Showing 57001 words to 60000 words out of 79609 words

Chapter 20 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1094

Win doguwa ba ce mai jiki sai dai ba wani can, sosai ba.

FaWa wa ta yi jikinta ta rungumeta. '' My Mommy, I'm back I miss you so much I know you do too?.'' Cikin Muryar shagwaSa ta yi maganar tana sake kwanciya a kan kafaWarta.

Murmushi Matar da aka kira da Mommy ta yi tana ajiye wayar hannun ta tare da sake kwantar da ita akan jikinta. '' My daughter, when did you come in? You didn't even let me know when you were on your way? Ai da na sa an yi miki tarba ta musamman.'' Ta faWi fuskarta na bayyana farin ciki da take ciki.

'' Uhm Mommy ina son na yi maku surprise you see, if I announce bai zama surprise ba ko?.'' Ta faWi tare da gyara zaman ta.

'' Amma yanzu don kawai wannan sai ki ?i sanar wa kowa to yanzu waye ya Wauko ki daga Airport?." Mommy ta jefa ma ta tambayar bayan da ta ga ma su aiki,na shigowa da akwatinta.

'' Mommy!! Kenan.'' Ta jaaa kalmar sunan cikin wata irinyar siga. '' So daman tun ina can, na riga na siya mota na gama tura kuWi da komai da komai, He is the one who bought the land suka kai min ita a airport so ita, ma na shigo na ?araso gida.''

'' But...''

'' But what Mommy? please Calm down okay. Ina lafiya yanzu ina Dady yake ne?." Ta faWi don kawar da maganar da Mommy ke da niyyar yi ma ta. Ta san ba zai wuce mita a kan, dawowar da ta yi ba tare da ta sanar ba.

'' Dady ki baya nan ya je wurin aikinsa amma ba jimawa za ki iya ganinsa. Yanzu ki tashi ki shiga daga ciki, sai ki yi wanka ki sauya kaya, na sani kin kwaso gajiya ga kuma yunwa, idan kin gama wannan ki sauko abincin na nan na jiran ki.''

'' Ok Mommy.'' Tana faWin hakan ya Mi?e tana nufar sama ta fara taku tamkar mai tausayin ?asa....





Ta ku har kullum mai kaunar ku
MRS AWWAL =???


*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?






037



Tamkar das,kararrar ?an?ara haka Inty da Aimanah suka daskare wurin sunkasa sakin ko kyakkyawan numfashi mai kyau. Tsabar tashin hankali da ruWu, don sun san cewa tabbas yau kashin su ya bushe, sai sun gwammace wa kuWa da karatu.

'' A contempt for me has come between me and you da nake magana kun wani tsaya min a wurin sai ka ce an dasa ku?." Ya faWi yana juyawa da alamar zai sauko ne. Don yana ta balkoni Win sashesa, da wani irin mugun gudu suka kwasa suka faWa parlon da suke da tabbacin nan zai yi, kuma idan suka sake ya riga su tofa, ba za su ce, ga irin abun da zai faru ba.


Abun da ya faru bayan da a ka sanar masa fitar wanda a waya Mami ke sanar da shi. Ko da take sanar da shi yana kan wani aiki ne, samm bai so fitar ba saboda idai yana kan aikinsa tofa baya ?aunar abun da zai taka masa birki a kansa amma ba yadda zai yi ne, saboda ba dai zai iya jaa da umurnin Mamin ba. Sai da ya kammala kafin ya mi?e ya fara shirya wa ya gama shirinsa tsaf, a ka kirasa a waya ya Wauka yana magana ne sai kuma ya nufi balkoni da ke cikin Wakinsa wanda zai iya bawa mutum damar ganin abun da ke wakana a harabar gidan, a nan ne kuma ya tsinkayi abun da Dagori ke faWi tun daga farko har ?arshe, duk a kan idonsa. Ya zuba ido ne kawai yana kallon gudun ruwanta amma a manakinsa sai ta aikata abun da ta ce.

Ransa ya Saci ainun sai kuma ya ga su Aimanah na shirin guduwa wanda hakan ya sake Sata masa rai sosai.


Suna faWowa parlon daidai Innaya na fito wa kitchen hannunta ri?e da cup da gudu suka ?arasa wurin gami da Suya a bayanta.

'' Kai lafiya za ku yo min nan kuna shirin kayar, da ni? Kun san ba na son irin wannan shegen wasan na ku ko?." Ta yi maganar tana ?o?arin wucewa amma me suka ri?eta gam-gam sai faWin suke .


'' Dan Allah Innaya ki cecemu wallahi mun san yau ?arya mu zai yi, ba laifin mu ba ne wall...,''

Maganar su ce ta tsin?e bayan da suka ga saukowarsa idon nan nasa sun kaWa sun yi Red. Duk kanninsu cikinsu ya gama Wurar ruwa duk da sanyin AC da ke parlon amma sun yi sharkaf da zufa.


**********
Dagori tana barin wurin su Inty ta shiga parlon har ta nufi Wakinta sai kuma ta juya akalarta zuwa kitchen. Ko da ta shiga ta tadda su Binta na girki ba ta kula suba kamar yadda suma ba su bi ta kanta ba ta buWe freezer ta Wauko lemun exotic tare da daukar Flash ta Wibi soyayen naman kaza dake ciki ta fita, kallon gefen ido Abida ta dube ta tare da zabga ma ta harara.

Kai tsaye Wakinta ta nufa tana shiga ta yi wurgi da jika da mayafunta a kan gado a kan cafke ta baje bayan da ta cire takalminta, ta yi zaman dirsham tana Wibar gara abun da.

'' Ke duniya daula ta yi yanzu a ruga ubanwa zai Waukar min wannan iskanci na cin nama da lemun jarka? Ashe ma har da na kwali akwai ban sani ba?. Kuma Aradu ya fi na jarkar daWi, ai wallahi zama daram wai kishiya ta yi saki.'' Tana faWin haka ta kwashe da wata dariya.


**********

'' Ohyaa ku fito na kafin na zo, kuma kun san sai kun raina kan ku.'' Ya faWin yana ciro belt Win wandonsa.

Kuka mai sauti suka fashe da shi. '' Oh ni Aminatu wai me ke faruwa ne? Kai Mai sunan Malam me suka mane?.''

Ta tambayesa tare da du?awa ta ajiye kofin hannunta. Amma sam bai amsata ba sai Aimanah ce cikin muryar kuka da majina take sanar ma ta abun da ke faruwa har ta gama tana saurarenta.

'' Uhm ni daman na san za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, to kai yanzu mene ne na su a ciki ne da za ka zo ka ce zaka rufesu da duka? Salon zalinci ta ya ga mai laifi a ce za a hukunta wanda bai jiba bai gani ba ita Mai Suna ita ce ta yi ma laifi don haka ita za ka je ka jibgi ja'ira amma waWannan kam, ba za ka taSa su ba.'' Innaya ta faWi tana sake kare su Inty da ta ga yana niyyar janyowa ya daka.


'' A'a Innaya suma fa da na su laifin ki na ji fa guduwa suke da niyyar yi? Waya sani ko ?arya suka yi wa ma ta don sun ga ba ta nan?, Sannan koma gaskiya ne ai kamata ya yi sunanar da ita illar haka amma suka ?aleta.'' Mami dake saukewa daga bene don ta fara jiyo hayaniya sama-sama ta faWi.

'' Ke ma dai Asiya kawai ki na son ki take gaskiya amma ni komai aka ce Mai suna za ta yi na san cewa za ta aikata don ita Win ba abun yabo ba ce, amma wanda ya mutu ake yi wa ?arya ba rayayye ba ai sai a kirata.'' Innaya ta faWi daidai nan kuma Dagori ta fito da Flash da gorar exotic da ta gama shanyewa.

'' Innaya lafiya na ganku cirko-cirko? Kuma na ji kamar ana kiran sunana?. Ta tambaya tana duban Innaya don sam hankalita bai kai wurin da Asad yake tsaye yana maka ma ta wani irin mugun kallon wanda yake, ganin wane kalar hukunci ya da ce ya yi ma ta ko ya wuce don daman can yana Wauke da cikinta.

'' To rasa ?unya bairan tunkunya waton ke ba ki san abun da kika yi ba ko? Yanzu ke wa ye ya ba ki damar a ce ku tsaya waje ku jira Asadu don ya kai ku wurin siyayya wanda ke za ta amfana wai, ki dawo ciki har da goron ba?a?en maganganu ke ga shi ba wanda ya isa da ke tambayar ki? Nake ki ban amsa.''

Dagori kuwa kallon Innaya take da ta wani ha?i?ance a kan wannan maganar, da ita samm ba ta laifin da ta yi ba. Sai da ta gyara tsayuwar ta kafin ta ce. '' Eh haka a ka yi Innaya ni fa ba na son rainin Wayo da wula?anta dan adam. Yanzu da Ya Ashraf ne wallahi ko minutes Waya ba za mu yi ba zai fito ya kai mu shi kuwa wannan.... Ta faWi tana kallon Asad da sai sanda Innaya na magana ta lura da wanzuwarsa ta ci gaba. '' Barin mu ya yi kamar ya shanya kaya kusan hours muna tsaye to ni ba zan iya tsayuwa ba ne, saboda kamar yadda yake jin shi Wan Abbi ne ni ma haka take yar sa ce Abbi Mahaifina ne to don haka duk wani iskancin......''

Ba ta samu damar ?arasawa ba sakamakon wata wuta da ta ga ta gikta ma ta a fuska. Wanda ba komai ba ne face zazzafan Mari da Asad ya Wauke ta da shi ne ya ja za ma ta haka. Tuni ta yi watsi da Flash Win da ke hannunta ba ta gama dawowa daga duniyar azabar marin da ya ma ta ba ta ji saukar ruwan belt ta ko ina a jikinta.

Wani uban ehuu ta sa tana faWin. '' Wayyo Allah na na shiga uku na gantale zama ku jama'a taimakamin Aradu ban gani za su kashe ni....''

Abun da take faWi kenan bayan da ta kai ?asa tana birgima.


'' Yawwa Asadu koya ma ta hankali ka zane min ita da kai ko a samu ta shiga natsuwarta.'' Innaya ta faWi cikin salon ?ara tun zurasa.

Dagori da ta gama fahimtar me ke faruwa, kuma ta ji bai da niyyar daina jibgarta ta ce bari ta yi aljanun ?arya kamar yadda ta saba don ta tsira da rayuwarta saboda ta lura da dukkan alamu kasheta yake da niyar yi.............



Ta ku har kullum mai kaunar ku

MRS AWWAL =???


*?DA??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????GA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?





038




Daga nan kwancen da take ta fara mi?e wa tana gantsarewa, duk da cewa har na da zafin da azabar dukan da yake ma ta tuni ta sauya murya tana faWin. '' Hhhhhh Yiiiiii! An taSo mu uhummmm, ka daina dukan koWiyar mu, lallai yau ka tono wu?ar yanka kan, ka daka daki goWiya ga jikan Sarkin aljannu na duniya. Hhhhhhhh Asad lallai ka gama yawo, dama ?ishi da yunwa ta kama mu mun daWe ba mu sha jinin bil'adam ba yau za mu shanye maka jini sannan mu yi kalace da namanka... Yayinda za mu ba da ?asusuwanka zuwa ga Agataburus wanda na san yin haka zai matu?ar bu?atarsa tare da ba mu bangarma hhhhhhhhhhhhhhhh.''

Ta kai ?arshe tana sakin wata uwar dariya har parlon yana amsawa.

Asad wanda ya ?ame a wurin tun fara zancen ta wanda ya dankanta hakan da ko ta samu taSin hankali ya zuba ma ta na mujiya yana kallon ta.

Da wani irin mugun hanzari Mami ta ?araso wurin ta jeyo Asad take tsaye tana faWin. '' Dan Allah ku yi ha?uri wallahi kuskure a ka samu yaro ne, ku masa afuwa ba zai yi sake wannan gangancin ba haihuwa ga damuna, ina mai nema masa afuwarku da ku yi ha?uri. '' Ta furta zufa na kwaranya jikinta don Mami kaf duniya ba abun da take ?auna sama da yaranta wanda ba ta ?aunar wani abu ya same su ko da kuwa ya'ya ne.

Cikin mamaki da rashin fahimta yake duban Mami da duk ta bi ta wani ri?ice.

'' Mtsssss aikin burrr in ji tusa to miye a cikin break ban da fulawa, ku har kuna ganin kuna da wani abun da za ku iya yi wa Mutum bayan Allah?. Ai Ubangiji ne kawai yake da wannan ikon, ko da kuke ganin kamar kuna yi wa mutane asiri kuma yana kama su to ku sani shi ma don Allah ya yarda ne hakan yake faruwa amma ku ba ku isa ku saka ko ku hana ba wannan ikon Allah ne ba naku ba don haka duk abun da kuka ga dama ku yi.'' Innaya ta faWi tana duban in da Dagori da ke kwance ?asa tana ?anannaWewa tamkar wani maciji.

'' Kee! Tsohuwa ki saita kalamanki.'' Cikin Waga murya Dagori ta yi magana don ta ga kamar Innaya na shirin kwaSa ma ta aiki.

Cikin sake shiga ruWu da rashin fahimtar duk zantukan su ya ce. '' Wai me duk wannan ke nufi ne.''

'' Ka ga Asad ka ba su ha?uri ka ji ko?."

Duban Mami yake mai magana don duk ta sake saka shi cikin ruWani. '' Mami wa ki ke magana? Su wa zan bawa ha?uri kuma?." Ya tambaya bilhakki don shi fa duk ya kasa fahimtar idan zantukan su suke nufa

'' Tambaya ta kuwa? Wai aljanu za ka bawa ha?uri.''

She?e?e ya dubi Innaya. '' Aljanu kuma? Daman ana ganin su? To ina suke a nan?.''

Da Wan yatsa ta cinna masa ida Dagori ke kwance tana gurnani kamar wani ra?umi ta ce. '' Ga su kuwa ai Aljanu ne da ?anwar ta ka kuma su ne suke ba ka umurni, yanzu dukan da kamata ne ya Sata ma su rai shi ne fa suka zo.''

Wata dariyar rainin hankali ya yi wanda ba kowa ne yake ganinta ba, don yana Waukar lokaci bai yi ta ba.

Su Aimanah ne suka shiga yin baya-baya don sun san tun da ya yi irin wannan dariyar lallai akwai matsala.

'' Ai kuwa yau za ku fita ne a jikinta don za ku ji a jikin ku.'' Asad ya faWi yana gyara hannun rigarsa.

'' Ai dai kam don su za ka jibga ba mai suna ba, ba zan hana ka ba yi ma su dukan kawo wu?a ai wannan zalinci ne su kama su shegen jikin Yarinya ?arama haka. Kuma su rasa jikin wa sai jikin jikata.'' Innaya ta faWi tana sake ?afafa masa.

Dagori kuwa jin haka cikinta ya Wuri ruwa tashin hankali don Wazun ma da ya san ita ce; ai ba ta wani ji da daWi ba balle kuma yanzu da tunaninsa zai ba sa aljanu ne ta san cewa ba wai sau?a?a ma ta zai yi ba. Ta fara nadama da dana sanin ta da aljanunnan da ta yi, ta Wauka za ta sha bilis ne kamar yadda ta yi wa Ashraf ashe ba haka zancen yake ba. Ita kuwa wace ila ce ta jata aikata haka? Duk dubararta bai fi ta samu ta yi amfani da wannan hanyar don, ta samu ta Winga horasa da aljanu ko ta rage ba?in ciki da raWaWin da take ji nasa ashe ita ce za ta kwana a ciki.

Ba ta gama tunanin da take ba ya tsin?e ne ta hanyar saukar ruwan belt ne a jikinta ta ko ina.

Mami kuwa baya ta yi don ta daWe ba ta ga sa cikin irin wannan halin ba kuma ta san muddin ya rufe ido to fa bai ji bai gani ne duk wanda ya zo gabansa to fa zai iya haWawa da shi ne.

Ihu take na neman taimako amma ko wa ya ?yaleta fahimtar da ta yi cewa sufa suna zaton aljanun ne ya sa ta faWi.

'' Kai jama'a yanzu kuna gani za a kashe ni?."

'' Asadu Mai Malam ci gaba da jibgar su haka suke idan sun ji wahala.'' Innaya ta faWi don ita a zatonta aljanun ne suke ke jin wahala suke fagewa da Dagori. Amma sai ji suka yi Dagori na cewa.

'' Wai ni kam Innaya me na kashe miki ne wallahi Aradu ni ce Dagori ba aljanu ba. Ku taimaka ku kwace ni, wurin wannan mahaukacin idan ba haka Aradun Allah za ku yi zaman makoki ne.''

Cikin muryar kuka take magana don har sar?ewa take tsabar ta jigata. Ga shi kuma samm kamar bai ji duk abun da take faWi duk uwar magiyar da take masa gami da ro?o amma samm bai sauraron ta.

Asad kuwa da duk abun da take faWa shi ba jinta yake ba don ransa ya kai ?ololuwar Saci da bai ji bai gani daman, shi haka yake idan ransa ya Saci do kunnuwansa toshewa suke idanunsa rufewa suke.

Dagori tun tana iya magana da motsin kwatar kanta har ta kai ta yi lumm ba ta motsi.......



Ta ku har kullum mai kaunar
MRS AWWAL =???

*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?



039


Bayan sati biyu tsaye take bakin ?ofa cikin shirinta na uniform tsaf wanda suka yi matu?ar yi ma ta kyau. Hannunta ri?e da ?yak?yawar kula mai kyau sai faman murmushi take yau kwananta biyu kenan da fara zuwa makaranta, ba ?aramin fama aka yi ba da aka kaita makaranta da ?at da siWin goshi don ma da sanayya aka Wauketa a primary 2 don ko da aka bincike ta ba abun da ta iya, ko sunanta ba ta iya rubuta wa ba, balle kuma aje ga zance wani abu wai shi turanci.


wanda bayan dukan da sha wurin Asad ya dakatar da zuwansu shopping ta kwana biyu tana jinya da gashin jikinta don ba laifi ta daku jikinta ya yi sanyi da lamarin Asad sai dai ?asan ranta ta ?udiri wani abun komai daran daWewa wanda ta sa a ranta cewa za ta rama.

Tun bayan dukan da ya ma ta ba ta sake bari ko da hanya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login