Showing 27001 words to 30000 words out of 99210 words

Chapter 10 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8224

turata a gado me taya sai emergency, da kyar suka iya shawo kan al'amarin dan harda oxygen suka Samata. Uncle saif ne ya kira Daddy ya sanar dashi halin da Noor keciki, sosai hankalinsa yatashi amma bazai iya zuwa ba, baze iya jure ganin Noor dinsa a wannan halin ba. Su hanifa suna waje sai ruskan kuka sukeyi suna rungume da juna. Doctor Awwal ne ya fito ya ce uncle saif yabishi office dinsa. Suna shiga suka zauna uncle saif najiran yaji me Doctor zaifada. Gyaran murya doctor Awwal yayi sannan yace " a gaskiya wannan yarinyar tana cikin mawuyacin hali, domin kuwa damuwa ne yamata yawa wadda yakaiga zuciyarta barazanar bugawa, amma don't worry she's out of danger, saidai kuma ina tunanin wannan ciwon ba yau ya fara ba, halan wasa takeyi da maganinta" wani irin zufa ne ya keto wa uncle saif yace" hakane doctor kuma muma munada laifi, da mahaifiyarta ce ke bata maganin, saita bukaci abata maganin kawai zatana shaa awurinta, damaa mun sani bamu bata ba" ajiyar zuciya kawai doctor yayi yace" karka damu zan kara rubuta mata wani maganin, insha Allah inhar tayi kokari tasha to zata samu sauki" godiya uncle saif yayi sannan ya karbi takardan prescription din magungunan ya fice daga office din. Har I zuwa lokacin Noor bata farka ba, wani daki aka kaita daga Anty jamila saisu Hanan adakin kowa ya zauna jigum jigum sunyi tagumi suna tausayawa Noor da halin datake ciki. Wayar Noor dake hannunsa Hanifa ne ya dau haske alamar kira, daukawa tayi amma batace komai ba, Nana daga dayan bangaren tace" haba Noor where did you keep your phone, inata kiranki amma baki daukaba" hanifa tace" Nana nice, muna hospital da Noor an admitting dinta" arazane Nana ta mike tace "what? Meyasameta,"? Duk abunda yafaru hanifa ta fadawa Nana. Ummi jin Noor na asibiti dukta rude dan dama suna zaune tare da Nana ne adakinta. " Nana menene, meyasami Noor" ummi tafada cikin tsantsan tashin hankali, duk yadda hanifa ta fada mata ta maidawa ummi, cikin hanzari ummi tace su shirya sutafi asibitin. Babu bata lokaci harda Dada aka shirya zuwa duba kawallinta. Driver Nana ta kira da sauri ya karaso sannan yajasu suka tafi.


*******
Aryan kuwa tunda yadawo daga gym din gidan yake bacci be tashi farkawa ba sai karfe sha biyun rana. Wanka yayi yasanya wani pencil jeans da white t shirt sannan yadau snicker fari kal yasanya. Sosai yayi kyau, turarensa masu sanyin kamshi ya fesa sannan ya dau p cap dinsa yasanya akai. Wayoyinsa da makullin motarsa ya kwashe yafice daga dakin cikin takunsa metafiya da imanin mata. Part din ummi ya nufa amma ga mamakinsa basunan dukkansu, wani ma'aikacin gidan ya tambaya yace masa yaji suna cewa zasu tafi asibiti. Mamaki ne ya kamashi to wanene ba lafiya. Ahankali ya taka ya fice daga falon ya shige motarsa yafice daga gidan.


*******
Moon ne zaune a falo karfe sha biyu da kwata na rana tana latsa wayarta sai faman dariya takeyi kamar tababbiya. Mahmud ne ya shigo falon yasameta a wannan halin. Zama yayi yace" baby, yau abokai na zasuzo pls inaso kimusu wani hadaddiyar girki, kinji" hararan takaici ta watsa masa kayi tsaki tacigaba da danna wayarta, mamaki ne ya kama Mahmud, me yarinyarnan take nufi dashi, kodai saboda ya daga mata kafa ne Yau satinta kusan uku agidannan amma kulllum yana hanyar siyan abinci? Tsawa ya dakamata yace"what nonsense Moon, me kike nufi da tsakin da kika min, nifa mijinki ne, kodan na daga miki kafa kina duk abinda kikaga dama shine zai baki right din wulakanta ni"? Mikewa Moon tayi ta daga masa hannu alaman ya dakata tace" kaga malam, ba baiwa aka kawo makaba, ni ko a gidanmu mamana bata bari na dau tsinke bare har kai kazo kanacewa inyiwa abokanka girki, ni ban girka abinda zanci ba shine zan girkawa wasu kattin mazan? Mamaki,takaici duk sune suka mamaye Mahmud. Lallai akwai sauran aiki agabansa, anya soyayyar daya kewa Moon, is it really worth all the insult? Girgiza kai kawai yayi ya fice daga gidan. Tsaki Moon tayi ta gyara zamanta tana surutai marasa kan gado.


******
Tunda su ummi sukaje asibitin Noor bata farka ba sai kusan maghrib kafin ta farka. Kuka sosai takeyi tana kiran Amminta, ta matukar bawa mutanin dakin tausayi, ummi tayi tagumi sai kallon Noor takeyi ba kiftawa azuciyarta tana cewa" tabbas bayan aurensu Noor da Aryan yakamata tabata kulawa sosai a matsayin wacce ta rasa soyayyar mahaifiyarta tun tana yar shekara goma. Da kyar su Hanan suka rarrasheta tayi shiru, tea me kauri Anty Jamila tahada mata tabata, bayan tasha kuma aka bata magani shima tasha ammafa da kyar. Bayan isha doctor Awwal yabata sallama tunda jikinnata yasamu sauki sosai. Tare suka fita daga asibitin tare da su ummi kafin kowa yadau hanyarsa zuwa gidansu.


*******
Aryan bedawo gida ba sai 9pm. Afalo yasamu su ummi suna dan taba hira. Zama yayi ya gaidasu, Dada tace" dannan tunda safe rabona da saka ka a ido, gashi kawalli na ba lafiya shine mukaje asibiti sai dazu muka dawo" shi Aryan bemasan wacece kawallin Dada ba dan haka gyada kai kawai yayi ya mike yabar falon dan damuwarsa ma tafi takowa haka yake gani. Yana shiga daki yazauna abakin gado yadafe kansa, zuciyarsa wani irin kuna yakeyi masa, bakin ciki duk ya mamayesa. Shifa haryanzu maganan auren nan kamar a mafarki yake ganinsa. Wazai kaiwa kukansa, tayama zai fara soyayya da wata,cije labbansa yayi da karfi yana mejin zafin har cikin kasan zuciyarsa. Lallai yarinyar nan zatayi nadamar aurensa dukda besan ko wacece ba. Gashi kuma amaganansu Abba auren nan da watanni biyu ne. "Ya Allah" kawai ya iya furtawa yana yamutsa kwantaccen gashin kansa. Da kyar ya mike ya shige bathroom danya watsa ruwa.

******
Bayan sun dawo gida tayi wanka ta rama sallolin da ake binta sannan tayi shirin kwanciya. Anty Jamila ce ta shigo hannunta rike da glass cup cike da ruwa aciki dakuma magungunan Noor. Noor na ganin maganin a hannunta tafara yamutsa fuska tana turo baki gaba. Itafa in akwai abinda ta tsana to magani na cikin su. Saida aka lallabata sannan tasha maganin tana kukan shagwaba. Batawani jimaba bacci ya dauke ta.


******
Washe gari da sassafe Mahmud yakama hanyar gidan Daddy dan yanzu wulakancin Moon yafi karfin tunanin me tunani. Jiya da abokan sa suka zo babu irin rashin mutunci da Moon bata musu ba, daga karshe ma fushi sukayi suka bar gidan ko abincin dayasiyo ma basuci ba. Tuki yakeyi amma zuciyarsa cike take da bakin cikin matarnasa. Abakin gate din gidan ya tsaya yayi horn. Megadi ya budemasa gate din ya shigo. Mamaki ne ya kama su daddy ganin surukinnasu da sassafe dan alokacinma breakfast sukeyi. Hararan takaici Mama ke ta aikawa Mahmud tunda ya shigo. Tsugunnawa yayi har kasa ya gaidasu Daddy cike da girmamawa. Kujera daddy ya nuna masa ya zauna. Bayan sun gama cin abinci Mama taki matsawa awurin dantanaso taji meke tafe da Mahmud din, tasan zuwansa da sassafennan ba alkhairi bane. Mahmud kansa na kasa yafara maidawa Daddy abinda Moon tamasa. In ran daddy yayi dubu to ya baci, mikewa Mama tayi da sauri tace" kaga Ahmad kake ko Mahmud whatever, wlh karyanka kace zakazo har cikin gidana kazo ka aibanta min 'ya, wlh kayi kadan, danma ka gode mun baka ita shine harkanada fuskar zuwa kaci mana mutunci ka zageta iyye"? Saikuma tajuya kan Daddy wadda mamaki yama gama rufesa tace" Nasir kagani ko, kaga abinda nake gudu ko,na tabbata da ka aurawa Moon wadda takeso daba haka ba amma dama Ku maza halinku day..." Bata gama rufe baki ba daddy ya daka mata tsawa yace"ke Hamida ki iya bakinki, ni yazo ya sama bakeba, what gives you the right to talk before me" shi Mahmud mamaki halin Mama yabasa, ashe dai Moon ba akasa ta dauka ba, lallai in babba ya yadda girmansa karami zai hau kai ya taka. Shidama yasani ma bezo ba inda yasan outcome din kenan. Daddy yajuyo ya kalleshi cikeda tausayi yace" Mahmud jeka, insha Allah zuwa anjima zanzo har gidan nasami Moon din kaji"? Kai kawai ya daga sannan ya mike jiki a sanyaye ya fice daga falon, Mama kuma tana rakasa da wani irin kallon tsana. Bankadeta daddy yayi ya wuce ta gefen ta yana mamakin irin rashin kamun kai na Mama. Tsaki tayi ta zauna tana surutai da zage zage.

*******
Yau beje aiki ba, haka kawai yaji ma zaman Nigeria ya gunduresa tunda maganar auren nan yataso. Wayarsa ya dauka ya kira Muhsin abokinsa ya narrating masa danshi kadai yake iya sharing problem dinsa dashi, ko Shareef ba kullum yake fada masa damuwarsa ba. Instead muhsin yaji tausayinsa saima dariya daya dinga masa yana masa sharri akan saisunzo cin shinkafan biki. Ransa sosai ya baci daga bayama ya kashe wayar yanajin ransa na kara baci. Shifa tunkafin ayi aurenma yaji ya tsani yarinyar bamayason ganin kalarta.

*******
Yau jikin Noor yayi sauki sosai tunda bata tafi makaranta ba, tare ma sukayi girki da mai aikin gidan dan jikinta yasaba da aiki kuma dukda watannin data dauka agidannan sam bata zama me kyuya ba. Ko kallon abincin ma batayi ba sai aikin cin snacks dama aikin kenan. Inkuma zata ci abinci toh ba sosai ba.


Da yamma Daddy ya tafi gidan Moon kamar yadda ya fada yamata tatas harda kukanta kamar na Allah. Sosai yaja mata kunni akan 'batawa miji rai, amma kamar ma ya shige ta wannan kunnin ne ya fita ta wancan.


Yau polisawa suka raiding wani club inda aka kwashe yan mata da samari gaba dayansu. Wani irin bad party suka hada harda su Lubna. Sunan party din wai *Wild and wet party" wasannin banza akeyi marasa kyan gani. Maza ne da mata ke masha'ansu son ransu. Wani acikin ma'aikatan wurinne ya kira polisawa ganin wasan na wuce gona da iri dan wasu tantiran har zina sukeyi agaban mutane. Lubna kuma da wani bad guy aka kama toilet suna zina, babu kayan kirki ajikinta haka aka jasu zuwa motan polisawan tanata wasu surutai cikin maye.(Wa'iyazubillah, Allah ka karemana imaninmu, ka kare mana 'ya 'yanmu da kannenmu).


********
Lokaci ba wiya, yau yarage wata daya bikin su Noor da Ya Shareef. Akowani bangare anfara shirye shirye ba kama hannun yaro. Ummi dakanta tatafi Dubai da wata kanwarta Anty Ounaisa, siyayya me tarin yawa sukayi na kayan lefe inda aka hada lefe kusan akwatuna guda 24. Komai dam dam ba'a magana. Sunkai kusan kwanaki uku kafin suka dawo. Nana karan kanta batasan da maganan bikin ba.

Hakan ya kasance a gefensu Anty Jamila, siyayya sosai sukeyi harda 'yan uwansu Daddy su Anty umaima. Wata kawar Anty Jamila Hjy Balaraba itace aka bawa hidimar gyaran jiki Noor. Hjy balaraba matace wayayya wacce tasan kan jikin mace dakuma gyara. Daga Sudan take amma tana aure anan Nigeria itama a Abuja take da zama. Har yanzu Daddy ko uffam bai fadawa Mama ba akan bikin. Noor kuwa bama tasan wainan da ake tauyawa ba. Karatunta takeyi sosai saboda sunkusa fara exams nan da sati biyu zasu tafi 200lvl.

Oga Aryan shima yadda take a wurin Noor hakan takasance agefensa. Shiyama mance da wani aurensa da za'ayi. Aikinsa yakeyi cikin kwanciyan hankali yariga yagama planning irin wulakancin dazeyiwa so called amaryartasa.(kardai ka tabo kawar Dada yawwa,hatta mu tsoron masifan ta muke ehe)


Ya Shareef andage sai suburbuda love akeyi da matarsa to be Na'ima. Shima shirye shiryen yake haka zalika Na'iman.


Yau Hjy balaraba tazo gidan Anty Jamila dan yau zata tafi da Noor gidanta har zuwa lokacin bikin, dan sai ana kwana biyar da bikin zata dawo gida. Daga can zatana zuwa makaranta. Bayan su Noor sun dawo daga makaranta, taci abinci Anty Jamila tace da ita" habibty shiga ki hado kayanki a akwati, zikibi Hjy balaraba akwai gyaran danakeso tamiki kinji" babu tunanin komai aranta ta mike ta shiga dakinsu tafara shirya kayanta a dan akwatinta. Tana cikin shiri su Hanan suka shigo, hanifa ta zauna abakin gado tace" Noor wani irin gyara za'amiki, nifa nasan Hjy balaraba gyaran amare takeyi" harara Noor ta watsa mata tace" toh sai akace miki ni amarya ce, halan kawai wani abun daban zata mun" kyaleta sukayi amma tabbas sunfara zargin wani abu, aide in bikin Ya Shareef kadai za'ayi meyasa za'ana kawo kayakin kitchen dasu abubuwan da'ake siyowa amare. Haka tagama shirinta sannan ta rolling dankwalin abayanta akai ta dau wayarta ta sallami su Hanan tafice falo zuwa wurinsu Anty Jamila. Hjy Balaraba kam tanata mamakin kyawu irinna Noor saikace ba bahaushiya ba dan ita atunaninta Noor din bahaushiya ce. Har waje Anty Jamila ta rakasu sannan tadawo ciki bayan sun tafi. Agaban wani tangamemen gida Noor taga sun parking. Sosai tayi santin kyawun gidan. Babban gida ne da part guda biyu sama da kasa. Afalo taga wasu yan mata guda hudu suna zaune suna hira, tunda su Noor suka shigo suke kallonta, kunya ne ya rufe Noor da irin kallon dasuke binta dashi. Awani dan madaidaicin daki Hjy Balaraba ta sauki Noor. Daki ne hadadde sai tashin kamshi yake, dama tunda tashigo gidan takejin wani irin sanyi da kamshi yana ratsa gaba daya ilahirin jikinta. Wani dan madaidaicin gado ne adakin sai wardrobe mai kofa biyu, sai kuma dan dressing mirror, komai na dakin tsaf tsaf." Kije kiyi wanka ki huta anjima zamu fara abinda yakawomu kinji 'yata" kai kawai Noor ta gyada sannan ta fara warware dankwalin abayan dake kanta. Take dogon sumanta ya warware har gadon bayanta. Wardrobe din dakin ta bude taga anjera towel kusan guda biyar, wani pink baby towel ta dauka ta wuce toilet. Sabulan wanka da kuma turaruka masu kamshi tagani, ruwan wanka ta hada a bathtub din mai dan zafi sannan ta shige tafara cuda ko wani lungu da sako na jikinta. Ta dau kusan minti ashirin sannan ta dauro alwala tafito. Wasu mayuka masu kyau tagani anjera asaman dressing mirror, dayake ana zafi shiyasa batama shafasu ba. Akwatinta tabude tafidda wata doguwar riga mai dan kauri tasanya. Doguwar hijab dinta ta fitar dan lokacin har anfara kiran sallan maghrib. Sallaya ta shimfida ta tada sallah. Bayan ta idar ta zauna a wurin har akayi sallan isha sannan itama tayi. Tana idarwa taji anbude kofa anshigo, wata yar budurwa ce akalla zata kai shekaru 16 ta shigo hannunta dauke da basket na abinci" gashi mama tace kici saiki fito kisameta afalo" Yar budurwar ta fada tana sakarwa Noor murmushi. Gyada kai Noor tayi itama tana murmushi. Bayan ta idar da azkar ta cire hijab din jikinta, basket din abincin tajawo gabanta, kuloli guda uku ne, daya farfesun kaza ne wadda yaji kayan hadi na musamman sai tashin kamshi yake, dayankuma fried pasta ne dayaji kayan lambu da su hanta, na ukun kuma chips ne akasoya da kwai incase bazataci fried pasta dinba. Kunun aya mai sanyi ne a jug shima yaji kayan hadi na musamman. Plate ta ciro ta zuba farfesun nan da chips taci, batawani ci sosai ba amma tas ta shanye farfesun danba karamin dadi yamata ba. Kunun ta diba cikin cup tashanye sannan tayi gyatsa tace Alhamdulillah. Basket din ta dauko ta fito daga dakin ta wuce falo. Azaune taga Hjy Balaraba da wannan yan matan data gani lokacin dasuka shigo. Mikewa Hjy Balaraba tayi takallesu tace" mujenku ba" dukkansu harda Noor suka bita zuwa wani daki mai girma sosai sai tashin kamshi yakeyi, duk cikin dakunan gidanma kamar wannan yafi kamshi. Towel taba kowannensu tace su tube su daura. Da mamaki Noor takarbi towel din azuciyarta tace" toh babban magana, ko me zamuyi oho". Kowacce acikinsu ta tube ta daura towel din amma banda Noor wani irin kunya takeji. Hjy Balaraba tayi murmushi tace "'yata karki damu aiba awuri daya za'a muku gyaran ba" abayan wani kofa ta labe ta tube kayan sannan ta daura towel din wadda iya rabin cinyarta ya tsaya. Bayan ta fito kowa yadinga kallonta suna mamakin irin wannan kyau ga kuma shape kamar ita tayi kanta. Su biyar ne so kowacce da dakin da Hjy Balaraba tanuna mata ta shiga. Hjy Balaraba itada kanta zatayiwa Noor gyaran dan haka, wasu kwalabe ta dauko da alama turaruka ne aciki ta mike wa Noor tace ta shafa su ajikinta. Babu musu Noor ta karba tana shafawa ajikinnata. Wani irin kamshi na musamman turaren keyi me dadin shaka,har wani lumshe ido Noor keyi tana cigaba da shafa turaren ajikinta. Bayan tagama saida tashafe kusan 30 minutes kafin Hjy Balaraba tafara shafe mata kwabin dilka akowani bangare na jikinta, lungu da sako, kunya kamar ta kashe Noor dan warware towel din tayi. Bayan angama shafeta da wannan kwabin kuma ta dauko wani abu a kofi tabawa Noor tasha, da dardar takarbi abun amma jin yayi mata dadi takafe bakinta ta shanye shi tas harda tande baki, wani tsumin Hjy Balaraba ta kuma bawa Noor tasha shima kamar waccan yanada dadi sosai. Wani inji Hjy Balaraba tasata ta shiga, abun za'a iya kiranshi da steaming machine, takai kusan awa guda aciki kafin machine din ya mutu dakanshi. Haka Hjy Balaraba tadinga durje wannan dilkan daga cikin Noor tas sannan tasata tashige bathroom din dake cikin dakin datyi wanka. Tun a wannan ranan Noor tafara ganin changes ajikinta, saitaji tayi wani irin sumul kamar ba itaba. Data fito daga dakin taduba katuwar agogon dake falo taga sha daya saura. Tana shiga dakin da aka sauketa bata wani dau lokaci me yawa ba bacci ya dauketa. Washe gari da safe tana cikin shiri Hjy Balaraba ta shigo dakin hannunta dauke da Kofi da kuma wata yar jaka ta mikawa Noor. Nonon rakumi ne fresh tabata saida tashanye tas sannan Hjy Balaraba tace" ga wannan jakan, hijab ne da niqab shi zaki sa saboda ba'aso mace tana dilka kuma tana shiga rana. Amsa Noor tayi ta bude jakan, farin hijab ne da niqab me kyau aciki. Babu yadda ta iya haka nan tasa shi amma kuma ba karamin kayu tayi ba kamar wata balarabiya.


Yau mamaki kamar ya kashe Nana ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login