Showing 75001 words to 78000 words out of 79609 words

Chapter 26 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1100

shi ne madubin mu, basira shi ne aikin mu, motsa zuciyar ma su karatu shi ne baiwar mu, mun rungume al?alami don haskaka al'umma




050




Zare glashin Win dake manne a kan ?yak?yawar fuskarsa ya yi, yana kare masa kallo tare da sake nazartar yanayinsa don duk wasu alamu sun gama nuna cewa ba gaskiya a tattare da shi. Cup Win Lipton da ke kan table ya Wauka tare da kurbar tea dake ciki kaWan ya ajiye. '' Uhmm Munir! Nawa aka biya ka ne?.''

Da wani irin razani ya Wago yana dubansa kafin cikin in'ina ya ce. '' Naa...'am... Sir mai ka ce.''

Wani guntun murmushi ya yi tare da juya kujerar da yake zaune ta juya da shi hannayensa ya dora duka biyu akan table Win. '' Au kurma kuma ka koma kenan na san cewa ka ji abun da na faWa kuma kana da tabbacin ba na maimaita magana ko?.''

Zufa ne ya yanke masa duk kuwa da AC dake kunne a Office Win.

'' Kai nake saurare ka san cewa ba na bukatar Sata lokaci don lokaci abu ne mai mahimmanci a wurina, ba na son kuma ka kai ga ka harzu?a ni don kamar fito da Mayunwancin zaki ne a cikin kasuwa.''

Ya kai ?arshen yana lumshe idonsa tamkar ba shi ne ya gama magana ba.

'' Sir ban fahimci zancen ne ba na kasa gane abun da kake nufi duk...''

'' Be quiet okay! Kada ka ce za ka min wani musu a nan na san cewa ka san zancen da nake.''

Ganin yanayin idanunsa na sauyawa ya sa Munir ya tsorata don ya sa cewa ransa ya soma Saci ne tuni ya fara magana.

'' Wallahi ban karSi komai ba iya bincike da na yi ne yanunamin cewa haka, amma ba wanda ya ban ko sisi ai yin haka cin amana aiki ne.''


Ba tare da ya ce komai ba ko ya buWe idonsa ba, ya juya masa da gaban laptop Winsa.

A zabure Munir ya mi?e tsaye zufa na sake ji?a masa jiki

'' Koma ka zauna!." Ya furta still idansa rufe. Komawa ya yi ya zauna kamar yadda ya ce, amma jin kujerar yake tamkar akan ?aya yake.

'' Kai nake saurare miye wannan?."

'' Allah ban san komai akai ba ban.....''

Wani irin buga table da ya yi lokacin Waya kuma yana mi?ewa.

'' Waton har yanzu daga hujja me ?arfi musu za ka ci gaba da min ko?, Lallai sun maka biya mai kyau wanda har za ka iya wannan ba tare da wani tunani ba, wannan shi ne ainahin gaskiya bincike da ka yi amma mi ya sa aka sauya shi? Har yaushe ka yi bincike akan cewa Mashkur yana da taSin hankali? waton hakan na nufin cewa mu duk bamu san aikinmu ba,..... Muna bincike akan mahaukaci, har yaushe ?aramar ?wa?walwa ka take baka cewa ni Asad Abubakar Majoh na yi lalacewar da zan yi sake da irin wannan muhimmin aiki?. To ka yi kuskure kuma ko nawa suka baka ka ji kunya da har za ka iya sadaukar da aikinka da alkhairi ka da mutunci ?asarka akan kuWi to yanzu nan ba sai an jima ba za ka girbi abun da ka shuka.''

Wata karamar ?ararrawa ya danna take ta yi ?ara cikin second sai ga jami'ai biyu sun shigo. Take Munir ya ?ara rikicewa.

'' Ku tafi da shi kuma ku tabbatar kun koyar da shi darasi yau Winnan ba sai gobe ba.''

A take suka kama shi don cika aiki su..


'' Don Allah ka yi ha?uri wallahi na yi nadama abun da na aikata kuma wallahi ba a son raina na aikata ba kamin afuwa kamin lamuni wallahi ba zan sake ba...''

Abun da yake faWa kenan cikin magiya da ban ha?uri, har sun kai kofa ya ce.

'' Ina son ka sani cewa a yau Winnan Mashkur yana kotu zuwa misalin 4:00pm za a yanke masa hukuncin kuma ka sani cewa waWanda suka baka kuWi kuma ka karSa tofa ba barinka za su yi ba saboda baka cika ma su aikin su ba.''

Yana gama faWin haka ya Waga ma su hannu alamun su fice ko sauraron magiyar da ya cigaba da yi masa bai yi ba. Suna fita ya koma ya zauna yana sauke numfashi na kansa dake ciwon don yawan magana da ya yi.


*************

Tsaye take a gaban madubi sai faman juyi take kai ka ce wata ?ar tsana ce, tana sanye da riga da siket ne jikinta na atamfa sun yi matukar yi ma ta kyau ainun. Ba kwalliya a fuakarta iya foda ne sai kwalliya sai kuwa Vaseline da ta shafa a lip dinta, don ko lip gloss ba ta amfani da shi tun da aka ce ma ta idan har ba mai mekeup ta yi ma kwalliya ba to za a sace ka ne ta daina.

'' Uhm uhm wannan irin kyau haka Sis sai ka ce wanda za ta je gasar sarauniyar kyau na duniya.''

Aimanah ta faWa lokacin da ta shigo cikin Wakin bayan da ta ?araso dab da ita, wani murmushi jin daWi ta yi don a duniya tana matukar son ta ji ana ya ba ta, waigowa ta yi tana ?ar dariya don kam ta ji daWi.

'' Aimanah da gaske na yi kyau?." Ta yi maganar cike da wauta irin ta ta.

Murmushi ita ma ta mayar ma ta kamar yadda ta yi ma ta.

'' Sosai ma ai in dan aka ce kyau kaWan ma ma?urar kyau kika yi ai ina mai tabbatar miki da a yanzu ko sarauniyar Ingila ba za ta nuna miki kyau ba ma sha Allah.''

Kanta ne ta ji yana neman fashewa ta wani sunkuyar da kai wai ita a dole kunya ta ji.

'' Kin ga Sis zo mu je kin san fa an ce ana gama La'asar zamu dawo.''

Ta faWa tana janyo hannunta suka fito. Suna ?arasowa tsakiyar parlon ana turo ?ofar parlon.

'' Assalamu alaikum....'' Karaf idonsa cikin na ta ya bi ta da wani irin mayye kallon yana sakin baki.

Har sai da Inty da ta mi?e daga zaune da take ganin fitowar su ta katse masa tunani da cewa.

'' Yaya Kamal ina yini?."

Yana wayancewa daga kallonta kurullar da yake musamman da ya lura da wanzuwar Mami a parlon, ya sunkuyar da kai na jin nauyin abun da ya yi.

'' Amm ina yini Mami?." Ya furta yana shafa ?eyarsa.

Mami lura da ta yi cewa kunyar ta kama shi ya sa ta nuna masa kamar ba abun da ta gani.

'' Lafiya lau Kamal ai na ma Wauka driver ne ya zau Waukar su."

'' A'a Mami ni ne dai, au fita za su yi kenan? Sai ina?."

Ya amsa yana ?arasowa ya zauna.

'' Eh wallahi za su je ne gidan Yayansu ne ka san tun da a ka yi bikin ba su je ba to sun matsa shi ne yau dai na ce su ta fi tun da gobe ne hutunsu na school zai ?are.''

'' Ah a gaskiya kam ya kamata su je su sha man Amarya... Kamar na ji kin ce driver suke jira?."

'' Eh na aikesa ne to har yanzu bai dawo ba shi ne fa duk sun ?osa ya zo.''

Sai da ya saci kallon Dagori kamin ya ce.

'' Tun da gani ai bari kawai na kai su zuwa magarib sai na je na Wauko su.''


Ya furta yana mi?ewa.


'' A'a har magarib ni cewa na yi da an yi La'asar su dawo haka.''

'' Kai Mami yanzu fa muna wajen 2:00pm har yaushe muka je suka yi fira muka dawo.''

'' To ai shi ke nan tun da ka ce haka sai ku tashi ku tafi ko?."

Da wani irin murna suka bi bayansa don Yana gama faWin haka ya fita, sallama suka ma ta suka fita suna murna.



Comments
Like
Share


Taku har kullum mai kaunar ku

MRS AWWAL =???

My group comments section =?G?
https://chat.whatsapp.com/IPtcuaB4eBbC5fxtv4ZUng?mode=gi_t

My channel =?G?
https://whatsapp.com/channel/0029Vb7Jri19mrGWdgsRwZ3M





*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?





051


Fuskarsa Wauke da murmushi ya dubi Dagori da ke hakince a gaban mota, ta wani Wora ?afa Waya a kan Waya.

'' Beauty gaskiya ke mai kyau ce, kin ko ga yadda kika yi wani irin kyau na musamman tamkar wata jinsin larabawa?."

Wani irin lumshe ido ta yi lokaci Waya kuma tana sakin wani irin murmushi na jin daWi ba tare da ta yi magana ba don sai ta yi sam bakinta ba zai iya buWe wa ba balle kuma ta iya yin magana tsabar yadda ta ji kanta ya fashe.

'' WOW kai ma sha Allah amma gaskiya ban taSa ganin wanda murmushi yake yi wa kyau irin ki ba, ke wallahi duk wani abu na ki me kyau ne ko me kika yi sai ya bada ma'ana shukkuran.''

Wannan karon ba ta hana kanta ba wurin yin dariya ba, ta gyara zaman ta tana dubansa da kyau ba wai shi ne mutum na farko da ya yabe ta ba amma na sa yabon yana zama na daban a duk lokacin da yake yi ma ta takanji tamkar ita Win tafi kowa matsayi a duniya.

Cikin wata irin yanga da ita kanta ba ta san cewa ta iya ba ta fara magana.


'' Amma ai an ce yan birnin daban suke to ka ga ai dole sun fi ni ?yau da komai.''


'' Wa ya faWa miki wannan maganar ai kaf matan garin nan babu wanda ta kai ki komai kawai sai dai su nuna miki ilimin da wayewa, sai kuma shekaru wanda duk waWannan nan gaba kaWan za ki mallake su. kin ko ga kin fi su.''

Karaf Inty da ke gidan baya ita da Aimanah ta ce.

'' A'a fa Yaya kamal wannan fa zuga ne kake kawai amma ba a rasa wanda ta fita ba ko a nan cikin garin Kaduna kuwa, kawai dai tana da kyau sosai amma kada ka ce tafi kowa saboda....''

'' Saboda me? ?ar hassada wato saboda an ce ina da kyau shi ne ba?in ciki ya motsa ko? To tsaya ki ji ba shegiyar da ta fini kyau a duk faWin duniya ma kin ji ko ni Winan ina zargin akwai jinin aljannu jikina.''

Kamal shi da Aimanah da ke dariyar yadda ta wani zaburowa Inty kamar wanda ta kashe ma ta mutum ya ce.

'' Kin ga Beauty miye haka wasa fa take miki waye mutum ya ce ba ki da kyau, amma kada ki sake danganta kanki da aljanu kin ji ko?."

'' A'a Yaya kamal bari na faWa ma 'ta ai gwada na ma ta kwatance da aljanun saboda ai an ce kaf, duniya sun fi kowa kyau.''

Daidai nan kuma suka ?araso bakin get Win gidan Ya Ashrap Win parking ya yi, ba tare da ya ba ta amsar maganar ta ba ya ce.

'' Yanzu ku je bayan magrib zan dawo na Wauke ku.''

Da to suka amsa suna fita daga motar suka shiga ciki. Sai da ya ga shigar su kamin ya ja motar ya bar wurin yana murmushi.



Da sallamarsu suka shiga parlon, a Wai daga cikin kujerun parlon take zaune tana dannan waya duban ?ofar ta yi lokaci Waya kuma tana amsa sallamar. Murmushi ta yi ta ajiye wayar.

'' Marabaku ku shigo mana kuka wani tsaya a wurin.''

Ta faWa fari'ar fuskarta na sake faWaWa. ?arasawa suka yi suna shirin yin masauki a ?asan cafke ta yi saurin cewa.

'' Kai! kai!! Me za ku yi? A'a duk tarin kujerun da ke parlon nan ace ku zauna a ?asa a'a ku zauna akan kujera mana.''

Kan kujerar suka zauna kamar yadda ta ce, kusan a tare suka haWa baki wurin faWi.

'' Aunty Khadijah ina yini?."

Ban da Dagori da kawai iya ina yinin ta ce.

'' Lafiya lau ya su Mami suna lafiya?."

'' Lafiya lau suke sun ce ma suna gaisheki.''

'' Ina amsawa, Zainab! Zainab!!." Ta ?waWawa mai aikinta kira

'' Na'am Aunty.''

Ta faWi daidai lokacin da take ?arasowa tsakiyar parlon.

'' Je ki kawowa Saki ruwa da lemu.''

Da to ta amsa tana juyawa hanyar kitchen, ba jimawa ta fito hannunta Wauke da tire ta zo ta ajiye akan Center table Win da ke tsakiyar parlon. Ba ta bar wurin ba sai da ta zubawa kowa lemu a cikin glass cup.

Duban ruwan da lemu Dagori ta yi ai kuwa sai cewa ta yi.

'' Amm Aunty na ji ana kiranki ko? To dan Allah Aunty chinchin Win biki ya ?are ne aka kawo mana iya ruwa kawai?."

Wata irin kunya ce ta kama su Inty Aimanah da ke shirin kai lemu bakinta ta ce.

'' Haba Sis miye haka?."

'' Ai ki bar ta kawai ta gama nuna wa duniya halinta tukunna.''

Inty ta tare tana ji tamkar ta tashi ta yi wa Dagori shegen duka.

'' Ah kubar ta miye don ta yi magana ai gidan Yayanta ne.''

Matar Ya Ashrap ta faWa don sam ba ta ji haushi ba ita Win mace ce mai kirki da girmama mutane, kuma daman Ashrap ya gama faWa ma ta halin Dagori kuma ko da ba ta tambaya ba wannan halin da ta nuna ya tabbatar ma ta cewa ita ce Dagori

'' Yawwa Aunty faWi ma su dai ai na ga gidan Ya Ashrap na yi ba wani gida ba kuma gidansa ai baya da banbanci da da wancan.''

Mai aikinta ta sake kira ta yi ma ta umurni da ta kawo ma su.

Tana ajiye Filat Win hannunta Dagori ta ce.

'' Yawwa Zainab sannu da aiki don Allah ki shiga kitchen ki samu ko wani abun ne ki girka mana mai daWi na san dai gidan amare ba su fiya girki da rana ba.''

'' Ai kuwa kamar kin sani ba na girki da rana saboda Baby yana zuwa aiki so ni Waya kawai ina bari sai ya dawo.''


'' Ai na sani Aradu ko ruga aka yi wa yarinya aure tofa ba ta girki ko na dare sai dai ango ya siya ma su a dandali.''

Tana dariyar zancenta ta ce.

'' Zainab jeki ki dora ma su girki.''

'' A'a ni kam kamin nan Zainab ki doramin indoman da kifin gwangwani tare da soyayyen kwai ko da kuda uku ne, don Aradu ba na wasa da cikina ba zan iya jiran ki gama girki ba.''

Da to ta amsa ta tana mi?e wa ta koma kitchen Win. Da wani irin mugun kallo Inty da dube ta aikuwa aka ci sa a suka haWa ido da ita.

'' Au ko ba harara ba? Yoo ai na ga idon ki a?asa nan ne zan san cewa kin iya harara, tun da muka zo sai wani mugun kallo ki ke jifata da shi sai ka ce wadda ta aikata wani babban laifi, to ai dai na ga gidan Ya Ashraf ne ba wani wuri na je kwaWayi ba, ko Aunty?."

Ta kai ?arshe tana jefawa matar Ya Ashraf tambaya. Murmushi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba, Aimanah ta ce.

'' Amma dai Sis wallahi ba ki kyauta ba ke shi ke nan duk ida kika shiga sai kin saida hali ai wannan ba abu ba ne mai kyau kuma wallahi sai na faWawa Ya Asad...''

Da wani irin saure ta ce.

'' Oh ni Dagori yanzu daga wannan abun shi ne har sai an wani kai ?arata to ai shi ke nan abar indoman Win kawai sai an gama abinci....''

Sai da ta gyara zamanta sannan ta fara magana tana duban ta.

'' Ni kuwa wannan wane kalar suna ne naki? Na jima ina son tambayar Baby amma tun da gaki shi ki faWa min.''

'' Wai ni...'' Ta faWa tana nuna kanta ba ta kuma jira amsa ba ta ci gaba. '' Dagori ne sunana.''

Cike da mamaki ta sake cewa.

'' Dagori! Kuma shi ne kuma gaskiyar sunan naki ko dai la?ani ne?."

'' Eh to da yake sunan Innaya aka samin kakarmu wanda ta haifi Baffa da Abbi to shi ya sa ake kira da Dagori, amma ainahin sunana Aminatu.''

'' WOW ga ki da suna me daWi amma an Sata shi miye kuma Dagori? To gaskiya daga yau za a daina kiranki da Dagori tun da gaki da suna me daWi, tun da ainahin sunan ne ba a son faWa to a Winga kiranki da Minal ko Amal, Minat ai shi ma duk sunan ki ne.''

Washe baki ta yi don kan sunayen sun yi ma ta daWi ta dubi in da su Aimanah suke tana cewa.

'' Aimanah, Inty ku zaSa min wane ya fi?."

Suma dai murmushi suka yi don dukan su ba sa iya fushi da ita.

'' Ina ga kawai ki zaSi Amal kamar zai fi ko Aunty Khadijah.''

Aimanah ta faWi na ta ra'ayin tana duban Aunty Khadijah.

'' Kai Sis ni kuma sai nake ganin kamar Minat zaifi daWi.''

Inty ta faWi tana duban ta ita da niyyar ita ba ta zaSi na ta.


'' To ni ai zaSi na baku duk wanda kuka zaSa amma ni ba zan zaSi na Waya ba salon Waya ya ga ban yi masa adalci ba.''

Dagori ta faWa ganin duka su ukun ita suke duba. Daidai nan kuma Zainab ta kawo ma ta indomie.

KarSa ta yi ta fara ci, su kuma suka shiga cinka sunan har daga karshe suka tsaya akan Minat.

A nan suka yini har sai bayan magrib kamar yadda ya ce ya dawo Waukar su in da Aunty Khadijah ta ji kamar kada su ta fi don ta ji daWin zuwan na su sosai da za su ta fi ta ba su turaruka da mayukan gyaran jiki, har mota ta rakasu kamin ta koma ya ja suka ta fi.


Sai da ya biya da su wani supermarket ya yi ma su siyeyya kamin ya kai su gida.



*************

Bayan sati biyu

Da wani irin ?arfi yake kiran sunan ta wanda har gidan yana amsawa.

'' Mai babban Suna! Mai babban Suna!! Mai babban Suna!!!."

Da sauri ta fito daga kitchen jin Abbi yana kwala ma ta kira wanda tun da take da shi bai taSa yi ma ta ba.

'' Na'am Abbi gani!."

Ta faWi daidai lokacin da take karasowa gabansa.

Wani irin ?yak?yawan mari ya Wauke ta da shi ta Wago da niyyar magana ya sake kai ma ta wani ta yi taga taga za ta faWi da sauri Ya Ashraf ya ri?e ta.

'' mutunniyar banza kawai waton duk yadda nake tunanin ki kin wuce nan ko? To wallahi ba zan Wauka miki wannan iskanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login