Showing 51001 words to 54000 words out of 99210 words
da sauri yajuya yafice daga dakin. Kuka noor ta saka tana gife bakinta saikace madaci aka samata abakin,pillows din dake kan gadon tafara jifa dasu tana kara sautin kukanta tana fadin" mugu kawai wlh ban yafe ba, macuci dama shiyasa ka yarda da sauri da ummi tace mu dawo gida, toh wlh barikaji saina gudu gobe da sassafennan nabar gidan zan koma gidan ummina yiii yiiiiii, kawai kawani zo kana lashewa mutum baki saikace wani mage, ni inama lily ne ya lashe min baki dana yarda bisakan kai, wayyo daddyna yiii"kara sautin magananta takeyi saboda yajita da kyau karya dauka tsoronsa takeji, shikuwa tunda yafita yana tsaye abakin dakinta duk abinda take fada akunninsa, dariya tabashi sosai wai dama lily ne ya lashe mata baki bashiba, wato dai ta gwammace kyanwa ya lashe mata baki amma mijinta na sunnah baida dama. Yana dariya ya shige dakinsa sannan yafara rage kayan jikinsa yashige toilet.
Tsabar kuka da majina har kanta yafara ciwo( nikuwa nace kaii noor rakinki yayi yawa, kiss nefa kawai ba dayan abunba hmm), rungume da pillow haka tayi bacci tana ajiyar zuciya. Bayan ya fito daga wanka ya shirya cikin kayan baccinsa riga da wando maroon colour sai baza kamshi yakeyi,zama yayi akan sofa din dakinsa yafara tunani, yanzu daya fada soyayyar yarinyar nan yazaiyi ya shawo kanta, da alama akwai tsoronsa atattare da ita shikuma gsky yafison matarsa ta sake dashi, to yanzu wazai kira yabashi shawara akan yadda zai shawo kanta, idan ya kira muhsin zolayarsa zaiyi, shareef kuma shegen mayen mace bazai dauka masa waya ba saidai in haduwa sukayi a office amma muddin yana gidane forget kawai. Ajiyar zuciya ya aje ya kwanta ya dau pillow dinsa ya rungume akirjinsa yana tunanin yadda yaji taushin lips dinta dazu, baiso ta tashi ba because he enjoyed that moment, murmushi yasaki har baisan lokacin da bacci ya daukeshi ba. Kiran sallan farko akunninshi, mikewa yayi bayan yayi addu'ar tashi daga bacci sannan ya fada toilet yayi alwala yafito, jallabiyarsa brown colour ya sanya sannan ya fita, kallon kofar dakinta yayi amma yaga duhu alaman bata tashi ba, matsowa yayi ya knocking mata kofar sannan ya juya ya fice. Jin knocking yasata mikewa da sauri danta tsorata dama kuma mafarki takeyi wai gashi nan yana mata abinda yamata jiya, tsaki tayi tace" shikenan ya rushe min kwanciyar hankali na, yanzu kullum zannan kwana cikin fargaba mtscheew" ahankali ta sauko daga kan gadonta ta shige toilet, minti kadan ta fito ta shimfida sallaya ta sanya dogon hijab dinta har kasa sannan ta fara sallah. Bayan ta idar ta zauna yin adhkar da karatun Qur'an,tana idarwa ta mike akan sallayan ta koma bacci dama ba isarta yayi ba.
Koda yadawo daga masallaci bai shiga dakinta ba nasa yawuce sannan ya canza zuwa kayan excercise ya fito, wanfo ne 3qtr da rigarsa armless saikuma snickers masu kyau, saukowa yayi ya shiga dakin excercise din yafara aikinsa na daga manya manyan karafuna. Yadda yake dagawa cikeda kwarewa kamar baya jin nauyinta. Kusan hour biyu ya dauka yanayi sannan ya fito yana share zufa da dan karamin towel dinsa. Kitchen ya nufa dan shan ruwa, azaune yasameta tana shan tea and bread harma tagama shirin makaranta. Kamar batagansa ba amma sarai tasan da shigowarsa, fridge ya nufa ya bude ya dauko bottle water ya kafa bakinsa, saida yashanye tas sannan ya cire bakinsa, kallonta yakeyi tundaga sama har kasa, tunani ya shiga yi to ai motarta na gidan ummi wakenan zai kaita, murmushin gefen baki yayi ya juya zai fice, da sauri kamar an tsikareta tace" school" juyowa yayi tareda kallonta yace" what about it"? Turo baki tayi tasan sarai yasan metake nufi amma ya basar lallaima wannan mutumin. Dayaga batada niyyar magana yakuma juyawa zai fice tace" motata na gidan ummi" murmushi ya kuma yi kafin ya juyo yace" i don't give a damn about that" yana gama fadi haka ya juya yayi ficewarsa. Kanta ta aza bisa island din kitchen din tafara kukan takaici, dazu ta kira ummi akan motarta tace wai driver bayanan ya kai nana school kawai tacewa Aryan ya kaita, gashinan shikuma dan bantan uban da kai kamar faranti wai he doesn't give a damn. Ai shikenan badamuwa rananta nanan zuwa itama. Mikewa tayi tadau jakarta dake gefenta ta rataya ta kama hanyar fita, tana fita kuwa taga motarsa afake yana jiranta, kamar batagansa ba takama hanyar fita daga gate irin ita tayi fushinnan, mamaki ne yakamashi wato ita uwar zuciya ko, aiko zai koya mata lesson, fitowa yayi daga motar yace" karki kuskura ki fita daga gate dinnan" ko tsayawa batayi ba tacigaba da tafiya, aharzuke yabiyo bayanta yanazuwa ya sungumeta akafadarsa yayi hanyar gida da ita. Dukansa tafarayi tana yasauketa amma ko ajikinsa, yana shiga dakinta kan gadonta ya direta yana huci itama tana huci, mikewa tayi da sauri ta nufi hanyar kofa aiko cikin rashin sa'a ya cafko waist dinta ta baya yakara maidata kan gadon. Still bata daddara ba takara mikewa a tsawace yace" what's wrong with you? Are you nuts? Nizaki nunawa zuciya"? Yakarasa maganan yana huci, zama tayi abakin kofar tafashe da kuka harda shure shure, shi abunma dariya yabashi saikace wata karamar yarinya kodayake karamarce. Bin gefen ta yayi yafice daga dakin dan shima shiri zaiyi ya tafi office. Yana fita ta mike takoma cikin dakin ta zauna saman gadonta ta dafe kanta,wannan wani irin mutum ne wai, muguntarsa is on another level, ahaka akeso suyi zaman aure anya zaiyu kuwa? Gabadaya sai tafiya makarantar ma ya fice akanta.
Bayan ya gama shiri cikin suit dinsa white colour yasanya agogonsa kirar Rolex da takalminsa kirar company Versace black colour shima, sosai yayi kyau kansa tasha gyara, abinda yafaru tsakaninmu dazu ya dameshi, kuma inza'a duba ai laifinsa ne tunda shiyace mata he doesn't give a damn. Amma still shi mijinta ne baikamata ace tana bijirewa umurninsa ba, karasa shirinsa yayi yadau jakar system dinsa da key ya fito. Still yanajin sheshshekar kukanta amma babu yadda zaiyi haka yajuya ya fice. Koda yafito har ya shige motarsa saikuma yayi tunani Kodai yakoma yabata haquri ne ganin jiya shiya hanata zuwa school, yau ma kuma ace same thing ai bai dace ba. Girman kan Aryan yawuce duk inda mutum ke tunani, haka yashare shawarar da zuciyarsa ta basa ya figi motarsa yabar gidan. Noor tanajin lokacin daya fita takara fashewa da kuka.
******
"Daddy dan girman Allah ka roke shi karya min haka, wlh bazan jure zama da kishiya ba, kataimaka kabashi haquri wlh na tuba nabi Allah nabar Mama bazan sake ba na yarda zan haifa masa 'ya'ya bama d'a ba" Daddy dake zaune akan cushion yana kallonta da wani irin ido, kallon bakin ciki kallon takaici yake binta dashi bai taba tsammanin rashin imanin su har ya kai wannan stage dinba, yanzu badan labarin auren Mahmud yataso ba da haka wannan maganan zai yi shuru kenan, Mahmud kuwa duk tausayinta yakamashi, dama agidan Daddy ake wannan shari'ar, "Moon I am so disappointed in you wlh, dama ance in daya ya bakanta ma daya zai farantama, Allah yasa ba ke Kadai na Haifa ba kuma bake Kadai na aurar ba dan haka in Allah ya yarda nan nada jimawa ba Noor zata haifo min santalallun jikokina tunda ke kinmin buqulun samunsu daga wurinki, kuma ki sani ba zan taba rokon Mahmud yafasa wannan auren ba saboda ke San.." Mama ce ta katse masa maganar sa ta hanyar fadin" amma nasiru anji kunya wlh, yanzu meya kawo maganar wannan shegiyar bayan ana kokarin kashe wani wutan , toh bari kaji, ko wannan yaron yayiwa 'yata kishiya bazata taba kamo kafafun Moon ba kuma bari kagani sai Moon dina tafara aihuwa kafin ita yarinyar taka, aikin banza aikin wofi" murmushin takaici Daddy yayi, yanzu agaban surukinsa take fada masa wannan maganar bako kunya harda kiran yarsa shegiya hmm tayi nisa. Itako Moon sai sambatu takeyi tace" Mahmud dan girman Allah kayi min rai karka yanka min wannan hukuncin ka canza wani wlh na amince zan maka biyayya" sosai Mahmud yaji dadin maganarta amma awaje saiya nuna har yanzu fushi yakeyi da ita " Moon kinfi kowa sanin inason yara amma haka kika rufe idanunki kika biyewa son zuciya kika aikata babban laifi, toh idan na yafe miki shi Allah kuma fa" mama dan tsaban takaicin abinda Moon keyi saikace mara gata sai wani rarrafawa take daga kafar wannan zuwa kafar wannan tana rokonsu, mikewa tayi tabar wurin, Daddy ne ya kamo hannunta ya matso da ita kusa dashi yace" Moon" amsa masa tayi da na'am," kiyi haquri kinji, kibari mijinki yayi abinda yaga dama, kinga anriga ansa ranar auren sa, bazaiyi kyau yaje yace ya fasa ba saboda ke, dan haka kawai ki rungumi kaddara kibarwa Allah komai kinji"? Yayi maganar yana shafa kanta, ahankali ta gyada Kanta alamar ta yarda amma tace" Daddy kace masa dan Allah kada ya hadamu gida daya da ita, abinda ban gani ba banjiba bazai dameni ba balle haryakai ga sabani tsakaninmu" murmushi Mahmud yayi yace yayi alkawari bazai hadasu gida daya ba. Haka Daddy yayi musu sulhu sannan ya musu fada da nasiha. A daren ranar Moon tahada kayanta tabi mijinta. Mama kamar tayi hauka tsabar bakin ciki. Jawa Moon kunni tayi akan karta kara takowa zuwa gidanta ko kuma takirata awaya, ko ajikin Moon din, Daddy ba karamin dadi yaji ba yadda Moon tadawo kan hanya.
******
Ummi ce ke waya da Abba,suna magana ne akan Aryan da matarsa, " gsky hakan yayi, karki maida mata da motar yanzu, inta kiraki ta tambaye ki akan motar kice driver yayi tafiya kuma Nana bata iya tuki ba,shi Aryan din yarika kaita makarantar, da haka inasa ran Insha Allah zasu samu kusanci da juna " sunjima suna magana kafin Abba ya katse kiran, hankalinta bai kwanta ba har yanzu, dazu da rana tayi magana da Noor kuma taji muryarta ashake hakan ya nuna cewa kuka tayi amma bataso ta fada mata. Ita yanzu tama rasa yadda zatayi, a idon Aryan dai kamar tafara hango soyayyar Noor amma ita Noor Sam ba haka bane, saima wani tsoronsa da takeji kamar wani mala'ika. Still dai bazata yi kasa aguiwa ba, kuma alwawari ta daukar wa kanta cewa cikin wata guda zata daidaita tsakaninsu( ummi anya? bakisan cakwakiyan da akeyi agidan can bane hala).
*****
Hutu Ya Shareef ya daukar wa kansa saboda Na'ima dake fama da laulayi sosai, komai na gidan shike mata kuma ba komai take iya ci ba sai yan wasu abubuwan. Saukinsa shine da weekend Hanan da hanifa suna zuwa su taimaka mata. Sam baya gajiya da dawainiya da ita,saima wani soyayya dake kara habbaka a tsakaninsu. Allah ya raba lfy amaryar yayanmu.
Wannan hutun da shareef ya dauka ba karamin batawa Aryan rai yayi ba, awurinsa kawai yake sa ran samun shawara, gashi ko ya kirashi badagawa zaiyi ba, shikuma harga Allah bazaije gidansa ba karyaje yaganowa kansa abin takaici yahanashi bacci tunda shi ba samu zaiyi daga wurin matarsa ba. Halindaya barta aciki yake tunani, Allah Kadai yasani ma ko taci abinci. Gaba daya ranan ya kasa tabuka komai a office.
******
Karfe 5:30 ta farka daga bacci ko sallan asr batayiba. Sharp sharp ta mike ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta fito da alwalarta takabbara sallah. Cikin sallan taji shigowar motarsa. Bayan ta idar ta zauna rufka tagumi, ita tama gama yanke shawaran bazata tafi makaranta wannan satin ba, tasan ko ma dai menene weekend za'a dawo mata da motarta shikenan ta huta da wulakanci. Yunwa sosai takeji rabonta da cin abinci tun safe kuma tea da bread ne. Mikewa tayi ta nufi wardrobe dinta, wani dogon rigar roba ta dauka ta zura ajikinta sannan ta dau hularsa tasanya. Flat shoe ta Sanya tafito,data iso kitchen din tama rasa mezata dafa, deciding tayi ta girka jallof din taliya, cikin mintuna kadan ta gama hadaddiyar taliyarta wadda yaji kayan ciki da kayan lambu sai tashin kamshi yake, milkshake ta hada sannan ta fito zuwa dinning. Zamanta keda wuya taji anja kujerar dake kusa da ita anzauna, da farko harta razana amma ganin wanene yasata sakin jikinta tawani matse fuskarta babu alaman wasa. Tana tsoma fork zatafara ci taga shima ya zura nashi, dama gashi tana kule dashi tunda safe ai batasan lokacin data bare baki tafara kuka ba, da abinci abakinsa yama kasa hadewa kawai sakin bakin yayi galala yana kallon ta, yanzu saboda yaci mata abinci yasa take kuka? Noor fa ta dage sai kuka takeyi kamar zare ranta akeyi, gaba daya kukanta ya hargitsa masa tunani, wannan wani irin mutum ce, yanzu tsaban yaranta saboda anciwa mutum abinci sai yafara kuka saikace wani last born. Ahankali ya zare fork dinsa daga plate din ya dau ruwa ya shaa sannan ya mike dan yama rasa mezaice mata, gashi abincin yamasa dadi kamar karya daina ci amma gashi tamasa buqulu. Tana ganin ya mike yabar wurin ta dau plate dinta da milkshake tashige kitchen ta kulle kofa. Saida tagama ci tas ta wanke plate sannan ta fito lokacin har an fara kiran sallah maghrib, haurawa sama tayi ta shige dakinta dan gabatar da sallah.
Sai wuraren karfe goma yadawo hannunsa rike da ledoji guda biyu,kitchen ya shiga ya dau plate sannan ya bude ledan daya siyo burger da chicken wings ya juye acikin plate din, dayan ledan kuma chips ne da banana smoothies, yunwa yakeji sosai bana wasa ba dukda cin abincin dare bawani damunsa yayiba amma yunwar yau na daban ne Kodai kila saboda one spoon din daya ci daga plate din Noor ne ya kara masa yunwan tunda ba koshi yayi ba. Burger din ya dauka yakai bakinsa yadan gatsara kadan, da kyar ya iya cinye na bakinsa saiyaji komai ma ya fita aransa, fridge ya bude ya sa abincin sannan ya dau bottle wata kawai yasha ya fice daga kitchen din. Yanzu haka zasu cigaba da zama da ita, shida gidansa amma ace saidai ta girka abinda takeso kuma taci ita kadai, dayasa cokali zaici saita fashe masa da kuka, gsky da sake shi yanzu bazai iya da wannan horon ba tunda ya riga ya dandana dadin abincinta. Yazama dole yasan yadda zai gyara zamansu tunda yanzu yariga ya fada babu hanyar fitowa. Wanka yayi ya shirya cikin kayan baccinsa, system dinsa yadauka yahaye saman gadonsa, tunani yafara yi mema zai fara searching, google ya shiga ya rubuta" how to make a girl fall for you" ahankali yafara karanta bayanan da aka fitar, daya ance" take her on a date" na biyu" buy her Flowers " na uku " be nice to her" na hudu" say romantic words to her" duk wannan abubuwan daya karanta abu biyu kawai ya iya dauka zai jarraba, na daya shine taking her on a date na biyu kuma be kind to her. (Toh fa mutumin Ku ya fada dumu dumu😂😂). Ahaka yaita searching different ways to win a woman's heart, wasu ya dauka wasu yayi watsi dasu. Sai kusan karfe goma shaa biyu sannan bacci ya saceshi yabar laptop din akunne kan cinyarsa.
******
Yau Friday, su Anty Aisha keta shirye shirye mijinta wato baban lubna zai dawo daga port Harcourt. Su Lubna anyi karatun ta natsu dan babanta baisan duk wani shirme datakeyi ba, hasalima tsoronsa takeji danshi mutum ne mai zuciya da kuma addini bazai taba bari wani daga cikin 'ya'yansa su zama lalatattu ba amma kash Lubna tawuce tunaninsa saboda goyon bayan data samu daga wurin mahaifiyarta. Itama Anty Aisha ta natsu sai gyare gyare takeyi harda kunshi da gyaran jiki. Masu aiki kam suna kai da komowa wurin gyaran gidan dakuma girke girke. In mutum yaga Lubna zai rantse ma bata taba soyayya ba balle har takaida sanin da namiji tazama wani kamila tunma kafin babannata ya iso( shegiyan miya😒)
Yau aka daura auren Mahmud Ja'afar da amaryarsa Sofiyya Ahmad. Koda labarin ya iso kunnin Moon ba karamin kuka ta shaa ba, amma tayiwa kanta alqawari bazata taba nuna gazawarta ba. Ba karamin tausayi tabawa mutane ba dukda yawancinsu basusan dalilin karin auren ba, amma aganinsu ai yayi wuri saboda kwata kwata aurensu wata bakwai kenan, wasu kuma zagin Mahmud sukeyi wai ya cika ruwan ido shiyasa haryayi mata kishiya kafinta cika shekara daya agidansa. Set din akwati guda akayiwa Moon amatsayin danna kirji. Bayan sallan isha'i aka kai wa Mahmud amaryarsa gidansa dake angwansu Mama wato hotoro. Sai muce Allah ya basu zaman lfy.
******
Washe gari
Wasu zafafan restaurant ne masu kyau da tsari yake dubawa awaya, wani daga cikin su wadda shiyafi sauran kyau da kuma tsada ya zaba inda ya kira masu kula da wurin ya making reservation na couple table. Bayan ya gama duk wani abinda yakamata ya mike ya dau key din motarsa ya sauko babban falo. Shara takeyi tana yan kabe kabe hadi da bin karatun dake tashi cikin sipikun gidan. Tsayawa yayi yana kallonta kamar ya zo ta bayanta ya rungumeta saboda wani irin kaunarta dake yawo cikin zuciyarsa, komai nata tanayinshi ne cikin natsuwa da kamala, awani bangaren kuma za'a kirata da childish saboda abinda tayi masa jiya, yara kawai aka sani da rowa amma gashi itama ta nayi masa( to ba kai kace itadin tatsitsiyar yarinya bace, ta ai halinsu take nuna ma). Girgiza kai yayi ya saki murmushi sannan ya fice daga falon. Tanajin ya fita ta sauke ajiyar zuciya tacigaba da aikinta. Shiko yana fita ya wuce wani boutique, yana ciki zagayawa idanunsa suka sauka akan wani kyakkyawar lafaya black colour yasha adon black stones, sosai lafayar ta dau hankalinsa. Wata sales girl yasa ta packaging masa kayar sannan ya dau wani half cover shoe shima baki mai kyau sai walwali yake gwanin ban sha'awa, set din Jewelry ya siya silver colour masu tsadan gaske. Komai aka hada masa sannan yabiya bayan shima ya dau abubuwan dayake buqata.
Toh fa Aryan dinku yafara siyayyar women attire nan gaba kuma zaifara siyan wannan abinda yake jin kunyarsa wato pad.😂😂
Mu hadu gobe muji yadda date dinsu zai kaya,