbas tayi kuskuren auren mijin Ishrah"
**
Yana gama hada kome ya muka musu.
"Ku tabbatar kun saka wannan a inda ake soya ko gashi. Ba dare ba rana, da haka zamu iya nasara akan Yaron, kuma zai tsane ta ba har abada. Sai dai da sharadi!"
A sukwane ya kalle su yana zare idanun shi.
"Ya m
ai duniya ina jinka"
"Daga ranar da suka ha
ɗ
u guri guda aikin zai lalace, dan haka a kula domin zamu iya rasa rayukan mu, shi kuma karku sake ku ce zaki tilasta mishi yin wani abu dole, domin zai iya bijire muku"
**
Ina idar da Addu'o'in na na n
ufi kitchen na ajiye dabinon na fito, lokacin shan ruwa nayi aka kawo dinning ila ganin yadda yake haba hana da Ishrah, zama nayi na fara da bismillah. Ina ci ina kallon su.
Lokacin sallah nayi na mike zan bar gurin.
"Raees bana son na kuma ganin
fuskar yarinyar nan anan"
"Karya kike yi! Wallahi karya kika yi. Ganin fuskana shi dolen ki. Kuma kin san me? Nan da kwana biyu zaku bani mijina domin ina mafarkin kayan aikin shi" na juya abu na.
Baki daya na addabi rayuwar su, a cikin kwana guda.
Cikin dare na tashi sakamakon wani irin haushin kare da nake ji, tashi nayi na fada ban daki nayi alola, sannan na tawo na canza kaya na fara sallah. Domin maganar Umma ya tsaya min a rai, duk da Muna waya da ita sau biyu sau uku.
"Aishafareeda!
Ba aure kika yi domin ki fito ba, wannan auren da kika yi sunan shi mutu kara ba, domin kuwa yaki ne a gaban ki. Kamar yadda Ishrah ba zata barni ba, haka kema ba zata barki ba. Aishafareeda koda ba zaki zauna da Ahmad ba, ku gwada nazari aikinsa mana, ida
n ace Umar ne a halin da yake ciki zaki bar shi haka ne? Aishafareeda wallahi ke daya Allah ya nuna min zaki iya tafiya da Ahmad, Aishafareeda ni uwa ce. Ina son ganin d'ana ya damu dani, kiyi tunanin idan Mahaifiyar kice a irin wannan yanayin ya zaki ji?
Ba zan miki dole ba, amma don Allah ki taimaka min Allah zai taimaka miki."
Kwalla ne ya cika min idanuna lokacin da nake kallonta.
"Wallahi mutum ne da ya taso bai da abokan gaba, bai da fitina. Aishafareeda tunda Ahmad ya shiga siyasa ya mant
a da ni, amma ni ban manta dashi ba, Aishafareeda ga Amanar Ahmad nan a hannunki, idan yayi kyau naki ne, idan ya b'aci nawa ne. Duk wani wanda ya zama wani abu a duniya da taimakawar mace bani bace ke ce!" Ta nuna ni da yatsarta. Kwalla ne suka shiga sauk
a daga idanuna.
"Kece kika jagoranci kowani nasarar shi, kece kika bashi kwarin gwiwa tun ba yau ba, baki fahimci mulkin naki bane, shi daura shi aka yi amma kece kika jagorancin zuciyar shi, duk wani abinda aka san kece jagaba ke ake bawa, Aishafareeda
Ahmad bai san kome akan siyasa ba. Ahmad bai shiga ya fita ba, bashi damar zama akayi amma bai san kome ba, Aishafareeda ke kuma kin san ciki da wajen siyasa, kin san abinda yake faruwa. Kinsan kowa, Sunan shi Raees ne ma'ana shugaba, domin cikar sunan ke
ce zaki Cigaba da rike shi ragamar shi"
Rike hannuna tayi sosai sannan ta Cigaba da cewa.
"Idan kika so zaki iya tafiya, amma ki sani amanar shi yana hannunki.....
🤷🏽
♀
️
Kishi a tsakanin zubda jini isn't free, if you need chat me.
04722821
05 Ramlat abdulrahman manga GT bank!
+2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
9/1/21, 3:19 PM - Buhainat
😝
: 38
Wannan matar ta bani dukkan yarda ta, ta kuma amince min a rayuwar d'anta, Allah ya ga niyyata bana
son Raeees ko ka
ɗ
an bana kaunar shi daga cikin zuciyata nake jin haka!
Haka na tadda sallah, ina yi ina sallama tare da gayawa Allah kukan mu, musamman ni da na dauki auren a kayadaddden lokaci. Kuma nayi imani idan har Allah ya bani Sa'a akan sh
i.
Karfe uku saura na idar, sannan na nufi kitchen, nasamu Mr Jamal yana aikin abincin sahur, indomie na dafa da kwai sai tea da goran ruwa. Na nufi dakina. Ina shiga na zauna na fara sahur sannan na kira Umar ya bawa Hajiya mu gaisa, haka muka sha
hira, kafin na kira Umma itama mun yi hira har na gama, sannan na dauro alola. Na gabatar da sallah nafillah bayan ketowar alfijir.
Ina idarda ana shiga sallah asuba, ban jinkirta ba na daura sallah. Bayan na idar na cigaba da azkar. Har sai da ra
na ya fito,sanan na bi lafiyar gobe.
**
"Raees muje ka ce ta fito daga yau masu aikin gidan nan sun huta ita zata cigaba da yin shi"
Sake baki yayi yana kallon Ishrat, wato Aishafareeda zai je ya d'ago?
"Tashi muje" ta kuma fada babu musu ya t
ashi ya bita.
Ce mishi tayi ya jirana, ta shiga kitchen ta dibo ruwan sanyi har da ƙanƙara, zata shiga ya rike.
"A'a Halimah zan sakata tayi amma ban da wannan domin wallahi koni ban isa ba balle ke" fisgewa tayi tare da nufar hanyar dakin.
Kam
ar wanda Allah ya sanar da ni na bude idanuna, ina kallonta. Wani shegen kallo irin kinsan wacece ni? Na mata.
"Raees ka mata magana" ta fa
ɗ
a,
"Hmm! Daga yau zaki na aikin gidan nan ne!"
A hankali na sauko daga gadon ina me kallon shi. Na tako har
gaban shi, na d'an kara tsayi kad'an nace mishi.
"Kai ne kazo dan kanka ko ita ta turo ka?" Na tambaye shi ina murmushi" rintsa idanun shi yayi yana jin wani irin wutar tsanar ta na haurowa mishi.
"Raees meye haka?"
A firgice yace Mata.
"Kinji abinda
tace ko?"
"Ke yar iska karuwa baki isa ba!"
"Mijinki ya gaya miki yadda abin yake, domin kuwa bai fahimcin abinda kike nufi ba" daga haka suka bar min d'akina.
*
Har aka yi sallah, babu zaman lafiya domin na buwayi Ishrah, kuma Addu'a nake, Allah ya
bani dama daya na mata mugun duka, shi kan shi Raees yanzun ta dawo daga rakiyar ta, sai dai a yadda na Fahimci abinda yake faruwa, Raees baya son zama inda nake, idan ma ya muka hadu, toh wallahi dauke kai yake daga kallona.
A hankali kome yake ta
fiya, ta bangaren Ishrah, ta rasa yadda zata fidda ni. Na gaji da zaman gida dan haka na fita. Dakyar na samu banki na cire kudi na nufi kasuwa, sai da nayi sayayya na dawo. Ina shiga cikin gidan ya kalle ni.
"Daga gidan uban waye kika fito?"
"Ban gane b
a?" Na fada a sanyayye, domin bana son idan yana fadar shi tana jin mu, zan wuce ya fisgo ni.
"Tambayar ki nake daga gidan uban waye kike?" Jan iska nayi domin a rayuwata, na tsani haka.
"Ahmad muje xan gaya maka."
"Babu inda zani, ki gaya min daga gi
dan Uban waye kike?"
"Ahmad!"
"Ina magana kina kiran suna na? Ki gaya min daga gidan uban da kike fito da aure na."
"Kasuwa na shiga!"
"Kasuwa?" Ya tambaye ni cikin gatse,
"Babu Super market ne ko mall?"
"Kayi hakuri nayi kuskuren fita babu izinin
ka, amma ita Halima me yasa baka saka ido akan ta ba? Sai ni kake zargi?"
Cikin fushi ya d'aga hannu zai mare ni na kalli cikin idanun shi.
"Ba zaka kuma marina ina kallon ka ba, kawai kayi hakuri nayi laifi" na tattara kayan na shiga cikin dakin.
Dama haka auren yake, wai idan mutum baya kaunarka shi kenan baka da ikon fita ko ina, matar shi da take, yawonta har da security, babu wanda ya damu da ita sai ni. Tunda na sayo Laptop dina, hankalina ya kwanta bani da matsalar kome sai na kaina.
Ba zance ban ga amfanin auren Ahmad ba, domin na fahimci baya sati biyu bai zai tafi ya duba Umma.
Ina jin shi wannan zuwan na shi yake gayawa Ishrat, zai kai Umma Jiddah a duba mata idon ta, nan ta shiga Bala'i na fito nace mata.
"Zuwa Jidd
a kamar an gama, mace sai dai ta mutu"
Cikin fusata mahaukaciya ta yo kaina, yana tare ta amma ina ta iso, taka kafarta nayi sai da yayi kara. Da sauri ya bangaje ni sai da na buge kafadana.
"Amma kana ganin yadda take min baka mata magana ba sai
ni? Meye nayi maka ne?"
" Tsane ki! Wallahi bana son ganinki, wallahi gwaara na zauna da bakin maciji da na zauna dake, ban san wacce irin halitta bace ke da ƙaddara ta Hadani dake, ku tafi bana son ganinki a kusa dani!"
Barin gurin nayi domin kuwa
a yanzun ban ci ta fushi ba, Insha ALLAH sai na saita ka a kan hanya zan rama.
Haka ya duba kafar karshe dai sai da ya kai ta asibiti aka duba kafar.
"Kinsan Allah, matukar kika ce zaki shiga harkan yarinyar zaki mutu, domin wallahi kashi daya ga
re ta, kuma zaka nakasa ki"
Har suka dawo ina d'akina, fitowa nayi sanye da riga body hook, sai wandon bom short na jeans, na wuce abuna kafata sanye da boot, na nufi dakin motsa jikin shi.
"Raees!" Kallonta yayi a gajiye,
"Kaga yadda yake yawo?"
Kura mata ido yayi sannan yace mata.
"Ina ruwanki da ita? Zaman Umma take, dan haka sai ki zuba mata ido, kafin lokacinta ya cika."
Murmushi yayi, tare da kisimawa a ranta dole yau ta nuna mata iyakarta ta kuma nuna mata tafi ta matsayi a gurinshi,
Suna zaune a gurin na fito, hangota nayi a saman cinyar shi tana wani Iskancin na daban, dauke kai nayi tare da sake murmushi mugunta, na wuce. Ba mijinta bane a gabana,aikin da yake gabana ya wuce tunanin shi.
Dan haka na samu na barsu a guri
n.
Bayan kwana biyu ban zata zai iya tura ni kai Umma Jiddah ba, sai da ka watsa min takardun mu, sannan ya tafi dauko umma.
Koda ya dauko ta mun kwana biyu da ita, har da Khadijah muka nufi Jidda, umma tayi ta bibiyar al'amarin mu, ko muna tare s
ai ta ga yadda muke waya dashi yasa hankalinta ya kwanta har zuwa ranar da aka mata aikin.
***
Tun bayan tafiyar Fareedah aka kawo mishi wasu jami'an tsaron masu kula da lafiyar shi, hatta itama Ishrah tana da su, haka bai ishe shi ba, sai da aka k
ara mishi da wasu jami'an sirrin na musamman, wa
ɗ
anda suka san aikinsu,kuma gwanaye a iya bibiyar rayuwar mutum idan aka saka su.
Ranar da muna cika wata daya da kawo Umma,. Ne muka nufi makka, muka yi Umrah Sannan muka wuce Madina. A can muka kw
ana biyu, sannan muka dawo gida Makka sannan muka tattara muka dawo gida, tun ranar da zamu dawo ya gaya mata.
Amma matan nan taki koda ruwan zafi ta dafa ma, lokacin da security da drive suka dauko
Kuma taki bada Umarni a dafa kome, tun kafi
n mu iso ya kirata. Ranar itama tasan cewa mijinta ya dawo akan Uwar shi.
"Halimatu ki tabbatar kin karbe su, Umma na ce da Khadijah. Don Allah ki amshe su hannu bibbiyu, sannan ki kula baa son taci abu me tauri, sabida idanun ta.
Bata bi ta k
anshi ba, ta kashe wayar. Kasancewa yau suna zama a majalisa, yasa hankalin shi ya rabu biyu. Kamar ya daka tsalle ya dawo gida, bayan an gama zaman ya taso zai dawo gida aka kira shi daga ofishin IG, akan an kuma ninka mishi jami'an tsaron, baya son haka
amma dake yau anyi magana akan rashin tsaro da kuma samun labarin da aka yi akan wasu yan garkuwa suka kama wani dan majalisar ta kudancin kasar, yasa ya amince da jami'an tsaron.
Yana fitowa ya hango su, dan haka suka zama kamar tail din shi, yana
jefa kafa suna d'agawa, haka suka isa gidan, yana ganin Umma kamar yaro karami haka ya kwantar da kanshi akan cinyarta. Murmushi yayi sannan yace mata.
"Umma kun iso lafiya? Ya hanya? Da fatan anyi aikin lafiya" cire madubin tayi sannan tace mishi.
"All
ah ya jagorancin al'amarin ka, Ubangiji ya kare ka."
"Amin Ya Allah Nagode sosai Ummana."
Kallona yayi yaga ina latsa wayata.
"Slut how are you?" Murmushi nayi domin kalmar baya da dadi, kura mishi ido nayi kafin nace mishi.
"Alhamdulillahi!
Mun same ka lafiya?"
"Alhamdulillahi" daga haka na mike tare da nufar dakina, na kwanta. Hala Ahmad ya manta igiyar auren shine a kaina? Da yake kirana karuwa! Meye nayi mishi da zafi haka? Meye na tsare mishi yana mijina amma yana kirana da sunan karuwa
?
Had'iye kwallar da ya zubo min nayi,.ina kwance ya shigo.
"Ki fito ki dafa mata abinda zata ci!"
"Baka ga kofar kitchen
ɗ
in a rufe bane?"
"I don't care, ki taso ko nazo na sauke b'acin raina akanki mara mutunci"
Tashi nayi a hankali,
domin Umma tana gidan, dan haka na nufi hanyar waje, na samu ya bude kitchen. Akan lokaci na daura abincin, dake ba'a son taci abu me sauri dole na daka mata sakwara da miyar ganye wanda yaji egusi da kifi, dake an Cigaba akwai abin kirb'a sakwara, da shi
na yi kome, sannan na kai dakin da take na baki, ashe matar gidan bata nan, dan haka har muka gama, bata dawo ba ban yi zaton zai iya cin abincina ba, domin koda kuma yi azumi a can kafin mu dawo Abuja, baya cin abincina, karfi da yaji ya saka umma shiga
kitchen itama kuma dake tana son haka sai tace wai na huta bana jin kwarin jikina, dan haka tayi ta had'a min wasu abubuwan tana bani a gabanta wai ko zan kara kuzari, wannan dalilin yasa bai tab'a cin abincina ba.
Yau din maganin Umma ne yasa shi ams
ar abincin har ya ci, duk da kamat ranshi baya so. Dakyar yayi loma bakwai ya mike, tare da nufar ban daki yayi ta kwara amai, wani irin tsanar yarinyar yake ji har cikin zuciyar shi. A duk lokacin da ya ganta zafi yake ji kamar zai kona mishi zuwa.
Shi yasa ko da yaushe yake kara nisanta kan shi da ita, haka ya gama ya fito, sannan ya zauna tare da fara aikin shi yana mamakin yadda Umma take ina ina da ita,.hatta Khadijah itama haka take mata..
Karfe bakwai na dare Ishrah ta dawo,.yana cike da
ita. Tana shigowa ta same shi rike da jarida.
"Ahmad"
"Daga ina kike?" Juyawa tayi tare da dubawa da wa yake? Taga babu kome maganar shi ya dawo da ita daga duniyar tunani.
"Meye na saka ki? Har ni zance ki dafawa Mahaifiyata abinci gata a hanya, Ish
rah ki saka kafa ki fita sannan ki rufe kofar kitchen
ɗ
in? Zaman waye kike?"
"Ahmad! Ni kake wa fada akan wata can?" Cikin fushi ya mike tare da takowa gaban ta.
"Kike ce me? Uwar tawa ce wata can?"
"Eh an gaya mata wata can sai me? Uwarta ka da
ta tsane ni? Uwarta ka da ta hanani zaman lafiya da kai, ita uwartaka ta gwal..." Marinta yai tare da nuna ta da yatsa.
"Baki isa ba, wallahi baki kai ba. Bar ganin ina lallab'a ki, kice zaki min yadda kike so ba zan dauka ba, karki sake ki zagar min uwa
. Domin ni ban zagi naki ba, akan me zaki zagi nawa? Meye Mahaifiyata ta miki? Na zata zan samu nutsuwa dake akan Mahaifiyata ashe sakarcina nake. Toh nake ba duk macen da zata zauna dani dole ta kaunaci Uwata idan ba zata...
🤷🏽
♀
️
Kishi a tsakanin zubda
jini isn't free, if you need chat me.
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank!
+2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
9/1/21, 3:19 PM - Buhainat
😝
: 39
"Eh mana! Dole ka fadi haka domin ka samu k
aruwa tana daura ka akan abinda ba shine ba, ita kuma tsuhuwar banza tana can a gefe.. kuma tunda ka mare ni wallahi dai na fanshe akan kowa, karka