Showing 42001 words to 45000 words out of 99210 words
ambaci abortion, moon ta zubar masa da gudan jininsa? Yanzu kiyayyar datake mai har ya kai wannan stage din da harta gwammace ta cutar da jininsa, lallai ya kai maqura da lamarin moon da mahaifiyarta kuma wannan karon bazai barta ba, jiki ba kwari ya fito daga office din doctor aliyu bayan ya gama basa baki, tabbas in wani zai tsare shi yanzu ya tambayesa wani abu, ba makawa kuka kawai zai fashe dashi, ayadda yake matuqar qaunar yara shine har Allah yabashi matarsa ta zubar mai? Maganan zuci kawai yakeyi harya karaso dakin da aka kai moon. Shiga yayi ya samu tana bacci bayan angama mata duk abinda ya kamata. Zama yayi akan kujerar dake facing dinta ha kura mata ido kamar yan nazartar wani abu, can kuma ya mike tsaye ya fice faga dakin da sauri, be tsaya ko ina ba sai wurin motarsa, a 360 yabar harabar asibitin inda kowa ke basa hanya kar mai afkuwa ta afku.
Abakin gate din gidansu ya faka motar yafito da sauri, ko buga gate din beyi ba kawai ya bugo kofar yashiga, afalo ya tadda mamansa da babansa zaune suna hira, ganin yadda ya shigo musu babu ko sallama yasasu mikewa da sauri suna tambayarsa lfy, zama yayi dirshan akasa ya fashe musu da kuka wiwiii kamar karamin yaro, hakan ba karamin tada musu hankali yayi ba, mamansa tace" mahmud menene lfy, kayi magana mana" still bedena kuka ba, cikin kuka yace " ta cuceni ta cuceni wlh, umma tacuceni gudan jinina ta zubar tsabar tsanar datakemin, meya mata dazata kashe shi yiii yiiii" yakuma bare baki yana kuka harda majina. Kujera Alhaji Ja'afar yanema yazauna yana yana share zufan fuskarsa. Umma tama rasa mezata ce, yanzu haka danta ke haquri da wannan yarinyar dukda irin halayen datake nuna mishi gashi yau tayi me kankat. Haka zmsukayita rarrashinsa suna basa baki akan karya yanke hukunci cikin zafi yabari inta farka sai aji meyafaru dayasa tayi hakan.
*******
Tun 5:00pm ta dora abincin yamma dukda itakadai zataci amma still bai hanata yinsa da wuri ba. Wayanta ne yayi kara ta daga taga ummi ce ke kira, dagawa tayi bayan sun gaisa ummi tace" 'yata naji Nana na cewa next week zaku koma school, hope dai kim fada wa Aryan ya yarda ko, in bai yarda ba kifadamin ni zan mai magana yanzu" kamar bazata ce komai ba saikuma tace" ummi namasa magana yace wai ba yanzu zan koma ba sai next month" tafadi hakanne tunda ummi tace zatayi masa magana atleast yanzu basai ta hadu dashi tayi masa magana ba, ji tayi ummi tace" karki damu, nizanyi masa magana duk yadda mukayi zankira insanar dake" godiya tamata sannan ta katse kiran. Tana shirin fita a kitchen din ta hangosa yashigo falon inda yadan tsaya yana shakan daddadan kamshin da yanzu ya riga yakama ko ina na gidan harda wani lumshe idanunsa, tabe baki tayi tana yatsine fuska shikuma ya bude idanunsa tas yasauke akanta, da sauri yajanye ya haura sama kamar mara gsky, ita abunma dariya yabata, ashema yafita jin kunya toh ai shikenan, yanzu ne kuma ita zata sake shikuma tahanashi sakewa shida gidanshi, murmushi tayi takoma cikin kitchen din tafara shirya abincinta tanayi tana maming waka ahankali. Bayan ta gama ta haura sama tashiga wanka, bayan ta fito ta shirya cikin kanan kaya riga da wando, wandon daidai guiwarta ya tsaya ko ina yabaje da kyau awandon rigar kuma da kadan ya wuce cibiyarta. Feshe jikinta tayi da turarenta masu sanyin kamshi ta nado gashinta da ribbon kalar kayanta sannan tasa crocs tafito falo. Zama tayi akan cushion ta dora kafa daya kan daya tana danna wayarta. Shikuwa fitowa yayi cikin shirinsa na zuwa masallaci, sanye yaje cikin jallabiya white wadda yake transparent har ana iya hango jeans dinsa da singlet taciki sai baza kamshi yake ga kansa datasha taba kaji hadisi gashinnan sai sheki yakeyi ya kwanta luf ta kasan hulan. Be lura da ita ba saidayazo dab da cushion din datake zaune akai, itakuwa idanunta na kan waya dan haka batasan da mutum abayanta ba. Ganin shigar dake jikinta yasa yanayinsa fara sauyawa musamman daya kellara idanunsa akan nashanunta dasuka dan fito ta saman rigarta, kutt ya hadiye wani yawu da sauri ya juya ya fice daga falon har yana hada hanya, itakuwa karan kofar dataji ne yasata dagowa ta duba amma bataga kowa ba dan haka tamaida hankalinta kan abinda takeyi.Murmushi tayi dan tabbas tasan shine yafita haka kawai kofa bazai bude kansa ya kulle ba. Mikewa tayi ta nufi dinning area dancin abincinta tunda tana period ba sallah takeyi ba.
Shiko ogan har aka idar da isha a masallaci amma bai dawo ba. Shikam ya lura wannan yarinyar akwai al matsutsai akanta, so take ta rudar da shi tahanasa sukuni shida gidansa. Tunani ya shiga yi can kuma sai yayi murmushi ya shafe gefen fuskarsa. Mikewa yayi ya fito daga masallaci ya nufo gida. Koda ya shigo tariga ta shiga daki dan haka ya wuce dakinsa ya watsa ruwa. Minti kadan ya fito da system dinsa ahannu dayan hannun kuma wayarsa ne akunne da alama waya yake. Dagashi sai guntun wando daidai guiwarsa sai singlet ahankali yake saukowa daga staircase cikin takunsa mai cike da aji. Zama yayi akan carpet kamar yadda ya saba yafara aikinsa. Noor naji lokacin daya fito, itakuma harga Allah yau kallo takesonyi a falo, falonma falon kasa dan haka itama tafito cikin kayan baccinta gown pink colour da kadan ya wuce cinyarta, gashinta ta sake ya zubo ya rufe har kirjinta, bedroom slippers dinta ta sanya ta fito sai baza kamshi take, tun bude kofar datayi ya ankarar dashi zuwanta, yi tayi kamar batagansa ba ta wuce ta kunna tv, sosai hakan datayi yabashi haushi dan yana buqatar concentration kan abinda yakeyi, tana zama ya mike yaje ya kashe tv batare daya kalli inda take ba, da mamaki take kallonsa,lallai ma so yake su kwasa da daddarennan da alama. Mikewa takarayi ta tafi zata kunna tv bayan ya zauna, dan tsaban mugunta datazo wucewa ta gabansa yasamata kafa saijinta kake timm akasa. Yar kara tayi tareda kama guiwarta daya bugu akasa, kallonsa tayi shikuma hankalinsa kan system dinsa yake kamar babu abinda yayi, tana hawaye ta mike tadan tafi nesa dashi yadda koya mike bazai iya kamota ba tace" mugu kawai, ban yafe ba Allah ya is.." bata karasa ba dan ganinsa datayi ya mike ya nufota gadan gadan, aiko a saba'in ta juya da gudu tayi hanyar kitchen. Shi abunma dariya yabasa dan haka ya murmusa ya koma ya zauna. Tana shiga kitchen tarufe kofar bamm tana haki kamar sunyi gasan gudu da damisa. Fridge ta bude ta fidda ruwa ta kafa abaki tashanye tana maida numfashi. Lallaima an hadata da mugun mutum, kenan dan yana aiki bazai bari mutum yayi kallo ba saikace wurinne kadai zai iya zama yayi, nikuwa nace toke falonne kadai akwai tv? Zama tayi akan daya daga cikin kujerun dake island din tana jira yakoma dakinsa karta fita tahadu dashi kilama jiranta yakeyi akofar kitchen din( kujifa saikace beda aikin yi😂). Har kusan thirty minutes ta kwashe a kitchen din daga taci wannan sai taci wancan duk dai kar bacci ya dauketa awurin, dataga ta gaji da zama kawai ta mike tayi hanyar fita, daidai shikuma zai shigo hada coffee dinsa yama mance wai da mutum aciki, tana bude kofa taji goshinta yayi karo da faffadar kirjinshi, komawa tayi da baya tana susa goshin, shikuwa mutuwar tsaye yayi kallon irin kayan dake jikinta dan dazu gashinta ya rufeshi, har ta dena jin zafin goshinta bai daina kallonta ba, musamman abin dake tsole masa ido, dagowa tayi ta kalleshi taga abinda yake kallo, data lura idanunsa kan kirjinta yake tayi saurin jan gashinta ta rufeshi, bankadeta yayi ya karasa shigowa kitchen din, dan tsayuwa tayi awurin kafin tajuya zata tafi taji yace" ke zonan" kamar bazata zo ba saikuma tajuyo sidib sidib tana zuwa inda yake tsaye, har ta karaso ko kallonta beyi ba yace" hadomun coffee kikawo mun afalo yanzunnan" yana gama fadin haka ya juya ya fita. Takaici ne ya kama Noor ta maimaita abinda ya fada yadda yafada tana wani tabe baki, kofi tadauko da dan tray dinsa da spoon tafara hadawa, kamar da gaske har zata sa sugar sai tayi wani tunani, table spoon tadauko ta duddula masa sugar dayawa wadda ya zarce misali. Ahankali tafito ta aje masa agabansa tayi saurin hayewa sama. Shikuwa bawan Allah ba tare da tunanin komai ba ya dau cup ya nufi bakinsa, wata uwar zakin dayaji ne yasashi sauke cup din da sauri yana yamutsa fuska. Yarinyar nan tagama rainasa kuma dole ya koya mata hankali, mikewa yayi tare da cup din ahannunsa ya nufi dakinta, yama zuwa kuwa yaji kofar abude kusa kai yayi ya shiga, itakuma tana shirin kwanciya taji shigowansa, kallonsa tayi taga cup ahannunsa da sauri tace" mekake mun adaki" ko kala bai ce mata ba ya tako har gefen gadonta ya tsaya tare da mika mata cup din yace" gashi shanye shi tas kibani cup" kallonsa tayi cikeda tsoro dan ta san batada gsky tace" ni banashan coffee" tsawa ya daka mata yace" will you take this and finish it up ryt now" tana hawaye haka ta karba cup din ta kafa abakinta tana kurba tana matsar kwalla, shikuwa dariya ne ke cinsa aciki amma ya matse, haka taita turawa har ya rage kadan kafin ya mika mata hannu yace tabashi cup din sannan yace" badai kinfadawa ummi nace bazaki tafi school sai next month ba, to shikenan kin jawa kanki sai next month din zaki koma,bakin tsiwan nan saina saita shi nonsense kawai" yana gama fadin haka ya juya ya fice. Kuka tasaka tana dukan pillow har ta gaji baccin wahala ya dauketa.
Shikuwa yana fita ya wuce kitchen yahadawa kansa wani coffee din yazauna yasha. Maganan sai next month Noor zata koma school kuma karya ya mata dan ummi ta fada masa kuma shi yace baida damuwa next week din zata koma dan dai kawai ya tsoratar da ita ne yasa ya fadi hakan kuma da alama hakansa ya cimma ruwa, inba haka yamata ba rainashi zatayi. Mikewa yayi ya kashe komai na fallon sannan yawuce daki, brush yayi da alwala sannan ya fito yayi nafila yabi lafiyar gado.
*******
Yausu Hanan ana gidan anty amarya matan ya shareef. Sosai suka sake da ita kamar sun dade da saninta, itama kuma na'ima dama akwai saukin kai dan haka sukaji dadin zama da ita, ya shareef kuwa ba kunya minti minti yake kiranta daga office itama kuma ta biye masa agabansu hanan suke wayansu. Hanifa ce ta kalli hanan tace" hmmm su ya shareef kenan, wazai hurga ni gidansu cat and rat muga me ake gwabzawa" dariya sukayi baki dayansu lokacin na'ima tafito dauke da tray na abinci mai rai da motsi an girka wa kannen miji. Sosai suka kwashi girkinsu ba kunya. Sai kusan maghrib suka koma gida bayan ya shareef yadawo daga aiki.
********
Mama ce ke jinyan moon bayan ta farka ta kirata ta fada mata halinda take ciki. Mahmud kuwa tun da yatafi bai dawo ba, mama sai faman zazzaga ruwan bala'i take wai matarsa na asibiti amma baizo ya dubata ba. Koda doctor aliyu ya shigo dubata yaga ai jikinma da sauki dan haka ya basu sallama yace sutafi. Gida mama ta tafi da ita tace bazata koma gidanta ba sai in shi mijinnata yazo dakansa tunda abunnasa rashin mutunci ne. Duk abinnan da mama ke fada sam moon bata ce da ita komai ba, wani irin guilty conscience ne ke kamata tun bayan abortion din. Batasan wani irin mataki mijinta zai dauka akanta ba, ga kuma fushin da daddy zaiyi idan yasan abinda suka aikata. Mama na lura da duk wani motsinta kuma taga damuwa kwance afuskarta dan haka tace" ke har wani damuwa kike wai kin kashe yaron ciki to sai me? Aiba mutum kika kashe ba tunda halittarsa bai gama haduwa ba, inma mutum kika kashe ai ba wani abu bane dan ni wlh ko rah..." saikuma tayi shiru, moon ko kallon mamaki take binta dashi, ai duk rashin imanin mutum bazai kashe dan adam kuma ace baiji komai aransa ba, kuma kamar mama taso cewa rah, metake nufi. Dama moon batasan abinda mama ta aikata ba dan haka da mama keta surutu tana zuwa kan "rah" sai tayi shiru. Hakadai moon ta karashe wunin ranan cikin kunci. To meyasa ma mahmud bai nemeta ba kodai shima ya kai maqura ne da ita, ita dai yanzu bazata ce ta tsanesa ba amma kuma batasonsa har yanzu.
*******
Da sassafe Noor ta farka tayi duk wani aikin dayakamata tayi tashige kitchen ta dauko cup da golden morn da madara sannan ta fito ta haye sama, daidai zata shiga dakinta taji alamar zai fito aiko da gudu ta shige ta kulle kofan da karfi harda sa key. Abunda yafaru jiya da daddare bazataso yakara maimaita kansa ba. Daa taso hanasa sakewa amma gashi shi yanzu yazame mata dodo, wani irin tsoronsa ne da bata taba jiba ya shige duk wani lungu da sako na jikinta tunda yamata wannan tsawar. Shikuwa yana fitowa yaji karar kofar data buga, ko kallon kofan beyi ba ya sauka yawuce wurin motarsa dan ya riga ya dan makara zuwa aiki gashi yanada meeting.
Karfe 12:00pm tana kwance afalo tana cin munch it taji bell na ringing alaman akwai mutum a kofa. Mikewa tayi ta nufi kofar, ta ramin dake kofar ta leka taga wasu mata biyu dukkansu kuma bakon fuska ne dan batasansu ba. Budewa tayi ahankali kawai taji an bankado kofar anshigo. Anty Aisha ce da Lubna, wani irin kallo Anty Aisha ta watsa wa Noor har saida gabanta yafadi, itakuwa Lubna ta matuqar tsorata da kyawu irinna Noor, bata taba tsammanin irin kyawun matar Aryan kenan ba, tabbas tanada kyau amma Noor ta dameta ta shanye akowani bangare. Da ido Noor tabisu har suka isa tsakiyan falon suna wani kallo tareda tabe baki. " sannun ku da zuwa" Noor tafada tare da tsugunawa dan kana ganin idon anty aisha zakasan ta manyanta itakuma lubna ko ba'a fada ba tasan ta girme mata. Kamar bazasu amsa ba sukace klau, mikewa tayi ta nufi hanyar kitchen dan sama musu abin motsa baki taji anty aisha tace" shi mijinnaki bayananne ko kuwa tsabar wulakanci ne bazaki kira mana shiba" juyowa Noor tayi ta kalli anty aisha dake binta da kazamin kallo, haka kawai taji matar bata kwanta mata ba dan haka tace "bayanan" tare da juyawa ta shige kitchen. Tsaki Lubna taja tace"toh mommy bayanan, itakuma wannan matartasa kinga sai wani makwarkwasa take yi dan taga tafi mu ko me" babu abinda anty Aisha tace tacigaba da kallon tsarin gidan, tabbas kam dan kyau gidannan yayi kyau amma hassada bazai barta ta fada ba. Can saiga Noor tafito hannunta dauke da snacks da drinks. Akan center table ta aje sannan tace" ga abin motsa baki, kuyi haquri abinci bai sauka koba" da sauri anty aisha ta cafke tace" au dama haka kike barin dana da yunwa kenan, ba dan bakin hali irinna uwarsa ba da Lubna itace daidai dashi ba wata tatsitsiyar yarinya ba" Noor bata iya rashin kunya ba amma yadda anty aisha ke zubda girmanta agabanta dole ta hau ta take. Babu wadda zai zagi ummi ta kalleshi ta kyale dan haka tace" ai duk nufine na Allah shiyasa kikaga ita Lubnan duk da bansan ko wacece ita din ba, bata aureshi ba" da mamaki ko wannensu ke kallonta, ehh lallai itama din ba kanwar lasa bace ashe. Haka sukayita jifanta da magana tana mayarmusu har suka harzuka suka fice agidan suna fadin haduwarsu ta gaba bazaiyi kyau ba. In ran Noor yayi dubu to ya baci, akanme zasu shigo suna zaginta harda iyayenta, inko haka halinsu yake toh tana daidai da wandonsu.
Sai yamma lilis yadawo gida, itakuwa tana daki lokacin daya dawo kuma tasa key kofa dan yanzu taka tsantsan takeyi da shi kar wannan kafcecen hannunnasa yakara ziyartan fuskarta. Shima kuma bai kulata ba ya shiga yayi wankansa ya fito cikin kananan kaya ya fice daga gidan.
COMMENT AND SHARE
10/23/23, 8:06 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼
REEMAH
PG 35_ 36
Kwanan moon uku kenan agidan mama amma mahmud bai taba daga waya ya kirata ko kuma yazo duba jikinta ba, yanzu kam abun ya fara damunta matuqa ga kuma guilt dake cinta amma mama ko damunta beyiba. Yanzu ma zaune take akan gadon mama tana cin apple mama ta shigo, damuwan datagani afuskar moon dinee yasata zama kusada ita tace" moon anya ba son yaron nan kike ba, naga kwanan biyu sai wani tunani kikeyi, toh bari kiji tunda wuri inkinsan kunya zakibani akan plan dinnan damuka hada garama tunda wuri ki tattara ki koma gidanki" kallon mama tayi tace" wlh mama ba haka bane, amma aiko arzikin dubiya naci ko, yaza'ayi ace nayi ciwo kwana nawa kuma yasan an roga an sallamemu a asibiti shine ko kirana baiyi ba awaya, kinsan ko dole na damu" harara nama ta watsa mata tayi tsaki ta mike tafice tanata mita. Kallonta moon tayi kawai ta girgiza kai tacigaba da gatsan apple dinta.
Shikuwa mahmud kwata kwata ma yanzu moon bata gabansa, aikinsa kawai yasa agaba gefe kuma ga wata santaleliyar budurwar dayasamu har sun fara soyayyarsu kuma shi da niyyar aure yake soyayya da ita. So dayawa yana daga waya danya kirata yaji ya jikinta amma sai wani zuciyar ta hanashi yin hakan, aishi akayiwa laifi dan haka ita yakamata ta nemeshi, kuma danma sununa masa cewa sun isa itada mahaifiyarta ai kamata yayi ta dawo gida amma sai ta wuce can gidansu dan haka inta gaji saita dawo the doors of tge house is always opened for her.
*******
Yau sunday kuma gobe Noor zata koma school dan ummi tayi waya da ita kuma ta fada mata cewa ya yarda. Tun wannan incident din coffee dinnan bata kara haduwa dashi ba sai in coincidentally ne kuma shima din boyewa takeyi saiya