Showing 45001 words to 48000 words out of 99210 words

Chapter 16 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8206

wuce sannan take fitowa. Shima aryan bai kara nemanta ba dan wasu lokutan da sassafe yake fita. Yanzu haka shirye shirye yakeyi akwai wani conference din da zai attending a uk kuma kusan one week zaiyi. Bai fada mata ba dan bawani shiga harkanta yakeyi ba. Bayan ya gama shirya kayansa cikin dan karamin trolley ya jinginashi agefe ya dawo ya zauna gefen gado, ko tunanin meyakeyi shi kadai yasani, can sai naga ya mike ya nufi wani drawer dinsa ya dau karamar envelope da paper hadi da biro. Dan gajeren rubutu yayi sannan ya dau rafar one thousand guda biyu yasa acikin envelope din ya aje kan side drawer na gadonsa. Bayi ya shiga ya watsa ruwa sannan ya fito daure da towel a kugunsa. Bayan ya gama shafe shafensa ya dau wani pencil jeans da tshirt black colour da pcap shima black ya sanya, sosai kayan suka fidda kyawunsa kuma farar fatarsa tayi kyau cikin bakin shigan dayayi,turarensa ya fesa sannan ya dau wayoyinsa da car key ya fito, kallon kofar dakinta yayi kamar me tunanin wani abu saikawai ya juya ya fice daga falon, motarsa yashiga sannan ya fice daga gidan. Direct gidansu ya nufa, yana zuwa ya tadda anfitar da akwatunan Dada yau zata koma, itakuwa tana ganinsa tace" dannan wato dan kayimin kishiya shine kake min buqulu bakaso kabarni naje naganta ko, toh ai hikenan, yanzu dai kaga zan koma amma inaso nan da watanni goma na dawo wankan jegon kawallina, inafata kana jina"? Kai kawai ya gyada sannan ya tsaya har saida yaga tashin su kafin ya shiga cikin gida. Afalo yasamu ummi itama yanzu ta shigo daga rakiyar Dada. Gaida ita yayi ta amsa sannan ta tambayeshi ya mai dakinsa, klau kawai yace, ummi ta karanci yananyin fuskarsa tace" i hope dai babu wata matsala ko, kuma Noor tasan da maganan tafiyarka"? Dagowa yayi ya kalleta sannnan ahankali ya girgiza kansa alaman a'a, da sauri ummi tace" what? meyasa baka fada mata ba, munan agida kafada mana tun tafiyar na sati daya, amma matarka na gida batasani ba, wai dan Allah wani irin zama kukeyi ne da yarinyar nan, pls Aryan inhar kasan bazaka rike amananta ba toh tun wuri musan nayi, i'm 100% sure ma kila babu abinda yataba shiga tsakaninku dan wannan yanayin daka nuna min nasan tabbas shi kake nuna mata agida, toh wlh ka kiyayeni ka fita a idona, kul naji wani abu makamancin fada ya hadaku ko sa'insa tom" tacigaba da masa fada ta inda taje shiga batanan take fita ba, ba yau Aryan yasaba nuna mata wannan halin ko inkula akan Noor ba duk lokacin data tambayesa ya take, Allah sarki marainiyar Allah ko wani hali take ciki Allah kadai yasani. Bayan tagama hucinta kawai sorry yacemata ya mike yafice, da kallon mamaki tabisa wato ma duk wannan yawun data bata sorry kawai zai iya fada, ai shikenan zako ta koya masa hankali, bari ya tafi tasan yadda zata shawo kan al'amarin.

Yana fita ya shiga motarsa yabar gidan dama sallamansu yazo yi gashikuma ummi ta hau kansa akan wannan mai bakin tsiwan. Lallai bari ya dawo saiya koya mata hankali ( daga baya kenan). Kiran shareef yayi amma har kiran ya katse be dauka ba, ransa ne ya kara baci yace" banza mayen mace kawai". Wani câfe ya nufa inda babu mutane dayawa ya shiga yayi ordern coffee. Yana cikin zamansa kawai yahango Lubna tsaye da wani kato ta wajen glass din dake cafe din suna jingine da motarsu,kiss sukeyi babu kakkautawa kamar zasu cinye leben bakinsu, tsaki Aryan yaja ya kau da idonsa a wurin, "yarinya duk ta gama lalacewa kamar ba diyar musulmai ba, wai ahaka take so na aureta, nonsense" yafada yana jan guntun tsaki. Juyawa yayi kuma yaga har sun shige mota sun bar wurin. Shi yanzu tunani ma yakeyi akan maganan ummi, yasuke so yayi da kansa, shiba son yarinyarnan yakeyi ba duk sunbi sun wani takura masa, ga itakuma uwar gayyar sai shegen rashin kunya amma ga tsoro, tunanin ranan da akayi incident din coffee dinnan yayi sai ya saki sassanyar murmushi dan ba karamin dariya tabasa ba datake shan coffee tana matsar kwalla.

Waya takeyi da yasmeen akan maganan komawarsu school bayan tagama taduba time taga sha daya saura, mikewa tayi ta sauko zuwa kitchen dan dora abincin rana. Bawani abu tayi ba, grilled catfish ne dayaji chips da su veggies sai jollof rice da salad, sai kuma pineapple juice, tana gamawa ta shiryasu akan dinning table, lokacin har an fara kiran sallah zuhr, haurawa tayi zuwa dakinta ta shiga wanka ta dauro alwala sannan tafito. Bayan ta idar da sallah ta mike ta bude wardrobe dinta ta fidda wani pencil skirt black ta rigarsa shikuma white da black cap. Sosai skirt din ya fidda shape din mazaunanta danya kame ta shima rigar ya kameta ya fidda shape din nashanunta wadda ake iya gani ta saman rigan, takalminta na yawon gida tadauko tasanya tafeshe jikinta da turare sannan ta dau wayarta ta fito dan yunwa sosai takeji.

Shigowarsa kenan ya hango abinci kan dinning, rabonsa da cin abincin kirki ya mance, kullum cikin shan coffee yake, haka kawai yaji yana sha'awar cin abincin dan yunwa yakeji bana wasa ba. Zuwa yayi ya zauna kan dinning ya bude food warmer din, jollof rice ne dayaji kayan lambu sai tashin kamshi yake, dayan kuma grilled fish ne da chips ga kuma pineapple juice me sanyi. Miyau ya hadiye sai kuma yazauna kamar yafasa cin abincin yace" a ido gwanin sha'awa a baki kuma Allah kadai yasan wani shirme akayi" plate ya dauka ya serving kansa shinkafa da kifin hadi da chips din. Bismillah ya furta yafara cin abincin, ido ya ware baiyi tsammanin sosai abincin zaiyi dadi ba, zai iya cewa ma tunda yake bai taba cin abinci mai dadi irin wannan ba( la la Aryan toh akunnin ummi) ci yakeyi yana kurban juice dinsa shima ba karamin dadi yamasa ba, baisan lokacin daya cinye harya kara wani ba, ga abincin ba dayawa ba daidai cin mutum daya ne haka ya cinye tas ya cinye kifin. Jiyayi ma kamar abincin bai isheshi ba, tagumi yayi yana kallon kulan inama abincin yadawo dan gsky yayi masa dadi. Fitowar Noor kenan daga daki har ta iso falo bata daina mamakin ganinsa akan dinning ba, toh meyakeyi awurin, karasowa wurin tayi dan itafa yunwa takeji bazata wani ji kunyarsa ta gudu awurinba. Kallonta yayi kasa kasa, yau kawai yaji tayi masa kyau kodai danya dade be ganta bane. Ko kallonsa batayi ba taja kujera tazauna harda daukan plate dinta zata ci abinci,abun mamakin datagani yasata mikewa tsaye tana kallonsa da plate din dake gabansa, aiko ba'a fada mata ba tasan shiya cinye mata abinci, kafa tafara bubbugawa akasa tana magana kasa kasa cikeda shagwaba da batamasan tanayi ba, shikuwa kallonta kawai yakeyi saiyaji shagwaban ya birgesa. Tsakaninta da Allah takeyi harda dan guntun kwallanta a ido tace" kawai kawai mutum yayi abincinsa an wani zo anciye masa tsaban mugunta irin na wasu, ni yanzu me ake so naci dan Allah" mikewa yayi yabar mata wurin, yau kawai jiyayi bazai iya bata amsa ba dan yasan shine da laifi, ohh Allah ashe dadi ne keta wucesa abaya gashi gobe zai tafi, ayanzu kam bayajin akwai wani abincin dayake buqata sama da nata. Kuka Noor tazauna tanayi dan ba karamin bakin ciki ya cusa mata ba, wato ma adukeka ahanaka kuka, dataga kukan bazai tsinana mata komai ba tamike takwashe plates din dayaci abinci tawuce kitchen dasu. Indomie ta dora awuta dan batajin zata iya girka wani abun mai wahala. Bayan tagama ci takoma daki ta kwanta tana jin fushinsa azuciyarta.

Oga Aryan dan kunya bai kara dawowa gidan ba sai kusan ten na dare lokacin Noor hartayi bacci, yaso ace yakara ganin wani abincin kan dinning, shi ba ma'abocin cin late night food bane amma tabbas in itace ta girka zaici hani'an. Wucewa daki yayi ya watsa ruwa yayi shirin bacci. Tunanin wannan envelope dinne ya fado masa, toh ya zaiyi yabata tunda ba magana sukeyi ba, wani idea ne yafado masa, slippers dinsa ya sanya ya dau envelope din ya fito daga dakinsa, kamar zaiyi knocking saikuma yafasa yabude kofar ahankali yashigo, kan gado ya hangeta tayi dai dai tana bacci. Wasu arnan kayan baccine ajikinta, gown mai shara shara babu abinda baya nuna wa ajikinta, babu haske adakin illa hasken bedside lamp. Ga gashinta daya watse kan pillow gwanin sha'awa. Ya bata kusan ten minutes yana karewa ko wani sassa na jikinta kallo, haka kawai ya tsinci kansa cikin wani mugun kasala, kai yafara girgizawa azuciyarsa yace"Muhammad Aryan control" envelope din hannunsa ya aje a kan bedside drawer dinta ahankali yajuya ya fice daga dakin. Ko dayakoma daki kasa bacci yayi, hoton jikinta ne ke yawo a kwakwalwarsa, ashe dama ba ciko bane, ashe na ainahi ne, lallai tanada tarin baiwa, ga iya girki ga shape. Da kyar ya samu bacci yadaukesa, cikin baccinma wani mafarki yayi dayasanya shi mikewa da sauri yana addu'a, wandonsa yataba yaji sharkab ya lalace, gefen sajensa yashafa tareda sakin murmushi yace"Aryan what's wrong with you" mikewa yayi ya shige toilet yayi wankan tsarki da alwala. Nafila yayi ya duba agogonsa yaga karfe biyar saura, mikewa yayi yafara shiri dan jirginsu karfe shida da rabi zai tashi. Three pieces suit coffee brown yasanya nacikin kuma milk sosai yayi masa kyau. Turare ya fesa sannan ya dau wayoyinsa da dan karamin trolley dinsa yafito. Kallon kofar dakinta yayi har na kusan two minutes kamar mai jiran wani abu sannan ya juya ya fice. Abakin gate ya tadda drivern ummi har yazo daukarsa. A masallaci suka tsaya sukayi sallan asuba sannan suka kama hanyan airport.

Kiran sallah ne ya tashe ta, mika tayi tare da addu'an tashi daga bacci, idanunta ne suka sauka akan envelope din dake kan drawer dinta. Hannu tasa ta dauka sannan ta bude shi, zaro ido tayi ganin kudin dake cikin, to wa ya ajje wannan dunbin kudin anan, sai kuma ta tuna ai su biyu ne kawai agida, wani dan karamin paper tagani aciki tafitar ta karanta abinda aka rubuta aciki"zanyi tafiya banda yawo, daga school sai gida, from Aryan" tsaki tayi dan tunawa tayi da abinda yayi mata jiya. Saukowa tayi daga kan gadon ta shige toilet tayi wanka da alwala. Bayan ta idar da sallah ta shirya cikin kayanta na makaranta ta combing gashinta ta nade shi sannan tayi rolling. Jakanta ta dauko ta zuba takardunta da abubuwan buqata sai key din motarta ta fito. Cereal ta hada tasha dan idan tace zata tsaya yin girki latti zatayi. Motarta na fake a parking space kamar ma wankesa akayi yayi neat, tana shiga ta danna remote din gate ta fice.


Sosai sukayi murnan ganin junansu. Hira aka shiga yi na yaushe gamo kafin suka wuce lecture hall. Karfe goma suka fito su dan huta kafin next class. Yasmeen ne ke tsokanar Noor tace" amarya kinga yadda kikayi wani fresh kuwa, me yayanmu ke baki sai wani sheki kikeyi" dariya nana tayi tace" tab wannan ko, ai ya Aryan sai ahankali kodayake Noor dinmu ta dabance, tasan yadda takeyi da abunta" murmushi kawai Noor tayi azuciyarta tace" da kunsan abinda ke wakana atsakaninmu da bakuyi wannan maganan ba". Time din next lectures nayi suka shiga.

******
8:00pm SCOTLAND

Wani tamfatsetsen gida ne mai shegen kyau kirar baturai. Zaune yake cikin kayan shan iska yana kurbar coffee dinsa yana karanta wani magazine. Wayarsa ne ta fara kara, murmushi yayi yadauka" ummi good evening", magana sukayi ko me tace masa naga yanayinsa yacanza. Ajiyar zuciya kawai yayi yace " all right ummi, ba damuwa na yarda" bayan ya katse kiran ya mike ya koma cikin gida ya wuce bedroom dinsa, kananan kaya yasa da snickers da pcap yafito. Wata farar matashiyar baturiya nagani ta nufo shi tana murmushi, shikuwa oga wani tamke fuskarsa yayi kamar baisan menene dariya ba, tana zuwa tawani bude hannu zata rungumesa, harara ya watsa mata ya daga mata hannunsa alaman ta dakata," ohh Aryan you can never change, this is uk not Nigeria, all this is normal but you don't seem to understand" baice mata komai ba har zai tafi saiya juyo yace mata" Natasha, i'm now a married man, this shouldn't repeat itself" yana gama fadin haka ya juya yayi tafiyarsa, kallonsa tayi kamar zatayi kuka tace" Aryan i've always loved you since we were in school why can't you just love me back, whyy" yana jinta ya share ta dan bata cancanci ya tsaya magana da ita, tun suna school bawani yinta yakeba. Haka tayita kukanta har ta gaji sannan ta juya ta tafi.

Shiko yawon zagaya gari ya shiga yi inda yazo wani pet shop yaga wasu kananan kittens kyawawa fari da orange, dama yana son kyanwa sosai gasukuma jarirai dan haka saiyaji sha'awarsu. Shiga cikin shagon yayi inda yanemi akirawo masa mai kula da wurin, wani bature ne mai suna John yazo suka sha hannu sannan ya sanar dashi akan wannan kittens din yake so. Nan suka gama magana Aryan yace mai ranan dazai koma Nigeria zaizo yadauka acigaba da kula masa da su har zuwa lokacin, kudi ya biya na abincinsu da sauran abubuwa sannan ya fito daga wurin. Tafiya yakeyi yana shakan daddadan iskan garin, haka kawai tunanin Noor yafado masa, wani irin missing girkinta yakeyi daga jiya zuwa yau, ko tamaga sakonsa? Ya tambayi kansa, haka yacigaba da tafiya shi kadai har ya gaji yadawo gida dan daga gobe zasu fara event dinsu yakamata yasamu yahuta.

******
Nan kuwa Noor nagani agidan ummi karfe shida na yamma itada nana suna girki akitchen, ummi ce tashigo dauke da murmushi a fuskarta tace" sannunku da aiki, Noor sannu kinji, gobe insha allah saikuje gidanki keda Nana ku kwaso kayanki na yan wannan kwanakin dazakiyi kafin mijinki yadawo" kai kawai ta gyada wani kunya ya rufeta wai mijinta. Haka sukacigaba da girkinsu suna hira itada nana suna zolayar juna, suna cikin girki wayar nana yayi kara ta dauka ta fice tana wani kashe murya, Noor tayi murmushi tace" Ya Muhsin kenan an iya zuba flaws..", babu wani bata lokaci tagama aikin abincin dama kadan yarage dan haka ta karasa itada mai aiki suka jera shi kan dinning.


Washe gari bayan sun tashi a school suka wuce gidanta inda suka kwaso kayanta wadda zata buqata kafin one week. Ummi tayi hakane dan bazata iya barin Noor tazauna ita kadai ba a wannan tangamemen gidan, shiyasa jiya data kira aryan tafada masa dukda ta fahimci baiso hakan ba kuma batasan dalilinshi ba amma babu yadda iya hakanan ya yarda tadawo zuwa lokacin da zai iso nigeria.

******

Fitowarsu kenan daga conference hall kowa ya fito agajiye danba karamin lokaci suka dauka acikin wurin ba. Sanye yake cikin wata dakakkiyar designer suit black and white yayi kyau ga wani bakin shades din dake fuskarsa, duk yadda wasu matan sukaso yin magana dashi bai basu daman yin hakan ba, mazan ma manyan cikinsu ne kawai yabasu daman yin magan dashi. Hotuna akayi na day one din activity din sannan kowa yafara komawa muhallinsa. Wata bakar Mercedes benz naga ya nufa inda wasu bodyguards ke tsaye suna jiransa. Yana isowa daya daga cikinsu ya bude masa ya shige, ahankali suka fara tafiya. Acikin harabar gidansa suka tsaya, bude masa akayi yafito zuwa cikin gidan. Kodaya shigo masu aikinsa har sun gama abincin yamma shi kawai suke jira amma ko kallon abincin baiyi ba, ada kenan ma bai damu da abinci balle kuma yanzu da aka dandana masa wani na musamman. Wanka yashiga a lokacin daya fito kuma har anfara kiran sallan maghrib a masallaci dake kusa dasu. Cikin gaggawa ya shirya ya fice dan samun jam'i.

*******
Cikin kwanan nan da Aryan yayi, ummi ta lura ko sau daya bata taba ganin ya kira matarsa ba kuma itama bata kira shi ba, nanne ta gane tabbas akwai matsala a zamansu, anya ba babban kuskure suka tafka da wannan auren hadin ba kuwa, Allah kawai ta fawwalawa al'amarin. Itakuwa Noor rayuwarta takeyi hani'an tama mance da batun basamude. Tana cin abinda takeso tasha wadda takeso gefe kuma karatunta takeyi cikin kwanciyan hankali.

*******
Yau Na'ima matar Ya Shareef ta tashi da wani zazzabi mai zafi wadda yayi sanadiyyar admitting dinta a asibiti, bayan yan gwaje gwaje da akayi aka gano tana dauke da juna biyu kuma irin mai zuwa da laulayi sosai dinnan ne. Murna wurin Ya Shareef kamar me, nan da nan ya kira mommynsa da kannensa harda Noor ya shaida masu. Suma sunyi murnan matuqa kuma suka mata addu'ar samun lfy. Da yamma aka sallameta bayan ruwan da aka sa mata ya kare. Tunda suka koma gida sai wani nan nan yakeyi da ita kamar kwai, ko Kofi baya bari ta dauka. Itakuwa tasamu wuri sai zuba masa shagwaba take son ranta.

*******
Lokaci ba wiya haka kwanaki suka shide. Yau Monday kuma yau Aryan zai dawo kasa Nigeria bayan sun gama abinda yakaisu. Tare da kittens dinsa da aka sa awani basket ya taho. Yau jinsa yake cikin nishadi shima karan kansa baisan dalilin haka ba. Jirginsu zai tashi karfe 12:00 pm na rana kuma six hours flight ne. Dan haka ya gama shirinsa da wuri jiran lokaci kawai yake.

******
Su Noor sungama lectures da wuri dan haka karfe biyun rana suka dawo gida. Suna gama hutawa ummi tace wa Noor " Noor yau ke zaki shiga kitchen kuma special girki nakeso kimin, I'm craving something sweet kinji"? Da sauri Noor ta gyada kai, Sam batada kyuya musamman ma asata aiki danta riga ta saba agidan Mama. Bayan sallan asr suka shiga kitchen itada da Nana wadda surutu kawai take tayata dan ummi tace tabarta ita kadai tayi girkin. Dukkansu biyun basusan dalilin ummi nayin haka ba kuma ummi bata fada musu ba. Tayi hakanne dan tana kokarin daidaita tsakaninsu su biyun, Noor da Nana basuda masaniyar cewa yau Basamude zai dawo. Abinci mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login