Showing 6001 words to 9000 words out of 79609 words

Chapter 3 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1088

Sai ta sake fashewa da kuka mai sauti wai azuwan duk abun ne ke damunta.


Tu ni gurin ya Wauka da salati a na ta ala wadai da halin Saminu, Saminu da ikon Allah ya sa ya daskare ko motsi ya ka sa ya zu ba ma ta ido yana kallon yadda take shirga masa uwar ?arya.

'' To yanzu dai Sarkin Noma ka ji da bakin yarinyar nan dai ba ta da masaniya akan wannan lamari dan haka wannan ?ara an janye ta, kai kuma Saminu dole anjima zamu zauna da Mahaifinka, dan wannan iskancin ba a wannan RUGA ba daga haka na sallami kowa.

Ba'ai aune ba sai ganin Dagori akai kan Saminu digirgir tana dukan sa faWi take. '' Sai mun illata ka tun da ka taSa mana goWiya sai, mun rabaka da duk wani ?arsashi ka, yiiiiiiii hmmmm sai mun tarwatsa ka mun hanaka sukuni uhmmmm yeeeeee yiiiiiiii.'' abun da take faWa kenan tana dukan sa ga shi ta cumui muye shi ba ta yadda zai iya zamewa sai da ?yat aka samu aka rabata da jikinsa, nan limam ya fara ma ta ru?iya aikuwa ta shiga birgima.


Kwance take cikin runfa Salame na ma ta fifita dan kam ba laifi ta ga ji, sosai sai faman juye-juye take. '' Hannu ko Dagori, waWannan mutane suna azabtar da ke ainun Allah ya yaye miki ya kuma ba su ha?uri amma ki na jigata, aduk sa'ilin da suka tashi.'' Salame ta faWa cike da tausayawa Dagori Nene kuwa da ke dama furwa ta taSe baki.

'' Kai kam kana da ?okari miye na tausayin wanda bai tausayin kansa, yanzu duk halin da take ciki ai aradun Allah ita ta janyo wa kanta a yi yaro banda ?iWan kalandu da zuwa dandali bai ajiye komai ba, sai ma 'yar ban zar rigima ta yau da ban ta jibi da ban to daman mutane Soye ai irin su suke nema, kuma wallahi Dagori idan ki na sauya halayenki tun wuri ki sauya dan gidan wani za ki kin......''

'' Y??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????iiiiiii mu adaina mana faWa adaina yi wa goWiyar mu faWa mmmmmmm uhmmmm yeeeeee idan har aka ci gaba da takura ma ta to zamu Wauketa mukaita can bayan duniya idan ba za ku sake ganinta ba, uhmmm mmmm.'' Ta faWa tana birkita idanu.

'' Nene kin dai ji abun da suke faWa wallahi ina jin tsoron su aikata abun da suke faWi?."

'' Mtsssss aikin banza da na wofi to su Wauke ta mana shi ke nan na huta da kullum ana kawon ?ararta.....''

'' Ke uwar yara mai nake shirin ji da gani? Wato tun zurasu za ki yi ko? Saboda idan sun Wauke ta ba ki da asara? To wallahi bari na faWa ma ki, kiyi gaggawar ba su ha?uri dan duk abun da ya samu Mai babban suna, wallahi sai Allah ne kawai zai iya raba ni da ke.'' Baffa dake fitowa a cikin bukkarsa ya faWa cike da umurnin.

'' Amma Mal....''

'' Za ki aikata abun da na saki ko sai raina ya Saci, haka kawai suda ba ganinsu ake ba yanzu ki fusata su kawai su yi Satan dabo da yarinya ba ki da asara to maza-maza ki ba su ha?uri!."

Nene haka ba dan ta so ba ta ce. '' Allah huci zuciyar ku ku gafarce ni.'' Tana gama faWin haka ta mi?e ta bar wurin ranta na ma ta ba daWi irin yadda Malam ke sangarta yarinyar ya yi yawa kuma wallahi ita tana zargin Dagori aljanun ?arya take da a iskanci irin na ta ba ?aramin aikin ta ba ne, ita fa tun da suka dawo Malam ke sanar da ita yadda akai wurin Hakimi, ta dai amsa ne kawai amma samm ba ta wani yadda ba, yadda ta san Dagori da ba ta yadda Saminu zai ma ta wannan zancen ba ta nemi ta tara masa mutane ba, yo ma har yaushe Dagori ta fara rufawa wani asiri ne wadda kowa ya san ta da neman yadda za ta tona asirin wani a fai-fai har ita ce za ta rufe wannan babbar maganar, da addu'ar shiriya kawai ta bi ta wadda ba kinta bai rabo da yi ma ta kullum.

"Hannun ku ku yi ha?uri da kalaman ta yanzu da Allah ku ta fi kubar goWiyar ku, ta huta kun ga ta ji gata sai ta samu abun da ta ci.'' Baffa ya yi magana cikin tausasawa, wata irin mi?a ta yi tana gantsarewa sai ta yi lumm tana sauke numfashi sai ta buWe ido a hankali tana sauke a jiyar zuciya.

'' Hannu ko Dagori hannu!.'' Salame ta faWa tana ka ma ta ta zauna tare da jin gina akan iccen da ke jikin runfar.

'' Hannu Mai babban suna, Wauki furar nan ki taimaka ma ta ta sha.'' ya yi maganar ya duban Salame, da to ta amsa tare da Waukar furar ta fara ba ta ai kuwa daman mutunyar yunwa ta isheta tuni ta fara sha.

'' To ni bari na je akwai abun da zan kawo miki Mai babban suna ko akwai abun da ki ke so?."

Washe baki ta yi. '' Eh Baffa bakina ba daWi ka zo min da burodi da lemun jarka.''

'' To shi ke nan zan kawo miki shi kawai ki ke so ba ki bukatar komai bayan shi?."

'' Eh Baffa.''

Fita ya yi Salame ta sake kai ma ta ludayin furar. '' Kin ga bar ni haka zan jira Baffa ya dawo ya kawon burodina na ci.'' Ba ta tamka ta ba taSa baki. '' Salame Wan kama ni ki kai ni Waki ina son in kwanta, kamata ta yi ta kai ta Wakin ta kwanta kenan sai ga Dije ta shigo daidai Salame na fita.

'' Hannu ?awata sai kuma nake jin shanrin da Saminu ya bi ki da shi?." Ta faWa tana zaunawa gefenta.

'' Hamm ke dai bari amma ai na yi maganinsa!."

'' To Allah kyauta shi ne fa na ce bari na zo na duba ki da jiki.''

'' Ke ni duk ba wannan ba zancen Waukar fansa ta, wurin su Hansai dan kin san wallahi ba zan bar su haka kawai su sha banza ba!." Ta kai ?arshe tana ta shi zaune.

'' Amma Dagori ai dakin bari kin samu lafiya ka min a.......''

'' Ke Dije ni za ki faWa wa abun da ya da ce na yi, ko an faWa miki ni kalalki cemai ?wa?walwar kifi? To tsaya ki ji ni ba na abuna sai tare da lissafi, kin ji ko?."

'' Allah huci zuciyarki.''

'' Amin daman kin san na ce, akwai ai kin da za ki min...'' ta gyaWa kai. '' To yanzu lokacin ya yi an shi wannan.'' Ta faWa tana Waga filonta ta Wauki wani, kullin magani ta ba ta. '' Wannan ina son ki tabbatar kin sawa Hansai da A'i a cikin abun da za su ci ko su sha...''

'' Amma Dagori ba na kisa ba ne?."

'' A'a na uwar kisa ne tun da nake da ke kin taSa ganin na yi kisa da zan fara yanzu, wallahi Dije ko ki yi yadda na ce ko kuma duk abun da na yi niyyar yi ma su ke ce nan zan yi wa!."

'' A'a Dagori wallahi zan yi yadda kika ce.''

'' Aikin banza yanzu ta shi ki je anjima kaWan zan zo kiyo na san duk su za su zo to ke ma ki tabbatar kin zo dan a gabana nake son komai ya kammala.''

Jiki a sanyaye ta mi?e tana amsa wa da to dan ba yadda ta iya dole ta ta yi ta fice.

Kwantawa ta yi tana shegewa da dariya mugunta Hansai kun gama yawo.....


Comments
Like
Share
Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???

?DAGA RUGA NAKE ?

NA
A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO
(Mrs Awwal)



=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa suka sauya tunanin al'umma cikin sau ?i_.'?






005


Hankali kwance ta gama shiyawa hanunta Wauki sandarta tare da goran ruwan ta rataya irin yadda wanzamai ke yi ta yi kyau sosai cikin fararen kayan sa?i na fulani, ta sha uban kwalliya sai ka ce wanda za ta je biki ta wani cika uwar hoda da janbaki, wanda tsaf zai isa mutane huWu, kora shanun take zuciyarta fal da farin ciki tana tafiya tana ?ar wa?arta yau duk yadda yara ke tsokanarta ba ta bi ta kan su ba ta ci gaba da tafiya, tun daga nesa ta hango su ta sa ki murmushi mugunta Dije ce ta ?araso wurinta. '' Dagori ka ?araso? tun Wazun nake duban hanyark na ga....''

'' Ke Dije ya isa haka kin aikata abun da na sa ki ko ya ya?."

'' Dagori kenan ai wannan tsohon zancena da ma abun da nake so sanar da kai kenan ka tari hanzarina!."

'' Hhhhhh lallai yau akwai kallo a gonar nan amma a cikin me kika zuba ma su?."

Sai da ta gyara tsayuwarta kamin ta ce. '' Cikin fura ne kuma har na ga sun sha amma ?aWan nan da anjima na san za su ?arasa sauran.''

'' Hhhhhh sai ni shegiya Dagori wa ya ce, ja da ni ai ba abu ne mai sau?i ba, ai Aradu yau sai kun kunyata ba dai ni ba.. Hmmm.''

'' Amma Dagori ba ki sanar da ni amfanin abun da na sa ka ma su ba?." Ta faWi aWan tsorace, dan ita tsoronta garfa ace abun da zai iya kashe su ne.

'' Mtsssss banza kawai wa ya faWa miki matsoraci na zama kwani ai duk wani jarumi to fa sai ya ajiye tsoro kamin ya cinma nasara, to ni duk kan abun da na sa a gaba to fa ba gudu ba ja da baya.''

'' To shi kenan, ni daman tsorona kada maganin nan ya cutar da su.''

'' Hmmm ke dai bari kawai ki sa ido ki sha kallo.''

Daga haka su ka ci gaba da kiwon su kamar yadda suka saba ita dai Dije duk wani motsin su Hansai tana kula da shi ta ga ko wani abu zai faru har suka zauna domin cin abinci dukan su fura ne kowa ya sha ya wanke ?warya ban da Dagori da ba ta zo da fura ba sai da Dije ta ma ta, ta yi amma ta ce ta gode dan ita a?age take magani ya fara aiki, ai kuwa ba'afi five minutes ba sai kuwa A'i ta runtuma ihu. '' Wayyo Allah cikina.'' Ta faWi daidai lokacin da cikinta ke bada sautin kuluuluu tare da barkewa da wata uwar tusa mai ?ara.

'' Kai A'i wannan wane kalar iskan.....'' Hansai ba ta samu damar ?ara sawa ba sakamakon ita abun da ya faru da A'i ya faru da ita, da gudu suka tashi har suna rigangan wajen shi ga wata gona dake kusa da su suka du?a sai gudawa shaaa tamkar ruwa.

'' Kai wannan abu ya min dad'i hhhhhh yau kam zan samu na yi bacci, cikin salama.'' Dagori ta yi zancen cikin dariya har tana kai wa Dije duka.

'' Ke Dagori ina kuma kika samu magana saka gudawa?."

'' Ke wa ya faWa miki maganin gudawa ne, ai Hamma Habu ne da ya je kasuwa shi ne fa ya ji ana tallar maganin basir shi ne ya siyo ahe dai magani bai da kyau ya na shaa sai gudawa da tusa, lokaci Waya sai yai goma a jere.'' Ta faWi tana duban su Hansai da suka dawo a daddafe sai kuma suka sake kwasa a guje mi za ta yi, ba dariya ba har da ri?e ciki tsabar ?eta.

'' Kai Dagori yanzu ke ba ki ji tausayinsu ba?."

'' Dije! Dije!! wallahi ki fita idona na rufe wane tausayin? Ai wallahi mutuwa kawai zan ga sunyi na tausaya ma su ba rama ki ga." Ta faWa tana zuwa ida su A'i suka dawo suka kwanta tamkar wasu matattu, ita kam Dije girgiza kai kawai ta yi tana bin bayan ta, su na ganin zuwanta suka Wago a wahale su na kallonta. '' Hansai da A'i kenan manyan gari, to ya ku ka ji wannan salon kuma na san yanzu kun ga ne banbanci aya da tsakkuwa?.''

Hansai ta Wago tana sauke numfashin wahala ta ce. '' Dagori ba dai ki na da sa, hannu acikin wannan gudawar ta mu ba?."

Sai da ta dubeta she?e?e.


'' Hhhhhh kwarai kuwa ni ce nan da kai na na sa maku maganin da zai saku gudawa, ke A'i ina son ki Wan maimaita min zancen da kika faWa rannan?." Ta faWi daidai tana du?awa kusa da ita, tare da mere baki. '' Ko da yake na san yanzu kin manta saboda a halin yanzu ba abun da ki ke iya tunani face gudawa, to ina son ki sa ni kuma ki saka aranki ni na fi ?arfin in yi wa wannan abar ba?in ciki. '' Ta faWi tare da nuna Hansai da baki. '' Kuma zancen GiWaWo ku kun san ni ban gaji ba?in jini da nauyin jiki wanda har sai an yi tallata kamin na samu mijin aure, ba iya samarin RUGAR nan ba har na ma?otan da ke zagaye da mu kun san yawan mutane da ke ruguguwa akai na, to idan kuna cin ?asa kukiyayi ta shuri, domin gaban rijiya ba wurin wasan makaho ba ne.'' Tana gama faWin haka ta juya tatattara kayanta tare da kora shanunta ta nufi gida.


Dije da duk ta tsure tun farkon fara maganar Dagori dan ta za ci za ta ambaci sunanta amma sai ta ji shiru, wata ajiyar zuciya ta sauke tare da duban su Hansai waWanda suka fita daga hanyacinsu sai zufa suke A'i ta na kuka ta ce. '' Duk ke ce kika ja mana da aranar bamu tare ta ba da duk haka ba ta faru ba yanzu ga shi ni, ko iya mi?ewa ban yi ta ya zamu koma gida?." Ta faWi tana ?ara sautin kukanta.

'' Kin ga A'i wallahi kada kisa in huce haushina akanki na ga duk ke ce kika ce na tsaya na ma ta gargaWi da habaici dan ta san yanzu da da ba Wai ba ne, san kuma yanzu za ki wani tsureni ki na min matsifa.'' Nan suka shiga cece ku ce har sai da Dije ta shiga tsakani, kamin daga ?arshe dai kasa kora shannun sukai sai dai Dije ce ta haWa da na ta ta kora sukuwa su na tafe sai tusa suke bugawa ko da suka shigo cikin gari yara sai binsu suke su na ma su dariya dan, tusa suke wata na bin wata.




Dagori tana koma wa gida ta mai da shanu cikin garkensu sai da ta mai da su yadda suke, kamin ta fito tana sauke numfashi. '' Wshhh Allah na.'' Ta furta tana mi?e hannayenta bukkarta ta shiga ta Wauko buta ta du?a ta fara alwala la'asar. '' Assalamu alaikum!." Ta tsinkayo ana faWa, ruwan bakinta ta furzar ta Wago mi?e wa ta yi ta kwasa da gudu ta nufe shi. '' Oyoyoo Hamma yanzu ka dawo? Hannun da hanya! Ka kawon tsarabata ko?.'' Ta faWa ta cumui muyer shi.

" Kai Auta ai ?ya jira na zauna tukunna yanzu na gaji.''

'' Yo ni Hamma Habu ba kai ne ka ce za ka yi min tsaraba kayan 'yan birni ba, kuma ka ce har da burodi da lemun jarka da gasanshen nama za ka kawo min."

Murmushi ya yi. '' Eh duka ni na faWi haka amma ai yanzu na shigo ?ya bari na huta na kwance kaya tukunna.''

'' To amma ai....''

'' Ke Dagori wai me ki ke son zama ne? Yanzu ya dawo ba za ki bar shi ya yi wanka ya huta gajiya ba kin tarbe shi da zancen wata tsaraba, koma tambayar shi ya hanya ba ki yi ba kin rufe shi da wasu tambayoyi ki na banza.''


'' Wallahi Nene na ce da shi ya hanya ko ba haka ba Hamm?....''

'' Rufemin baki za ki matsa ki ba shi hanya ko sai na tatdaki a wurin?." Ta tunzura baki tana matsa wa.

'' Ai Nene da kin bar ta kawai idan ba ta yi min ba to wa za ta, je ta yi wa?."

'' Hmmm ai shi kenan tun da dama kai da Malam kune ke ?ara sa ta tana yi duk abun da take.''


Yana murmushi ya ce.


'' Nene kenan kin ga ko gaisawa ba mu yi ba.''

'' To idan ta bari kenan?."

'' Na sameku lafiya?."

'' Lafiya lau ke Salame zo ki ?arbi kayan mijinki.'' Ta faWa ta 'na kallon Salame da tun shiguwar shi tana zaune cikin runfa kunya da kawaici irin na Fulani ya hanata mi?ewa, har sai da Nene ta ba ta umurni tukuna mi?e ta nufarshi ta ?arbi kayan tare da masa sannu da zuwa ta nufi bukatarsu, ya bi bayan ta.

Dagori da ta so ta bi bayan su Nene ta ma ta wata uwar tsawa adole ba dan ta so ba da juya tana kunbure kunbure da turo baki ta shege bukkarta.

'' Ina kuma za ki ba alwala na ga ki na yi, ba?." A dole ta fito ta yi alwala ta koma Waki..




Comments
Like
Share

Taku har kullum mai kaunar
MRS AWWAL =???

?DAGA RUGA NAKE ?

NA
A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO
(Mrs Awwal)



=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa suka sauya tunanin al'umma cikin sau ?i_.'?





006





'' Ka ga Hamma Habu kawo fitilar sai na haska ma, yadda za ka ji daWin ciro kayan tsarabar da kyau.'' Dagori ta yi maganar tana sake kai nama bakinta tare da kurbar lemu har da wani girgizar kai.

'' A'a Auta bar shi kawai ke dai ci gaba da cin namanki da burodi.'' Ya yi zancen yana ci gaba da ciro kaya ciki ganah masgo.

'' Dagori ga tuwonki tun Wazun na ajiye miki kada yai sanyi, yadda...'' Da sauri ta Wago tana ?are ma ta kallon raini tare da ce wa.

'' Amma wallahi Salame ke dai ban san wace kallar mata ba ce, yanzu tsabar Sakin ciki da hassada har wani tuwo kika ajiye min? Salon na cika cikina da tuwo na ka sa cin kayan daWin da Hamma Habu, ya zo min

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login