Showing 66001 words to 69000 words out of 79609 words

Chapter 23 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1096

a cikin gidan nan, to a kan me zan takura salon cibi ya zama ?ari ?ari kuma ya zama ?ababa, to ba da ni ba. Yanzu da ka fahimta da kanka ai shi kenan ko?, nan-nan na faWa ma cewa Maysah ta dawo ba tare da ta sanar wa kowa ba, mai ka faWa? Cewa ka yi ina sa ma ta ido da yawa to ya kake son na yi?."

Bai tamkata ba don jin cewa Maysah na cikin damuwa duk ya bi ya kidama shi. '' My Daughter me ke faruwa? Waye ya taSa min ke? Me ki ke so ne?."

Ya jero ma ta tambayoyin cikin za?uwa da son jin ta ba shi amsar da yake da bu?ata.

A jiye spoon Win hannunta ta yi kamin cikin shagwaSa ta fara magana. '' Dady ka kwantar da hankali ba komai kasancewa idai ina cikin damuwa kai ne mutum na farko da ya kamata ka sani ka kwantar da hankali ba abun da yake damuna am better ok.''

Ta faWa cikin salon da za ta kwantarwa Mahaifinnata, hankali sannin da ta yi cewa shi Win mai nuna damuwa ne a duk kam nin wani abu da ya shafeta.

Tamkar wanda ya yi gudun tsira haka ya sauke numfashi mai nauyi, wanda tun lokacin da Mommy ta sanar da shi abun da ke faruwa yake ri?e da shi.

'' To haka nake son ji Maysah kin san kaf duniya ba abun da nake so da ?auna sama da ke don Allah ki daina Waga min hankali irin haka, kuma ina son ki dawo da walwala ki kamar a baya kin ji ko?."

Ya yi magana cikin nuna tsantsar kulawa da kwantar da murya tamkar ba ?ar shi yake yi wa magana ba.

Murmushi ta yi tana amsawa. '' In sha Allah Dady kada ka dumu.''

'' Hmm.'' Kawai Mommy da ke zaune ta faWa don ba yau ba ne karo na farko da ta ga haka amma abun na Alhaji kullum daWa yin gaba yake, ta kasa fahimtar wannan wane kalar so ne yake yi wa Maysah don so tari yakan nuna kamar ya fita son Maysah duda cewa, ita Win ita ce ta haifeta amma bai shakka kowa bai kuma kunyar nuna damuwarsa a gaban kowa idai akan damuwar Maysah ce. Duda kasancewa, ba ita kawai ya haifa ba amma ita Win ta zama mafi soyuwa a cikin ?a?an shi.

So da kaunar da yake nuna ma ta ne shi ne sila kuma ya taka muhimmiyar rawa wurin sangarta,ta.

Mas'ud Jarfata shi ne asalin sunan Mahaifinta haihafen Wan garin Kaduna wanda kowa ya san family Jarfata babban family ne wanda ya yi fice kuma ya yi suna afannin kasuwanci, da kuma karatun nasara, wanda idai ba su zo na Waya ba to tabbas za su zo na biyu a cinin jerin manya-manyan ?an kasuwa ma su hannu da shuni na cinin jahar Kaduna. Kamar yadda ?a'idar family Jarfata take ya ma su jiki tun Yaro ko Yarinya ya ta sawa ake saka shi a makarantar boko wanda da kuma nuna masa muhimmanci kasuwanci, don mafi yawa daga family sun fi karatar business. Duda akwai likitoci da kuma jami'an tsaro da Alkalai amma sun fi karfi a kasuwanci.

Haka take a wurin Mas'ud wanda ya tashi da himma da kwazo wurin sana'arsa wanda yake sarin kayan daga ?asashen ?etare zuwa kasatai Nigeria wanda kuma, cikin iyawar Ubangiji ya sa ma shi hannu ya yi fice da suna, fiye da tsammani. Luba wato Mommy ?ar ?anwar Mahaifiyar shi ce wanda tun tasowar shi yake so da kaunarta haka yake ita ma a na ta Sangaren, ba a wani Sata lokaci ba a ka Waura ma su aure.

A shekarar farko Allah ya azutasu da samun ?aruwa ida suka samu ?a' mace sun yi murna kuma sun nuna matukar farin cikinsu Ranar suna yarinya ta ci suna Khadijah, wanda ta ta so cikin gata da so da ?auna shekaru biyu tsakanin suka sake samun ?aruwa, in da Allah ya zurtasu da samun ?aruwa Wa Namiji wanda ya ci suna Muhammad suna kiran shi da Ammar.

Ammar na da shekaru uku aka haifi Maysah ida Alhaji Mas'ud ya ba da mamaki don ya yi abun da bai taSa yi ba tun da ya Wora ido kan Maysah ya ji wani irin so da ?aunarta ya shige shi, fiye da duk na sauran yaran, da aka haifa masa wanda kuma ya kasa Soye hakan Maysah ta ta so cikin gata da so da ?auna Mahaifinta wanda tun Mommy na yi masa magana akan ya daina don kada sauran yaran su fahimci haka, amma ya yi fafur a kan shi fa bai ma ga abun da yake ba a haka ta gaji ta zuba masa ido.

Tun daga kan Maysah kuma ba su sake samun haihuwa ba ta tsaya cak, 'yan uwa ba yadda ba su yi da Mas'ud akan ya ?ara aure ba tun da Mommy ta daina haihuwa amma ya kafe don shi Mutum ne mai kafiya ya kafe akan ba zai ?ara ba haka kuwa aka yi.

Maysah ta ta so da wani irin farin jini in da tun a cikin dangi ake nuna ana sonta amma ita ba kowa gabanta in da take ganin ma soyayya tamkar shirme ce, ko hauka haka a cikin yayun abokanta da ma abokan kasuwanci Mahaifinta amma sam ta ?i bawa kowa daman akan haka. Wanda kuma gudun Sacin ranta ya sa Mahaifinta zuba ma ta ido don Khadijah bai bari ta gama karatu ba ya yi ma ta Aure in da ta ci gaba da yin sa a gidan mijinta.

Duka sauran yaran shi ne mai zaSa ma su in da za su yi karatu saSanin ?ar gaban goshi da ya ba ta zaSi in da a take ta ce ita a Istanbul take son karutun sanin da ya yi tana ?aunar garin tun zuwanta na farko garin ya burgeta, ya sa bai yi mamaki ba ya ammin ce. Ashe rabon ta haWu da ta ta ?addarar ne............


Comments
Like
Share


Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???


*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?









045



Ta gamu da tata ?addarar wato Asad, Asad ne ?addarar da ta gamu da shi wanda tun a kallon farko ya samu nasarar yin awon gaba da zuciyarta wanda tarin maza ke dafifin wajen nema auranta ta ?i to yau karon farko ita ma ta ga wanda take so wanda zuciyarta ta ji ta aminta da shi kuma take da burin ya zama abonki rayuwarta. Sai dai kash, shi sam ba ta gaban shi. Ta haWu da shi ne a wani taron na yaye Walibai da aka gudanar ida aka gayyato shi tun daga nan ta ji ya ta fi da ita, nan ta fara neman hanyar da za ta haWu da shi har ta samu. Duk wata hanya da ya dace ta bi ta bita amma sam ya ka sa fahimtar ta a rin maskilanci na shi, har sai da ta kai ga ta fito ta bayyana ma shi rin da ke kunshe a cikin zuciyarta, babban rashin na sara da ta yi shi ne fatali da wannan ?o?on baran na ta da yi.

Ranar ta yi kuka wanda babu mai lanlashin ta ta yi kuncin zuci, wanda take tunanin cewa shin haka waWanda suka kawo ma ta ?o?on baran su suke ji? Lallai idan haka ne suna jin ciwo mai raWaWin a rayuwa.

Sam ba ta gaban shi duda ya sanar da ita cewa shi yanzu ba soyayya ce gaban shi ba amma ta nace ta jure duk wanin ?yara da yake ma ta, so tari za ta sake shi amma ko ci kan ki ba zai ce ma ta ba haka za ta kara shi zamanta da surutunta da magiyarta ta gaji amma ba zai kulata ba wani sa'in ma haka yake bar ma ta wuri haka za ta ?ara shi zama ta koma.

A rashin mai da hankali a karatu da take ne ya sa har ?an ajinsu suka wuce ta ida ya bar ta maimaita aji.

Da ta dame shi da zuwa Office haka yake sa a hanata shiga haka take faman kiran shi a waya wanda idan ta fara ba ta san ta bari ba har sai ya Waga ita kanta da za a faWa ma ta cewa wai za ta yi wannan na ci wallahi da sai ta ?aryata hakan musamman kuma a ce akan Namiji, Namijin ma wanda ba ta gaban shi.

Ba ta gama sarewa da lamarin Asad ba sai wannan rana da ya duSeta cikin idonta yake sanar da da ita cewa ta nemi wani ta aura bayan ya san cewa ta sha sanar masa zuciyarta ba wani sai shi woton shi ba ta ma gaban shi.

Maysah fara ce doguwa ba wai irin dogayen nan can ba amma ba za ka sa ta shun gajeru ba, tana da kyau na nunawa sa'a sannan tana da diri wanda duk wani Wa Namiji yake da bu?ata ta ko ina ba ta da makusa, amma ta rasa dalilin da ya sanya sam ba ta gaban Asad.



Wannan kenan dawowa cikin labari





****************
An lashe zangon farko na karatu in da Dagori ta fito da sakamako na ?arshe tun a makaranta, a ka sanya Walibai suna ma ta shewa na tarkwalcin da ta yi wanda ita ko a jikinta, ba?in ciki ta bai fi daga ranar an daina zuba ma ta abinci a kula da chocolate da Abbi ke ba su a kullum ba shi ne damuwarta, ba na wannan banzar takadar mara amfani ba da ita ko kasheta za a yi wallahi ba ta san ma'anarta ba. Da har ta ga wasu idan an ba su suke murna wa su kuwa har da kuka haka suke.


Zuna zaune a parlo su Inty na duba takardu ya yi da Hajiyar ke harde akan kujera tana cin pizza ya buWe kofar da sallama ya shigo.

'' Assalamu alaikum.'' Ya faWi yana duban tsakiyar parlon.

'' Oyoyoo!. '' Su Inty suka faWa suna nufar shi. BuWe ma su hannuwa ya yi suka kuwa faWa masa.

'' ?an makaranta ya kuke ya karatu? In jin dai an yi abun gari ko?." Ya furta yana duban yanayin fuskokinsu.


'' Wallahi Ya Ashrap wannan karon kyautata sai ta fi yawa ni na yi I came first in class .'' Aimanah ta faWi tana mi?a masa Reward Winta.

Murmushi ya yi yana dubawa. '' Kai ma sha Allah gaskiya kin yi ?o?ari kyautarki ta musamman ce. Ke fa?.'' Ya faWi yana duban Inty, Wan Sata fuska ta yi.

'' Uhm Ya Ashrap wai fa ni na yi ta Uku.'' Ta faWi tamkar za ta yi kuka.

'' To ke ma kin yi ?o?ari amma ki ?ara dagewa wancan karon ma fa haka kika yi ta Uku... ''Duban shi ya mayar akab Dagori. '' Ke fa Hajiya na nawa kika yi ne?.''

?agowa ta yi. '' Wai ni!?." Ta faWi tana nuna kanta.

'' A'a ni kin ji.''

Ko a jikinta sai ma ?ara ci gaba da ta yi da cin pizza Winta ta ce. '' Yooo ba sai na san akan abun da kuke magana ba. '' Ta furta irin ita ba ba ta masan akan me suke magana ba.

Sai da ya zame daga ri?on da Aimanah ta yi masa don Inty tuni ta zame daga jikin shi ya ?araso cikin parlon tare da samun, wuri ya zauna.

'' Ba ki ga sun kawo min sakamakon su na duba ba? Ke ina ta ki takardar da aka ba ki ne?." Ya yi maganar cikin salon da za ta fahimta ganin cewa Samm ba ta fahimci karatun ba.

Sai da ta gyara zaman pizza daga kan cinyarta kamin ta ce. '' Mtsssss! Ka ga Ya Ashrap raba ni da kayan haushi nan fa shegen Malamin nan, ya zo ya Winga kiran sunan mutane yana ba su wancan shegiyar farar takadar da ba ta da wani amfani wasu idan an ba su su kafa murna wasu kuma su kafa kuka, haka na ?osa a ba ni Aradu na Wauka wani abun daWi ne a cikin takadar, in da idan abawa wani ya ga ba a masa rabon adalci ba da yake kuka ashe hotiho ne sai da aka ban na ga ba komai jiki haka ma don ban yi murna ba ko kuka aka sanya suka min dariya yooo ni ko a jikina su ta shafa ba ni ba sau?in ta ma ina zuwa na tadda wannan puza na rage zafi.''

Ta kai ?arshe iya gaskiyarta don ita fa sun Sata ma ta rai da ta yi za ton wani abun daWin ne ya zo ba haka ba.

Su Inty kuwa mai za su yi ba dariya ba.

'' Kai bana son iskanci kun ji ko?." ''

Ya faWi cikin alamun jan kunne.

'' Aradu Ya Ashrap bar su sune abun dariya da kullum ba su da aiki sai na kallon littafi wanda ni ban ma san uwar me suke kalla ba yanzu fa ko kallo a tsakanin nan sun daina, ba sa wani aiki sai duban littafi ai in ?are ma ba sa mai da hankali a cin abinci yoo na yi ma su magana ba sa ji na ?yale su ai na ga cikin su ne ba na wani ba. Kuma ni gaba ta kai ni gobarar titi a Jos.''


Tsabar takaici ma kasa magana ya yi waton Yarinyar nan, idan ya fahimceta ba abun da ta fahimta duk wannan lokaci yawon zuwa makaranta kawai take, wanda bai da amfani.

'' Ya Ashrap ka yi shiru ba ka ce komai ba.'' Dagori ta faWi jin bai yi magana ba.

Sai tsainkayar murya ta yi ana cewa........



Comments
Like
Share

Taku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???
*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?




046


Juyawa ta yi don duban mai magana. '' To mai ki ke son ya ce da ke sakarya kawai wanda ba ta san ciwon kanta ba, daman can ni ban wani yi farin ciki da kaiki makaranta ba don dama na san ba wani abun kirki za ki yi ba. Yarinya kamar jikar ifiritai sam ba hankali, balle kuma natsuwa ban da shirme da shashanci ba abun da kika saka a gaba.''

Innaya da tun shigowar Ashrap ta fito ta samu wuri ta zauna ba tare da kowa ya lura da wanzuwarta ba, ta faWi tana jin kamar ta rufe Dagori da duka.

Budar bakin Dagori sai cewa ta yi. '' La'ilah Innaya daman ke cikin ifiritai kika fito ne? Ko dai Majoh ne a cikin su? Ko da na ce Aradu ko ?an ruga suna faWan min haka ashe da walakin to Innaya da.....''

'' Ke bana son hauka kin ji ko?." Ashrap ya faWi yana da katar da ita daga shirme da take zubawa shi wallahi ya fara zargin aljanun kanta sun fara zautata.

'' Bar ta kawai Ashrapu bar ta ta gama ?aren tanadi tukunna, wannan yarinya ina zargin ba a gasa ma ta jibi ya gasu ba don wannan hauka ya yi yawa.''

Sai da ta turo baki gaba kamin ta ce. '' To wai ni miye laifina na ga ke da kanki kika ce da ni jikar ifiritai to su waye kakannina ba ku ba? Shi ne kuma don kawai na tambaye ake son manna min hauka.''

Innaya na shirin magana aka turo ?ofar aka shigo Kusan dukansu suka dubi bakin ?ofar. Abbi a gaba sai Asad da ke bayan shi, da wani irin sauri ta sauka a ?asan cafke in da su Aimanah ke zaune, in da tun bayan barin Ashrap daga wurinsu suka samu wuri suka zauna.

A kan kujera suka yi masauki tuni ta sha jinin jikinta.

'' Mai babban Suna!." Tsigar jikinta ne ya tashi jin Abbi ya kira sunanta babu wasa a ciki magana.

'' Na'am Abbi.'' Ta amsa cikin taushi murya kamar ba ita ba ce a yanzu ta gama tsiwa.

Sai da ya gyara zama kamin ya ce. '' Shin idan kin je makaranta ki na karatu?."

Shiru ta yi ba ta yi magana ba, to me za ta faWa cewa idan ta je bacci take yi ba wani abu sai idan an tashi breakf ta ci abinci ta yi wasa komai za ta faWa? Don ita iya abun da take yi kenan idan ta je makaranta, to ita ko a ruga ai ba wani karatu take tun da ta ri ga ta gama raina Malamin na su.

'' Ke mara kunya da ke ake kika wani shiru sai idanu kamar an tsura kwarto.''

Innaya ta katse ma ta tunani. Ba ta bi ta kan zancen Innaya ba ta dubi Abbi.

'' Eh Abbi ina yi sosai.'' Ta shirgawa Abbi ?arya barin ma da ta san cewa Asad na wurin ai ?aryar ce kawai mafita gareta don idan gigi ko ila ya jata ta sanar wa Abbi gaskiya a yadda ta lura da Asad tsaf zai iya kaririyata alaso a samo mai Wauri.

Sam Abbi bai gamsu da zancen ta ba don irin yadda ta jima kan ta ba shi amsa kamar da kyau wani abun amma sai bai nuna ba ya ce. '' Ok amma ni Malaman makaranta na ku ne suka kirani akan ba?ya karatu yanzu haka ma ke ce kika kulle aji.....''

Da sauri har ta zaburowa ta katse Abbi da cewa.

'' Aradu ?arya suke min ni kuma? Yaushe aka yi haka? Aradu ni ce ta biyu da na fara fita bayan an tashi har yaushe na rufe aji? Ka ji sharri da rana tsaka ni tun da na shiga makarantar nan ban taSa rufe ajiba amma ka ji Malaman nan shegun ma?aryata suna son kullamin sharri Aradu....''


''Be quiet, you hear me!.'' Ya faWi da wata irin tsawa don tun da ta fara magana take hawa masa kai, irin yadda take Waga murya.

Ba wai don ta fahimci abun da ya faWa ba sai don kawai ta san cewa abun da ya faWa yana da ala?a da maganarta haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login