Showing 42001 words to 45000 words out of 79609 words

Chapter 15 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1091

yardar Allah, ki kwantar da hankali duk wani tashin hankali da za mu nuna ba shi ne zai bayyanata ba na mu kawai addu'a ne, ba na ji an ce sun kira shi mai sunan Baba? To mu jira mu ji daga garesa abun da suka ce.''

'' Kai! ?an Innatai wallahi fita sabgar wannan miskilin Asadu Win, ba ka san shi ba ne da ta kaici zai iya kaika yanzu fa kafin ku shigo, su ka yi waya da mutane amma tsabar gwaninta irin ta shi, ko ya tsaya ya yi mana bayanin abun da ake ciki haka ya haura sama ya bar mu cikin kokonto, ba mu san a wane hali Yarinyar nan, take ba.''

'' Innaya ki yi ha?uri kin ga yanzu fa ya dawo ?asar a kwai gajiya da zaman jirgi da ya kwaso so yana bukatar hutu ne....''

'' Kai! Ashrafu rufemin baki wane hutu kuma an sace Mai suna? Kuma duk shi ne sila nifa na daina ganin laifin ta tun da na ji daga ina matsalar take, Kai amma Allah waddaran kama don duk kama ce ta janyo ma ta kamarta da suka kani da Asadu Win duk shi ne ya janyo mana wannan fitinar. Allah sarki yanzu ko a wane irin halin take.''

Jikin kowa dake wurin ya yi sanyi ?alau duk kannin su suna tausayawa akan halin da Dagori ke ciki Abbi ne ya Wan gyara zamansa ya ce. '' Yanzu dai zancen maganar police duk babu ta a ajiye ta a gefe tun da har Allah ya yi Asad ya dawo to na tabbatar cewa Mai babban suna ba lallai ta sake kwana wurinsu ba idan kuwa ta kwana to ina sa ran zuwa gobe ta dawo garemu.''

Baffa da ya Wan samu nutsuwa da zancen Abbi ya ce '' To Allah dai ya bayyana mana ita.'' Don ya kawar da zancen ya ce.'' Yanzu gobe yaushe ne Waurin Auran? Kuma nawa za a fara Waurawa cikin su?."

'' Haba dai Hamma ai zancen aure kan babu shi sai mun ga an somo Mai babban suna tukuna. Ai ban da wannan da tuni gidan nan, ya gama cika da mutane to dai mun sa an dakatar da shirin komai har sai ?ura ta lafa.''

'' A'a samm ba a yi haka ba Waurin Aura na nan, kamar yadda a ka saka shi don wannan ba zai sa a Waga ba, ai sai a yi harakar ?aranta kawai a yi duk abun da aka tsara, in sha Allah Mai babban suna za ta bayyana.'' Baffa ya faWi aransa yana jin daWin ganin duk yadda suka bi suka damu da gudan jininsa. Kuma ya san cewa, kara ce kawai za su yi masa ba wai don ransu ya so ba.

'' Amma Hamma ai ....'' Bai bar sa ya ?arasa ba ya Waga masa hannu.

'' In dai na isa kuma na kai na saka to a yi yadda na ce; Aure ba fashi muddin muna numfashi.''

'' Amma Hamma ai sa.....''

'' A'a Asiya kada ki ce komai, abun da Malam ya faWa shi ne ya da ce don Satan Dagori bai kamata a ce an dakatar da Auran ba. A ci gaba da komai kamar farko.'' Nene ta yi saurin taron numfashin Mami da ke shirin magana.

'' Eh to gaskiya Abubakar Wan Uwanka ya fika gaskiya zancen a jiye bikin bai ta so ba. Amma, duk wasu biWi'a da aka Wauko to a soke su, a dai Waura Auran kawai sai walima cikin gida hakan shi ne ya da ce...'' Innaya ta dakata da maganar saka makon kukan da Maamah ta fashe da shi.

'' Ni gaskiya ba wani Aure da za a Waura har sai an ga Sister na haba dan Allah ta ya a ce Sister ta Sata ba a san halin da take ciki ba kuma ace za a yi wani biki ni dai ban amince ba.''

'' An shi nan na ce da ke, kin ji ko ja'irar banza wato mu za ki nuna wa bariki ? Ka ga munafurci wurin Yarinya to bari a yi na shi Ashraf sai ke a bar na ki sai har idan an ga Mai suna.''

'' Ni fa Innaya ba haka nake nufi ba.''

Dariya ku san duka mutanen wurin suka yi don kan ta ba su dariya......




Kwana biyu bana online sakamakon number ta da ta daina Whatsapp ina mi?a sakon godiyata zuwa ga WaWannan mutane da suka nuna min ?yauna na rashin ganina har suka kira su ji ko ina raye=??=?O?=?O?=?O?

Yayanmu
Mrs Naseer
Abubakar seleee
Mazurari
Ke ma ban manta dake ba M N S na ji sakon gaisuwar ki ina matukar godiya kuma na ji daWi sosai da sosai =?O?=???


Comments
Like
Share
Taku dai mai kaunar ku har kullum
MRS AWWAL =???


*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*=???
'?
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i.'?






027




Da hasken fitilar wayarsa ya samu nasarar kunna wutar Wakin ba wani haske ne da ita ba amma kuma ta taimaka masa wurin ganin abubuwan da ke Wakin room ne, mai kama da laboratory farin ?yallen da ke lumluSe ya yayesa take wani ?ayataccen table ya bayyana, wanda ke Wauke da na'urorin zamani na bincike, da kayan aikin kimiyya na zamani. Handkerchief ya ciro ya shiga goge kujerar da ta yi kura kafin ya zauna Cikin ?warewa da sanin maka mar aiki ya fara sanrafa supercomputer Winsa cikin minutes da baifi 15 ya samu nasarar abun da yake nema wani ?ayataccen murmushi ya yi wanda ya fito da zallar ?yansa irin na Fulanin asali, a fili ya furta

''Mashkur, you ve moved too far. Now you ll realize what it means to mess with someone s family and it won t be easy to undo ka yi naka wasan yanzu ka jira nawa ya zana nan zuwa.''



*************
Kamar yadda Baffa ya bu?ata haka aka yi washe gari an Waura Aure, ba tare da wani jinkiri ba sai dai ba wani shagali ko wasu abubuwa da aka shirya kamar, daga farkon don halin da ake ciki. Iya Malamai Mata aka gayyato suka zo suka ba je kulin wa'azi wanda ya matukar ?ayatar kuma ya saka, zukatan al'umma, cikin nutsuwa da dare a ka kai Amaryar gidanta wanda tasha na sihohi. Haka shi ma Ashraf an Wauko masa Amaryarsa aikai masa gida, sai dai muce Allah ba da zaman lafiya.

Nene, da Baffa kuwa freestanding kawai suke amma suna cikin tsantar tashin hankali, wanda bai misaltuwa. SaSanin Habu da Innaya da kullum cikin kuka take wata kalar so take yi wa Dagori duk da kuwa ta san, ba ne tun Farko amma tun bayyarar su take jinta har cikin ranta. Ga shi har zuwa yanzu Asad bai ce da su komai ba, duk kuwa yadda suke a ?age da susan halin da take ciki. To ganinsa ma wahala yake yi ma su balle ta kai ga su yi wata magana akan hakan.

Cike da tausayi Salame ke kallo Nene da ta kusa 2hour a zaune tana Addu'a, tun bayan da idar da sallah Azahar ga shi, har La'asar ta taddata tana wurin zaune. wanda ko shakka babu duk Addu'a take a kan Allah ya bayyana Dagori. Aranta ta ce. '' Allah Sarki Uwa kenan, ita ce mai shiga damuwa akan damuwar ?anta haka kuma ta shiga ?unci a duk sa'in da ya yi nisa da ita. Uwa ce kawai ke yi wa ?anta Addu'a ta manta da kanta, a wurinta ne kawai ake samun soyayya chikakkiya wanda babu garwaye a cikinta, ita ce ke nuna farin ciki zallar a duk sanda Yaron ta ya samu cigaba na rayuwa, Allah ba mu ikon kyautatawa tsakanin mu da iyayanmu."

Turo kofar da aka yi ne ya sa ta Waga kai don ganin waye Mami ce; a bayanta Yar aiki ce, hannunta Wauke da tire na abinci tsakiyar Wakin ta ajiye tare da Waukar Filet ta zuba ma su abinci daidai Mami na zama kan kujerar three seater da ke Wakin, sai da ta gama ta ajiyewa kowa a gabansa tare da ruwa da lemu kafin ta fita.

Lura da Nene ta yi kamar Mami na son ta yi magana da ita ya sa ta tsagaita a Addu'ar da take.

Salame ta ce. '' Ina yini Mami?."

Murmushi mai kyau Mami ta yi kafin ta ce. '' Lafiya lau ya gajiyar aiki jiya na ga kin sha aiki sannu da ?okari?."

Ita ma dai murmushi ta yi. '' Haba Mami sai ka ce na yi wani abu.''

'' Wani abu ne mana ai kin yi ?okari. ''

'' An yini lafiya?.'' Nene ta faWi cikin dasanshiyar murya.

'' Lafiya lau Yaya ina yini? Ya?." Mami ta ba ta amsa tana ?ara karantar yanayinta cike da tausayawa.

'' Lafiya.''

'' Na ga tun safe ba ku fito ba, an ce ko kayan karin da aka kawo kamar ba kuci komai ba? sai yanzu da nake fotowa don na Wan haura sama ina gyara abubuwan da aka yi jiya nake samun labarin wai ba ku ci abinci ba? Yanzu ke Salame ai ke ce ya da ce a ce kin je kin Wauko abinci ko har yanzu bakunta ki ke?.''

Salame dai ba ta yi magana ba, don sai take ganin ko dai Mami ta manta cewa suWin Fulani ne don tun zuwansu ta lura kamar a kwai ta zara da banbanci mai yawa tsakanin rayuwarsu kamar wata duniyar ne ta je ta daban irin yadda suke gudanar da rayuwar su kamar da kwai banbanci wai ?a da Uwa su zauna, ?ugu-?ugu akan kujera Waya har fa rungumar juna ta ga suna yi ita ko yaushe za ta iya wannan ne. Tana Yar musulmi, acewarta.

'' Yaya dan Allah ki ragewa kanki damuwar nan, in sha Allahu ta kusa dawowa garemu don ana kan bincike ne, kuma na tabbatar, tun da Asad ya saka hannu a ciki komai zai zo da sau?i in sha Allah. Ki kwantar da hankali, dan Allah kada wani abun ya zo ya same ki.''

Mami ta faWi cikin salon kwantar da hankali.

'' Uhm.''

Ta sani cewa akwai ciwo da damuwa a ce an sace Wanka ba tare da ka san a wane hali yake ciki ba.

'' To Allah Allah yanzu ki samu ki ci abincin nan.''

Nan ma dai kawai ta ce da ita '' Uhm. '' ba za ta matsa ta ba ko ta takurata hakan ya sa ta mi?e ta fita.



*************

Cikin kwanaki uku kawai, Dagori ta fita daga hayyacinta kallo Waya rak, za ka yi ma ta ka san cewa tana cikin matsanancin hali, ba lallai a kallon farko ka iya gane ta ba ta yi wata irin muguwar rama dama can ba wani naman girki ba ta yi ba?i. A kallon farko za ka za ta ko mahaukaciya ce don yanzu Cizo ya sauya ma ta Waki ya kaita wani Wakin wanda babu komai cikinsa face tarkacan kaya marasa anfani Wakin bai da maraba da bola wato juji.


Kwance take ?asan Wakin wanda kura da yana na gama cika wa rigar jikinta ba ma lallai ka iya gane wace, kala ba ce tsabar kura da dadti gashin kanta kuwa da yasha gyara ya hargitse, ban da kura da ya kwasa ba za ka gane wane kala ba ne.

Birgima take a kwance a ?asa hannunta dafe da cikinta wanda idan ta taSa hatta sawun awazunta tana iya jinsu wanda take da tabbacin da za a, tsaya da kyau tabbas za a iya ?irgasu, yunwa da ?ishirwa duk sun bi sun ?assara ma ta jiki.

Hatta ?warin da ke cizonta ba ta da ?arfi ko, kuzari korar su har tana mamakin ko me suke samu a jikin na ta ne, da suke faman ciza. Haske ne ya dallare ma ta ido, wanda ya maye ma ta gurbi da duhun Wakin. Amma samm ba ta da kuzari iya Wagowa balle ta kalli mai shigowa.



****************

Cikin kwarewa da sanin makamar aikinsa yake sarrafa supercomputer Winsa, duk tsawon wannan lokaci ko, kwanani ko kofar gida baya zuwa yana Waki yana gudanar da aikin da ba dare ba rana, ko abinci ba wani samun lokacin cinsa yake ba sam bai da wani hutu sosai koyaushe yana kan aikinsa wanda ku san daman, duk wani rabin rayuwarsa ya shafesa ne a kan sa. wata ?aramar na'uwarsa ce ta yi ?ara, tuni ya sake nutsuwa tare da gyara zaman Bluetooth Winsa .


*************


'' Hhhhhhh shegiya ta RUGA an ji maza yanzu ke ce kika dawo haka? Lallai ashe daman duk wannan tsiwar ta ki akwai maganinta? An shi.'' Ya faWi yana jefa ma ta ledar hannun sa a jiki. '' Dan Ubanki bread da ruwa.''Amma ko motsi ba ta iya yi na kirki balle takai ga ta iya ci.

Wayarsa ce ta yi ?ara ya Wauka ganin ba ta motsi, ya Wauka bacci take. Ya Waga wayar. '' Hello sai Oga. ''

Da yake wayar a speaker take ana iya jin me na cikin wayar ke faWi. '' Cizo Ka saurare ni da kyau ka ji abun da, zan faWi ma. Tun da shi wancan Wan iskan Yaron ya ?i yi mana abun da muke so, to zan ba da jinin Yarinyar nan ga ?ungiya wanda na san muddin na yi haka zan, samu ?arin matsayin. Wanda kuma shi ne tsani akan samun nasarorin na nasiyasa.''

'' Ai kuwa Oga hakan shi ne daidai domin Yarinyar nan, ta ishe ni, don gudun ma nake ta Saras, kamar alamu sun nuna, ta kusa margayawa.''

'' To kada ka damu yau ne kwananta na ?arshe a duniya, idan ka yi ha?uri hours da suka rage ma tare da ita, ?alilan ne. yanzu, ina son anjima da dare ka Waukota ka kawo min ita a nan, gidan gonata daga nan kuma sai barzahu.''

A tare suka she?e da wata iriyar dariya daga nan ya fice daga Waki yana rufa kofar.

Wanda bugun kufar ya tafi daidai da zubar hawayen Dagori, da ta gama jin komai. Ba ta da karfin iya yin kuka don babu wani kuzari tare da ita. '' Ya Allah ga baiwarka Allah ka kawo min mafita, cikin sau?i. '' Ta faWi hawaye na sake sulalo ma ta..............





Masoya chakwakiya ke nan wannan lamari to koya za ta kaya ku biyo ni don jin yadda za ta kaya.

Dan Allah ku nuna min ?auna ta hanyar sharing da like comments ko ba ku son channel Wimu yaje Barrel ne?

Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???

*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*=???
'?
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i.'?







028






'' Ya zama dole na samu yadda zan gudu daga wurin nan don ba zan zauna ba a yi kuWin jini da ni, Aradu wannan ba mai yiyuwa ba ne. Bayan duk tarin burukan da nake Wauke da su a ce; lokaci Waya an yanke min su. Ina sam wannan ba za ta saSu ba wai bindiga a ruwu. Yanzu wannan Ni! Dagori ai abun kunya ne a wurina a ce, ni ce kwance a wula?an ce duk ina kissata da iya mugunta,ta suka je ne? Har da zan bari wani Cizo ya yi nasara a kaina, Aradun Allah sai na nuna masa ni Win nan cikakkar Yar RUGA ce, don sai na koyar da shi darasin da ba a taSa koyar da shi ba. Idan har ban shayar da kai ruwan mamaki ba to daga yau, a canzan suna daga Dagori zuwa Dussa.'' Ta kai ?arshe magarta tana kwafa wada ko da a ce da wani a Wakin ba zai iya jinta ba saboda rashin ?arfi da kuzari.


Ta sa hannu ta janyo ledar da Cizo ya jefo ma ta wata irin wawura ta kai wa bread, tamkar shi ne, Cizo. Kafin a hankali ta Wan zame ta jingina da jikin bangon Wakin. '' Ai dole na ci ko don na samu ?arfin yakar wannan azzalumi, Aradun Allah duk wani zaluncin da ka min kai da Wan iskan Oganka.'' Ta faWi tana ci gaba da cin bread ta.



*************
'' Mashkur, ka tabbata messing with DSS agents is not a joke! Kai ka jawo distance ta zama closeness you brought me back when I had moved on. So, be ready& because this time, no mercy!.''

Ya danna maSallin ShadowLink, wata ?aramar na ura da ke bai wa jami an DSS damar sadarwa, ba tare da Soye komai ba. Ana Waga wayar ya fara magana, ba tare da ya jira wanda ya Waga ya yi magana ba.

'' Hello sir, I ve completed all investigations on my end. I ve gathered substantial evidence that can be used to arrest Mashkur along with his loyal supporters.''

" Well done. I m glad to hear that. Now, what do you need?."

'' I would like you to assign me three dedicated operatives to assist further.''

'' Kada ka damu listen for their arrival at any time abun da nake so so da kai ka wai ka zauna cikin shiri.''

'' Thank sar.'' Ya faWi haka ya yanke kiran mi?e wa ya yi tare Waukar wata yar karamar jaka wanda ya gama haWa kayan da yake bu?ata a ciki. Ya fito rufe kofar ya yi tare da danna na'urar kofar ta rufe tamkar, ba ta taSa wanzuwa a wurin ba. Kai tsaye toilet ya faWa ya kai ku san 1hours kafin ya fito jikinsa Waure da towel


Shirinsa ya yi cikin ?ananun kaya back ma su haWe da jacket sai rigar ciki da ta kasance white ya makutar kyau sosai, yana sanya takalmin sa ne Mami ta shigo.

'' Yau kuma ina zuwa haka?." Ba tare da ya Wago ba ya ba ta amsa.

'' Zan je wani assessment ne.'' Ya faWi daidai yana Wagowa.

'' Yanzu Asad har akwai assessment Win da ya fi kwato wannan Yarinyar daga, hannu waWannan azzalumi?.''

Sai da ya yi shiru na second tare da shafa sumar kansa wanda hakan kamar ya zamo Wabi'arsa, kafin ya ce. '' Mamina shi ma wannan aikin mai mahimmanci ne but...''

'' But what? Ka ga Asad hankali kowa da ke gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login