Showing 15001 words to 18000 words out of 79609 words

Chapter 6 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1117

kuma zamani, amma duk wannan ba mu fidda ran cewa zamu sake ganawa watan wata rana, duk tsawon wannan shekara ban gaza da bincike neman ida kuke ba domin ban taSa sawa raina cewa ba kwa raye ba.'' ya kai ?arshe yana goge hawayen da suka zubo masa.


'' ?an Innarsa ina Innarku take? da Malam?.'' Baffa ya tsinkayi muryar Innaya na jefa masa tambaya dan ya san da shi take tun da ba ta ambatar sunnarsa sai dai ta ce da shi Wan Innarsa wato Inna Karime take masa inkiya.

Wani abu ne ya ji ya tsaya masa a ma?oshi amma sai ya dake cikin sanyin murya ya furta. '' Innaya sai dai mu yi ha?uri dan tun da Inna ta samu labarin hatsari kuma ta yanke jiki ta faWi wanWa tashin da ba ta yi ba, kenan sai a kushewa sati biyu tsakanin su da Malam shi ma rai ya yi halinsa dan dama shi ma tun da ya samu labarin bai sake lafiya ba, ni ma dai Allah ne kawai ya yi zan rayu bayan duk abun da ya faru to bayan na samu sau?i shi ne na ga ba zan iya ci gaba da zama a cikin rugar ba mu kawo hijira daga Yola zuwa nan Kano muka haWa zango a nan dajin Fargori, satin mu Waya da sauka nan Allah ya sauki Nafisa ta samu Wa wanda na sawa sunan Wan uwana Abubakar muna kiransa Habu daga kan Habu Nafisa ta Winga wabi duk ta haifa sai su koma saida ta yi hakan kusan biyar duk sai an yi suna suke komawa wanda na yi wa Inna Karime takwara har sau biyu amma duk ba su tsaya ba sai da ta samu ciki Mai babban suna, wanda su nanki ta ci ana ce mata Dagori amma ni inakiranta da Mai babban suna, sai Hamma ta dake kiranta da Auta dan daga kanta ba ta sake haihuwa ba har ga shi Habu ya yi Aure.'' ya faWa yana nuna ma su Salame.

Tun da ya fara maganar Innaya ke zubar da hawaye tana salati cikin kuka ta ce. '' Yanzu ka na nufin cewa na rasa Yayata da Malam Innalillahi wa inna illahirin rajiun! Allah ka ji?ansu da rahama ya kai haske ?abarinku Allah ka yafe maku laifukanku Allah sarki Yaya halinki na gari ya biki Allah kyauta ta tamu bayan taku.'' Ta kai ?arshe tana kuka mai cin rai.

Na aka shiga lallashi dan duk sai mutuwar ta dawo masu tamkar sabuwa dan suma daurewa kawai suke dan kada su sake Waga ma ta hankali garin son kawar da zancen Nene ta ce. '' Abubakar amma ta ya kuka gane ida muke? bayan wannan lokaci ga shi kuma ka ce ba a garin kano kuke ba Kaduna? .''

Sai da ya numfasa dan jikinsa ya yi sanyi ainun tun da ya samu labarin muwar nan sai duk jikinsa ya sake mutuwa murus ya ni sa kamin ya ce. '' Haka ne bayan tsawon wannan lokaci da ya shuWe ba yan duk wahalar neman da na yi amma ban sameku ba duk bayan lokaci ina zuwa Yola ko za'ace kun waiwayi gida amma shiru kake ji tamkar an shuka dusa, ranar kwatsam muna kallon TV tamkar a mafarki na ga ana ganawa da Hammana tare da 'yan jarida wanda suka zo Waukar rahoton akan shirin su da suke na al'adu, komai daWewar lokacin da canji ba zan taSa mantawa da Wan uwana ba hakan ta sa na kira Innaya akan ko dai idona ne ke min gizo ai kuwa cikin kuka ta sheda cewa kai Winne, ban yi ?asa a gwiwa ba na sa aka bincika min a wace jahace kuma wane daji ba jimawa na samu duk kan abun da na ke so shi ne ba mu yi ?asa a gwiwa ba muka yo tattaki dan mu sake tabbatarwa.'' Ya ?arasa yana murmushi mai cike da ma'anoni.

'' Allah sarki a lokacin mu muke faman yi maku addu'ar neman gafarar ashe ku kuna can kuna faman neman mu ruwa a janlo?. '' Baffa ya yi maganar ciki wani maWaukakin farin ciki na banyanar Wan uwannasa tare da Mahaifiyarsa.

Nan aka fara gabatar da juna. '' Abubakar amma ka ce su biyu ne yaran maza amma takwarana kawai na gani ina shi mai suna Babana?."

Sai da ya saki wani murmushi kamin ya ce. '' Eh Ashrap ne kawai Asad na Istanbul wurin karatu, to shi ya sa ba mu zo tare ba amma idan ya dawo to zai zo.''

'' To ma sha Allah Allah Ya yi taimaka, yanzu ku tashi mu je masallaci ga kiran la'asar can an fara.'' Baffa ya faWa suna mi?ewa ya dubi Nene. '' Kamin mu dawo a sama mana abinci don kin ga sun kwaso yunwa.'' Yana gama faWin haka suka yi gaba ya yi da matan Nene ta ma su iso zuwa ciki domin su yi sallah.


Nene iso ta ma su aciki ida ta kai Asiya Wakinta sai Innaya da ta ce za ta kai ta Wakin Baffa duk da akwai wata bukatar sai da ba'a gyare take ba tun da ba mai zama a cikin ta amma Innaya ta kafe akan samm ba za ta shiga Wakin Baffa ba dole ta sa aka kai ta Wakin Dagori, tun da ta kafe ko Wakin Nene ba za zauna ba wai duk irin kunya ta su ta fulani.

Duk kan suka shiga gabatar sallah wanda Nene na gamawa ta fito ko da ta fito ta tarar da Salame na aiki abinci, ta zauna cikin runfa ta fara dama fura.


Mutinniyar taku fa da?at ta yi sallah dan Wauki da zumuWin da take tamkar mayye ya yi Amarya tana gamawa tun tana kan sallaya ta dubi Innaya. '' Tsohuwa wai da gaske ke ce kika haifi Baffa da cikin ki? Ke ce Mahaifiyarsa? da man Baffa yana uwa?."

Maganarta ce ta ?arshe ta ba ta dariya har ma da su Aimanah dan su ba iya maganar da ta yi ba, ke ba su dariya har da irin yanayin hausarta da ba ta fita sosai sai dai kuma hausar ta ma su daWin, Innaya murmushi ta yi na tsantsar farin ciki da take ciki a yau dan ita kawai ta san irin farin ciki da daWin da take ji na banyanuwar Wanta ta kwashe tsawon shekaru tana kuka da alhinin ba tan zuri'arta, sai bayan tsawon lokaci ta yi arba da su duk da ta yi matukar jin ciwon mutuwar mijinta da abokiyar zamanta wadda take jinta tamkar 'yar uwa, amma hakan bai zai ha na ta jin daWin haduwa da iyalin Wanta ba sukuma iya soyayyar da za ta nuna ma su shi ne addu'a da neman gafarar Allah ta ni sa kamin ta ce. '' Mai suna ai babu wanda za'ace bai da uwa a duniya sai dai idan sun rasu kamar yadda shi Baffan naki Mahaifiyarsa ta rigamu gudan gaskiya...''

'' Yanzu Innaya ki na nufin ba ke ce kika haifi Baffa ba?."

" Eh kamar yadda na ce miki Yayata ce Mahaifiyarsa kuma ki na zaune kin ji Allah ya ma ta rasuwa.''

'' To Allah jikanta.'' gabaWaya suka amsa da amin ta buWe baki da niyyar magana Nene ta le?o.

'' Dagori na ce wai ke dai ba za ka taSa hankali ba ko? Waton a na aiki abinci ga Salame can aiki ya ma ta yawa kai kuma kana nan kana Wan bazanr suruntunka na faWi ba'a tambayeka ba, za ka ta so ne ka yi zaune ina magana." Nene ta faWa tana ajiye wa Innaya kwanyar fura aganta ta juya ta ajiyewa su maamah suma a gaban su. '' Ga wannan ku fara taSawa kamin a gama abinci."

Godiya suka yi ma ta ita dai Innaya sai murmushi take, za ta fita ta zabga wa Dagori harara wanda a take ta gane mi take nufi ta mi?e da hanzari tana nufar wa je.

Ciki ciki ta fara magana. '' Lallai Baffa zuciya ba ta yi maka rana ba waton sabar zuciya ta sa kabaro rugarku ka dawo nan ashe ka ja an haifemu a kyauye na tabbatar da a ce ya ganka tun farko Aradun Allah ba zai barka ka ci gaba da rayuwa a cikin ruga ba haba Baffa gaskiya ni ba baka kyautan ba amma ko yanzu ai ba ta Saci ba dan....''

'' Wai ni kam uwar mikike a wurin tsaye da ba za ki zo, ki kama aikin ba?." Nene ta faWa cikin Wan daga murya sumui sumui ta zo ta wuce. '' Yarinya sam ba ta ji ace duk da akwai ba?i a gida sai kin nemi ki saida hali ko?."

Sannin da ta yi daman akwai laifi da ta ma ta jiya ya sa ta je ta kamawa Salame aiki..........

Comments
Like
Share


Taku har kullum mai kaunar
MRS AWWAL =???

?*DAGA RUGA NAKE* ?

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABBITYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?

=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa suka sauya tunanin al'umma cikin sau ?i_.'?





011



Sai da suka idar da sallah magarib kamin suka yi zaman cin abinci wanda Salame ta girka samu tuwon shinkafa miyar kuka da ta ji man shanu a tsakar gida suka zauna su na cin abinci sakamakon lokacin zafi ne, su na gabawa daidai ana kiran isha suka tashi don gabatarwa sun gama suna Wan taSa fira sai ga su Baffa sun shigo gwanin sha'awa suka jero shi da Wan uwannasa sai fira suke abun su cike da farin ciki su na zaunawa kan tabarma Baffa ya yi dariya irin ta su ta manya ya furta. '' Ai na san cewa dole ne ka manta wasu ai na ga ?o?arin ka da ka iya tuna mutane da yawa a ciki.''

Murmushi ya yi mai Wauke da dariya kamin ya ce. '' Haba Hammana ai ba kowa ne za'a ce an manta ba sauran ma saboda kawai shekaru da canji yanayi amma ace an tashi tare an yi wasa tare ace an manta cikin sau?i, ai da Wan wahala.'' Baffa ya Wauki ruwa ya wanke hannunsa tare mi?a wa Wan uwannasa yana furta.

'' Ga ruwan ka wanke hannu, ko da yake ban san ko ba za ka iya cin abinci da hannuba? Ka san ni sam ban iya cin abinci da cokali ba na fi gane na sa hannu, domin cika wannan sunnar ma'aiki. ''

" Hamma kenan ashe dai har yanzu halinka na nan baka sauya ba? ai ni ma tun da na zo nan ai yadda ka yi haka zan yi. '' Ya kai ?arshen maganar ya saka hannu cikin kwanon tuwon Baffa bai tanka shi ba kuma ya san da haka dan muddin yana cin abinci to fa ba zai sake magana ba sai ya kammala.

Suna kammalawa Nene ta dubesu tana murmushi. '' A'a Abubakar an samu Wan uwa ko kulamu ba za'a yi ba? .'' Ta kai ?arshe ta na ?ar dariya.

" Hmm Adda kenan wallahi duk farin ciki ne ke Wawainiya da ni domin na kasa yarda yau Hamma ne zaune a gabana sai nake ganin tamkar idan na yi nisa da shi ba zan sake ganinsa ba, yanzu bana kaunar abun da zai sake nisantani da Wan uwana domin yanzu ban da Innaya shi ne kawai ya rage min tun da Allah ya yi nufinsa akan Inna Karime da Baba sai dai fatan Allah ya jikansu ya kuma yi masu rahama. ''

Ku san duka suka amsa da amin, Baffa ganin da ya yi daga maganar Innaya ta sake shiga damuwa dan duk da duhun dare amma ya iya lura da yanayin ta ya sa ya wayance da Wauko wani zancan na daban. '' Uwar yara kin ji wani abun daWi kuma ashe Ashura kai ko da yake iya sunan ba dari na ce Takwara da shi da maamah Aure ya kusa nan da sati biyu, to shi ne ya ce yana son gobe za su koma saboda shirye-shirye auren kuma wai yana son mu je tare da su, to ni dai na ce ba yanzu ba abari ina da wasu ayunkan da nake ban kammala ba, ke da Salame da Mai babban suna sai ku bisu alaso ni da Habu sai aturo mana wanda zai kai mu ana gobe, bikin. ''

'' Kai ma sha Allah ka ce muna da hidima to amma Malam ni sai nake ganin kamar ta ya za'a bar gidan haka saboda wasu ayunka gidan ai kai da Habu ba zaku iya ba kawai bari, dukan mu sai ranar da zaku sai mu tafi gabaWaya da.....''

'' Haba Nene ai wannan samm ba adalci ba ne ta ya za'a ce mutafi gobe ke kuma kic e a'a ni dai gaskiya idan har ba za ki ba ni kam ?afarsu ?afata haba ai wannan ba dan ke ce ba wallahi sai na ce ba?in ciki kike dan gar na je birni na Webe ?warkwatar ido ai...'' Dagori ta yi saurin tarar numfashin Nene dan tun da ta ji zancan tafiya take washe baki dan kaf rayuwarta ba taSa zuwa birnin ba kuma ta samu dama zuwa har ta daWe shi ne Nene za ta yi ma ta ba?in ciki zuwa.

'' Wai ni kam Dagori ban hane ki idan manya na magana ki na saka baki ba ko akwai sa'arki acikinmu iyee.''

'' Adda bar ta kawai ai gaskiya ta faWa ina dalili za ki hanata zuwa duk wani shiri a gabatar da ita.'' Asiya da tun zuwanta Dagori ta shiga ranta dan ko dan irin san da take yi wa Abubakar ne amma sai ta ga suna matu?ar kama da shi tamkar ya yi ka?i, amma ba ta tunani ko acikin yaranta akwai mai kama da shi haka sai ko... Tunaninta ne ya katse sakamakon maganar da ake

'' Wannan haka ne Maminsu, kuma ita ma Adda maganarta kan gaskiya take to yanzu dai ita Adda sai ta zauna amma kan Mai babban suna ita da matar Habu tare zamu da su alaso ku sai ku bari sai jibi Waurin auran sai ku zo.''

'' Baffa Wan barni da gaske da ni za ku amma dai akwai kayan daWi acan irin su burodi da lemun jarka da kosai da nama da....''

'' Kun ga dalilin da ya sa na ce mu bari sai mun tafi tare ko?. '' Nene ta yi maganar cikin jin haushi abun da Dagori take.

Dukan su dariya ta ba su aikuwa suka dara har da Abubakar kamin ya ce. '' Mai babban suna dan ni ma haka zan Winga kiranki da shi duka akwai su har ma da abun da baki ambata ba akwai sa kin ji ko.''

Ta washe baki har kunne. '' To Baffa birnin ku tashi kawai mutafi yanzu tun da dai ina da kaya wankan ki.''

Aimanah ta dafa ta dan ita ce kusa da ita ta da na dariyar zancen ta ta ce. '' Sister kada ki damu ai idan kin je ba za ki dawo ba ki na tare da mu ko? Sannan kuma ba sunansa Baffan Birni ba ki kirasa da Abbi yadda muke kiransa. ''


'' Waton Auta guduwa za ki yi ki bar Hamma ki ko?."

Cikin muryar shagwaSa ta ce. '' Ka ga Hamma Habu ba damuwa kana ji sun ce na je to ta ya zan?i ai kamar ban kyauta ba ko to maganar gaskiya ni kam bin su zan amma ba damuwa sai, kai ma ka zo mutafi dakai wallahi ba wata takura, ko Abbi?." Iya gaskiyarta take maganar da ita fa kam ba wanda ya isa hanata wannan tafiyar Sallema da aka sanar ma ta za ta Winga samun burodi da lemun ai ba wanda ya isa ya ma ta hijabi da shan wannan daWin ina sam ba za ta bari ba.

Abbi na murmushi ya ce. '' Kwarai kuwa Mamana ai dukan su ma ina jin Wauke su zan yi mukoma can.''

Ashrap da tun Wazun yake saurarensu amma bai ce komai ba dan damuwarsa rashin network da bai samu ba Salle ya ji daga masoyiyar ta sa ya furta. '' Gaskiya Abbi ba zamu da ita ba a bar ta kawai ka san fa cewa ta yi muWin y'an yankan kai ne to, ka ga kada mutafi da ita a yanke ma ta kai dan haka a bar ta kawai, ba za ta bi mu ba....''

'' Hamma Ashiru wallahi rashin sa ni shi ne ya ingiza ni na aikata wannan amma ina ni ina, cewa maku y'an yankan kai, dan girman Allah gar kamin shamaki da jin daWi wallahi na tuba na bi ku na bi Allah, kuwa Allah ku tafi da ni, Aradun Allah sharin aljanu ne da kuma sharin sheWan ya sa na, na yi abun da na yi amma yanzu na bari wallahi ka bincika cin mutunci ba halina ba ne Aradun Allah kaf rugar nan na fi kowa natsuwa da sanin ya kamata ba ni rigima Salle kuma...'' Sosai suke dariya wai Ashiru Ashrap ya zama Ashiru ga shi ta dage sai neman kare kanta take.

'' Ke suWa ya isa haka kin tsinke sai ka ce lalatatce fanfo to duk abun da kika faWa ai ba Waya dake gaskiya ka ga Ashrap wannan da kake gani kaf rugar nan babu fitinanniya irin ta ku....''

'' Haba Nene idan ba za ki ta ya ni, wannan ya?in ba ai bai kamata ace kin kwancan zani a kasuwa ba.'' Duka mutanen wurin dariya suke Aimanah da Inty sai dariya suke Inty har da kai wa kwance tsabar dariya.

'' Kin ga Mai babban suna kwantar da hankaliki kin ji ko babu wanda ya isa ya hana ki ta fiya kin ji ko idan ma suka yi wasa ba sai na Wauke ki gabaWaya ba.'' Abbi ya faWa yana dariya irin ta su ta manya.

Daga nan suka ci gaba da fira su cikin nishaWi kamin kowa ya je yakwanta ko da suka kwanta Dagori ka sa bacci ta yi ta tashi ta fara haWa kaya gudun kada ta manta da wani abun kuma ta san dai ba zai fi sanmako za su yi ba, to ba gara ta shirya kayan ba dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login