Showing 6001 words to 9000 words out of 99210 words

Chapter 3 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8197

wato maimoon dan haka da ita zaiyi amfani ya koya mata hankali. Gidan wani abokin aikinsa alhaji ja'afar yatafi. Maigadin gidan ne ya bude masa gate bayan yayi horn, dama yariga yasanar da abokinnasa zuwansa dan haka ya samesa agida. Yasamu tarba mai kyau awurin uwargidan alhaji ja'afar. A babban falon sa na baki daddy yazauna bayan an sanar dashi ga alhaji nan zuwa. Wani dattijo ne mai kimanin shekaru 60 yashigo falon dauke da sallama abakinsa. Hannu suka sha da daddy irinna abokai dinnan. Uwar gidan alhaji ja'afar hajiya halima ta gabato masa da abin motsa baki ,tare sukaci shi da alhajin suna hira. Bayan sun gama ci Daddy yace" alhaji dama da wata magana nazo dukda ba sabuwar magana bace, magana ne wadda aka dade anayinta amma sanadiyyata aka watsar dashi. Wato alhaji dama abaya nayi tunanin Sam bazanyiwa yarana auren dole ba amma kuma a halin yanzu, yara sun zama abinda suka zama sakamakon wasu iyaye matan." Tuni alhaji ja'afar ya harbo jirgin daddy amma baice komai ba sai murmushin dake dauke afuskarsa. Daddy yacigaba da cewa" inhar bazaka ki ba alhaji kamar yadda kanema abaya yau gashi nima ina neman alfarma, ina nemawa 'yata maimunatu auren danka Mahmud " murmushin fuskar alhaji ne ya fadada abinda yadade yana so gashi yau Allah yabasa aruwan sanyi. " wlh ni na dade da yarda da wannan zancen, ai dama tuntuni da yanzu ma anyi auren domin ba karamin so naga Mahmud yakewa maimoon ba amma Alhamdulillah, saidai kuma wani hanzari ba gudu ba, ina fatan ita yarinyar zata yarda" "ai karka damu alhaji tunda ni nazo na nema aikasan babu wata matsala insha Allah" haka sukacigaba da tattaunawa akan yan uwan alhaji dazasu zo su nema auren Mahmud din officially. Sai dayayi sallan la'asar yabar gidan yanata sake saken yadda sai bullowasu mama da maganan auren.

Yana isa gida ko ta kansu baibi ba, itama mama ko ajikinta tunda dai bada Noor ya dawo ba. Maimoon ma sai murna takeyi tace " mama wlh bakiji wani irin farincikin daya ziyarci zuciyata ba da wannan shegiyar bata dawo ba, amma saidai matsalata daya yanzu wazai rika yin aiki da girki kingafa niba iyawa nayi ba" mama ta mata hararan wasa tace" karki damu nayiwa hafsu magana gobe zata kawomin masu aiki guda biyu" murna wurin maimoon kamar me(ayya yarinya kin kusa kuka). Daddy ne ya fito yawuce su ya tafi dakin Noor yana waya da ita tana fada masa inda ta ajiye takardun makarantarta wadda za'a yi amfani dasu wurin nema mata anan Abuja. Da harara su mama suka rakashi dashi harya bacewa ganinsu. Tsaki maimoon tayi tace"wlh mama duk da yarinyarnan tabar gidannan amma da alama bazata bar min babana ba, haba yanzu kuma metakeso Allah kadai yasani"mama bata ce da ita komai ba tana wani kunkuni wadda ita kadai tasan me take fada.

********
Su anty Aisha ne da kawarta Hajiya shamsi a gaban boka gangaran, anty Aisha ce tace" boka dama yaron dan uwana ne bayason yata itakuma tana sonsa gashi mahaifiyar yaron itama ta bada nata gudunmuwan wurin hana dan uwana yarda da auren yaren, nikuma harga Alla..." Bata karasa ba sanadiyyar tsawan da boka yamata" ke!!! Karki kara kiran min sunan wani Allah anan aida kinsan dashi bazaki zo nan ba"anty Aisha ta tsorata da sauri tace"kayi haquri boka"(hmmm). Boka yayi wasu incantations(addu'o'insu na bokaye) amma sam baiga wadda yakeso yagani ba hasalima saiwani haske yake gani amma dan ya riga kware acuta yayi kamar yaga komai yace" shikenan wannan aikin ai mai sauki ne amma yanzu ki ajje min dubu dari biyu wadda zan aiki aljani zuruu yayimin wata siyayya"(kunji wani karya, ashe aljanu ma nazuwa shopping mall😂😂). Babu wata wata anty Aisha ta zaro bandir din dubu daya guda biyu ta ajemasa agabansa. Hajiya shamsi tace" toh boka yaushe zamu karbi magungunan, ko yanzu aljani Zuruu zaije yayi siyayyan yakawo ka hada maganin"? Boka ya watsa mata wani kallo tayi saurin tsuke bakinta shikuma yace" zuwa sati mai zuwa zaku iya zuwa ku karbi maganin" godiya suka masa suka fito daga dan bukkan nasa wadda ke saman wani tsauni, ahankali suke gangarawa gashi sunci uban takalma na manyan matan Abuja, wani dan dutse ne anty Aisha ta taka suuuuuu kakeji tana tafiya kasa da sauri kamar ta hau lilon sliding. Dariya ne yaso kama hajiya shamsi amma ta dake tadan kara Sauri harta karaso wurin anty Aisha wacce tuni takai kasa sai rike kwankwaso take tana yatsina fuska alamun zafi. "Sannu ya akayi hakan yafaru" hajiya shamsi tafada tana taimakawa anty Aisha ta mike. Ahankali ta taka har wurin motansu sannan hajiya shamsi ta tada ita suka tafi.

*******
Yau Dada tayiwa su ummi zuwan bazata wadda hakan yabasu mamaki sosai, Dada dasai an kai ruwa rana take yarda tazo hutu anan Abuja yau saigata batare da katin gayyata ba. Sosai su ummi sukaji dadin zuwanta dan Dada akwai dadin zama amma fa akwai surutu kamar ba bafulatana ba duk abinda yazo bakinta ita babu ruwanta fada takeyi. Nana ce tashigo dakin ummi dake anan Dada ke zama duk lokacin data zo. Sanye take da wani gubyun wando dadai guiwarta sai riga armless da kadan ya rufe cibiyarta earpiece na kunninta tanajin waka, tunda ta shigo Dada ke watsa mata kallon rainin wayo dama bawani shiri sukeyi ba insuka hadu kamar cat and rat" aikin kenan, babu abinda kika iya sai shiri cikin kananun kaya saikace jikar mongo park , kin aje kafa kamar ta sauro babu wani auki kullum saicin taliyan tsutsa(indomie)" itako Nana ko ajikinta dan itama yan surutun basa kusane dasun kwasheta da Dada. Ummi kam babu abinda tafada dan inda sabo tasaba da wannan hayaniyar tsakanin Dada da Nana, intazo to fa kullum cikin raba fada take tsakaninsu kamar 'yan biyu. Aryan ne ya shigo sanye da suit dark blue yana rike da briefcase dinsa da alama yanzu ya dawo daga aiki. Nan da nan ko ina ya gauraye da daddadan kamshin turarensa. Fuskarnan murtuk babu alaman dariya. " oyoyo dan gidan azeezu, miji agidan Dada makiyanka sun buga dakai sun kasa" yariga ya saba dajin wannan kirarin dan haka murmushin gefen baki kawai yayi, zama yayi kusa da ita yayi magana cikin hausansa mai kama da larabci yace" wifey yau kece a bait dinmu" saikuma tayi narai narai da fuska kamar zatayi kuka tace" yanzu mijin wai ace ban isa nayiwa wannan yarinyar mai kama sa kwarangwal magana ba saita wani hauni da ihu saikace zatacire dan tsohon dodon kunnena" idonsa ya mayar kan Nana danya San da ita Dada keyi shigan dayagani ajikinta ne yasa ya gane abinda Dada ke nufi"hey, will you get out and change this useless outfit of yours " yadaka wa Nana tsawa wadda hakan yasata fita da gudu kamar zatayi kuka. Itakuma Dada tayi wani murmushin jindadi tace" yawwa ko kaifa mijin shiyasa nake kara sonka kamar na tare agidanka amma babu daman yin haka Kasan ance fas lo ( first love😂) yafi Shiga rai tokaga babu yadda zanyi nabar wannan tsohon" shi maganarta ma dariya yabasa kawai ya girgiza kai, sai lokacin ya lura da ummi dake zaune acan gefen gado dan tunda ya shigo idonsa ke kan Dada, gaida ita yayi sannan yamike ya wuce bedroom dinsa.

Yana Shiga yafara tube kayan jikinsa har yarage dagashi sai boxers sannan ya wuce bathroom yadan watsa ruwa. Yana fitowa ya dau wayarsa ya kira ummi akan Nana takawo masa abincinsa daki. Yana aje wayar ya cigaba da shafa mansa ya fesa turare,closet dinsa ya nufa inda yake ajiye kananun kayansa yabude yadau 3qtr da wani polo green yasanya. Yana fitowa daga closet din daidai Nana tayi masa knocking tashigo da abincin. Har zata fita yace"ke" juyowa tayi atsorace dan yadda ma yakirata bataji da kyau ba inkuma ta fita binta zaiyi ya kifa mata mari akan meyasa batazo ba kuma taji ya kirata, ohhh Ya Aryan sai Allah. " ki fita harkan Dada, whenever she complains to me about you again sorry to say, RIP" yamata alama da hannunsa yana yanka wuyarsa, atsorace tagirgiza kai tafice dagudu tabar part dinsa ma. Murmushin gefen baki yayi ya zauna yafara cin abincinsa.

*******
Noor ne dasu hanan zaune afalo suna shan fruits suna dan hira. Wani matashin saurayi kyakyyawa chocolate color yanada dan jiki kuma baida tsayi sosai yashigo da sallama abakinsa duk suka jiyo suka kalleshi, ido ya zaro waje ganin Noor. Da sauri yakaraso yazauna baima amsa gaisuwarsu hanan ba" Noor kece agidanmu yau? Noor batace komai ba sai murmushi kawai data keyi tace"Ya Shareef ina wuni" lfy lau yar lelen uncle nasir. Shareef ya amsa mata. Yayi mamakin ganinta a gidan gashi kuma duk ta rame fiye da yadda yasanta ada. Shareef shine babban yaron anty jamila wadda ke aiki a company din Aryan kuma abokinsa. Su hanan sukace" Ya shareef kashigo muna gaidaka amma ganin Noor saikayi kamar baka sanmu ba" Murmushi mai sauti yayi yace" to ba dole ba ai abin mamaki ne naga lelen uncle agidanmu kuma nasan ba hutu tazo yiba tun da har yanzu ana school." Itadai Noor bata kara cewa komai ba sai murmushinta mai bayyana tsananin kyawunta take. Anty jamila ce ta shigo falon tasamesu suna hira Ya shareef ya gaidata yace" mum yau kawai saiga Noor a Abuja" anty jamila tazauna kusa da hanan tace" ehh wlh dogon labarine dazu muka zo da ita nida dadyynku"bai kara tambayarta komai ba kawai suka dasa sabuwar shafin hiran harda noor aciki, itafa Noor talkative ce saidai intana wurin da bata samu sakewa ba shine za'a ganta tayi shiru. Har maghrib yayi sannan kowa ya mike dan gabatar da ita.

******
Bayan isha'i su Daddy suna zaune a falo shida Mama wadda yanzu tagama sake ranta akan babu wani matakin da Daddy zai dauka akansu saboda abinda sukayiwa Noor. Daddy kamar yasan abinda take tunani yace" hamida kiramin maimuna" kamar bazata motsa ba sai kuma tatashi tafara tafiya kamar wadda kwai ya fashewa aciki tanufi dakin maimoon. Akan gado tasameta tana waya da saurayinta salis." Ke maimoon daddynki yana kira" tsaki moon taja tacewa saurayinnata tana zuwa daddynsu yana kiranta. Mikewa tayi tabi bayan mama sukazo falo. Zama moon tayi akan cushion kusa da mama Daddy ya kallesu ya dauke kai. Ko mai zaice musu oho, abinda su mama suke tunani kenan. "Ke maimuna ya sunan wannan saurayinnaki"? Daddy ya tambayi maimoon take tafara murmushi dan once in a blue moon daddy ke tambayarta maganan samarinta" daddy salis" gyada kai daddy yayi yakara tambayarta"kuna tare har yanzu ko kuwa"? Da sauri mama ta tari numfashinsa tace"ai har gobe suna tare soyayya kuma sai abinda yakaru yanzu ma dashi take waya adaki" shiko daddy kamar abinda yakeso yaji kenan yace" shikenan, daga yau kice masa karya kara kiranki, kice masa babanki yamiki miji" dammm haka zuciyoyin mata biyun ya buga" kan bantan uba, toh wlh nasiru baka isa ba, kayi kadan, yar tawa kwaya daya jal zakawa auren dole?itako moon kuka ta fashe dashi tana cewa bata yarda. Tsawa yadaka musu yace" karku yarda kumaidani sha sha sha, nasan abinda nakeyi sarai, ok wato yarki itace gwal, Noor kuma jaaka ko? Toh wlh bari kuji na fada muku nariga na gama maganar dazanyi kuma babu wanda ya isa yasa na canza maganata"mama ta mike tsaye tana buga kirji tace"ni hamidatu na isa nasa ka canza maganarka naka wasa ne , wlh dani kake zance nasi.." Bata karasa ba taji saukan lafiyayyun maruka guda biyu afuskarta, Daddy yace" badai kina takama da kinada yan uwa masu karba miku baki ba? to shikenan mu zuba mu gani, wlh thumma billahi idan kika yi gigin shiga hanya ta akan maganan wannan auren saina mugun sabamiki" ya juya ya nufi hanyar waje saikuma ya juyo kamar baigama magana ba yace wa mama" kuma plaza dinki guda biyu dana gina miki na karbi abuna, shagunanki na saloon da bakery shima duk na kwace abuna" yana gama fadin haka yafice. Hannu mama tasa akai takurma wani uban ihu tace " shikenan makiyana sunyi nasara akaina, wayyo ummata wayyo abbana" itama maimoon kukan takeyi tana wa Noor Allah ya isa dan itace silan wannan hukuncin da daddy ya yanke akansu(daga baya kenan).

*******
Tunda anty Aisha ta iso gida take jinyar kwankwasonta dan yayi mugun tsami gashi wurin sai zugi yakemata. Mai aiki tasa ta danna mata wurin, tana tabawa ta kurma ihu tace" shegiya zaliha kasheni zakiyi, yar banza kawai fice min anan wawiya kawai" zalihan na fita daga dakin daidai Lubna na shigowa danjin ihun da mamanta tayi. Da sauri ta karaso gaban gadon tana tambayarta " mommy lfy, duka akamiki ne naga sai kama kwankwaso kike, ko ko dad ne yaja dannaji jiya da daddare sai ihu kikeyi kamar zaki rushe mana gida" (kai Allah wannan lubnan sam batasan me kalmar kunya ke nufi ba, wato taji ihun mamanta ne lokacinda harkar auratayya yashiga tsakaninsu da babanta shine fa take tambayarta ko shiyaja mata ciwon kwankwaso)anty Aisha takaiwa lubna bugu itakuma ta kauce " nonsense ba duk saboda ke bane, naje wurin boka garin saukowa daga tsauni na sulale kasa" dariya lubna ta sheke dashi harda kama ciki, itakuwa anty Aisha kota kanta batabiba, anya ba karaya tasamu a kwankwasonta ba kuwa? Bata kara cewa lubna komai ba, itakuwa tantiriyan wani abokin harkanta ne ya kirata a waya akan tafito gashi a gate. Mikewa tayi tafita bayan ta gama wayar ko kallon mamanta batayi ba.

******
Kusan karfe goma da rabi amma su Noor basuyi bacci ba sunata hira. Sanye take cikin night gown din hanan silk maroon colour. Iyakansa cinya ko ina ya cike rigar kamar zai yage. Kayan hanan ne kawai ke iya sizing Noor saboda tafi hanifa jiki kadan. Hanifa tace" Noor wani course kikacewa dad ya choosing miki" Noor tadanyi murmushi tace" law" ido hanifa tazaro waje tace law? Noor takalleta da alaman mamaki" toh menene aciki ai shima kamar ko wani course ne" hanan tace " to menene dalilinki na zaban law"? Mamaki ne ya kamasu ganin hawaye a idanun Noor da kyar tabude baki tace" saboda na tona asirin mama kan abinda tayiwa ammina da kanina suhail" Kallon kallo su hanifa sukayiwa juna, hanan ta juya ta kalli Noor tace" me mama tayiwa anty Rahma"? Murmushi kawai Noor tayi ta girgiza kai tace" karku damu with time zan fada muku".....

Tohhh sabuwar magana me Noor take boyewa gameda mama?? Zamuji cikakken labarin Noor zuwa gobe insha Allah.


Nagaji

Reemah✍️
10/5/23, 9:17 AM - Reemah: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 11_12

Wacece Noor?

Ainahin sunanta Nuwaira Nasir Mahmoud. Mahaifinta Alhaji Nasir Mahmoud mutum ne mai faran faran da jama'a. Kowa yasanshi da taimakon na kasa dashi bisa dan rufin asirin dayake dashi tunma kafin yazama babban dan kasuwa a yanzu. Matansa biyu Hajiya Hamida da kuma Hajiya Rahma. Hajiya Hamida itace uwar gidansa kuma yarinya daya Allah Ya bata wato Maimoon wacce suke kira da moon. Har aka dau wasu shekaru amma Allah baikara azurtasu da wani haihuwanba, bisa hakan yasa mahaifiyar Daddy ta tilasta mai kara aure. Hakan ba karamin girgiza mama yayiba. Hajiya Rahma tana aiki ne akarkashin daddy a lokacin yanada shagon saida zanuwa kuma itake ke zama ashagon. Ya dade yana sonta saikuma dama tazo masa lokacinda mahaifiyarsa tasashi kara aure. Mama tunba yauba tadade tana tsula rashin mutuncinta amma babu yadda Daddy ya iya da ita dan alokacin mahaifiyarsa ba karamin so take nuna mata ba.


Bayan anyi auren Daddy da Hajiya Rahma wacce suke kira da ammi, soyayyar inna wato mahaifiyar Daddy yakoma kan ammi, hakan ba karamin daci yayiwa mama ba. Acikin shekaran aurensu ammi Allah yayiwa inna rasuwa lokacin ammi nada karamin cikin Noor. Mutuwan ya tabata sosai dan wasu abubuwan da Mama ke mata agidan inna ce kawai ke iya taka mata birki.

Bayan wata shida Ammi ta haifo 'yarta mai tsananin kama da ita wacce taci sunan Inna wato Nuwairatu amma ana kiranta da Noor. Mama tayi bakinciki amma basosai ba kasancewar ba namiji ammi ta Haifa. Babu irin kiyayyar da mama bata nunawa noor tun Ammi na raye kuma haka ba karamin damun Ammi yakeyi ba amma kasancewarta mace mai haquri da kawaici yasa bata magana akai.

Wata rana daddy da su mama da Ammi sun fita sai aka bar Noor da Moon sai mai aikinsu. Mai aikin tana kitchen tana shara kawai saijin kukan Noor tayi. Fitowa tayi tana tambayar Noor meyafaru sai tace" Ya Moon ne tace wai bazata bani cakulet (chocolate) dinta ba" juyowa hadiza tayi ta kalli Moon wadda ko ajikinta abinda tayiwa 'yar uwarta ba tace" haba Moon ba yar uwarki bace, pls ki diba mata kinga tanata kuka" Moon ta kalli Noor tace" ni ba yar uwata bace mamana tace mun ba ita ta haifeta ba dan haka ni ba yar uwa ta bace" Babu yadda ta iya haka ta kyalesu ta wuce yacigaba da aikinta Inda Noor keta kuka amma ko ajikin Moon.


Bayan shekara goma amma Ammi bata kara aihuwa ba. Noor ta girma tayi wayo kyawunta sai kara fitowa yake na ainahin buzayen nijar dan Ammi yar nijar ce sunyi hijira itada iyayenta da yar uwarta Jamila.

Sosai Ammi keji da ita dan ita kadaice gatanta saidai in Daddy yana gari shima sosai yakejin Noor har cikin zuciyarsa. Noor akwai shiga zuciyar mutum kasancewarta kyakkaywa ga kuma biyayya babu inda ta rago Ammi a haquri, saidai Noor akwai surutu inta samu wuri.

Cikin yan kwanaki Ammi keta zazzabi atsatstsaye kuma bata nuna wa daddy cewa bata jin dadi ba. Laulayi takeyi irinna masu Sabon shigan ciki. Saida cikin Ammi yakai wata hudu aka gane ciki ne da ita. Sosai Daddy yayi murna, soyayyar duniya yadora wa ammi da abinda ke cikinta.

Mama tunda ta gano cewa ammi ciki ne da ita tafara Shiga da fice wurin ganin cikin yazuba amma abuna Allah haka ya raya cikin har yakawoshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login