Showing 9001 words to 12000 words out of 79609 words

Chapter 4 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1089

da su ke kuma mai baki ci sai ki ci ko? To duk wani salon ma?ircinki wallahi ido biyu nake kallon ki, ki yi gaggawar matsamin da wannan tuwon na ki dan ya fara hawamin kai, ya na hautsina min zuciyata dan na fara jin tashi zuciya, ko so ki ke na amaye naman da Borodin da na ci tsabar ba?in ciki w.....''

'' Kai Dagori kul na sake jin bakinka a wurin, kai Habu wane kalar rashin mutunci nake jiyo tana ?arewa matarka amma tsabar rashin sanin ciwon kai ya sa ka, ka sa Waukar mataki a gabanka tana faWawa matarka maganganu na rashin Wa'a amma ka zuba ma ta ido da kunnuwa kana saurareta.'' Nene da ta idar da sallah Isha'i ta k ta faWa cikin faWa.

'' Nene amma na ga laifin Salame ne na mene ne ta ga fa tana cin abinci sai ta ma ta,ta yin wani tuwo a ...''

'' Habu an shi nan gidanku na ce.'' Ta faWa tana masa Wakuwa. '' Gidanku ka ji wa to duk wannan abun da ta yi ba ta yi wani laifi ba wallahi Habu ina jiye maku kai da Malam abun da zai je ya dawo a kan yarinyar nan, na lura samku baku wani tsawata ma ta ko nuna ma ta abun da take ba daidai ba ne, ina jiye lokacin da ba na raye na tabbatar da ba zaku iya tsawatar da ita ba dan duk alamu sun nuna haka.'' Cike da kunar rai ta kai ?arshe tana duban Salame da ke tsaye tamkar wata yar sanda ta zubar da hawaye ace ?anwar miji ce za ta yi,ma irin wannan a gaban mijinka amma shi ko a jikin shi, ta share kallar.

'' Ke kuma Salame daga yau ina son ko yunwa kika ga za ta kashe Dagori idan ba ki iya zuba ido ki yi kallo to ki bar wurin, daman yarinyar nan ina da haushinta sam ayukan gidan nan ke ce mai yin su ita ta zama yar cin banza to daga yau na kashe Waukar abinci ki ce za ki kawo ma ta kin ji ko?.'' Ta gyaWa kai. '' Kai kuma Habu zuwa gobe ina son magana da kai.'' Da to ya amsa ya nuna ma ta kaya.

'' Nene wannan atamfar da wannan leshin duka na ki ne har ma da hijabi kin ga ni?." Ba ta amsa shi ba ya ajiye su a gefe ya ci gaba da maganarsa. '' Su kuma wannan yadukan biyu da hula duk na Baffa ne, kuma duka su a Winke suke wannan kuma dogayen riguna ne irin na birnin har da mai buje uku na siyowa Auta da mayafi da takalma dan a ci gaba da 'yan matanci ko Auta Baffa?."

Cikin murna da jin daWin ta ce. '' Kwarai kuwa Hamma Habu ai wallahi sai na nuna wa 'yan matan rugar nan ni ba sa'ar su ba ce dan ina da Hamma mai ji da ni da.....'' Ya buWe baki da niyyar magana Nene ta karSe da.

'' Ke dan Allah saurara ma haka, kai duk na ji ina na matarka suke ko ita babuta a kayan sai na ji?." Murmushi ya yi mai Wauke da dariya.

'' Nene kenan ita ma na siyomata kin ga su.'' Ya Wago kayan yana nuna ma ta. '' Kin ga ita ma atamfa ne da shaddar sai na ?ara ma ta ita ma da doguwar rigar irinta Auta da takalma da.....''

'' Wayyo na ba ni na,shiga uku na na lalace wayyo....'' Dagori ta runtuma ihu har da Wora hannu a ka.

'' Auta lafiya miya faru?." Habu ya faWa ya haska fitilar hannunsa ko zai ga abun cutarwa daya sameta.

Cikin kuka har da sheksheka take magana. '' Yanzu Hamma da ni da Salame yawan kayanmu... Waya da ita, amatsayina na yar uwarka ta jini shi ne ba za ka fifitani da matarka wayyo na shiga uku shi kenan, Aradu asiri ne Hamma asiri Salame ta ma ta, raba ni da kai na shi ga uku na gantale an raba jini da tsoka wayyo ni Dagori wayyo ni,ni yar uwar Hamma.'' Dagori ta tubure tana ihu tare surutai tu ni ta shire sauran lemun daya rage amma ta rige ledar namanta gamm a hannun, aikuwa ba ta yi aune ba sai saukar duka ta ji a jikinta ta ko ina.

Da sauri Habu ya mi?e ya ri?e igiyar da ke hannun Nene wadda take jibgar ta tamkar ta kama Sarawo. '' Nene dan Allah ki yi ha?uri kibarta haka, wallahi duk abun da take yarinta ne ke damunta kin ga fa du,du,du nawa Auta take ni fa idan banda kayan Salame sun ma ta yawa sai duka na haWa na ba ta allaso idan na koma zan dawo sai na siy.....''

'' Habu ka matsa ka ban wuri.''

'' Amma Nene....''

'' Na ce ka matsa.'' ?in matsawa ya yi dan ya san tun da har Nene ta yi fushi haka tofa idan har ya bar ta za ta iya yi ma ta illah.

'' Nene dan Allah ki yi ha?uri amma gaskiya ba zan bar ki, ki ma ta rauni ba wannan igiyar fa ta Waure shanu ce wallahi, ko ni aka daka da ita sai na yi zazzaSi balle kuma Auta haba Nene.''

'' Wai mene ne ke faruwa nake ji hayaniya?." Baffa da ke shigowa hannunsa ri?e da cabbi ya faWa.

Bai samu mai ba shi amsa ba sai ma Nene da ta ci gaba da magana. '' Ai kuwa ta janyo kayan sun zama haramiyarta, haba yarinya gabaWaya ta bi ta gama raina kowa ba a gariba ba gida ba.'' Ta kai ?arshe tana sakin igiyar hannunta da Habu ke ri?e da ita

'' Wai ni kam ba tambayar ku nake ba? mike faruwa kuka min shiru Kamar ba da ku nake ba.'' Habu ne ya waigo.

'' Afuwan Baffa ba mu ji shigowarka ba...'' Nan ya kwashe dukan abun da yake faruwa ya sanar masa.

Jin jina kai ya yi ya Wan yi shiru can ya ce. '' Maganar gaskiya abun da Mai babban suna ta yi sam ba ta kyauta ba, amma ke ma Uwar yara matakin da kika Wauka ya yi sauri da yawa kai kuma zancen ka bawa Mai babban suna kaya duka da na matarka, bai tasoba ke! Mai babban suna." Ya duba bayan ?asa sai wayammm babu ita. " Ina mai babban sunan ta ke?." Ya tambaya tare da dan dubawa.

'' Wallahi Baffa kila ta gudu ne Waki nan take kwance.'' Ya faWa yana nuna ?asa.

Abun da ya faru shi ne, Dagori da zafin da raWaWi su ka yi ma ta rukdugu dan ba laifi ta daku aikuwa tana samu Habu ya ceceta ta arta a na kare, ta bar gidan da gudun bypas.

'' A'a to ta na ina?." Baffa ya faWa bayan da ya duba cikin Wakinta ba ta nan.

Salame da ke gefe tsaye tun farkon farawa ta furta. '' Ai ta bar gidan tun lokacin da ya kwaceta.''

'' To ina ta je?.'' Yanzu ma ita ce ta ?ara ba shi amsa.

'' Ina zaton ba za ta huce gidan Dije ba.''

'' To bari na je na tafo da ita.'' Habu ya yi Maganar ya fara tafiya.

'' A'a dawo ai can ma ai gida ne gareta bar ta sai da safe tukun.

Juyawa Nene ta yi ta shige Wakita Baffa kuwa kan shinfiWarsa ya je ya zauna ya fara cin abincinsa, shi kuwa Habu kayan ya shiga haWawa kowa da wurinsa ya je ya du?a kusa da Baffa suka sake gaisawa kamin ya ba shi na shi.

'' Na gode sosai Allah ya yi ma rayuwa albarka ya ?ara buWe hanyoyin samu na alkhairi.''

Murmushi ya yi yana jin daWin addu'ar Mahaifin na shi har cikin ran shi. '' Amin ya Allah Baffa. ''

'' Ka tashi ka je ka kwanta saboda tun da ka zo baka wani huta ba da safe sai mu yi magana. ''

'' To Baffa sai da safe. ''

'' Allah ta shemu lafiya.'' ya amsa da amin yana mi?e wa.



Da gudunta ta faWa har ta karo da Inna da ke fitowa banWaki. '' Subbuhallah waye wannan kuma?." Ta faWi ta na dafe goshinta, Dagori kuwa do?e ta yi tana dafe gwiwoyinta sai faman ha?i take.

''Da...go..ri..ce.'' Ta furta aranrabe.

'' Dagori lafiya kuwa? a daran nan kuma kika shigo haka sai ka ce wadda aka biyo.''

'' Inna... Nene ce wallahi ka..she.ni za ta yi.''

'' Ke Dagori ba na son hauka da shirme kin ji ko, wane kuma kisa? A na zaune ?allau.''

'' Wallahi Allah Inna Nene yau kam kashe ni take da niyyar yi, yanzu dai ina Dije?. ''

'' Tana cikin....'' Ai ba ta ma jira jin ?arashi ba ta faWa cikin bukkar Dije, akwance ta sameta ta wani afka ma ta ban da ta yi saurin juyawa ta koma gefe da ba abun da zai hana ta faWa ma ta.

'' Innalillahi kai waye ke shirin sabauta ni?.''

'' Mtsssss ke banza ni ce.'' Mi?ebwa ta yi zaune.

'' Dagori lafiya dai ko?." Ta faWa tana dubanta.

'' Mtsssss dan gidanku ki dube ni da kyau ki gani na maki kama da lafiya.''

Sai da ta gyara zamanta kamin ta ce. '' To miya faru?.''

Nan ta sanar da ita abun da ke faruwa ta Wora da ce wa. '' Hmmm ni wallahi ba ma dukan ke damuna ba illa wai ace Hamma Habu yawan kaya Waya ya siyomin da wace bar zar matar ta shi wallahi, nifa dama ba wani san ta nake ba balle yanzu ya ?ara siya ma ta ba?in jini.''

Dije da ta yi shiru tana saurarenta har ta gama, abun ma ita dariya ya ba ta sai dai ba damar yin haka ta ballowa kanta ruwa, ba ta shirya ba.

'' Wai ina magana kin yi shiru tamkar ba ki ji na?."

'' To me zan ce kuwa salon in yi laifi abu ya dawo kai na ban ji ba ban gani ba a'a duk yadda kika yi.''

'' Uhm ai kuwa ni na san abun yi shi ke nan yanzu ga nama nan muci dan ni kam a nan zan kwana.'' Ta faWa tana fidda ledar naman aikuwa Dije ta washe baki suka shiga ci suna fira har suka gama suka kwanta sai bacci.



Washegari har zuwa misalin 11:00am suka fito zuwa wajen aikar da Inna ta ma su a hanya suka hango dandazon yara baibaye da wata dalleliyar mota, da sauri ta ja hannun Dije suka ?arasa wurin. '' Kai kai kai kada shegen da ya ba su amsa, uwar me na ji kuna kwatance?." Tu ni jikin yaran ya Wau rawa Waya ya ce.

'' Daman gidan uban RUGA suke tambaya shi ne...''

'' Shi ne uban me shi ne za ku sanar ma su? marasa kunyar yara wato ban da Allah ya turo ni, kuma na zo akan lokaci ku da so kuke ku faWa ma su ko? To ku matsa.'' Ta faWa tana ture yaran ta ?arasa gaban motar.........

Comments
Like
Share

Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???

?DAGA RUGA NAKE ?

NA
A'ISHAT SALISU SALLAU
(Mrs Awwal)



=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa suka sauya tunanin al'umma cikin sau ?i_.'?






007



Daidai gaban motar ta tsaya tana wani ri?e ?ugu ta dubi mutumin da ke zaune a mazaunin driver. '' Kai wane dalilin ne da kai wanda kake neman gidanmu? Ko da yake ba mamaki 'yan yankan kai ne, ko Sarayin mutane waton kun samu labarin Baffa na da tarin garke shanu shi ne kuke son a nuna maku gidansa dan ku je ku Wauke shi ko? To Aradu ba ku i sa ba, ko da ku na...'' Maganarta ce ta Wauke sakamakon wani ?yak?yawan saurayi da ya fito cikin Wayan motar da ke baya ya ri?e mulfin motar tare da Wora hannunsa akan sajensa ya dakatar da ita sanye yake da ?ananun kaya riga da wando Black and Red sai tabarau wanda ya matukar hawa da ?yak?yawar fuskarsa, wani razani ne ya shigeta bayan da ya buWe bakinsa ya fara magana.

'' Ke! Wai ke wace irin yarinya ce da sam She doesn't know what she is? na ce za ki nuna mana gidan ko sai na.....''

'' Wayyo Allah Dije Aradun Allah y'an yankan kai na dubi kayansa Aradun Allah irin na Waya daga cikin hin Win nan da ma su shan jini suke sawa na higa uku.'' Tana faWin haka ta kwasa a guje Dije ta bi ta da kallo ta girgiza kai ta mai da kallonta awurin saurayin.

'' Mu je na nuna maku." Shiga motar ya yi suna bin bayanta.



Da gudu ta faWa cikin gidan tamkar wata mahaukaciya '' Nene! Nene!! Nene!!! Mun shiga uku rayuwarmu na cikin hatsari Nene ki na ina?." Sai faman dube-dube take.

Nene da ke bakin runfa tana Wora tire shanya . '' Kin san Dagori ki kiyaye ni mene ne za ki faWo wa mutane gida kamar wadda aka biyo?."

'' Nene yanzu ba lokacin tambaya ba ne Nene mu yi gaggawa guduwa Aradu suna zuwa ba su samu Baffa ba Aradun Allah jininmu shi ne zai zama abincin su kin ga Nene mu gudu.'' Ta yi Maganar tana jan hannun Nene tamkar wata yarinya, kamin Nene ta yi magana ta tsakiya wata murya na sallama.

'' Assalamu alaikum.'' da sauri Nene ta kalli wurin har tiren hannunta yana suSucewa a hannuta cikin rawar murya ta furta.

'' A..Abu..ba..kar... Kai ne..ko dai gizo ne..'' Sai kawai ta zube ?asa a sume.

'' Wayyo na shiga uku na lalace shi ke nan, Aradun Allah mayu ne sun ka.. she Nene Wayyo Allah shi ke nan sun mai da ni marainiya Baffa ina kake? Aradu saura mai babban suna Wayyo...'' Na ta faWi ta na bigima sai faman shure-shure take.

Da gudu Salame da hayaniyar Dagori ya fito da ita, ta nufi randar ruwa ta kamfata tana zuwa ta sheka ma ta cikin seconds sai ga shi ta sauke a jiyar zuciya mai ?arfi, tare da taimakon mutanen wurin ta samu ta kwantar da ita cikin runfar ta Wago ta kallesu. '' Bayin Allah su waye ku? Wanda daga ganin ku zai sa ta suma? .'' Salame ta faWa tana ?are ma su kallo ganin duk ba ta san su ba.

'' Ke Salame ma za a je a kira Malam yanzu, kuma ki sama ma su wurin zama kamin ya zo.'' Nene ta yi magana ta kallon mutumin da tun da ta farfaWo take kallonsa tamkar shi ne kawai ke wurin.



*Wacce Dagori?*

Muhammad Majoh dan asalin jahar Yola ne a ?aramar hukumar Numail a cikin daji domin sun kasance fulanine RUGA ne ma'ana fulanin asali Majoh mutune mai matukar sa ni da hangen nesa wanda tun tasowarsa yake da tarin baiwa wanda yakan iya hangen abun da zai iya zuwa yadawo ba wai, na tsafi ko sitboba a'a rin sanin nan wanda akasan duk wani cikakken bafulatani da shi, Mutum ne mai tsaftsauran ra'ayin akan abun da ya sa gaba mutum ne kai fi Waya wanda ba ya canza magana yana da mata biyu uwar gidan sa Karime mace mai dattako da sanin ya kamata, wadda ko alokacin da zai ?ara aure ba ta tada hankalin ta ko Waga masa hankali ba, ya auro Aminatu yarinya ?arama wadda a lokacin da da aka aura masa ita ba ta fi shekara goma ba, da aka kawota haka Karime ta ja ta ajiki tamkar yar cikinta domin ita Winma awurinta hakan yake ta na girmamata sosai tamkar uwa haka ta Wauketa.

Zama suke mai tsafta wanda ya ?arawa mijin na su natsuwa acikin zuciyarsa tsawon shekaru huWu kamin Aminatu ta samu ciki farin ciki wurin mutane biyu ba'a magana tsakanin Majoh da Karime sai ka rasa wa yafi wani farin ciki Sam Karime ba ta nuna hassada ko ba?in ciki akan kyautar da yar uwarta ta samuba dan ita ba ta haihuba, tattalinta take sosai bayan wata tara ta sankato Wanta na miji mai matukar kama da Mahaifinsa farin cikin wannan ranar ba'a magana domin baki ba zai iya faWa ba, a sha biki ida yaro yaci suna Suleman, Suleman ya taso cikin soyayya da gata wanda Karime da Majoh ke nuna masa dan ita Aminatu idan ba nono zai sha ba to fa ya na wurin Karime.


Suleman na da shekaru Uku a duniya Aminatu ta sake samun ciki wannan karon ta sha wahala sosai wanda da ga ?arshe sai da akazo nan Numail a assibiti ta haihu ta samu namiji wanda tun a assibiti aka sanar da su ba za ta sake haihuwa ba, ga murna ga kuma wannan alhini da suka tsinci kansu a ciki,sum yi batukar alhinin amma daga baya suka falwalawa Allah komai, sun dawo gida ida yaro ya ci suna Abubakar wanda duka rin?onsu ya dawo wurin Karime.

Suleman da Abubakar sun taso cikin so da kaunar junansu, wata rana turawa suka zo da ga birnin domin wayar da kai mutane akan karatun boko tuni Suleman ya yi sha'awar ko da ya sanarwa Mahaifinsa fafur ya ce shi sam bai amin ce ba aka juya amma ya ce ina shi fa Wansa ba zai yi karatun boko ba adole ya ha?ura ba Wan ya so ba a na haka aka kai su almajiranci birni ko da suka shigo birni Suleman ya ha Wu da mutane to daman yana da sha'awar karatu wata rana yake sanarwa yaron da yake yin wanke wanke a gidan su ai ya na da sha'awar karatun boko nan ya ba shi shawara akan ya fara zuwa ko ta gwamnatin ne domin ya cika burinsa, da wannan zancen ya dawo ya kuma Wauki aniyyar cima burinsa ko da kuwa zai yi dako ne domin cinma burinsa.

Jin da ya yi cewa dole sai da kuWi ya sa ya tashi tsaye akan neman duk bayan suka tashi da ga karatu yakan shiga kasuwa ne ya yi dako dadai sauran ayukan, da za su kawo masa kuWi dan zama yai komai da ruwan ka; ba jimawa ya tara kuWaWen da yake da bu?ata tuni ya fara shirin zuwa makaranta, sai dai abun da ya faru daga baya shi ne ya kashe nasa wannan burin na sa, dan kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login