Showing 69001 words to 72000 words out of 79609 words

Chapter 24 - Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel

11 Jul 2026

1093

ya sanya ta ja bakinta ta yi shiru, don akwai tarin maganganu a ciki saboda ba ta gama wanke kanka daga sharri da ?azafin da waWannan Malamai suka ma ta ba.

'' Why brother ka yi ma ta hankali mana yarinya ce kuma ba ta fahimci abun da ake nufi ba. ''

Ashrap da tun bayan da Dagori ta gama goge masa hadda bai sake magana ba ya faWi don zuwa yanzu ya fahimci wani abu game da ita.

'' Ka ga Ashrapu bar shi ya koya ma ta hankali daman shi ne mai saita ma ta nutsuwarta, don sam na rasa gane me ke damunta wallahi.''

Abbi ne ya yi gyara murya ganin da ya yi cewa Innaya kamar tana son tunzura Asad ne.

'' Innaya gaskiyar fa Ashrap mai suna dududu nawa take ne? Kuma har yaushe ta shigo birni balle ta gama fahimtar yadda rayuwar birni take ba ta isa ta banbance tsakanin rayuwar birni da ta ruga ba, ya kamata abi ta a sannu in sha Allah za ta gyaru kuma za ta ba ku mamaki nan gaba ko Mai babban Suna?."

Ya kai ?arshe yana jefa ma ta tambaya ganin duk ta wani tsorata.

'' Aradu Abbi gaskiyar ka ni fa ban gane maganar da suke yi wani yare suke wanda ni Samm ba fahimtar shi nake ba, shi ya sa magana ta gaskiya domin Allah bacci nake yi ba wani karatu da nake yi yooo ni mai zan fahimta bayan ba jin abun da suke faWi nake ba.''

Murmushi Abbi ya yi bayan da ya gano bakin zaren.

'' Mtsssss ka ji sakarcinta ko waton mai suna bacci ki ke zuwa yi a makarata? Ja'ira mutunniyar kawai nan fa tana rigan kowa shirya wa ashe ba uwar da take yi, a makarantar to ma wai me ki ke zuwa yi a makarata? Ko da yake a fili zancen yake yawo ki ke zuwa tun da dai kin faWa bacci ki ke abun ki.''

Tsabar takaici ne da ciwon kai da ya dirar masa ya sanya shi mi?ewa don wannan surutun ya soma yi masa yawa, bai yi wa kowa magana ba ya haura sama kamar yadda ba wanda ya yi masa magana don sun san cewa hakan na nufin ya gaji da maganar da ake yi ne.

'' To yanzu dai na fahimta ida matsalar take, ke Mai babban Suna ko dai miye matsalar ki ne a makarantar? Shin karatun ne ba?ya fahimta? Ko kuwa yanayin yadda suke koyarwa ne ke ba?ya ganewa?."

Abbi ya sake gefarta da wasu tambayoyi don shi duk ya fahimci ida zancen yake nufa amma yana son jin ta bakinta ne.

'' Ai Aradu Abbi dukka ni ba ni fahimtar komai yoo me zan gane bayan ba sa yin hausa balle kuma fulatanci, Aradu ban fahimta komai sai dai in ga bakinsu na motsi.''

Ta faWi cikin sakewar da ta samu don daman a takure take da zaman Asad a wurin don shi da ya bar wurin ta ji tamkar an zare ma ta ?aya har iskar wurin ta ji ta sauya ma ta.

'' Mtsssss.'' Innaya ta yi wani tsa?in takaici tana gyara zama.

'' Yanzu Abbi best solution kawai a sama ma ta wanda zai Winga yi ma ta lesson, a gida don daman can abun da ya da ce a yi kenan, duba da cewa Walibai sun fita ?okari kuma sun wuce ta.''

Ashrap ya faWa yana ganin hakan shi ne kawai mafita don Dagori lamarinta akwai bu?atar tsayawa a kai.

'' Wane kuma lusso kada fa a haWa ni da wani katon arne, Aradu idan kuka yi wasa sai ya arnartar da ni ni ma na daina Sallah kun ga wa gari ya waya? Don Aradu arnan nan kaWan suke jira su.....''

Dugurin da Innaya ta kai ma ta ne ya sa ta dakata da barin zancen da take yi. Ba wanda ya tanka ta Abbi ya ce.

'' Gaskiya ne zancen ka ni ma abun da nake tunani kenan, don haka yanzu sai ka samo wanda zai na yi ma ta lesson Win ka samo kwararre kuma mai ha?uri ka ji?."

'' To Abbi.''

Daga haka suka tsaya akan zuwa gobe in sha Allah zai bincika..........


Comments
Like
Share


Taku har kullum mai kaunar ku

MRS AWWAL =???


*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?




047


Kamar yadda aka tsara hakan ce ta faru don kuwa Ashraf kwana biyu tsakani ya samo mai koyar da ita wanda a ka shirya da shi kullum zai zo da misalin ?arfe 4:00pm har zuwa 6:00pm awannin biyu kenan.


Abunka da kuWi masu gidan rana, tun kan huWu yana gidan don a nan ma ya yi sallar La'asar..

'' Amma dai Sis wallahi sam ba ki kyauta wa kan ki yanzu tun Wazun fa bawan Allah can ya zo yana zaman jiranki amma kin zauna sai faman ciye-ciye ki ke.''

Aimanah ta faWi cikin Sacin rai don abun da Dagori take yi wallahi soma isarta. Tun zuwan shi aka sanar da ita amma ta yi zamanta sai ciye-ciye take. ?agowa ta yi ta dube ta.

'' Yoo dai na ga aikin kuWi yake biyan shi fa za a yi to miye a ciki idan ya jira ni?."

Ta faWi tana ci gaba da cin namanta.

'' Hmmm amma dai Sis da kin ajiye naman nan alaso idan kin dawo sai ki ci.''

Inty da ke karatun wani littafi ta furta ba tare da ta Wago ta dube ta ba... Aimanah kuwa sororo ta yi tana dubanta.

'' Au ashe ma karan hauka ne ya cije ni da zan ajiye wannan kayan daWi na je wajen wani abu wai shi karatu.''

Aimanah da takaici ya ishe ta ta ce.

'' To shi ke nan bari na haura sama sai na sanarwa Ya Asad cewa ga mai....''

Ai ba ta jira ta ?arasa ba ta mi?e tana cewa.

'' Au abun har ya kai haka to ai bari na je don ba na son ganin wannan Ya Asad Win aradu, ni daman wasa nake maku.''

Ta yi maganar tana Waukar sauran naman ta yi waje... Wata irin dariya su Inty suka kwashe da ita bayan fitar ta Inty tana ajiye littafin hannunta ta ce.

'' Sister dube ta yadda ta razana daga kin faWi sunan Ya Asad lallai su Sis an ji jiki.''

'' Hmm ai kin san ba wai ta sha da daWi ba ne wurin shi ko kin manta gamonsu? Ai ni wallahi Ya Asad ya burge ni da ya zane shegun aljanunta, tun daga ranar ai ba su sake zuwa ba.''

Aimanah ta furta tare da zamewa daga zaman da take tana kwanciya a kan kujerar.

'' Ai kuwa Sister wallahi ba su sake tashi ba, Allah wani lokaci Sis tsoro take ban ke ba ki lura da zubin idanunta ba kamar fa ba a daidai suke ba sai nake ganin kamar suna sauya kamanni?."

Cikin dariyar zancen Inty Aimanah ta fara magana.

'' Kai Sis ban da sharri wane kuma sauyawa sai ka ce aljana? Kawai dai kin sawa ranki ne amma ba wani sauyawa da idonta ke yi.''

'' Hmm ba za ki gane ba amma ni dai kam ina gani ke ma ki saka ido da kyau za ki ce na faWa miki.''

Dariya ta sake yi ganin yadda a gasken gaske take zancen ta.



Tana fita kai tsaye ta nufi wurin sha?atawa da ke gefen Swimming pool, in da ta hange shi zaune a Wai daga cikin kujerun wurin. ?arasawa ta yi a kujerar da ke kallon shi ta zauna tare da kai nama bakinta, dubanta ya yi ya girgizar kai na yadda ta zo ko sallama babu balle kuma gaisuwa, kusan 1minute ba wanda ya yi magana, can ya yi gyaran murya. Ganim da ya yi bayan cin abinci ba abun da take sai kale-kale.

'' Am da farko dai Assalamu alaikum... Sunana Amiru ni ne wanda aka Wauko domin koyar da ke karatu, in da in sha Allah nake tunanin za a cinma abun da ake so ni dai abu Waya make so a wurin ki shi ne ki mai da hankali ki nutsu don mu samu abun da muke da bukata, ina son duk abun da zan koyar da ke to ki zauna ki fahimce shi da idon fasira. ''

Sai da ta gama sauraren shi tsaf kamin tana lashe hannu kamar wata mayya ta ce.

'' Ka ce sunanka Amiru ko?."

Ta jefa masa tambaya.

'' Eh haka ne amma za ki iya kirana da Uncle. ''

Ya ba ta amsa yana sake gazgata zancen Ashraf da ya ce dole sai ya yi ha?uri da ita, aikuwa ga shi nan dai da alama zai sha fama da ita.

'' Sabon salo shafawa duwawu kwalli kai kuma da wannan salon ka zo? To ba da ni ba gaWa a ?abari, shi sunan naka mai ya cishi ko na ce mai ya same shi ne da za ka wani ce na kira ka da Ungol to ba zan iya ba, da sunanka zan kiraka idan baka son sunan me ya hana tun a gida ka ce a sauya ma shi sai ni nan za ka wani ce na kira da Ungol to na ?i Win, Amiru zan kira ka iyee ba na son wani fi'ili.''



**********

A hankali yake sake duba decomment Win tare da yin rubutu akan laptop Win shi sosai ya dukufa akan aikin shi Wan ciza leSen shi na ?asa ya yi bayan da ya gano abun da yake son ganowa. Wayar da ke gefen shi ya Wauko wata number ya kira ringing Wai a na biyu aka Waga. Daga can Sangaren aka fara magana.

'' Hello Sir yanzu nake shirin kiranka saboda na gama duk wani bincike da ka sani kuma na gano daga ina wannan decomment Win suka fito a Office Win Munir ne suka ?araso zuwa nawa Office Win, kuma bincike na ya tabbatar min da cewa shi ne wanda ya jagoranci hada duk wata hujja da ke ciki.... Dukkan nin wasu hujjojin suna nan a tare da ni yanzu haka na tura ma su ta email Winka za ka iya dubawa.

Mi?e wa ya yi tsaye daga zaunen da yake tare da ture tables Win gaban shi ya saka hannu yana dafa kujerar da ya tashi a kai.

'' Good aikin ka ya yi kyau sosai ni ma daga ta rurina na gano wani abun amma ina so ka samin ido sosai akan Munir don akwai abun da nake zargi game da shi.''

Ya yi maganar tare da yin taku ya nufi balkonin Win da ke cikin Wakin shi hannu ya sa tare da yaye labule wurin take haske ya mamaye Wakin amma sai me zantukan Dagori ne abu na biyu da ya soma shiga cikin dodon kunne shi wanda ya daskere a wurin yana kare ma ta kallo yadda take zuba wa mutumin da ya girmeta rashin kunya.

Taku ya yi yana ?arasawa daidai makarin benen ya dafa shi da hannu sosai yake tunanin wane irin hukunci ya dace ya yi wa wannan yarinyar wanda za ta shiga taitayinta don ya ga alamar yarinyar tana da bukar haka.

'' Hello Sir kana jina kuwa sai magana nake amma ka yi shiru?."

Daga can Sangaren Jabir ya faWi jin da ya yi shirun ya yi yawa.

'' I call you back.''

Shi ne kawai abun da ya faWa tare da kashe kiran.



Amiru kuwa sauke numfashi ya yi yana ?arewa Dagori kallo tabbas ya ji ba daWi ka santuwar yarinya ?arama tana kare masa tanadi haka amma sai ya kawar ya ce.


'' To na ji shi ke nan miye sunan Walibar tawa ne?.

'' Ka ga Malam ba sunana Waliba ba sunana Dagori sai ka gane ba na...''

'' Ke!."

Wata uwar tsawa da Asad ya daka ma ta ne ya sa ta mi?e wa babu shiri don ta gane muryar shi, saboda muryar shi ko da a bacci ta farka to za ta iya gane ta. Zabar yadda ta hadda ce ta kuma ta zauna ma ta a ?wa?walwa...................



Comments
Like
Share


Taku har kullum mai kaunar ku

MRS AWWAL =???

*?DAGA RUGA NAKE?*

*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*


*HABIBTYN JAJIRTATTU CE* >?p?>?p?


=??? *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*=???
'?
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ?asaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sau?i_.'?




048


Mi?e wa ta yi har Flash Win da ke kan cinyarta yana faWuwa naman da ke ciki tuni ya tarwatse a ?asa, ba ta ko bi ta kan naman ba ta yi saurin yin bayan Amiru.


'' Dan girman Allah Ungol Amiru ka taimake ni Aradu kashe ni zai yi Wayyo ni Allah Dagori yau na mutu. Kuwa Allah ku zo jana'izata da wuri ko kun samu gawata da sauran mutunci, don yau na san ko gawata ba lallai ba ne a samu damar gane ta Wayyo ni Allah Dagori na gantale shi ke nan Baffa da Hamma Habu na maku ganin karshe.''

Cikin wani irin tashin hankali da rikicewa take magana don ita ma kanta ba ta ce ga abun da take faWi ba ita dai kawai ta san cewa magana take, baran ma da ta Waga ido in da ta jiyo sautin Muryar shi ta ga wayam baya wurin tuni hawaye sun gama wanke ma ta fuska.

Amiru kuwa mi?e wa ya yi kamar yadda ya ga ta mi?e yana mamakin yadda ya ga ta wani ri?ice sai sautabu take shi wallahi dariya ma ta ba shi duk wannan rawar kan na ta daga tsawa Waya ko ya ce magana Waya tabi ta wani fita daga hayyacin ta haka.

Ai kuwa sai fitowar shi ta gani waje, Amiru bai aune ba ya ji an cumui muiye shi da wani irin ?arfin.

'' Kawa Allah da Manzonsa kawa haihuwar da iyaye ka suka yi ma ka taimake ni ka Wauke ni daga cikin gidan tunkan wancan azzalumi ya ?araso wurin nan, Aradu bai da imani kuma bai san ta in da ya bi ya wuce ba yau kashe ni zai yi mahaukaci ne Aradu, ka taimake ni.''

Ta yi maganar tana sakin wani irin kuka bilhakki da gaskiya duk ta bi ta wani fita daga hayyacinta.

Daga ta tsallaken Swimming pool Win ya ja birki yana harWe hannaye shi a kan ?irjinsa fuskar nan ba Wigon annuri a kanta.

'' Zo nan!."

Ya furta a takaice wanda sam ba za ka ce shi ne ya yi maganar ba, ta san dai cewa da hausa ya yi magana amma ita sam ta manta idan an ce zo, me hakan ke nufi ta sake Suya bayan Amiru cikin muryar kuka ka ta ce.

'' Ungol Amiru me ya faWa?."

Ta faWi cikin shakewar murya tana sake makurewa bayan shi. Tausayi ta soma ba shi don duk wadda ya ga Dagori a wannan yanayin to dole ta ba shi tausayi.

'' Cewa ya yi ki je....''

'' Wayyo Allah watan mutuwa ya kama kawa Allah kada ka yi duba da tarin rashin kunyar da na yi ma ka cece ni.... Aradu aljannu ne da ni sune ke saka ni duk wani abun da nake Aradun Allah ba wai ina yi ne ason raina ba,sharin mutane Soye ne.''

Ta furta cikin sigar magiya da ro?o.

Ya buWe baki da niyyar magana suka yi ido huWu da Asad wani kallo da ya watsa masa ne ya sa shi haWiye kalaman shi.

'' Za ki zo ne ko sai na zo da kai na?."

?aga kai ta yi ta dubi Amiru ya kyauda na sa don ba wani abu da zai iya yi ma ta, masu iya magana sun ce wargi ma wuri gare shi.

Dubanta ta mayar wurin Asad wani Irin kallon da ma ta ya sa ba shiri ta fara nufar shi, tafiya take tana waige Amiru ko zai taimaka ma ta amma sam ko ido ya kasa haWawa da ita.

Ita dai ba ta san ya aka yi ba kawai dai ta tsinci kanta ne dab da shi. Sun kuyar da kai ta yi ?asa Kamar wata munafuka tana wasa da yatsun hannunta.

'' Ni sa'ar ki ne da za ki wani zo ki min ?ere,re a kai?."

Tun kan ya gama rufe baki ta yi saurin zubewa ?asa ta kwanta.

Dubanta ya yi cike da mamaki anya kuwa Dr nan gaskiya ya faWa masa da ya ce wai kanta ?alau ba ta da ciwon hauka shi dai ya kasa yarda da zancen, don duk wasu alamu sun gama nuna cewa ita Win akwai abun da ke yi ma ta motsi a kai. Shi da ya ce ta du?a shi ne ta wani zuSe ta kwanta a ?asa.

Tunani yake akan wane kalar hukunci ya da ce ya yi ma ta ne yadda nan gaba ko da mutum na ?asa da ita ne ba za ta ne mi ta tozarta shi haka ba, don wannan tozarci ne.

Wani murmushi mugunta ya yi bayan da ya gama tunanin lokacin da ya tsinkayi zancenta da su Aimanah.


'' Ni kuwa Sis na so a ce kin daure kin hau sama Win nan, babu fa abun da zai faru da k??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????e da kin ga yadda tsarin da zubin sama na san da kullum sai kin hau musamman bangaren Ya Asad wallahi don ma baya barin mu mu shiga ai hmm ba a magana kawai.''

Inty da ke kwance kan cinyar Mami ta faWa.

'' Uhm ai sai kuma ki yi idan halinki ne ke ni fa kaf a birnin nan babu abun da bai min ba irin wannan abun shin bene ko bono yake? Oho dai kuka sani amma ba ta yadda ni ba aljana ba, ni ba bokanya ba, ni kuma fatarwa ba haka kawai na kama hawa sama garin ya,ya to ba da ni ba, faWawa Delu mijinta zai ?ara Aure.''


Ta yi zancen bilhakki da gaskiya tana Waunar cingom. Dariya suka saka ma ta.

'' Kai jama'a yanzu Sis mu da ke hawa kenan ba mutane ba ne.''

'' Kin ga Aimanah kun ji kun gani ne zama gidan mayye, ganganci da kurwa amma ni ba da ni ba.''

Aimanah ta buWe baki da niyyar magana, Mami ta ce.

'' Kun ga ya isa haka ku bar ta mana tun da ba ta so ku shi ku je ku yi sallah ga ta can ana kira.''

Murmushi ya sake yi lokacin guda yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login