Showing 24001 words to 27000 words out of 79609 words

Chapter 9 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1119

tambaya kenan kika rigani, ke Inty to wai ma ina ne gabas Win ku take? Ko duk in da ka ?alla daidai ne?."

'' Wallahi Allah Sister Dagori da abun dariya ki ke ta ya ko ina zai zama gabas? Bayan mu ba a cikin Ka'aba muke ba.''

'' Yoo ni na sa ni ai na za ci a birni ko ina gabas ne.''

Mi?e wa ta yi. " To a'a ba ko ina yake gabas ba ni bari na je zan yi sallah.'' Ta yi maganar tana nuna ma su gabas ta fita.

Tashi Salame ta yi ta sauya kaya ta koma toilet ta Wauro alwala ta fito ba ta bi ta kan Dagori ba, ta Wau sallayar da Inty ta kawo ma su ta shinfiWa ta ta da Sallah, Dagori kuwa toilet ta shiga.

Tana sallame sallah Dagori na fitowa ta ma Wauka a can za ta kwana dan har ta yi sallar La'asar dan sun yi Azahar a Kano La'asar ce kawai take kansu ta na addu'a ta dube Dagori dake Wingar ruwa tamkar wanda ruwan sama su ka yi wa duka. '' Ke lafiya duk kin wani ji?a jikin ki?."

'' Hmmm ke dai bari Salame na jima ina cuWa jikina garuwan ya?i daukewa haka na saka kaya amma sam ruwan nan ya ?i Wauke wa ga shi can sai yoyo yake na jira na jira amma ko alamar Waukewa bai yi ba haka na bar shi idan ya ga ji da kansa ya Wauke.''

'' Mene ne ake zancen kawo wa da Waukewa?." Da sauri ta dubi kofar.

'' Yawwa Inty gwara da kika dawo Aradu ruwan saman birni ya ?i Waukewa na jira har na gaji na bar shi can.''

Cikin rashin fahimta Inty ta ce. '' Wane kuma ruwan sama? .'' Dan sam ba ta gane me take nufi ba.

'' Amm na manta sunansa amma dai a cikin ban Waki yake ko sharwa, oho dai na manta to fa dun da na sa ya kawo ya ?i Waukewa, kuma na gama wanka amma sam bai Wauke ba.''

Da sauri Inty ta shiga toilet Win, mamaki ta yi ganin shower a kunne sai zubar ruwa take kashewa, ta yi daidai Dagori na shiga. '' Laah kin ga ya Wauke ai dama na ce da kansa zai gaji ya Wauke ga shi kuwa.''

'' Ba Waukewa ya yi ba kashe wa na yi.'' Ya kuna tare da kashe wa, tana gwada ma ta yadda za ta yi.


Dukkanin mutanen gidan sun hallara a kan dinning table ban da Innaya da sam ita ba ta iya cin abinci a falon, Dagori ta zo ita ta nemi wuri ta zauna cikin Wai daga kujerun dake dinning Win, dan Salame ta ce ba za ta iya futowa ba ko Wazun ita kawai ta san ?arfin halin da ta yi har ta iya cin abinci a restaurant tare da su hakan ta sa Mami ta sa aka, kai ma ta na ta.


'' To gani Mami.''

'' Ok 'yata an fito kenan? Maamah saka ma ta abinci.''

'' To Mami. '' Ta faWa tana Waukar Flash ta fara zubawa kenan Mami ta ce.

'' Wai ina Yayanku ne bai fito ba?."

'' Uhm Mami ai ya jima da fita.'' Inty ta faWa ta na yar dariya.

'' To ina ya je da daren nan ko huta gajiya be yi ba?."

'' Mami zance mana kin san dama a takure yake dan tun da muka tafi rugar su Baffa ba network to bai samu ya yi waya da ita ba shi ne ya je, ya ganta.''

'' Ok shi ke nan amma ai da sai ya bari sai ya ci abinci?."

Wayar Abbi ce ta yi ringing murmushi ya yi bayan da ya duba mai kiran ya Wauka cikin fari'a ya ce. '' Dan halak kamar ka san yanzu haka tinanika nake cikin raina.'' Sai da mai kiran ya Wan yi shiru amma za ka iya jiyo fitar numfashisa da alama ya Wan yi murmushi ne, kamin cikin wani irin Cold voice ya ce.

'' That's my Abbi, but you are also my life musamman tun jiya fa nake kira amma She is not coming to na damu ganin duka number's na ku.''

'' Sorry mun manta ne ba mu sanar ma ba mun je ruga ne...''

'' ruga kuma Abbi, what did you say? Ruga a cikin wannan matsalar what is so important that you would go so far? Haba. ''

Murmushi Abbi ya yi Mami ta ba sa amsa da yake wayar a Speaker take. '' My Son, thank God, we left safely and we are back ina fatan dai kai ma kana lafiya ko?."

Sai da ya sauke numfashi kamin ya ce. '' I'm fine amma mi ya kai ku riga?." Ya faWa acikin voice Winsa mai kama da na sarakai.

'' Yaya dam....''

'' Ke Aimanah ku yi ma mutane shiru..'' Mami ta faWa cikin gargaWi kamin ta ci gaba. '' Ai na san cewa za ka zo cikin satin nan ko? To idan ka zo koma mene ne sai ka ji a lokacin.''

Sai da ya yi shiru na tsawon second kamin can ya ce. '' Mamina gaskiya ba lallai na dawo ba because muna da wani text ne da ya yi daidai da lokacin so kawai zan bari sai bayan biki zan zo.''

'' Amma Asad auran ?an uwanka ka ce ba za ka samu zuwa haba Asad why text ace za ta hana ka zuwa?." Shiru two minutes bai ce komai ba kuma shi bai kashe ba ganin haka Abbi ya san ko, kwana za'a yi to fa ba zai yi magana ba kuma ba zai, kashe ba ya sa ya katse kiran.

'' Ni Abbi sai nake ganin kamar Ya Asad bikin ne kawai bai son hallarta ka san shi bai son hayaniyar mutane da kuma, takura meybe shi ne dalilin da ya sa ya, yi wannan zancen amma tun da ya ce zai zo bayan auran shi ke nan ai.'' Maamah ta kai ?arshe maganar tana Waukar juice Win gabanta ta Wan sha ?aWan.

Kamin Abbi ya ba ta amma sai ji sukai Dagori ta ce. '' Tab amma wannan koma waye shi an yi Wan rainin wayyon Aradun da agaba na yake ba abun da zai hana na wankesa tass ka ji fa wani rainin wayyon fa idan an yi magana sai jika ya ji?e kamin ya ba da, amsa Hmmm ji daga ?arshe ma shiru ya yi ya daina magana ai Aradu da kabar shi ai kuWinsa ne ke tafiya nan fa idan Hamma Habu ya kira har sauri yake a gama magana dan kada kuWinsa ya ?ara, kai amma yana yanga yoo Aradun Allah ko ni ban iya wannan yangar tashi ba duk kuwa kwarewata a iya yaudarar samari da yanga amma Aradu wannan ya sha gaba na kai yoo wannan da mace ne Aradun Allah mijinta ya shiga uku don kuwa sai ta zauta shi.''

Murmushi Abbi ya yi. '' Mai babban suna ke nan ai wannan ba wai yanga yake ba haka halinsa yake, kuma shi Win ba wai wani ba ne a wurin ki shi ma Yaya yake gurinki.'' Abbi ya faWa samm bai ji zafi ko ganin laifin maganarta ba dan ya san a irin wauta ta su ta fulani wannan ba komai ba ne.

'' 'Yata amma wannan kayan ai a nan ba'a saka su ina irin waWanda kika cire? ki Winga saka kalarsu .'' Mami ta tambayeta tana duban kayan tsa?i dake jikinta.

'' Ai Mami wannan kaya da ki ke gani ?arshan wanka kenan Aradun a ruga idan na sa su zo ki ga yadda samari ke kallo na.'' su Aimanah me za su yi ba dariya ba Inty har da ?warewa.

'' Ok kenan dai ba kida wasu sai wannan?.''

'' Eh ai garin sauri duk waWannan na haWo ba wasu.?

'' To Maamah gobe ke da su Inty za ku je shopping tare da ita sai ku zaSa ma ta kayan da suka dace da ita, amm har da matar Yayanta. ''

'' To Mami.''

'' kamin nan ke Aimanah tun da ke ce mai ?aramin jiki kamarta cikin kayanki ki sama ma ta wanda zai yi ma ta duk da na ga ma ta fiki ?aramin jiki amma ki dai duba mata sai ta sauya wannan.''

'' Ok Mami, amma yanzu tun da dare ne ai kawai na bacci zan ba ta gobe sai na ba tana, fita.''

'' Uhm kawa dai ya ne ke kuma Maamah sai ki bawa matar Habu.''

'' Ok Mami.''

Mami ce ta mi?e tabar wurin dan Abbi dama ya shiga daga ciki daga haka kowa ya shiga watsewa Aimanah ce ta ?arshen tashi ta dubi Dagori dake ta lodar abinci. '' Sister ke ba za ki shiga ki kwanta ba dare ya yi?." Ba tare da ta Wago ba ta ce.

''Ki tafi kawai ni ina nan ba yanzu ba.'' Ba ta sake magaba ta tafi abunta.

Tana barin wurin Dagori ta mi?e ta shiga buWe kuloli akan kular dake Wauke da da naman rago idonta ya sauka. '' kai jama'a duk wannan da gwagwajiyar ba za su ci ba, kai 'yan birni na abun da suka so, to wannan rabon Dagori ne. " ?auke kular ta yi gabaWaya ta zauna ?asa ta shiga ci, sai da ta cinyesa tass ta lashe kula kamin ta yi gyatsa ta mi?e ta nufi kan dinning Win ta Wau lemu juice ta sha ta kalli cikinta.

'' Amma wannan ciki an yi munafuki duk wannan uban abu da yau na zuba ma amma ka nan jiya iyau ba canji amma za ka ci ubanka ne nan da kwana kaWan za ka mi?e.'' Ta faWa tana nufar hanyar dakin da aka kai su da ?et da ?et take tafiya ko da ta shiga dakin ta tarar da Salame ta ci abinci ta koma kan gado ta yi Wai Wai.

'' Uhm ka ga fa su Salame ba'a iya samun banza ba wato aci an koshi an kwanta, to ai ba sabanba wai gwaro ya yi amarya an dade ba'a haWu ba ai, to amma tsare ni kada ki ishe ni da tusa. '' Ita kan Salame ba ta ma san ta na yi ba har ita ma ta shiga toilet ta wanke hannu kamar yadda aka nuna ma ta ta fito ta kwanta...........


Comments
Like
Share

Taku har kullum mai kaunar
MRS AWWAL =???

*?DAGA RUGA NAKE*?
*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?

=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa suka sauya tunanin al'umma cikin sau ?i_.'?






017


Can cikin dare Dagori kamar a mafarki ta ji wani irin ciwon ciki ya taso ma ta, wanda ba shiri ta farka tana dafe ciki ji kake kululuuu cikinta na kuka da sauri ta mi?e ta faWa banWaki.

Ko kan gari ya waye Dagori ta yi zarya a banWaki ya fi a ?irga idanunta kuwa sun yi zuru-zuru, ko da asuba da Salame ta farka ta ga halin da take ciki sam ba ta kula ta ba dan kallon Waya ta yi ma ta ta fahimci halin da take ciki, a ranta kuwa Allah ?ara ta yi ma ta har ta gama sallah da duk abun da za ta yi ta kwanta abun ta.


Da misali: karfe 11:00am suka fito tsaf cikin shirin su na zuwa shopping dan da Dagori ta fara alaye amma ta na jin fita ta ware daman ta samu sau?i sosai, Maamah ce ke driving motar sai Aimanah dake zaune a gaba ita kuma da Inty, Salame, su na baya kamar an mintsineta ta furta: " Ni kam Aimanah wai wannan Wan rainin wayo da na ji Abbi, ya na magana da shi waye shi? Na ji kamar Abbi ya ce shi ma Yaya ne wai, amma kamar bai wani iya hausa sosai ba? Kamar koyarta yake ko? Wani yare na fa yake wanda na ka sa gane masa.''

Aimanah ta waigo ta dubeta. '' To ai nan sai na ce ke da shi duka Waya ke ma fa hausar ta ki ba wani tsayawa ta yi a ba?in ki ba, idan ki na magana tamkar ki na koya wallahi wani sa'in so da yawa hausar ki ce ke bani dariya....''

'' Kin ga Aimanah ni fa ba wani dogon zance na ja ki ba kawai amsa za ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ki ba ni, kin tsaya ki na min wani dogon larabci.'' Ta katseta cikin tsiwa dan ita ba abun da take son ji ba kenan.

'' Haba Sister... '' Inty ta furta tana da fa kafaWarta. '' Sunansa Ya Asad ?ani yake wurin Ya Ashrap, ya kasar waje karatu dan shi ne ya sa baki ganshi ba, Ya Asad mutune wani iri idan na ce wani irin ina nufin murWanWen hali ne da shi yana walahar sha'ani zai yi wahala ka ga ne wane irin mood yake ciki domin ku san ko wane lokaci fuskarsa a haWe take, ko mu makusantansa ba wani ganin fara'arsa muke ba, shi kamar hannun riga ne tsaka nin sa da Ya Ashrap domin ba sai na ce dake komai ba aWan zaman ?aramin lokaci da muka yi dake kin fahimci waye Ya Ashrap, Mutun ne mai son dariya da barkwaci, duk da mu ?annansa ne amma idan kika ga yadda yake janmu da wasa tamkar abokan wasa, saSanin Ya Asad da ko da wasa ba mu isa mu yi wani abu a gabansa ba dan shi ba wasa ne yanzu jiki zai tsami bai da son mutane sam bai son hayaniya wannan dalilin ya sa aka nema masa karatu a wajen Nigeria, duk da dukan mu a cikinta muke karatu, to kuma hakan sai ya ?ara sa ka shi zama wani silent, ko a can sam bai da wasu tarin abokai dan ya tsani abun da zai saka shi ya yi surutu tsawon wani lokaci, ko abun da zai sa ka shi a damuwa.''

Tun da ta fara maganar Dagori ke saurarenta sai da ta kammala tsaf kamin ta mere baki. '' To bai min ba, duk abun da kika faWa a halanyarsa ba Waya da yamin a ciki daman fa ni tun daga jin muryarsa na ji bai wani kwanta min ba daga jin muryarsa ka san dan wula?anci ne, kuma zai yi izza kai wata ?illan ma wani mummuna ne kin san munana sun fi kowa rainin wayo to bai min ba kuma na ji na tsanesa." Ta faWa iya gaskiyarta tana jin wani tsana da haushinsa na rufeta kai ba, ta fatan haWa ido huWu da shi.

Inty da ikon Allah ya sa ka sa magana dan kan Dagori ta goge ma ta hadda a gabansu take furta wai ta tsani Wan uwansu gaskiya ta sare da wauta irin ta Dagori.

Maamah dake driving ba tare da ta waigo cikin murya mai alamun tsokana ta furta; '' Kin ko ga sam Ya Asad ba ya son rikici da shirme irin na ki da zai zo auran nan, na tabbatar sai kun yi daru da shi dan sam ba ya Waukar sakarci ki na masa laifi zai sa ki Winga hawa bene ki na sauka.''

'' Tab aikuwa ba zanba sai ka ce ba ni ce Dagori ba, tab ki ce da akwai ya ?i ko da yake ai ya fa zuwa balle ya zo ya takura mana mu da gidanmu ai ya yi ta zamansa kin ga mun huta.''

'' Kai Dagori wallahi duk wannan maganar da ki ke cika baki ne kawai, da ace za ku yi ido huWu da shi da kin gane abun da ake sanar miki wallahi idonsa kawai abun tsoro ne idai ya yi ma wani kallon to fa sai cikinki ya Wuri ruwa.'' Aimanah kai ?arshe ta na ?ar dariya.

'' A'a fa ki gyara zancen ki cikinki dai zai Wuri ruwa ba nawa ba, kuma duk wannan zancen da kuke dan ba kusan wace,ce Dagori ba ne amma da sannu za ku sani ko Salame?.'' Ta ?arasa ta jefa wa Salame tambaya.

'' Uhmmm!.'' kawai ta amsa daidai nan Maamah ta yi parking a wani katafaren supermarket.

Ba tare da kowa ya amsa ta ba ta fito tana ware ido. '' Kai jama'a komai dai na birni da ban ne.'' Ta faWa tana ba wa idonta abinci har suka shiga ciki.

Sun yi siyanya da yawa dan duk zari irin na Dagori sai da ta ce; subar su haka kama daga kan dogayen riguna, atamfa, shadda, duk ka Winkanku da takalma, da mayafai, har da hijabbai duk an siya ma su cike da mamaki sai take ganin kamar an yi armubazaranci da kuWi.

Sun zo biyan kuWi ke nan suka ji an ce. '' Karimah Abubakar Majoh ashe a na ganin ku?." Ku san a tare suka waiga wani kyakkyawan matashi suka gani da ganinsa ka san kuWi sun zauna dan ba sai an sanarma ba za ka gane irin yaran nan, ne na ma su hannu da shuni.

Murmushi ta yi. '' A'a wa nake gani kamar Kamal Wakili?."

'' Yes Besty ni ne ana ganin ku? .''

'' Eh wallahi ya bayan rabuwa?."

'' Alhamdullah za'a ce siyyaya kuka zo ne?."Ya faWa ya duban kayan gabansu da ake lissafi.

'' Eh wallahi.''

'' Ok to ku je mota ko zan biya sai na zo mu sake gaisawa.'' Dagori da ba'a ka sa da ita balle ace ta kwasa ta yi karaf ta ce.

'' Au wai kai ne za ka biya to kin ga Inty mu koma mu ?aro wasu da ma saboda ina tunanin kuWi ne ya sa na ce, mubar su haka, amma tun da yanzu shi zai biya mu je Aradu dama na ga wani abun da nake so kawai barinsa na yi amma yanzu banza ta sauka mu je ko?.".......


Kai Dagori wannan za?ewa haka to bari na daka ta a nan

Comments
Like
Share
Su ne za su sa ku ga sabon update mai yawa kuma akan lokaci


Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???

*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION (J.W.A)*=???
'?
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i.'?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login