Showing 48001 words to 51000 words out of 79609 words

Chapter 17 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1097

yi magana ya furta.

'' Kai! Habu daina ganina haka, da jikin tsufa, nan da za a saka gasar tseren gudu, da tsaf zan lashe zango farko. Sannan zancen kwanan Salame da Mai Suna sam ba zai yiwu ba, saboda Mai Suna da kuke gani ta raina Salame to haWin ba zai ba. Ni Win dai ni ce daidai Mai Suna don wannan dole sai da mai zafi tare da ita.''

Sun gamsu da zancen Innaya daga ?arshe dai aka ce Innaya da Salame su kwana nan su Inty suma suka ce nan za su kwana amma tuni Ashraf ya ma su jan ido akan ai ba gidan biki ba ne kwana za su yi damunta surutu.

Sun zo fita ne suka lura da ledar da Asad ya a jiye Abbi ya Wauka yana buWe wa.

'' Allah sarki kaza ce ya siyo da lemu.''

'' Kaza kuma ina take? Ba ni nan na san ni, ya siyowa tun da ni ce ban da lafiya." Dagori da tun da Baffa ya daka ma ta tsawa ta nutsu, jin zancen kaza ya sa ta zaburo da ?arfi tana mi?e wa zaune.

'' Subbuhallah! Ke! Mai Suna mene ne haka kuma? To dai kaza ba za ki ci ba.'' Innaya ta faWi cikin mamakin Dagori.

ShagwaSe murya ta yi har tana shirin kuka ta ce. '' To ni Innaya Saboda me,me na yi kuma?."

'' Saboda Asad ne ya kawo kin ga bama bari ki ci ba, ba mu sani ba ko mugun nufinsa ne zai cika a kanki, tun da bai samu damar shanye miki jini a can ba kin ga kada ya zo nan,ya yaudare ki da kaza ya shanye miki jini ko?." Innaya ta faWi fuskartar babu Wigon wasa ciki.

'' To ke Innaya waya faWi miki za a iya shanye wa mutum jini a cikin kaza?.'' Dagori ta faWi har da ?ar gudun,kwalla.

'' Ke! Mai Suna na raba ki, sufa babu yadda ba za su iya yi ba. Kin ga kawai ki bar mana kazar nan, mu ci.''

'' To kuma ai ba sai kun ci ba kada kuma a shanye maku jini.''

'' A'a mu kam sai mun ci ai ba abun da zai same mu tun da ba da sunan,mu a kai ba.''

Haba Dagori me za ta yi ba kuka ba tuni ta fara zabga hawaye cikin kuka ta ce. '' Aradu ni ko za a shanyen jini, sai na ci taya zanna kallon gawa ba hawaye Aradu sai na ci.''

Ashraf da ke dariya ya ce. '' To dai kenan yanzu kin yarda ko, shanye miki jini za a yi za ki ci kaza?.'' Cikin kuka ka shirSan ta Waga masa kai.

'' ?ata kwantar da hankali kin ji ko? Ba me sha miki jini, kuma za ki ci kaza.'' Mami da ke murmushi ta furta don ita sam lamarin Dagori bai Sata ma ta rai.

'' Aradun Allah ma Mami zan yi bismillah.''

Dariya ma ta ba su, daga haka suka yi sallama suka bar Wakin ya rage daga Innaya sai Salame, da Dagori da tuni ta fara cin kazarta har ta manta da irin zagi da cin mutuncin da ta yi wa wanda ya kawo kazar.

A resection suka samu Nene suka tafi don sam ba za ta iya zama a ciki ba, tana ganin abun da Dagori take ba don da su Win mutanen kirki ba ne, taya za tana zagin da cin mutuncin Wan su suna kallo ta san dole ne su ji ba daWi a ransu.



*************

Asad yana fito wa Office Win Dr ya wuce yana shiga suka gaisa ya dubesa ba tare da ya yi magana ba na wani lokaci can Dr ya ce. '' Asad i you okay.''

Sai da ya sauke numfashi kafin ya ce. '' Dr anya da kuka duba Yarinyar nan ba ku ga komai a tare da ita ba?."

Cikin Wan mamami Dr ya ce. '' Kamar na me kenan?."

Sai da ya gyara zamansa kafin ya ce. '' Ina nufin kamar ba abun da ke damun ?wa?walwarta?."

'' No gaskiya ba wani abu mai kama da hakan,a tare da ita. as you said, look carefully to mun ma ta duk abun da ya da ce amma sam ba ta tare da wata lalurar bayan harbi sai me Malaria ita kamar yadda na faWa ma a baya sakamakon cizon sauro ne, amma bayan wannan ba wani abun.''

?an shiru ya yi na second kafi ya ce. '' kana nufin ba ta tare da ciwon hauka kenan? Her memory is normal?. ''

'' Kwarai kuwa haka nake nufi.''

'' Ok thanks Dr.'' yana faWin haka ya mi?e tare da yi masa sallama ya fita aransa yana faWin.

'' Waton dai idan na gane Yarinyar nan, ba abun da ke damunta face tsabar tsantsagwaron iskanci? Lallai watan koya miki hankali zai soma don ni ba na to take responsibility.''

Wayarsa ce ta yi ?ara ya Waga. Ba tare da ya yi magana ba, jin da mai kiran ya yi an Waga ya sa ya, ce. '' Oga mun gama duk wani abu da ya da ce. Yanzu haka muna CID record da su sai dai Wayan da muka samu a cikin gidan kamar ba rai a jikinsa amma mun samu mun aika shi nan, asibiti yanzu haka Doctor's na ba shi kulawa sai dai har zuwa yanzu ba mu san a wane hali yake ke ciki ba.''

'' Ok that's good.'' yana faWin haka ya yanke kiran tare da fita harabar asibiti parking lot ya nufi kai tsaye wajen da motarsa take ya nufa ya shiga tare da mata key yana barin asibitin gabaWaya.

Daga nan gida ya nufa don ya gaji yana son ya Wan samu nutsuwa, ko ya,ya ne ga kuma jinin da duk ya Sata masa jiki yana shiga gidan daman ba kowa kai tsaye sama ya haura ya rage kayan jikinsa ya faWa toilet, wanka ya yi sosai sai da ya tabbatar ya gamsu da yanayin jikinsa don duk sai faman wanke jiki yake saboda tsabar ?an?ami da yake ji na jinin da ya taSa shi.

Ya Wauki tsawon lokaci kafin ya fito daga toilet Win yana fitowa ya zura janlabiya ya tada sallar Isha'i da bai yi ba sai da ya gabatar da Sallah, ya jima a zaune yana jero Addu'a kafin ya mi?e ya haura kan gado ?aramar laptop Winsa ya janyo wanda yake gudanar da ?ananun bincikesa aiki idan baya son shiga laboratory.

Wayar da ke gefensa ce ta fara ringing duban screen Win ya yi ganin mai kiran ya sa ya safa sumar kansa, tare da cigaba da aikin da yake kiran ne ya yanke wani ya sake shigowa duban screen Win ya sake yi still dai wannan number ce, sanin da ya yi muddin ba Wagawa ya yi ba to fa ba daina kira za a yi ba ya sa ya Waga tare da saka wayar a speaker.

Shiru ya ratsa na wani lokaci can cikin murya shagwaSa da sangarta da alamar mamanlakiyar muryar ya iya sanfarata aka fara magana. '' Oh my soulmate now, son of God ka yi min adalci ke nan? So why would you leave without letting me know? Hakan na nufin ban da wani muhimmin a wurin ka ko?."

Ta furta tana sake ma?ale murya cikin sigar jan hakali. Ba tare da ya daina abun da yake ba ya sanya hannun Waya ya safa sumar kansa, amma bai yi magana ba sai ma cigaba da ya yi da aikinsa.

Jin bai yi magana ba ya sa ta fashe da kuka shagwaSa. '' My na san fa kana jina dan Allah kamin magana mana ko na ji sanyi.'' Ta faWi tana Wan karawa kukanta sauti ?aWan wanda ba zai zamo ta kura ga mai saurare ba. Sai dai a wurin Asad tuni ya fara hau masa kai cikin murya mai Wan ?arfi ya ce .

'' Please, please, leave me alone zuwa yanzu ya kamata a ce kin fahin ce ni, so please ba na son irin wannan I refuse kuma kin sani.'' Yana kai nan bai jira jin me za ta ce ba ya yanke kiran tare da kashe wayar gabaWaya.

Duk ma sai ya ji ba zai iya aikin ba don ta ?ara, ?ara masa wani Sacin ran bayan wanda waccan mahaukayar Yarinyar ta sa masa. Kwanciya ya yi tare da ya uban tsaki a karo na barkatai.......



To ma su karatu wannan page Win ina jin shi ne na ?arshe a gaskiya yadda kuke nuna min bai min dad'i because littafin nan free book ne amma like da share su gagareku, ina ganin a comment section Way Way ku ne suke comments. Idan ba ku son posting ku faWa min sai na dakata
'
Comments like share pls =?O?=?O?=?O?=?O?=?O?=?O?

Ta ku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???

*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?





031


Washegari tun da safe Mami ta sa ?an Aiki suka shirya abincin da za a kai wa ?an asibiti. Nene, da su Aimanah aka sanya driver ya kai su, don ita Mami akwai wani meeting da za ta je na wurin aikinta.

Sun samu Dagori jikin da sau?i sosai, Inty ce ta zuba ma ta abinci planted ne da soyayen kwai wanda aka masa haWi tamkar soup, ta mi?a ma ta. KarSa ta yi tana faWi. '' Inty wancan Wayar kular mene ne a ciki?."

Murmushi Inty ta yi. '' Kayanciki ne da.....''

'' An shi nan! Na ce an shi nan.'' Ta faWi tana mi?a ma ta Flash Win da ta ba ta. KarSa ta yi tana faWin.

'' Sister lafiya kuwa?."

'' Ban sani ba kin ji yanzu don tsabar ba ki da mutunci, da kuma ba ki Wauki mara lafiya da muhimmanci ba, ga nama shi ne za ki haWa ni da wani dankalin ku na birni. Anya Inty, ke kam dai albasa ba ta yi halin ruwa ba. Alhalin Mami da Abbi, Aradu duk ba haka suke ba...''

'' Ke! Rasa ?unya, ba na son iskanci ke abun da ki ke, gadarsa ki yi ne? Kaf cikin zuri'ar mu babu mai irin halin ki. Kin san ki daina ganin ba ki da lafiya yanzu sai na tashi na saSa miki kamanni ko?." Innaya ta tare da don na ta ga tana son wuce gona da iri.

Nene da ke fitowa toilet da ta shiga kama ruwa ta zabga ma ta wata uwar harara. Ita dai ba ta san ya za ta yi da lamarin Dagori ba, don kullum abun na ta ?ara gaba yake ta rasa ta ina suka kuskure akan tarbiyyar Dagori don sam halin da take ba Waya da su ne suka, Worata a kai. Daidai tana zauna a kan kujerar da ke Wakin ta ce.

'' Ai Innaya da kin bar ta wannan Yarinya da a asibiti na haiheta tsaf, zan iya rantse wa akan saura min ita a ka yi, daga dangina har na Mahaifinta babu Waya mai irin halinta. Aradu haka ake fama da ita ko a RUGA, na za ci idan ta shigo birni ta sauya amma ina yanzu fa dubi ko wannan abun da ya faru da ita samm bai wani sauya ta ba. Ya zame ma ta darasi a rayuwa ba. Ai dai Allah ya ba ta lafiya mu tarkata mu koma ruga, kowa ma ya huta. Gwanda can da suka saba da halin ki.''

Daidai lokacin Inty ta gama subawa Dagori kayancikin, ta mi?a ma ta sai da ta kai naman bakinta kafin ta ce. '' Ai kuwa Nene wannan karon ha?uri kawai za ki yi, don Aradun Allah ban ga me mai da ni ruga ba. Ai ni tuni na ga wurin zama, ni kuwa me zan yi a ruga? Ai ni da ruga sai dai na kawo muku ziyara kawai.''

'' Wannan ne, kuma ba ki isa ba. Babu ta yadda za ki zo ki Winga Wagawa mutane hankali tun da dai ba canza hali za ki yi ba.''

Cikin marairaice wa Aimanah ta ce. ''Dan Allah Nene ki bar mana Sister a nan wallahi muna jin daWin zama da ita.''

Dagori da zancen Nene bai wani dameta ba don ta san dole ne a bar ta ko da kuwa ba a so ta ce. '' Kin ga Aimanah kwantar da hankali ai ni zama daram ba in da za ni, yooo ko kuna so ko ba ku so ai dole na zuna don ni kin ganni nan ?aWangaren bakin tulu ce, abar ni na Sata ruwa a kuma kashe ni a fasa tulu, to ya muka iya don ni abun nema ne ya samu wai matar driver ta haifi taya kin ga sai ai ta garawa ko.''

Dariya suka saka har Innaya ganin yadda ta ha?i?ance kuma sai cin namanta take hankali kwance.

'' To wannan ne kuma bi ki isa ba koma wa ruga ya zama wajibi gare ki ......''

Turo kofar da a ka yi tare da sallama ya dakatar da ita daga maganar da take. Kamal ne ya shigo tare da wani hannunsa duka biyu ri?e da ledojin wanda karab sai a kan, idon Dagori ta wani washe baki tana duban ledojin hannunsa.

Gaishe da su Innaya da Nene suka yi su kuma su Inty suka gaida su.

'' Beauty rigima ba magana? To ya jikin?."

Turo baki ta yi gaba tare da turo harshe ta lashe baki. '' Uhmm ni fushi nake da kai.''

'' Subbuhallah! Me kuma na yi? .'' Ya faWi yana zama a gefen gadon.

'' Ba kai ba ne ka gudu ba ka ba,ni kuWina ba. Wanda a sanaWin su a ka nemi shanye min jini.''

Dariya ya Wan yi mara sauti. '' Oh My Beauty ki yi ha?uri.'' Ya faWi yana ri?e kunnuwansa.

Tuni kan ta ya ?ara girma ganin ana ba ta ha?uri kuma, a ce babban kamar Kamal. '' To zan ha?ura amma sai ka ba ni kuWina, don Aradu sanaWin kuWin nan ba kalar tashin hankali da ban gani ba. ''

'' To shi ke nan zan bayar kin ji? Yanzu ba ki ba ni amsa ta ba ya jikin naki da sau?i?."

'' To jiki Alhamdullah, sai dai godiya sannan likita ya ce idan ana son jikina ya yi ?wari da kyau sai ana siya min kaza da kayan daWi.''

Ba Innaya da ba ta gama sanin halin Dagori ba. Ko Nene, da Salame sun sure da lamarinta don duk ida kake tunanin Dagori ta wuce nan Innaya da mamaki ?aryar Dagori ta kusa sumar da ita ta ce.

'' Ke! Mai Suna, yaushe ne likita ya faWi haka? Bayan muna tare da ke.''

'' Kai Innaya Wanzun ne fa ki na banWaki ya shigo yake sanar min da haka, ko ba haka ba Salame.'' Ta faWi tana duban Salame.

Salame dai ba ta iya cewa komai ba to me za ta ce bayan ita ba ta san lokacin da aka yi haka ba. Kuma idan Dagori tsaf idan ta ce ba haka za ta nemi karta mata rashin mutunci.

'' Shi ke nan Beauty na sani wannan gaskiya ne. Ba dai kaza ba? To ki kwantar da hankali yanzu nan zan je na siyo ki." Kamal ya faWi yana yar dariya, wanda suka shigo tare ne ya ce.

'' Amma iya kazar a ka ce ko har da wani abu?.''

Dagori da sai a yanzu ta lura da wanzuwarsa ta furta. '' Eh to a yanzu dai iya abun da suka faWa kenan. To ban mu san me za su ce gaba ba.'' Ta furta ita adole gaskiya take faWi.


Ledojin hannunsa ya Wauka daga ?asa ya mi?a ma ta. '' To ga wannan yanzu bari mu je sai mu siyo kazar. Ita kawai ki ke da bu?ata ko da wani abun?." Ya yi maganar yana mi?e wa.

Kafin ta yi magana Innaya ta yi karab. '' Ka ga Kamalu ka bar shi kawai ba sai ka siyo ba wallahi Mai Suna ?arya take ma. Kai ka taSa jin idan mutum ba karyewa ya yi ba, a ce sai ya ci kaza? Kuma godiyar Allah ne kawai da ba ta da shi jiya nan Mai sunan Malam ya siyo ma ta kazar ta ci. Ka duba ko da kuka nama ne take ci, don dai kawai ita ta zama kura ka tafi kawai abun ka ba sai ka siyo ba.''


'' Amma Innaya da kin bari na siyo ma ta tun da tana so ai, ba wani abu...''

'' Kamal na ji sunanka ko?....'' Nene ta faWi . '' To mun gode sosai da kulawa amma wallahi ka ji na rantse ba za ka siyo ma ta ba tun da ita samm ba ta da kunya balle hankali, kamar yadda Innaya ta ce, kafiyar ka kawai.''


Daga haka bai sake magana ba don ba zai iya musu da manya ba ya juya ya ma su sallama zai tafi karab ya ji Dagori ta ce. '' To Kamal za ka tafi ina kuWina?."

Waigowa ya yi yana murmushi ya sanya hannun cikin aljihu wandonsa ya ciro kuWi ma su Wan yawa wanda shi ma bai san ko nawa ba ne ya mi?a ma ta. Nan ma abunkinsa ya ajiye ma ta wasu a gefenta.

Tuni ta washe baki don wannan kuWi ya rage ma ta wani zafin hana sa siyo ma ta kaza da su Nene suka yi.

'' Na gode fa Allah biya. Duk da, ai gumina ne saboda kuWi nan ba irin wahalar da ban sha ba.''

Murmushi ya sake yi. '' Beauty rigima Allah dai ya ba ki lafiya.''

Daga haka suka fice daga Wakin.

'' Muhammadur Wan Abbdallah! yanzu ke Mai Suna abun da ki ke kenan maula? To Allah shirye ki wannan hali na ki sam ba mai kyau ba ne.''

'' Hmmm, haba dan Allah Innaya wane kuma kalar maula a zaune ?alau nifa kuWin nan, hak?i na ne, don rawa na yi mutane suka watsa min ko don ba ki san cewa sanadiyyar kuWin nan ne har ya sa aka sace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login