Showing 99001 words to 99210 words out of 99210 words

Chapter 34 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8202

Ammi, su Ammi dasu Daddy da sunaina suma sun zo. Tarone wadda ya kunshi farin ciki, kowa na cikin nishadi, Abba ya kalli kan ahalinsa ya yi murmuahi ya furta Alhamdulillah. Ga Noor da Nana sun zama cikakkun lawyers masu zaman kansu, ga kuma su Hanan sun zama cikakkun business women sunki bin field dinsu bayan makaranta sunce saidai business kawai. Ansa auren su nan da watanni biyu inda hanan zata aure partner dinta in business, Hanifa kuma wani babban matashin computer software developer zata aura. Aryan na rikeda hannun Noor suna zaubawa junansu kalaman soyayya basu ma maida hankalinsu kan mutanin dake falon ba, kawai jin muryar Dada sukayi tana fadin" Muhammadu Aryan mijin Nuwairatu, ahaka zaka kare rayuwarka ai kullum kana manne da yarinya kazama MIJIN TACE" dariya kowa ya fashe dashi afalon dan ba karamin dariya maganarta ya basu ba.


Tammat bi hamdulillah.

Yau nakawo karshen MIJIN TACE. Nagode da kulawarku gareni. Godiya ta musamman zuwaga Ashanty, Mom sani, Amna El yaqoub, sune suka inspiring dina na fara rubutu, kuma Alhamdulillah ina samun goyon baya daga wurinsu. Bazan mance dakuba my fans, kun taka muhimmiyar rawa awannan tafiyar, da babu ku da wannan littafin bazai taba samun cigaba. Ina muku fatan alkhairi akoda yaushe.

Taku har kullum

REEMAH✍️

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login