Showing 3001 words to 6000 words out of 99210 words
nuna musu wai tuntubi tayi, badan daddy ya yarda ba kawai ya taimaka mata suka shiga falo mama kuma na murmushin mugunta.
Itako Noor tun jiya jikinta yayi tsami sai kuka take ta na addu'a Allah yakawo mata wadda zai fitar da ita. Tanajin muryan mama dana Daddy amma baza ta iya magana ba dansun daure mata hannu da bakinta, daga baya kuma saitaji tsit babu kowa awurin. Kuka takeyi Allah ya dauki ranta ta huta da wannan azaban datake sha a hannun kishiyar uwa...
*******
"Dear wlh ni ina ta mafarkin ya rahma kuka takeyi tana cewa zasu kashe mata 'ya" anty jamila kanwar ammin Noor tafada wa mijinta kamar zatayi kuka" jamila karki damu ai nasan nasir bazai bari komai ya sami Nuwaira ba. Amma ni na miki alkawari in har muka tafi kano gobe zamuje mu duba ta, idan mukaga bata samun kula to tabbas yazame mana dole mu dawo da ita nan abuja kinji? Kai kawai ta gyada masa amma zuciyarta sai faduwa yake kamar wani abune ke shirin faruwa da Noor dinta. Haka yaita tausarta har tadan kwantar da hankalinta.
******
Daddy kuwa hankalinsa a matuqar tashe yake dan har bayan la'asar babu Noor babu labarinta. Tunda ya fita sallah la'asar bai dawo ba sai kusan karfe biyar da rabi. Yana shigowa ya kalli BQ din ya tuna abinda yafaru da safe. Haka kawai yaji hankalinsa bai kwanta da abinda mama tafada masa ba. To kodai ya duba wurin yagani? Haka kuwa akayi ya nufi wurin amma saiyaga kofar akulle. Lekawa yayi ta window zuciyarsa tabuga dammmm. Noor? Abinda yafada kenan a matuqar razane. Da sauri ya koma wurin kofar ya daki kofar da kafarsa aikuwa ta bude dantaji bugu. Noor kwance take akasa numfashinta na fita sama sama ga jini abakinta da alama aman jini tayi danko ina ya baci da jini, ga kuma jikinta daya nuna zanen bulala rada rada. Da sauri yayo kanta ya dauketa kamar jaririya ya fito cikin gidan. Mama ce ta fito da sauri dan ita tama mance da zance Noor tun bayan abinda yafaru da safe. Daddy tagani da Noor ahannu yana kuka kamar ba namiji ba. Ko kallanta baiyi ba ya bude motarsa yasata sannan yayi horn maigadi ya bude masa da sauri dan shima yaga abinda yafaru. Gudu sosai yakeyi ikon Allah ne kawai yakaisu lfy. Wani private hospital ne babba yakaita aiko babu bata lokaci aka fara bata taimakon gaggawa. Sun dade akanta kafin ta dawo normal. Oxygen suka sa mata sabida numfashinta da baya fitowa da kyau dama kuma tanada asthma. Daddy sai kuka yakeyi yana Allah ya isa ga Wanda yayiwa 'yarsa haka. Anan ya wuni amma Noor bata farfado ba.
*****
Ummi da Nana suna zaune suna hira wayar ummi yayi kara alaman sako ne yashigo. Da sauri taduba kamar dama jiranshi takeyi, aikuwa ta fadada murmushinta sakon Abba ne ya shigo akan gobe insha Allah zai dawo. Nana tace"ummi lafiya kike murmushi" murmushin wasa tamata tace " mijina ne zai dawo gobe shiyasa nake murna". Dariya Nana tayi danta saba da ganin irin wannan tsantsar soyayyar da iyayenta ke nuna wa juna, itama addu'a takeyi Allah yabasu abokan zama haka musamman yayanta wadda yake buqatar wacce zata tarairayeshi tabasa kulawa na musamman. Haka ummi takira Salisu driver tayimai list din abubuwan dazata buqata dan girkin tarban mijinta sannan tace Nana tabishi, haka sukatafi itakuma tacigaba da wasu abubuwan.
******
Abba ya turowa Aryan sako akan zai dawo gobe, yasaba da abbansa sosai kusan shine abokinsa anan Nigeria sai kuma wani abokin aikinsa shareef tunda har yanzu yaki sakewa da mutanin Nigeria. Kakanninsa ma dake Adamawa Baffa da Dada suma yana matuqar sonsu dan basu da damuwa musamman Dada tanada wasa da dariya irinnan kakanni da jikoki, tun bai iya wasan ba har ya koya dan takan zo ta kwana biyu anan abuja. Wasu gidaje yake dubawa a laptop dinsa, gidajen kamar ba a Nigeria ba sunyi kyau sosai shi akabawa contract din komai daya shafi electricity da kuma technological abubuwan dake gidan dan haka yamaida hankalinsa, gidajen na wani babban mutum ne a masar. Wayarsa tayi kara ya duba yaga Anty Aisha ce ke kiranshi tsaki yayi kamar bazai amsa ba sai kuma ya amsa amma baice komai ba" hello" naji an fada. Cire wayar yayi daga kunninsa ya duba number da kyau kamar ba wacce ta jira bace ke magana" hello "ta kara fada " hello"shima ya fada....
Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼
REEMAH
PG 7_8
Aryan bai kara magana ba sanin wadda ta kira, wayan na kunninsa har kusa two minutes amma babu wadda yakara magana daga dayan bangaren, kitt yaji an kashe wayar tsaki yaja ya jefar da wayan yayi kwanciyarsa dan dama ya gaji da typing din dayakeyi a laptop din. Wato dai tunda ya blocking Lubna a wayarsa shine ta dau na mamanta danta dameshi? Lallai yarinyarnan yasakemata fuska sosai in ba haka ba to mazajen data kebi basa biya mata buqata yadda takeso ne dazata wani dami rayuwarsa? Haka dai yaita tunani yana jan guntun tsaki har bacci yadaukeshi.
******
Noor bata farka ba har daddy yaje yayi sallan isha'i. Su mama bama suyi gigin zuwa dubata ba dan sunsan halin daddy kuma sun tabbata yanzu yariga yasan waya mata wannan abun. Shima daddy ko takansu baibi ba. Ya bari ne Noor tasami lfy dan a yanzu ma baima san wani mataki zai dauka ba, mama ta dade tana tsiyanta tun ammi na raye amma dayaso ya dauki mataki sai ammi tahanashi, wani zazzafan hawaye ne suka sauko masa yai saurin sharewa. Noor ne tadan fara motsi hakan yasa yai saurin tashi ya matso kusa da ita, bude ido tayi tana kalle kalle kawai idanunta yasauka a kan Daddy wani irin kuka ne ya taso mata amma baya fita saboda oxygen din dake bakinta da sauri Daddy yakira Doctor suna shigowa suka samu takara sumewa dirshan Daddy yakara zama akasa yafashe da wani irin kuka kamar ba babban mutum ba, wlh idan wani abu yasami 'yarsa bazai taba yafewa mama ba yarasa dansa abaya amma yanzu bazai iya daukan rashin Nuwaira ba. Doctors sunyi iya kokarinsu amma Nuwaira bata farka ba. Doctor samir ya kalli Daddy yace Alhaji kasameni a office dina. Daady yatashi yabi bayansa kirjinsa na bugun uku uku meyasami Noor dinsa, office dinsa suka shiga yaja wani kujera yazauna agaban doctor din. Doctor ya kalli Daddy yace" Alhaji ita wannan yarinyar bata da yan uwa ne"? Ya yasauke nannauyar numfashi yace" batada uwa ni kadai takeda shi anan garin" " to babu wadda yake tare da ita agida ne ko kuwa Ku dai kuke zama" ya kara jefo masa tambayar " she's together with her step mum and her step sis" abinda doctor ke jiran yaji kenan dan shatin dukan dayagani a jikin Noor yasan dole akwai wadda sukayi sanadin haka" Alhaji bazan boye maka gsky ba amma 'yarka tana dab da fadawa cikin depression kuma inaganin ta dade tana ajiye abu azuciyarta wadda hakan shima yaso janyo mata hypertension amma munyi iya kokarinmu kuma zamu dorata akan magunguna ingantattu insha Allah zata samu sauki" kuka kawai Daddy yakeyi yanzu yana zama da 'yarsa shekara da shekaru amma har ta shiga wannan damuwar baisani ba? Anya ba haqqin Noor yadauka dayaki barin anty jamila ta dauke ta ba, yasani anty jamila zata kula da ita sosai fiye da yadda shi zaima kula da ita. Maganan doctor samir ne yadawo dashi" gsky Alhaji ina baka shawaran in Allah yabata lfy kakai ta wani wuri ko wurin yan uwanka wadda ka tabbata zata samu kulawa awurinsu akaita can kafin Allah yabata lfy" ko da doctor bai fada shi abinda ma ya yanke kenan inbahaka ba mama na dab da kashe masa 'yarsa. Godiya yayi wa doctor ya fita zuciyarsa na kuna.
Haka ya kwana cikin dacin rai yana salloli da addu'o'i. Noor ko bata kara motsawa ba har washe gari.
Su anty jamila da sassafe suka dau hanya zuwa kano dan hankalinta ko kadan yaki kwanciya jitake ajikinta wani abu yasami Noor dinta. Sun iso kano kusan karfe goma da rabi na safe. Taxi suka tare zuwa hotoro angwan su Noor itada mijinta Alhaji Saif. Suna isowa suka sallami taxi din suka knocking gate amma babban gashin hankali suka tarar inda maigadin yake fadamusu abinda yafaru. Anty jamila bata san lokacin data fashe da wani irin matsanacin kuka ba. Yanzu abinda yasami Noor dinta kenan shine Ya Nasir ko ya fada mata(haka take kiranshi). Mijinta ne ya tare taxi suka tafi asibitin da maigadin yafada musu. Suna isowa ta shige da gudu tabar mijinta yana sallaman mai taxi. Daddy tagani abakin kofa yana magana da wata nurse shima yana ganinta yayi mamaki sosai danko babu wadda yafada wa cewa suna nan "yanzu ya nasir ka kyauta kenan, 'yata tana asibiti shine ko ka kirani kafada min"? Anty jamila tafada tana kara rushewa da wani kukan. Hannunta yaka ma zuwa dakin da nuwaira ke kwance kamar ba itaba. Duk ta rame tayi fayau fuskarta kamar babu jini bakinta ya bushe. Matsowa kusa da gadon anty jamila tayi tana kuka ta kamo hannun Noor tana murzawa ahankali. Alhaji saif ne ya shigo ,shima saida jikinsa yayi sanyi ganin Noor kamar babu rai ajikinta. Haka kowa yazauna adakin jugum jugum babu mai magana acikinsu. Kusan 30 minutes anty jamila taga Noor tafara motsawa ahankali da sauri tamike takoma kusa da ita tana murmushin jin dadi. Har Noor tagama bude idanunta tasauke su tas akan anty jamila sannan tafara bin kowa adakin da ido hawaye na bin gefen fuskarta a lokacin doctor yashigo shima yaji dadin ganin tafarka. Dubata yayi sannan yacire oxygen din abakinta yanzu numfashinta ya normalising. Kowa a dakin murna yakeyi Noor tasamu lfy, kokarin tashi tayi anty jamila ta taimaka mata ta zauna tana sauke numfashi awahale. " Ku hada mata tea mai dan kauri abata amma karku bata solid food yanzu sai zuwa anjima" doctor yafada tare da ficewa daga dakin. Tea anty jamila tahada mata dama akwai kayan da Abba ya karya dashi adakin, ahankali takebata tea din tana kurba har ta gama sha sannnan ta taimaka mata tayi brush tawanke fuska. Abba ya matso kusa da ita ya tambayeta ya jiki kai kawai ta daga masa alaman amsawa ,shima uncle saif ya gashsheta.
Sai kusan la'asar doctor yakara dubata kuma Alhamdulillah jikinta yasami sauki sosai amma sai gobe zaiyi sallama. Abba yace" shalele insha Allah ana sallamanki bazaki koma wannan gidan ba zaki bi antyn ki abuja kinji"? Murna sosai wurin Noor Allah ya mashi addu'arta. Sosai suma su anty jamila sukayi murna at long last Abba ya yarda Noor takoma abuja tareda su. Haka sukayita hira gwanin sha'awa.
********
Yau Abba yadawo daga kasar turkey. Gaba dayansu suna dinning anacin lunch babu wadda ke magana sai karan plate da spoon. Bayan sungama cin abinci aka bude sabon shafin hira Abba ke tambayan Aryan " babana ya maganan ginin gidanka, nafa gama design din kuma nabaka amma baka kara min magana ba anfara gininne? "Ba'a fara ko ba amma ina sa ran insha Allah by next week zasufara, contractor din yamin magana cewa nayi masa uzuri akwai wani aikin dasukeyi ne amma by next week insha Allah" kai kawai Abba ya gyada shi so yake agama ginin Aryan din kafin ya bullo masa da maganan aure amma yanzu inya mai magana saiya fara kwana kwana yana waskewa har a share maganan. Nana tace" Abba next week matric dinmu fa kuma nasan zakace baka gari dan Allah ka attending kaji abbana" ta fada tana shagwabe fuska irinna autanni. "Karki damu shalele insha Allah zamuzo " Abba yafada yana shafa kanta. Shiko Aryan in akwai abinda bayaso shagwaba ne, abokinsa na wurin aiki shareef na yawan fada masa cewa inyayi aure kuma yasamu matar da ta iya shagwaba abin zai birgeshi, anya? Hmm Aryan kenan. Ummi na magana da Abba tace" kaga dear in aka gama ginin gidan Aryan kaga sai asami abban lubna da maganan auransu koko? Annurin fuskar Aryan da Abba ya dauke kamar an dauke wuta. Itafa ummi da gaske tayi maganan dan sam batasan halin lubna ba amma Abba da Aryan sunsani. "Dear dan Allah karki kara min wannan maganan ni naki jinin auren dangi" Abba yafada. Aryan mikewa yayi yabar musu falon dan miskilancinsa ma babu abinda zai iya cewa ummi. Nana ma tashi tayi tabarsu awurin dan harga Allah ta tsani lubna amakaranta daya suke kuma tana ganin dukkan abinda takeyi kama daga rungume rungumen mazan datakeyi ko agaban uban waye amma itama bata fada wa ummi ba amma fa tayi alkawarin inhar aka tilasta wa Ya Aryan auren yar iskannan saita fada musu dan har video take mata in tana wannan shashancin as evidence. Abba yakara warning ummi karta kara masa maganan auren Aryan da Lubna amma sam bai nuna mata dalilinsa nayin haka ba, shiko kadan bai ki jinin auren dangi ba kawai sabida lubna ne da uwarta. Kullum sai anty Aisha ta kira ummi tafada mata maganan banza cewa ita ke hana Abba ya aura wa lubna Aryan shiyasa itama ummi takeso taga ko zata iya shawo kan uban da dan ko Allah zaisa su yarda gashi kuma batayi nasaran hakan ba. Halin Abba da Aryan sai Allah saikace yan biyu.
******
Mama da maimoon ne afalo sunyi tsuru tsuru da ido tun jiya da daddy ya tafi asibiti da Noor bata kirashi ba kuma shima baikirata ba. To me zata cemasa? Ya jikin Noor bayan tasan ita tasata awannan halin? Itafa addu'a ma takeyi Allah yadauki ran Noor kowa ma yahuta(Allah yafiki mama). Maimoon ko wayarta ta dauka tacigaba da game dinta kamar babu abinda ya dameta da ciwon yar uwarta.( Allah ya kyauta)
********
Anty Aisha ce zaune a babban falon ta a sama tana waya da wata kawarta naji tana cewa" ki kyale yar banza wlh sai Aryan ya auri lubna, yo in naka bai rufa maka asiri ba na wajene zai rufe maka? Yanzu ki kalli lubna wani namiji ne bai san halinta a waje ba kuma na tabbata bazasu yarda su aureta ba.In ba rufa rufa nayi naga Aryan ya aureta ba haka zan zauna da yarinya gode gode agida? Hajiya shamsiyya wadda suke waya da ita tace" haba Aisha saikace anmiki asiri,yanzu wannan matar mai kama da aljanu ne tafi karfinki? Malam gangaran ai shine mafita kawai muje wurinsa amana maganin 'yan taurin kai" dariya anty Aisha taayi kamar wata tsohuwar mahaukaciya tace" shiyasa nake yinki shamsi kinsan duk wata hanyar da zamuyi mu magance matsala, gobe zanzo saimu tafi wurinsa" ahaka suka shirya yadda zasu tafi wurin boka (wa'iya zubillah. Allah ya wadar da iyaye mata masu wannan halin Allah kamana katangan karfe da mugu). Tana aje wayan lubna tashigo fuuu babu ko sallama tana wani kumbure kumbure " nifa mommy Allah na gaji da irin halin da Aryan ke nuna min haba. Saikace banida gata, duk mazajen danake nima shikadai naji inaso tsakani da Allah amma kuma ace yaita juyani kamar waina? Anty Aisha takamo hannunta tazaunar da ita " karki damu yar mommy munkusa yin maganin dan banzan ai badai ko kula ki bayayi ba toh daga gobe zai fara kula ki kinji? Murmushi lubna tayi tana jin dadin maganan mommyn nata. Hmmm ba gilin gilin ba tayi mai, wasa kukeyi da yaron malamai masu hadda fa.
Ya wasan zata kaya ne tsakanin su anty Aisha da Aryan? Shin zasuyi nasara? Zamuji agaba insha Allah.
Happy independence.🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬 Allah ya bamu zamu zaman lafiya a kasar mu Nigeria ka bawa shugabannin kasanmu ikon yin adalci atsakanin mu.
Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼
REEMAH
PG 9_10
Washe gari aka bawa Noor sallama ko gida Daddy yaki barinta ta tafi. Daga asibitin Daddy yasa driver dinsa yakaisu anty jamila abuja tunda ta jirgi sukazo to yanzu kuma da Noor zasu koma, gashi itakuma batada passport. Tayi kuka sosai saboda zata rabu da daddynta sanadiyyar su mama. Anty jamila nata rarrashinta har suka shige mota. Ahanya ma taki cin wani abu sai ajiyar zuciya takeyi alaman tasha kuka. Sun iso garin Abuja misalin karfe 12:00pm, straight gidan uncle saif suka tafi. Yaran anty jamila hanan da hanifa wadda suke sa'a da Noor sunyi murna sosai ganin abokiyarsu kuma 'yar uwarsu. Itama Noor dintayi murna atleast yanzu zata huta ta sake. Cikin dakinsu su hanifa suka kaita sunata janta da hira, anty jamila ce ta shigo hannunta rike da tray din abinci. "Noor taso kici abinci kisha maganinki na rana" anty jamila ta fada tana ajiye trayn agefen gado. Noor turo dan karamin bakinta gaba tayi,itafa harga Allah batasan magani. Dariya su hanifa suke mata itakuma sai shagwaba take zubawa anty jamila(hmm su Noor abin nema yasamu) wacce keta lallabinta taci abinci, abakinta ma take bata har tagama cin abincin, sabon drama akayi kafin ta yarda ta shaa magani. Bayan tasha anty jamila tasa Noor taje tayi wanka hanan kuma ta fiddo mata da wata doguwar riga mai kyau blue colour yasha adon white stones. Fitowa tayi da towel daidai kugunta tana tsane dogon sumanta. Su hanan da hanifa baki galala suke kallon Noor, gsky Allah yayiwa Noor baiwar diri kaiii. Itako bama ta kula da kallon dasu hanan suke mata ba. Zama tayi ta shafa mai ta dan murje fuskarta da powder ta sha fa lipstick, asananne hanifa tayi magana"wlh Noor duk mijinda yasameki ba karamin sa'a ya kwasa ba, kalli bombom dinki saikace kinsa tintin wann.." Shiru tayi sakamakon bige bakinta da hanan tayi" kincika surutu kamar wani tsohon radio, fadi ba'a tambaya ba" itako hanifa sai aika mata da harara takeyi tana rike da labban bakinta, Noor sai dariya takemusu, fadansu na birgeta baya wuce two minutes sun shirya. Ahaka suka cigaba da argument dinsu itako Noor sai kallon drama take tana dariya.
******
Daddy bai koma gida ba saida yagama yanke hukuncin dazai dauka akansu mama. Yasan weakness dinta kenan 'yarta kwaya daya