Showing 18001 words to 21000 words out of 99210 words

Chapter 7 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8214

bayansu kawai yabi da kallo kuma idanunsa akan Noor duk da baiga fuskarta da kyau ba amma kayan jikinta shiyafi burgeshi, samun kansa yayi da sakin wani sassayan murmushi, da sauri kuma ya tamke fuska harda marin gefen fuskarsa.

Abinci kala kala aka kawo musu masu rai da motsi. Suna ci suna hira ana daukan videos. Su Nana kam sunma mance akwai wani awaje yana jiransu. Saida suka shafe kusan hour daya da rabi sannan wayan Nana yafara kara. "Inna lillalhi wa inna ilaihi raaji'uun" Nana tafada tana aza hannayenta akai. Kallonta sukayi baki dayansu sai sukaji yasmeen itama tasaka salati. Hannu na rawa Nana tadau wayar ta kara a kunninta" you don't seem to care about your life, RIP Nana " taji yafada, kafin tayi magana taji kit ya kashe wayar. Yasmeen ce ta mike tace " bestie nidai gsky su Noor zanbi wlh bazan iya da fadan Ya Aryan ba" mamaki kam ya gama cikasu Noor dan haryanzu basu fahimci mesuke nufi ba. Mikewa Nana tayi ta dau jakarta ta kamo hannun yasmeen dukda tana tirjewa tana tasaketa amma sam taki, har waje suka tafi suma su Noor suka bi bayansu bayan sun settling bill dinsu. Atsaye suka hangeshi yana danna wayarsa kamar babu ruwansa. Har suka iso baidago ya kallesu kuma yana sane. Sum sum Nana tabude kofar baya zata shiga taji yace" ke waye zaki maida driver dinki, are you nuts" da sauri tace sorry ta dawo ta bude kofar gaba ta shige tana sauke ajiyar zuciya.

Hanifa ce ta taba Noor tace"la Noor kinga abokinki" wani uwar harara ta watsa wa Hanifa tace"ke kika sani ai, mutum babu ko digon imani azuciyarsa ko ina yasamu ya bude baki yana tsawatawa mutum" karaf a kunnin Aryan, sai yanzu ya dago ya kalli wacce ke magana, idanunsu ne ya sarke dana juna, takowa yayi har inda take ya kama labban bakinnan mai tsiwa ya murdashi da karfi harsaida taji zafi. Buga hannunsa Noor tayi da karfi tana mai sakin kara. Hankadeta yayi har ta kusan faduwa ya watsa mata wani irin kallo sannan ya juya ya shige motarsa ya fice aguje.

"Allah ya isa nikam Nuwaira Allah ya hadani da mugun dayafi Mama, wlh bazan yafe ba mugu kawai" duk abinda take fada su Hanan sai dariya suke mata. Hannunta Hanan takama amma tana turjewa tana surutai. Har bakin mota suka jata suka turata aciki sannan Hanifa taja suka bar wurin. Har suka isa gida Noor bata dena magana ba inda bakinta har ya dan kumbura yayi jaa. Suna shigowa suka hadu da Anty jamila a falo, dariya ta fashe dashi tace" habibty dadin abincinne yasanya bakinki ya kumbura"? Noor kamar ta fashe sabida takaici, kukan shagwaba tafashe dashi tana bubbuga kafa a kasa tawuce daki. Su Hanan suka labartawa mamansu abinda yafaru tsakanin Noor da Aryan. Sosai Anty jamila tayi dariya tana mamakin fada irin wannan saikace masoya.


Short page


SHARE AND COMMENT


REEMAH✍️
10/8/23, 5:36 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH


PG 19_20


Yau Saturday babu Inda su Noor suka tafi duk suna gida. Hira akeyi afalo wayan Noor yafara kara, daddy ne ke kiranta,dagawa tayi ta kara akunne hadi da sallama ya amsa" shalele kina klau dai ko"? Ya tambayeta cike da kulawa, Alhamdulillah daddyna, nayi kewarka sosai Daddy " Noor tafada a shagwabance. Murmushi mai sauti Daddy yayi sannan yace" shalele dama kiranki nayi na sanar dake auren Moon ranar juma'ah mai zuwa insha Allah " zumbur Noor tamike kamar an tsikareta tace what!! Daddy Ya Moon zatayi aure shine ban sani ba harsaida aka kusa? Su anty jamila ma abun ya matuqar basu mamaki toh yaushe Noor din tazo da har ansa auren Moon amma batada labari. Daddy ne yace" I'm sorry banso na fada miki lokacin ba sabida jarabawar ki amma yanzu tunda kin gama shiyasa nace bari na Sanar dake" wani irin tsallen farin ciki Noor tayi harda rawanta na shaku shaku su Hanan sai dariya suke mata. Bayan sun gama wayan anty jamila tace" amma Ya Nasir be kyauta min ba kodayake ba auren ki bane be sanar dani ba balle ya dameni, su karata can ni bazan je ba" Noor tace" habibty ai ya wuce abinda sukamin Allah zai saka min, habibty dan Allah kar kice bazaki ba in kika fadi haka Daddy bazaiji dadi ba" su Hanan ma sukace gsky mommy gara mu tafi baki dayan mu bazamu yarda Noor ta tafi ita kadai ba karsu Mama su cutar mana da ita. Murmushin jin dadi Noor tayi tana kara godewa Allah daya bata yan uwa masu ji da ita. Da kyar suka samu Anty Jamila ta yarda akan Monday zasutafi ayi duk wani abun biki tare dasu.



"Dada dan girman Allah kifita harkata, wannan tsohuwar kodai mu kishiyoyi ne acan kafin a haifemu a'a, duk kinbi kin takurawa rayuwar mutum, ni tsohonki ma ba kishinki yakeyi ba tunda yabarki kika dade baki koma garinku ba" Nana tafada tana haki kamar wacce tayi gudu sanadiyyar cakul kulin da Dada ta yi mata kamar zata shide sabida dariya, Dada na dariya tace" ai in kikaga na koma Adamawa saina tabbatar wannan mijinnawa yayi aure, yaro saikace aljana ta aureshi, ko irin kuskus dinnan da akeyi da budurwa awaya ban taba ganin yayi ba" daidai Aryan na fitowa daga part dinsa yaji maganar da Dada keyi,azuciyarsa yace" toh yau arrow dinta kuma akaina yasauka kenan" bata rai yayi daidai zai shigo falon karma Dada tasamu fuskar yimasa wani maganan dazai bata masa rai. Dada naganinsa tace" kaga dan albarka yanzu kuwa nake maganarka tare da wannan mai siffan kajin makotan" tafada tana murguda wa Nana baki. Zama yayi amma baice dasu kala ba. Dada tayi surutunta harta gaji ko gizau beyiba. Nana ko dariya kamar ya kasheta yadda Aryan yayi kamar badashi take magana ba, Dada ta fusata tace"dama nasani ai kaima kamar ubannaka ne sai shegen miskilanci saiku karata can, inkaso ka dawwama babu aure, nidai nagodewa Allah inada dan tsoho na" sai yanzu ya dago ya kalleta sai kawai ya girgiza kai ya mike ya fice. Abinda yakara tunzura Dada kenan fada kuma yakoma kan Nana kamar itace ta mata laifin.


Yana fita ya shige daya daga cikin motocinsa Bugatti ya fice. Tuki yakeyi ahankali cikide kwarewa gwanin sha'awa haryakai site dinsa dake Asokoro danya kwana biyu bai tafi ba. Masha Allah, gida ya gama haduwa saura tarewar mai shi kawai. Tsarin gidan ba irinna Nigeria bane, gida ne babba hawa biyu mai kyau. Farfadan gidan wadda yasha interlocks red colour shima gwanin sha'awa, gawani car park wadda zai iya daukan motoci kusan shida har da kari ma in akwai. Katafaren gida ne wadda aka fanta shi white colour kota ina yayi kyau(sauran bayanin gidan sai ankawo lucky bride din Aryan). Shima sosai gidan yabashi sha'awa ya tabbata anan Abba ya karar da kwarewarsa wurin designing din gidan. Bayan ya gama zaga gidan wadda babu komai acikinsa sai tarin dattin kayan aiki ya wuce office dinsa. Aduk lokacin dayake free inhar babu abinda zaiyi toh ya gwammace ya tafi office dinsa Inda babu wadda zai damesa yayi zamansa wani lokacin har dare kafin ya koma gida.(jama'a anya Aryan mutum ne🤔)

******
Acan gidan Daddy kuwa yan uwa da abokan arziki an fara taruwa tun ana sati daya bikin Moon, Mama kam yanzu ta zage dantse se gyara Moon akeyi ciki da bai. Su Anty umaima sunyi kokarin ganar da Mama akan illan rashin iya girki da tsaftar gida ga 'ya mace,amma duk lokacin dasuka tunkareta da maganar sai tace" wlh 'yata bazata tafi gidan wani tayi masa bauta ba, Moon bazata dauki koda tsinke ne agidan wannan yaron ba wlh, ai ma sai rashin mutuncin yayi yawa aduke mu kuma ahanamu kuka" ahaka kowa taja bakinta tayi shiru dan saita musu rashin mutunci mara iyaka.

******
Kamar yadda su Noor suka shirya yau Monday su ka kama hanyar kano, motoci biyu sukayi, Inda na farkon su Noor neda su Hanan, na biyun kuma su Anty Jamila ne da uncle saif wadda zai raka matarsa sannan su dawo kafin ranar auren. Karfe daya daidai suka sauka agarin Kanon Dabo. Agidan Uncle saif dake kano suka sauka. Gidane babba mai kyau bungalow 4 bedroom. Suna isowa sukayi sallah suka ci abinci akan sai washe gari zasu tafi gidansu Noor. Anty Jamila dalilin Noor kadai yasa tazo bikinnan amma Sam bataso zuwa ba dan Mama ba matar da kawaici ya kamaceta bane. Suna zaune adakinsu suna hira Nana ta kira Noor, bayan sun gaisa takecewa" bestie ga ummi" Nana tafada tana mikawa ummi wayar," assalamu alaikum 'yata" ummi tafada cikin tsananin son yarinyar, wani irin farinciki ne ya ziyarci Noor jin ummi ta kirata 'yata" wslm ummina ina wuni"yadda suke waya sai mutum ya rantse sun dade da Sanin juna,Hajiya Dada na gefe tana Allah Allah abata waya tayi magana da kawallinta, suna gama wayan ummi tamikawa Dada, da Sauri ta karba ta kara akunninta tace" hello kawallina" murmushi Noor tayi tana mamakin wannan irin sonda sukemata kamar sun dade da saninta" kawalli ina wuni, ya jikin tsufa" Noor tafada tana dariya ciki ciki, in akwai abinda Dada bataso shine aceda ita tsohuwa,toh fa kowanene sai anyita dashi. Matse fuska tayi irin tayi fushinnan tace" kunji wannan kawallin yanzu saimu kunce kawancen, ke badan wannan barbada kumatun da bana sawa ba aina tabbata nafiki yarinta" dariya mai sauti Noor tayi tace "Allah ya huci zuciyarki hajiyata" bayan sungama gaisawa dasu ummin, Noor take fadawa Nana aisunzo biki a kano. In mutum yaga kawancen su Noor da Nana saika dauka ma 'yan uwa ne ba kawaye ba musamman yadda iyayen kowannensu keji da su. Su Hanan suma saida suka gaisa dasu ummi kafin suka katse kiran.



*******
Meeting sukeyi da clients dinsu dasuka zo daga America a babban meeting room din company dinsa, wani round table ne babba mai cin kusan mutane talatin. Sanye yake cikin wata dakakkiyar suit mai azaban kyau Maroon colour. Fuskarnan babu alaman wasa ko Kadan. Duk bayanin da ake korawa a meeting din ko uffam baiceba sai gyada kai kawai yakeyi. Saida aka gama sannan yayi dan magana ya concluding meeting din. Lunch aka serving amma shi ruwa kadai aka basa kunsan mutumin naku baicika damuwa da abincin waje ba. Komawa office dinsa yayi ya zauna yana dan latsa wayarsa yaji an bankado kofa anshigo. Wani irin tsinannan gown ne dogo mai tsagu har cinya, taci gashin doki yana lilo abayanta , bakinnan nata yasha hot red lipstick. Ko dago kai beyi ya kalleta ba dan ya riga yasan wace ta shigo,smirking kawai yayi azuciyarsa yace" ehh lallai dukan be isheta bane". Har gaban desk dinsa Lubna tatako tana wani girgiza karuwan nonuwanta ita adole tana abun birgewa. Kafa daya ta daga ta dora akan table din tana cin chewing gum kas kas, duk abinda takeyi ko kallanta Aryan beyi ba, abunda ya kara tunzurata kenan ta zagayo har inda kujerarsa yake ta kamo tie din wuyansa ta dago fuskarsa, wani kallon sama da kasa ya watsa mata ya kwace tie dinsa a hannunta ya bige hannunta daga kirjinshi, murmushi tayi tace" haba baby love bakai kace kana buqata ta ba yanzu kuma na zo kanaso ka wulakantani"takarashe maganar tana bubbuga kafa akasa alamar shagwaba, zeyi magana tayi saurin hade bakinsu wuri daya, mamaki, takaici, haushi,tsana duk suka hadu suka dabai baye shi, duk yadda yaso ya raba bakinsa daga bakinta amma ya kasa har shedan naso yayi tasiri akansa, astaghfirullah yafara furtawa wani irin karfi yazomasa ya tureta da karfi sai gata dabas akan duwawunta akasa. Wani irin wahalallen numfashi da sauri sauri yake saukewa yanaji kamar ya cire bakinsa daga fuskarsa saboda takaici. Mikewa lubna tayi tana gyara rigar jikinta tayi murmushi wadda ita kadai tasan ma'anarsa tace" dukan daka min ba mancewa nayi dashi ba, kuma yanzu na dauki fansata kajira kaga abinda zanyi wlh saika regretting taba jikina dakayi da sunan duka" tana gama fadin haka ta fice fuuu kamar balbela. Tana fita ta fashe da dariya harda rike ciki, wani ma'aikacin office din wadda cleaner ne ya fito daga wani corridor shima yana murmushi, wani waya ya mika mata ta kunna video din abinda suka gamayi da Aryan yanzu, dariya ta kuma fashewa dashi ta bude jakarta ta zaro rafar one thousand guda biyu ta mikawa mutumin. Har kasa ya tsunguna yana godiya tawuceshi tayi tafiyarta.


Aryan abun duniya ta isheshi,yama rasa mezeyi yasamu sukuni, ya akayi Lubna taci nasara akansa. Dukda Ac dake office din bai hana zufa karyo mai ba. Dayaga zaman office din zai gagareshi ya mike ya dau duk wasu abubuwansa yafice, kana ganinsa kaga wadda baya hayyacinsa. Abakin kofa yaci karo da shareef amma ko kallonsa beyiba.

Yana isa parking lounge ya figi motarsa da gudu mutane na kaucewa dan yadda sukaga driving dinsa sunsan ba klau ba. Tafiya kawai yakeyi ko traffic light baya kallo, ikon Allah ne kawai ya kaisa gida lfy, yana Shiga babu kowa afalo dan haka ya wuce daki. Kayansa ya tube dagashi sai guntun wando ya shige bathroom dinsa. Shower ya sakar wa kansa dan Kansa wani irin juyi yakemai bana wasa ba, inama zai iya ihu amma babu dama, hannunsa yasa ya bugi bango yana jujjuya kansa, tsanar Lubna da mahaifiyarta na kara ruruwa azuciyarsa da ruhinsa baki daya, ya kai kusan awa daya kafin ya fito, ko towel din jikinsa be kunce ba ya kwanta flat akan gadonsa yana kallon POP din dakin yana tunani. Kardai yarinyar nan plan ta hada masa tana kokarin tarnishing image dinsa, lallai kuwa dashi take zancen, zai nuna mata yafita hauka itada mahaifiyarta. Yana wannan tunanin aka kira sallan zuhr ya mike jiki ba kwari ya fice ya tafi masallaci.


Itakuwa Lubna editing video dintayi inda wurin kissing din kawai za'ana gani banda inda ya tureta sannan ta sake a shafinta na twitter. Minti goma yayi wuya video yafara yawo a ko ina, mutani sai zagin Aryan sukeyi wasu na cewa awaje yana wani jijji da kai abayan fage kuma ashe tantirin dan iska ne, wasu kuma suna cewa basu yarda ba sharri akemasa, itakuwa Lubna wani irin dadi taji harda nunawa Anty Aisha wacce tamafi Lubna murna.

Nana na cikin kallo awaryarta tana scrolling Twitter dinta kawai aka hasko mata wannan video din, batasan lokacin data saki ihu ba tana girgiza kai, da gudu ta sauko daga kan gadonta tanufi dakin Aryan, abakin kofar falo taci karo dashi yadawo daga masallaci, hannu na rawa ta mika masa wayar, wani irin dummmmm zuciyarsa tayi, kansa ya fara juyi, ashe zarginsa daidai ne, besan lokacin dayayi wurgi da wayan ba, Allah ya taimaka yafadi akan carpet babu abinda yasameshi. Su ummi da Dada suka fito daga daki dan sunji ihun Nana, ummi ce ke tambayar Nana meyafaru amma ina kuka kawai Nana keyi kamar anmata albishir da mutuwa, Dada ta kalli Aryan wadda ke tsaye kamar mutum mutumi idonsa sun kada sunyi ja jawur. " subhanallahi, karamin maigida lfy, meke damunku dan Allah kuyi magana mana, ke kazar makota meke faruwa, wani ya rasu ne" tadinga jero musu tambayar amma babu wadda ya tankata awurin. Ummi ce taji kamar karar abu awaya ta kalli kan carpet taga wayar Nana, zuwa tayi ta dauki wayan, abinda taganewa idonta ne yasa ta sakin wayan akasa wannan karon ya fadi akan tiles screen ya fashe. Kafafunta ne taji bazasu dauketaba kawai tanemi wuri tazauna akan carpet din tacire dan kwalin kanta tana fifita dashi, hawaye kuma na zarya daga idanunta,amma Lubna da anty Aisha sun cuceta dan bazata taba yarda da wannan ba, tasan halin kowanne acikin yaranta kuma tasan sarai sharri akawa Aryan.

Dada kam tayi magana harta godewa Allah kawai sai itama ta joining dinsu tafara kuka wiwi tanacewa" wlh in tsohona ne ya mutu Ku fadamin tun yanzu nima na bishi yiiiiii yiii" tana kuka tana fyace majina abun tausayi abun dariya. Shiko Aryan wani irin juyi yaji kansa namasa ahankali yafara takawa har cikin dakinsa yana shiga ya murza key akofa. Gaban dressing mirror dinsa ya nufa, da wani irin karfi ya daki mirror din tarwas ya fashe hannunsa yafara jini kayan kan dressing mirror din yafara watsi dasu yana harbe harbe. Su ummi suna falo sukaji karar fashewar abu, da gudu suka nufi bakin kofan dakin amma sukajita akulle, kaya kawai yake zubarwa akasa,ummi ce tafara dukan kofan tana cewa" Aryan pls don't harm your self wlh nasani sharri akamaka I trust you,pls son ka bude kofar dan Allah " Nana ma na ihu tana dukan kofar tace"Ya Aryan dan Allah karka harming kanka, pls open the door" Dada tama rasa mezata ce dan babu abinda ta fahimta sai kuka itama ta keyi tana karamin maigida ka bude kofarnan karka wakanka illa" duk abinnan da sukeyi awaje ko gizau Aryan beyiba, in akwai abinda ya tsana shine a tarnishing image dinsa yanzu kuma Lubna tashiga inda bazata iya fitowa ba dan babu makawa saiyayi maganinta. Jirinda ya dibesa ne yasashi zama akasa ya kama kansa dake barazanar fashewa.


******
Noor na kwance akan gado bayan ta idar da sallah suna hira itada Hanifa sukaji salatin Hanan. Juyowa sukayi suna kallonta Noor tace"ke miye haka meya faru zakina wa mutane salati" wayan hannunta ta mika musu wayan. Zaro ido Noor tayi ta kara zooming vidoen da kyau, haka kawai taji kamar wannan videon ba gsky bane," kai wlh niban yarda da wannan video dinba, sharri kawai akemasa kuma sai Allah ya tona asirin mugaye" hanifa ta fada tana girgiza kai. Waya Noor tadauka takira Nana amma wayanta is unreachable daga bayama saitaji wayan akashe, haka kawai saita tsinci kanta dajin tausayinsa duk da batasan ko gsky bane amma ita zuciyarta yafi bata sharri aka masa. Haka suka zauna adakin sunyi jugum jugum kamar anmusu mutuwa.


Ya Shareef ne yana kai kawo a office dinsa kana kallonsa kaga tashin hankali kwance a fuskarsa. Knocking secretary din Aryan yayi ya shigo yacewa Shareef"sir, yan press ne agaban company din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login