Showing 60001 words to 63000 words out of 79609 words

Chapter 21 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1092

ce ta haWa su ba, don kaf duniya babu fuskar da ta tsani ta gani kamar fuskarsa ba don tana da wani buri a?asan ranta ba da tuni irin dukan, da ya ma ta ya sa ta nemi a mai da ta ruga amma ina samm, ba za ta iya bankwana da wannan kayan daWin ba.


A jere suka fito saura ?iris su yi karo da ita. '' Kai Sis ba dai nan kika tsaya ba kuma kan hanya?." Inty ta faWi tana gyara zaman jikarta da ta kusa suSucewa.

Ba ta amsa ma ta tambayar ta ba sai ma cewa da ta yi. '' Amma gaskiya kun fiya nawa yanzu dan Allah duk me kuke jira sai yanzu kuke fitowa?."

'' A'a Sis kenan sabon shiga muna nan da ke sai an ce ki yi wannan uban sanmakon kin?i. Duk can takalmin mu suka katse.'' Inty ta faWi tana yar dariya.

'' Ke ma dai ?ya faWa ni fa na kasa gane ma ta idan za mu tana murna da kuma an koma breakf shi ke nan kuma sai ta koma wata silent kuma sai ki ga tana murnar dawowa.'' Aimanah ta yi maganar

'' Innalillahi! Wai ni kam za ku zo mu tafi ko dai na tafi kawai ku sai kun gama wannan tsinan nan surutun naku da ba ya ?arewa?." Ta faWi idonta na kan kofar da ake buWe wa fuskarta ce ta faWaWa da murmushi ganin mai fitowa.

'' Abbi ina kwana?." Ta faWi tana wani runsunawa don kwanan nan wani sabon salon ladabi ta bijiro da shi.

Shi ma murmushi ya mayar ma ta da shi. '' Lafiya lau ?an makaranta ya karatun in jin dai ana mai da hankali?." Sunnar da kai ta tana Wan shafa goshin kanta

'' Hmm, Abbi wallahi Sis ba wani mai da hankali da take, in ma karema zance kullum sai ta yi faWa da ?an ajinsu, sai cin zalin su take ka san tafi su girma....''

'' Ke Inty ke na tambaya ne? Ki bari wadda na tambaya ta ba ni amsa.'' Abbi ya katse inty da ta yi zurbur wajen ba shi amsa.

'' A'a bar ta kawai Abbi ai ba son gaskiya su ?an iskan yaran kin tambaye su dalilin da ya sa nake dukan su? Yara sai shegen rashi kunya da rashin tarbiya, ga uwa uba rashin girmama manya, to ni kuma shi ya sa nake koya ma su tarbiya tare da gyara ma su zama.''

Shi kam Abbi dariya ma ta so ba shi yadda ta ha?i?ance, bilhakki da gaskiya ita wai gyara yara za ta yi.


'' To na ji mai babban suna yanzu dai abun da nake so da ke ki daina dukan yara mutane kin ji ko? Idan sun miki wani laifin ki sanarwa, Aunty Winku ba kyau Waukar doka da hannu muddin akwai na gaba da kai a wurin.''

Abbi ya yi maganar cikin salon da za ta fahimta, a irin dubara ta su ta manya. Amma sai dai mutunniyar ta ku wai a banza ?iba a kunne rama a ta kashi. Sai ma cewa da ta yi.

'' Abbi Aradu yara ne samm zuciyata ba za ta iya Waukar iskancin su ba ta ya ace fa duk na fisu girma amma samm ba sa iya girmamani haba Abbi ya kamata kaduba wannan lamari.''

'' Na ji na fahimta amma ke ma ki bi umurnin da na ba ki muddin ke ma ki na son na ?asa da ke ya ga girmanki kuma ya bi abun da ki ke so.''

Abbi da ya fahimci Dagori samm nasihar da ya yi ma ta, ta shiga ne ta kunne dama ta fita a na hagu ya faWi yana kallon reaction na ta.

Shiru ta yi ba ta yi magana ba, ganin haka da Abbi ya yi ya za ci cewa ta gamsu ne da bayanansa ya ce.

'' To ya yi shi ke nan kuna iya tafiya kada ku makara.'' Ya faWi yana saka hannusa aljihu wasu chocolate ya Webo ya bawa kowa har yana ?awa Dagori fiye da yadda ya bawa su Aimanah.

Tuni ta washe baki tana faWin. '' Muna godiya Abbi Allah biya da gidan aljana.''

Murmushi ya yi yana amsawa da amin daga haka kuma suka shiga mota driver ya ja suka bar gidan.



**********

Asad zaune yake cikin ?ayataccen Office Winsa wanda idan ba an faWa ma ba, to fa ba za ka taSa cewa wai wannan Office Win a Nigeria yake ba. Kamar kullum yana cikin shigarsa ta ?ananun kaya kamar yadda ya saba cikin salo da hikima yake sarrafa supercomputer Winsa da yake ta faman aiki ai kai, tun da ya shigo Nigeria sam bai samu hutu ba daga wannan sai wancan daga wancan sai wannan kullum cikin aiki yake. Kallo Waya rak, za ka yi masa ka fahimci cewa ya rame ya Wan yi duhu kaWan.

Ya ji lokacin da aka murWa handle Win kofar don shi mutum ne mai ?arfin ji koya motsi yake to fa zai iya jinsa amma sam bai Wago daga abun da yake ba. Kamshi da ya ji ne ya sanar da shi ko waye a ta cikin glass Win fuskarsa ne ya lumshe ido gami da matse hannunsa.

Cikin takunta na isa da ?asaita ta fara taku ?arar takalminta yana jin saukarsa har cikin ?wa?walwarsa sakamakon bayason ?ara ko ya take tana damunsa ne. ?arasowa ta yi daidai kujerun biyu da aka ta nada saboda ba?i ta je ta yi masauki a kai don ta san shi dai ba cewa zai yi ta zauna ba, don sanin halin aka ce ya fi sanin kama.


'' Now that's what you should do ace ka san cewa saboda kai ne nake zaune a can amma ka yi tafiyarka ba tare da ka sanar da ni ba? Ni ba ma duk wannan ne damuwata ba illa yadda tun da ka zo ko kira balle kuma sako, haba my soulmate please tell me ko na ma wani abun ne ban sani ba wallahi I won't to do it again okay.''

Ta faWi har tana haWe hannayenta alamar ban ha?uri ba ta yi aune ba sai kwaranyan hawaye ta gani suna ma ta kwanya tamkar in dararo....




Taku har kullum mai kaunar
MRS AWWAL =???

https://whatsapp.com/channel/0029Vb7Jri19mrGWdgsRwZ3M





*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?



040


A hankali ya sauke wani nannauyar numfashi tare da shafa sumar kansa, duban ta yake amma ya kasa magana. Sam shi ba ya son takura ko wani abu da zai Sata masa a rai amma ya lura cewa kullum suka haWu to fa sai ta sakar masa ciwon kai saboda kukanta.

Cikin muryar kuka ta ce.

'' My soulmate please tell.....''

Da sauri ya Waga ma ta hannu alamar ya isa jin da ya yi za ta sake ruWasa a hankali cikin cool voice Winsa ya fara magana, wanda ba dan da cewa daman ta tattara hankali ta wurinsa ba da ba ta yadda za ta iya jin shi.

'' Dan Allah Maysah ki daina wannan shirmen na ki. Ya isa haka ban san ko sau nawa ki ke da bukatar na sanar da ke abun da, kullum kin san shi ba. Wanda kalma ce da ya kamata a ce kin haddace ta a ?wa?walwarki so please ki fita daga rayuwata, saboda babu abun da yin hakan zai amfane ki da shi. Aure ki ke so ko soyayya kulawa duka wannan ba za ki samu daga wurina ba... You see, continuing to pursue her is useless. Maysah na san cewa ki na da tarin masoya ma su son ki, to ina mai ba ki shawara da ki fitar da Waya daga cikin waWannan mutane ki aura ke mace ce, lokacin ki kurarre ne.''

Shiru ya yi yana dafe kansa jin yana sara masa don ya daWe rabon da ya yi magana irin wannan, mai tsawo haka.

Maysah da ta daskare a kan kujerar da take hawaye kuwa tuni suka ?afe tsabar tashin hankali da ta shiga don wannan hukuncin da Asad ya yanke ma ta daidai yake da ya yanke ma ta duk wani jin daWi na rayuwa, kai zai fi ma ta sau?i a ce rabata ya yi da duniya a kan dai wannan hukuncin mai sauri da ya ma ta.

Cikin murya mai nuni da irin kunci da zafi da ke zuciya wanda amon muryar ke fita da alamun sare wa ta ce.

'' Ba zan iya ba! My soulmate ba zan iya ko da kuwa na ce zan iya na san cewa ?arya nake, My soulmate kai Win rayuwata ne. Ka sani cewa ni taka ce wallahi Mom da Dady wallahi saboda kai suka haife ni, rayuwata ba ta da wani amfani idan babu kai a cikinta. What do you want me to do or do you need my heart to pursue?.''

Ta furta tana sake ?arawa kukanta sauti. Da sauri ya sake runtse idonsa gami da shafa sumar kansa yanayin fuskarsa na sauyawa ya wani sake tamke fuska cikin, tsare gida ya ce.

'' I said, have you seen how crazy I am? Na rasa har sau nawa ki ke da bukatar sani na tsani wannan kukan ba na so duk wani abun da zai zame min Headache amma ke na lura burinki kullum ki na Woran wani zafin kai fiye da wanda nake da, Maysah ba na son yawan magana a kan abu Waya kullum, yawan surutu ba halina ba ne amma kin kasa fahimtar hakan duk saboda irin wannan abun ne na shirme ya sa na tarkata zancen soyayya na jefa shi kwandon shara. I forbade you from coming to my workplace, why? Kuma ke a haka ki ke tsammanin cewa zan so ki bayan duk abun da ki ke ki na yin wanda ba na so ne? Please and please...''

Shiru ya yi don daga haka ba zai iya ?ara ko kalma Waya don zai iya cewa ya jima bai yi zancen mai tsawo irin na yau ba.

Mi?e wa ta yi fuskarta ta yi fayau da ita hawaye duk sun wanke ma ta fuska.

'' My soulmate yanzu ni kake kira da ciwon kai? Now the benefits of love are gone, hmm, the truth is that love is not lawful for me. Zan tafi amma ka sani ba wai yana nufin cewa na daina sanka ba ne, Asad Abubakar Majoh ka sani sanka kamar jinin jikina ne wanda ba zan iya rayuwa babu shi ba zan tafi amma ka sa aranka zan jira duk lokacin da ka ji ka shirya aure to don Allah ka tuna da cewa akwai wata mai dakon soyyayar ka a gefe. Ko da zan mutu ban yi aure ba zan jira ka I love you Keep this in your heart forever, Maysah, and say,.''

Tana kai nan ba ta ko jira mai zai ce ba ta juya abun ta ta yi tafiyarta.

Sun kuyar da kansa ya yi ?asa yana sauke numfashi.


**********

'' Hey, what kind of nonsense is this? I'm teaching you to sleep. ''

Matar da ke tsaye kan Dagori da ke ta faman bacci ta ta Waura kanta a kan table take ta sharar bacci ta faWi tana Wan dukan kafaWarta.

A Wan tsorace ta farka. ''Lokacin cin abinci ya yi ne?." Ta faWi tare da yin mi?a tana mi?e wa.

'' You're crazy, go back and sit down and tell me everything I taught you. ''

Dagori kuwa ware ido ta yi tana duban Malamar tare da 'yan ajinsu da duka ita suke kallon.

'' Tabb yooo ai sai ki yi ni ko kashe ni za ki yi na san me kika faWa. Kin ga Malama idan za ki min Hausa ki yi idan kuwa ba za ki yi ba ki min fulatanci amma ni ina nake jin abun da ki ke faWi ki na magana kamar ki na kwalanniya.''

Tuni yaran da ke jin Hausa a cikin ajin suka Wau yin dariya don kam ta ba su dariya. Malamar ce ta tsawatar ma su tana tambaya Waya daga cikin su me take cewa da yake Malamar ba bahaushiya ba ce.

Tuni wata yar kanzagi ta sanar da Malamar me Dagori ta ce.

'' You're telling me that. '' Malamar ta faWa tana nuna ta.

'' Ai kuma sai ki yi wai mahaukaci ya faWa rijiya ya ce wanka ma nake yi, idan kin so na yi magana Aradu ki yi Hausa idan kuwa ba haka sai mu kwana nan ba wahala, don shi yafi komai sau?i wai cire wando taka.''

Dagori ta faWi. Lura da ta yi dai da alama Malamar ba ta jin Hausa ta ce. '' Ni kin ma zo kin tsayan a kai ga shi sai tashin wari ki ke, Aradu har ya fara hawa min kai, anya wannan na wanka kuwa ba tsaka tsami take ba? Kai da alama dai kam don wannan uban wari ba a banza ba Aradu ko garWi albarka.''......


Hmmmmmmm >?? Dagori


A gaskiya yanzu yadda kuke sam ban jin daWi haka a ce like da share na gagarar ku, da na ce zan kyaleku ne kawai amma idan ban sanar da ku ba ai ba ku sani ba.

To dan Allah ku Winga like da share yanzu a haka kuke son book Wina na gaba ya zama free kuwa?


Dan Allah na ga sauyi a wannan page Win.


Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???
*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.



041




'' Wai ni kam lafiya kuwa kin kira ni ki na cikin matsala na zo kuma sai kuka ki ke? Ko daman kin kira ni ne don na zo na kalli kukan ki ne?.''

Ta yi maganar tana duban ta yadda ta wani rungume filo, sai faman darzar kuka take sai ka ce wanda aka aikowa sakon, mutuwa. Cikin muryar da kuka ya ci ?arfinta ta fara magana.

'' Ruky rayuwata ba ta da sauran wani amfani! Zuciyarta na gab da yin binWiga ta tarwatse, numfashina gab da daina aiki, ban san ya zan yi ba Ruky na rasa madafa.''

Cikin ruWu da kiWima Ruky ta hauro kan gadon ku sa da ita. Dafa ta ta yi. '' Maysah me ke faruwa ne? Ki sanar da ni sai wanka mai kama da jirwaye ki ke yi min wanda na ka sa fahimtar in da zancen ki ya nufa.''

A hankali ta kwashe komai da ke faruwa ta sanar da ita sai da ta gama tsaf, tana sauraron ta. Tsawon lokacin ba ta yi magana ba jin shirun ya yi yawa ne ya sa Maysah cewa. '' Ruky da ke nake magana anya ki na tare da ni kuwa? .''

Wani uban tsaki Ruky ta yi. '' Amma wallahi Maysah kin ji kunya kuma, kin yi asara, yanzu dan Allah tsabar zubar da aji har ta kai ki ga kamar Asad yana duban cikin idonki yana faWa miki wai ki fita daga rayuwar shi? Kuma tsabar kin bawa kare zuciyarki wai har ki ke kuka a kan shi, wallahi ni na ji daWi da har ya iya sanar da ke gaskiyar da ke ransa kuma yake iya tunatar da ke cewa ke ma Win ki na da tarin masoya, ko ba komai ya san cewa ba wai kin yi kwantai ba ne ko kin rasa mashinshi ni. Please Maysah ki farka daga wannan bacci na ki mara amfani.''

Ta kai ?arshe tana kwantar da murya cikin amo mai nuni da lallaSawa. Sai da ta ja majina kafin ta Wago rinannun idanunta ta suka koma tamkar idon zomo ta ce.

'' Ruky ba za ki iya gane kunci da zafi da nake ji a zuciya ba ne Ruky ina son Asad ina ?aunarsa Ruky I love Asad for ever why ya ka sa fahimta ta Ruky ban da kyau ne? Ko ban da ilimin? Ko dai ban kai mace da Asad zai so ba ne?..."

Kuka ya ci ?arfinta wanda ya hanata ?arasa abun da ke ranta.

Ruky cikin tausawa ?awarta don ta fahimci halin da take ciki, ta janyota jikinta. '' Please Calm down okay duka wannan ba gaskiya ba ne Maysah ki na da kyau wanda duk wani Wa Namiji yake da bu?ata a wurin 'yan mace, ki na ilimi zama haka na addini uwa uba ki na da dukiya wanda kowa ya san family Jarfata babban family wanda suka gaji arziki ba taka haye ba. Ban don ma so makaho ne bai san daidai ba ina ke ina kula Asad wanda tarihi ya gama tabbatar da cewa shin Win daga tsatson matsiyata ya fito har me za ki yi da shi, amma ina so ki fitar da Asad Abubakar Majoh daga rayuwar ki kamar yadda ya bukata. Ki fitar da Waya daga cikin ma su kawo ?o?on baran su gare ki. Ki tuna daga ciki, akwai 'ya'yan governor's akwai na sarauta da manyan manya ma su hannun da shuni a ?asar nan why ba za ki fitar da mutum Waya daga cikin su ba.''

A hankali ta zame daga jikin Ruky tana sauke nannauyar ajiyar zuciya.

'' Wallahi duk waWannan da kika lissafa ba su gabana saboda ba su zuciya take so ba Asad Win kawai take muraWi wallahi ko da a ce bai da komai na ji na gani zan auresa kuma zan zauna da shi balle kuwa Asad duk ya fi waWannan da kika jiro Saboda shi yana neman na kansa ne su kuwa sun dogara ne da dukiyar iyayensu saSanin shi da yake tsaye da ?afafunsa wanda ni duk ba wannan ne, gabana ba shi Win shi nake kauna kuma zan jirasa komai ni san zamani. Ko da kuwa hakan na nufin zan mutu ne ba tare da na yi aure ba.''

Tun da ta fara magana Ruky ta saki baki da kunnuwa take saurarenta har ta gama magana ba ta ce da ita komai ba don ta fahimci cewa ?awarta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login