Showing 69001 words to 72000 words out of 170719 words
alkhairi, ranar da Aishafareeda ta cika kwana uku, suka dawo.
Har gidan tazo ta kawo mata tsaraba ta tambayi ya jikin Khadijah, sun tab'a hira kafin ta bar
gidan, Hajiya ta gaya mata an mata miji dan haka g sadakinta.
"Akan me? Meye nayi miki Hajiya zaki amshi sadakina dubu goma? Ai ko rasa miji nayi kya amshi abu me daraja, bana son auren nan domin dole zaki min"
"Toh ai nasan da iyayenki suna raye ba
zasu min haka ba, amma tunda kin zabi abinda kike so Nagode"
Aikuwa ya fara kuka, dole na ajiye abinda nake ji na bata hakuri, sannan na ce ka hakura, amma sai na gyarawa mutumin nan zama.
Washi gari
Ofishin Jam'iyyar GDP na nufa, tun da aka samu d
amar hayewa gwamnati kome ya kare, zama nayi a gaban Daddy ina kuka tare da gaya mishi abinda ya faru.
"Toh Aishafareeda baki san kin girma bane? Kuma ai kema zaki ji nutsuwa a ranki, kiyiwa Hajiya Biyayya, domin tafi son kiyi aure sama da zuwa nan
da kike yi"
"Amma"
"Kiyi hakuri" ya dakatar da ita, yasan za a rina, domin bai zama dole ta amshi mijin da aka bata ba.
"Ki kwantar da hankalinki, idan aka yi auren sai na baki shawara sai a raba auren. Kinga ai ba za a ce baki tab'a aure ba ko?"
"
Eh kuma haka ne." Na kalle shi tare da murmushi.
"Tashi kije Allah ya tabbatar da alkhairi "
"Amin Ya Allah"
Fita nayi na barshi, sai da na bar shi ma na tuna kamar yana cikin damuwa. Komawa nayi nayi, tare da zama ina kallon shi.
"Daddy meke damunka
?"
Ajiyar zuciya yayi sannan yace min.
"Babu kome"
"Da kome mana, ai ba haka kake ba, ko baka da lafiya ne?"
"Lafiya lau"
🤷🏽
♀
️
Kishi a tsakanin zubda jini isn't free, if you need chat me.
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank!
+23470
35133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
8/30/21, 10:06 PM - Buhainat
😝
: 34
Mikewa nayi da na fahimci baya son magana na bar mishi ofishin, amma duk wanda ya kalle shi, ya san yana cikin damuwa, kuma damuwar bata boya ba
.
...
Kiran wayata ya sani lallubar wayar, Khadijah na gani.
"Yan mata"
"Umma na son ganinki"
Ta kashe wayar," gidan na nufa.
Tana zaune akan abin sallah.
Zama nayi ina kallon ta, kafin tayi sallama tana addu'o'in, tare muka shafa.
Ka
llona tayi tare da ajiye min abincin da yake gefenta.
"Ci sai muyi magana!" Ba musu na fara ci ina jin kwalla na zuba min.
"Me yasa kike kuka?"
"Ba Hajiya bace zata min auren dole"
Na fada bayan na cire hannuna a cikin abincin.
"Toh me yasa baki fito
da mijin ba? Kinga da ba zata miki auren dole ba"
"Umma ko na samu mijin bana samun wanda zai dace da rayuwata, umma bana jin dadin yadda nake rayuwa, amma kuma dole na samu wanda zai iya tankwara ni, idan na samu yake sona zan iya saka shi a damuwa."
"Kamar ya?" Ta tambaye ni,
"Umma, nayi rashin jin da zai saka kowa ya guje ni, duk wanda zai aure ni ba karamin jahadi yayi ba, amma wani abu daya da nake da yakinin akan shi duk wanda zan aura zai kasance mutum ne da yake da ra'ayin kanshi wanda zai zam
a shi yake juya ni bani nake juya shi ba.
Wanda zai fifita dangin shi sama dani, wanda yake sauraron damuwar nashi, idan na samu wallahi zan zauna, amma matukar wanda na samu bai da wannan halin toh ni zan juya shi.
Gashi can ta amshi kudin wani tsoh
o can,.salon na sauke kan mutumin kawai"
"Idan baki manta ba, kin tab'a min alƙawarin duk abinda na fa
ɗ
a zaki min?" Ta fada tana kallona. Jikina ne yayi sanyi na rike hannun ta.
"Na tuna!" Na fada a raunane..
"Toh insha Allah ba zaki yi danasanin aure
n da zaki yi ba kinji." Na gyada mata kai.
"Allah yayi min Albarka" a hankali na mike tare da barin gidan.tun daga ranar ban kuma zuwa gidan ba, sai dai maganar auren ya dake ni musamman yadda ake ta rurrufe al'amarin, nakan zauna nasha kuka, domin
nasan da iyayena suna raye ba zasu min haka ba, Hajiya kuma ta gaji dani.
Dan haka nayi wani irin sanyi, saura sati biyu aka turo min yan uwa Ummin su gyara min jikina, tunda suka fara na ajiye zuwa ko kofar gida, sannan abinda yake sani kuka yadda
angon bai zo ba, muka bai damu da yazo ta ganni ba.
**
"Lallai zaku aikata kuskuren da zai sanya ku, a damuwa duk inda ya dafa Allah yana tare dashi. Karku mai dani mutumin banza mana, taya ina aiki tsawon shekaru ashirin da daya, yau kuce zaku fit
ar da bukatar ku, toh bari na gaya maka. Daga ranar da kuka isar da bukatar ku, wancan gawar zai fadi, idan kuma haka ya faru, kun ringa rasa damar ku kenan.
Ce muku aka yi yana son mulkin ne? Cusa mishi kaunar abun nayi, kuma idan kuka sake kishi ya za
ma a tsakanin zubda jini, kun gama domin zaku fadi.
A lokacin da kuka sake ya fita daga daurin gwarmai da kuka mishi zaku gane baku da hankali, fitar min a gaba"
**
Tunda ya samu Ishrah ta bar kasar, da mahaifiyarta da Yayunta, hankalin shi yayi g
ida. Sai aikin da ya rike shi da aiki yayi dan haka yana gamawa, yayi daidai da hutun da suka samu. Sakamakon watan azumi da yazo .
Dan haka koda suka yi waya da Ishrah tace ba zata samu dawowa ba, sai sunyi Umrah sati biyu sallah zata dawo, dan h
aka ya kame kanshi, ban da kula yan mata. Kuma kar ya kuskura yace zai tafi gida.
Haka ya ce mata toh, yana gama abinda zai yi yaji a ranshi zai tafi yayi Sallah a gidan Umma.
Karfe bakwai ba dare ya isa gida, yaki tafiyar jirgi mota ya biyo, da
n haka yana isowa, gidan iyayen Zakaria. Kayan da yazo dashi ya sauke musu, sannan ya zauna yaci tuwo miyar kuka ba karamin dad'i yaji ba.
Sunyi hira kafin ya bar gidan, Umma tana tsaka da addu'a yayi sallama, a sallama. Kirari ta shiga yiwa Ubangiji
, tana kara godiya a gare shi. Kafin tayi sallama.
Bude mishi hannu tayi, ya karasa gabanta, ya kwanta akan cinyar ta, yana murmushi.
"Umma haka kawai naji ina kewar ki, Umma don Allah kiyi ta min addu'a."
"Bayan manta umma da aka yi na tsawon wat
a kusan tara? Dan haka Umma bata tab'a gazwan ba, akan ka"
"Insha gobe zaku koma sabon gidan mu "
"Nan kuma fa?"
"A saka yan haya"
"Toh Allah yayi maka jagora"
"Amin Ya Allah."
A daren ta mike ita da Khadijah, dashi suka shiga aikin had'a kay
an gidan, gefen Salim suna shiga anan suka ga wani abin da yasa suka kasa tab'a kome.
Wato wani irin abu kamar doll na itace aka sassaka aka saka a bakin kofar shiga gidan, sai kuma tulin kashi da aka zuba yana tsutsa.
A daren Umma ta je ta k
ira Malam Babba, shi da Almajirai suka karya abun bayan sun saka mishi wuta, hayaki ya tashi sama.
"Insha ALLAH, gobe zamu yi saukar Kur'ani, Malam Ahmad. Kana tare da idanun al'umma, gashi ita Mahaifiyar ku baku bata kulawar da ya dace ba, ban san m
eye damuwar mutane akan ta ba, Lokacin da Allah zai bata ku bai yi shawara da kowa ba, amma ita yanzun bata isa moran abinda ta haifa ba? Kayi sakaci da har aka samu damar sarrafaka, dan haka zaka zauna a nan hAr sai anyi sallah zaka tafi.
Insha ALLAH
zaka ga fa'idar haka, sannan ka shirya Insha nan da kwana biyar, akwai abinda zaka samu, gidan nan kan ki barshi domin duk wani abinda kika nima kika rasa a gidan nan aka fara, dan haka ku barshi ko haya kun saka."
A daren suka rufe shashin Salim,
kayan gidan ma basu dauki kome ba, domin malam ya gaya musu karsu tab'a kome. A daren suka koma gidan Ahmad da ya gina a g.r.a,
Washi gari. Umma ta saka shi a gaba har gidan Malam, aka bar Khadijah a gidan, tunda suka isa gidan, ake saukar Alqur'a
ni, har kusan karfe biyu na rana, sannan aka yi yanka, bayan anyi sadaka.
"Insha ALLAH kuna isa gida, ki murza wannan ki bashi a cikin ruwan addu'o'in nan ya shafe jikin shi da shi, ba mutum ba ko aljani sai ya bar shi a gurin. Insha ALLAH kome zai da
wo daidai."
Sannan suka dawo gida,. aikuwa tayi mishi abinda aka fada ya shafe jikin shi, tare da maida kayan shi. Can kuwa ya fara amai. Sosai kamar zai yi aman kayan cikin shi. Kafin ya kwanta a gurin.
Wani aikin sai Uwa, umma ce ta kwashe ta gy
ara gidan, sannan ta dafa mishi abincin mara nauyi, tayi sallah la'asar. Tana addu'o'in ya farka ya shiga ban dakinta yayi alola, tare da fitowa ya gabatar da sallah La'asar, anan suka yi addu'a, bayan ta idar ta kawo mishi abincin. Ya zauna yana ci yana k
uka. Domin abubuwan da suka faru yana dawo mishi. Wayar shi ce tayi kara. *Salim*
"Ina ka shiga ka manta da Umma?"
"Bana Nijeriya ne, ina bangkok. Akwai matsala ne?"
Nan ya kwashe kome ya gaya mishi.
"Amma yaya wallahi da zan tafi ba dauki kome na bawa
Adamu, domin bayan mun zo Lagos da kwana biyu, yazo na bashi sako ya kawo mata, har da katin atm din da ka bani! Sannan da nazo nan kwanana biyu wayata tab'ata, sai yau Allah ya taimaka muka hadu da Ishrah. Sun zo tokyo na amsa, shima sai da Mahaifiyar ta
, ta saka baki taba ni, amma babu kome wallahi "
Nan ya mika mata wayar suka yi magana da Umma, baiwar Allah nan addu'o'in take ta zubawa Yaranta, tare da musu Uzuri"
Sun yi hira bayan nan ta mika mishi wayar , ya kira mata Nuhu suka gaisa, tar
e da jajjanta abinda ya faru na rasuwar Zakaria, bayan sun yi magana da Rukayyah.
Bayan sallah isha Umma tace.
"Malam Ahmad, gashi nan ka tafi ku gaida tare da tambayarta meye zata yi na bikin?"
Ta mika mishi Number Aishafareeda, karb'a yayi ya
na kallonta.
"Ince inji?"
"Eh" ta bashi amsa a gatse.
"Toh" mik'ewa yayi tare da fita ya kira Number, sun gaisa a mutunce. Har tayi mishi kwantaccen gidan su, ya shigo motar shi ya tawo har kofar gidan. Mamaki ne ya kama shi.
"Toh Hajiya wa zata yiwa a
ure? Kar dai Salim?" Kiranta yayi bayan ya fito daga motar, yana jingine, dake babu wanda yasan ya shigo gari, sai Bagauda da ya kira ya gaya mishi, amma zai zo duba shi.
Bayan ya kiranta, can ta fito da katon hijab
ɗ
inta har kasa. Kallonta yayi lok
acin da haske ya haskata. Mamaki yayi dama tana nan.
Tun zuwan da tayi Abuja ya manta da kasonta. A hankali ta iso gurin shi.
"Uwar Daba da karuwai?" Shiru nayi ina kallon shi kafin na d'ago kai nace mishi.
"Meye ya kawo mijin tace gidan mu, raggon
maza wanda ya rako maza duniya"
"Karki min rashin kunya? Dan ba sabon abu bane, a gurin ki ai kinsan waye ne?" Ya fada kamar zai buge ni.
"Ai kato da gora ne?"
"Kina Cross limit!" Ya fada kamar zai bangaje ni"
"Ok da zafi ne?"
"Zan ci mutuncin ki"
"Sai dai muci mutuncin juna"
"Meye had'aki da Mahaifiyata?" Ya tambaye ni, a zafaffe.
"Ban sani ba" na juya zan shiga cikin gida yace min.
"Idan ma wani abu kika mata ko ki kunce, domin sai na b'ata fuskarki da yake saka ki jin kanki!"
"Ko daya
ni barazana baya bani tsoro, kawai kayi kuka da abinda zai samu Ishrah mana." Ina fadar haka na juyawa ba bar shi a gurin.
A fusace ya isa gida. Ko zan bai yi ba yace.
"Umma! Meye ha
ɗ
in ki da ƙaruwar yarinyar nan? Idan ita zaki aurawa Salim, toh
wallhi yarinyar babu abinda bata aikata ba!"
"Ba salim zan aurawa ba, kai ne zaka aure ta" kamar saukar aradu yaji kalmanta, kamar an tarwatsa mishi zuciya. Jiki a sabule ya kalli Umma.
"Duk matan garin nan a rasa wacce ta dace dani sai karu..."
"Ba z
an maka dole ba, amma wannan karon xan zare hannuna a kan ka, ba kai
ɗ
aya na haifa ba. Ba zan kashe kaina akan ka ba. Sannan kuma kace zaka juya min baya ba, idan Ishrah ce ta haife ka, ka tafi bana son abinda ka bani, yau zan bar gidan nan, idan kuma nic
e na haife ka toh ina son ka auri Aishafareeda da budadden zuciya."
"Na amince" ya fada tare da ayyana yadda zai zab'a mata rashin mutunci.
.... Ina shiga gida ba birkice musu da tambayar su waye mijin da xan aura.
Umar da shigowar shi kena
n, yace mata.
"Ahmad Bala Raees sanata."
"Wayyo Allah na, wallahi ba zan aure shi ba, Hajiya don Allah ki aura min Umar da na auri wancan me zubin samudawa"
"Ai baki isa ba, wallahi ba zan aure ki ba, ke dan bakin ciki Ni da nake shirin fara zuw
a gidan sanata zaki min bukulu, wallahi aure an gama"
Kuka da ihu da birgima bayi shi, Aunty Aina'u Kanwar Ummina ne taji haushi bata san lokacin da ta dauki wayar caji ta shiga tsula min ba.
"Zaki kashe ta ne? Taji da bakin i shekaru ashirin da wani
abu mana, tunda aka saka auren nan baiwar Allah nan take tarradin abinda zai kawo tsaiko a auren ke har kin isa hana ayi auren? Insha ALLAH Ahmad kin aure shi sai dai ki mutu!"
Naci duka domin bata bari an karbe Ni ba, sai da jikina yayi laushi. Ranar
kwana nayi da zazza
ɓ
i, washe gari aka kai ni asibitin.
Ranshi yana can yana shirya yadda zai ci mutumcin yarinya,yadda ya shiga jikin Umma sai ya ga gatan ta...
*Sorry akan typing error*
🤷🏽
♀
️
Kishi a tsakanin zubda jini isn't free, if you need c
hat me.
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank!
+2347035133148 or 08130269641 Yan Nijar ga Number da zaku biya: +227 84 50 64 76
Anya kuna tare da labarin?
🤣😂
8/31/21, 5:26 PM - Buhainat
😝
: 36
Kawai ina pretend ne amma ni kadai nasan abin
da nake ji, haka aka yi yar karamar liyafa,. Unguwar mu, wanda matasan unguwarmu suka shirya min.
Gurin ya kawatu kuwa, domin duk wanda ya ga gurin sai yayi Magana. Bayan sallah isha, dangin Ummina suka min nasiha Hajiya kamar ta san nufi na tace
min.
"Nana A'ishatu! Don Allah ki zauna a dakin mijinki idan kika min haka kin gama min kome, nasan kina da kudiri a ranki, zaman ki da Ahmad shine kwanciyar hankalina karki manta tun kina yarinyar kike abinda kike so ban tab'a hanaki ba, yau ina rokon ar
zikin ki. Ki zauna a dakin auren ki."
Rike hannun ta nayi hawaye na zuba min.
"Insha ALLAH!" Na fada mata ina kuka. Haka aka fitar dani har mun iso waje na koma dakin da gudu na fada kanta, ina kuka. Dakyar aka d'agani a jikinta, ina son hajiya. Yau
da aure zai rabani da ita sai naji kamar yau aka kawo ni gurinta.
Umar ne ya riko ni tare da saka ni a motar da Ahmad ya turo na dauka na, sannan yan uwan Ummina da na Abbana suka shiga, aka nufi da ni gidan shi da yake g.r.a, muna isa aka wuce da
ni shashin Umma, cikin farin ciki ta mike tare da saka hannu ta amshe ni.
"Shigo da kafar dama, Haske" haka na shigo ta kai ni har bakin gado tana fa
ɗ
in yi addu'a kafin ki zauna" nayi sannan ta zaunar da ni.
"Ki hakura da kukan haka," wani irin dad
'i dangina suka ji, domin ba su zata yadda ake gaya musu akan Umma ya kai haka ba, dan haka suka ce mata.
"Hajiya ga Yarki mun kawo miki, da fatan ,zaki riketa kamar yar cikin ki"
"Insha ALLAH" ta fa
ɗ
a tare da kallona tana murmushi, haka suka tafi suka
Barni da ita, basirah da Khadijah ne a dakin, toh bani da kawaye. Haka muka kwana, gurin karfe uku na dare. Nayi mafarkin wai ana ta bin mu, dakyar muka kwace a hannun wanda ya ke bin mu, muna tafiya motar mu ta kama da wuta. A firgice na farka tare yin
addu'a.
Sak irin mafarkin da yayi kenan, shima ya tashi..abinda yazo mishi ya shiga ban daki yayi alola tare da daura sallaya ya fara sallah nafilla.
Nima haka, ina cikin sallah Umma itama ta shigo taga ina sallah fita tayi. A ranar babu wanda
ya rutsa sai bayan sallah Asuba wajen karfe shida bayan na idar da azkar da karatun Alqur'ani. Haka ya saka umma kara yarda da auren sha'anin Ubangiji ne, ba shirinta bane.
Da safe ya shiga falon Umma ya gaishe ta, yana zaune.
"Umma yau zaku
yi wani sabon abu ne?"
"Eh toh budan kai ne" ta bashi amsa.
"Haka toh bari na gani" ya fada tare da mik'ewa ya fita, zuwa can kuwa ya dawo da kudi ya ajiye mata.
"Abinda zaki bukata"
"Toh Allah