Showing 90001 words to 93000 words out of 99210 words

Chapter 31 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8228

da Sauri saboda jin ihun yara, tace itace zatayi mata wankan jego, dan haka anan zata zauna. Ga mamakinta saiga Aryan akan gado ya dau 'ya'yansa both hand yana rarrashinsu Noor na kwance still bata motsa ba. " wai yar nan meke damunki, tun jiyan Allah akace min yarannan basu ci komai ba amma ke ko ajikinki, bazaki taimaka kibasu nono ko zasusha suyi shiru ba" Dada ta fada tana karbar Hussain daga hannun Aryan, in ran Aryan yayi dubu toya baci, shi ai bemasan cewa basuci abinci ba har yanzu daya sata agaba har saita basu. Ammi da sunaina suka shigo hannayensu dauke da tray na abinci, Noor na ganinsu ta mike ta gyara zama taga abinci, ashe dai har yanzu. Haba Dada ta rike tana kallon ikon Allah, wato ita ta cikinta ta sani amma bata 'ya'yanta ba, ahankali ta dafa gado ta mike ta sauko kasa kan carpet dan har yanzu ciwon nata bawai warkewa yayi ba, baje kafafu tayi kan carpet tayiwa sunaina nuni da gabanta akan ta aje mata tray din, ita Ammi abunma dariya yabata, ana masifa tabawa yara nono amma ko ajikinta ita kawai cikinta tasani. Tsaki Dada tayi tace" ai shikenan, Ku barta karku kuma cewa ta basu, idan suka isheta da zafi zata basune, kunjimin ja'irar yarinya ina yabonki sallah ashe ko alwala ma baki iya ba" mikawa Aryan Hussain tayi ta fice daga dakin tana surutai, Ammi da sunaina ma suka fice suka barsu su kadai. Zama yayi agabanta yadora babies dinsa kan ciya yana jijjigasu yana rarrashinta kan tabasu nono, turo baki tayi tace" Baby, kaga yarannan kadan ya rage su jefa ni duniyar da Ammi ta leka ta dawo, ni bazan shayar dasu ba ni yunwa ma nakeji" haushine ya kamashi, me take nufi bazata shayar dasu ba, watabari ya shayar mata dasu, a dan tsawace yace" Noor are you serious, wazai shayar miki dasu, ke baki tausayin bayin Allah ne da halin dasuke ciki, tun jiya fa rabonsu da cin abinci, ke bagashi ana kawowa kika fara afka ba, toh sukuma mekikeso suyi, plsss love kibasu nono kinjii plsssss" ya ja karshen maganar cikin sigar lallashi, narai narai tayi da ido tace" toh amma bari nagama shan tea dinnan karyayi sanyi" gyada kai tayi alaman ya yarda sannan yaciba da wasa da yaran, iyanzu sunyi shiru sai ajiyar zuciya suke saukewa alaman sunci kuka sun gode Allah. Bayan tagama sha ta karbi Hussain daketa mamula hannu, farar t-shirt ne ajikinta daga waje ma ana hango farin bra din dake ciki, dago rigan tayi zuwa saman chest dinta, mukut Aryan ya hadiye yawu, sun cicciko bulbul Masha Allah ba haske har wani shining sukeyi, ita kanta zafi yake mata saboda ruwa ya cika fam, abunka da Sabon shiga tama rasa ta ina zata fara bashi, ciro guda daya tayi ta kai masa saitin bakinsa, aiko caraf ya cafke yafara zukowa, ihu tayi tareda salati ta fuzgo bakin nononta daga bakinsa, aifa yaro ya tsala ihu inyaaa inyaaa, Ammi ta shigo da sauri tana tambayar lfy, Aryan ne ya fada mata gashi gashi, fada tashiga yiwa Noor tace" haka kowace mace ta fara, kuma zaki saba nan da wani dan lokaci, ai zafinnan zai marine inkika hanasu sha garama ku taimaki juna su rage miki radadi" tana fadin haka ta fice tana fadin Daddy ya sangarta Noor dayawa. Itako Noor tana matsar kwalla haka ta daure tasamasa abaki yana zukowa, yana sha tana kuka Aryan na rarrashi, saida ta basu suka koshi sannan suka kwantar dasu suka cigaba da hiransu. Karfe goma da rabi ya koma gida cikeda kewar matarsa.


Anan kuwa Lubna a gida ta aihu, Anty amarya ce ke kula da ita. Itama yaronta yayi girma sosai tunda shi gaki watanninsa, da kallon yaron ta gano wanene babansa, yayi baki kamar sadiqboii komai nasa ya kwaso babu kamanninta afuskarsa, dukda shi sadiqboii din kyakyyawar ne ba laifi saboda black beauty ne. Da kyar ta yarda ta shayar dashi, haka kawai take jin tsanar yaron a ranta, tsanar datakeyiwa mahaifinsa ne ya shafe shi, sosai Daddynta yayi mata fada kafin ta yarda ta shayar dashi. Babu wani danginta dayazo dubata, tunda taji Noor ma ta aihu sai jininta yayi sanyi, tasan itada ganin wani family member dinta kila sai bayan suna, Allah sarki, da ta aihu ta hanyar aurene da kila yanzu itama ana nan nan da ita kamar yadda akayiwa Noor. Rayuwa kenan, abinda ka shuka shi zaka girba.


Acan gidan Ummi su matan Alhaji Jibril suka sauka da sauran mutane banda dada dake gidan ammi, kafin the next day suma sutafi ganin babies. Ummi tayi kokari sosai wurin ganin ta providing dinsu da duk wani abinda suke buqata. Sunji dadi da akace ammin Noor tadawo dama sunji tausayin yarinyar lokacin dasuka ji cewa Amminta ta rasu shekarun baya. Kowa ranan ya kwanta cikin farin ciki.


Ammi fa ta addabi Daddy lallai saita ga suhail dinta. Tun yana kaucewa har kawai ya sanar da ita maganar mutuwarsa, sunyi sa'insa sosai dan Ummi ta fusata akan rashin gaya mata da baiyi ba. Daren ranan su kadai ne basu kwanta cikin dadi ba.


COMMENT AND SHARE

REEMAH✍️
11/15/23, 8:36 PM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼

REEMAH

PG 63_ 64

✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯

Karfe bakwai yayiwa Aryan agidan Ammi, Dada abun duniya ya isheta taita addabarsa wai akanme zai wani zo musu da sassafe jarababbe, shidai ko ajikinsa yana rike da Hussain wadda yagama shan nono yana wasa dashi, Noor kuma na feeding hassan. Ammi ce tayi sallama itada sunaina suka shigo da tray na breakfast an shake shi da kayan ciye ciye maisa yawun bakin mutum tsinkewa, aiko tunda Noor taga ankawo abinci ta mikawa Aryan babyn ta sauko kasan carpet din dakin ta baje aka fara Sana'a. Kwata kwata bata wasa da wannan fannin musamman ma yadda yaran ke tsotso sosai. Da misalin karfe goma su Anty Jamila da sauran mutane su matan Alhaji Jibril da sauran matan gida aka taru agidan Ammi anzo ganin babies. Gaba daya ranan Noor tana daki itada Aryan dayayi male male kan gadon Ammi kamar dakin uwarsa,ko kunya bayaji haka su Anty Jamila zasu shigo da babies in za'a basu nono suna gama sha kuma za'a fitar dasu. Ammi karan kanta dataga dai Aryan baida niyyar tafiya saita bar musu dakin gaba daya. Dada kuwa tayi mita ta gaji ta fita harkansa. Sai shagwaba Noor ke zuba masa shikuma yana biye mata saikace karamar yarinya, yo karamar yarinya mana mutum ya aihu amma yarinta yaki barin kansa. Shi da kansa ya taimaka mata tayi wanka, haka zai kulle kofar dakin da key har sai sun gama abinda sukeyi sannan ya bude. Da yamma kuwa kowa ya watse saiya rage Ammi da Anty Jamila da sunaina, Dada tabisu matan Alhaji Jibril dan cewa tayi rashin kunyan Aryan yafi karfinta bazata iya zama ba😂😂.

Sai sha dayan dare yabar gidan, shidinma saida Anty Jamila tasashi agaba dan ta lura baida niyyar tafiya ma gaba daya.

Sosai Noor da babies din ta suke samun kulawa yadda ya kamata, babu abinda takeyi daga ci sai sha saikuma bacci,Allah ma ya taimaka yaran basuda rikicin dare dan haka suke baccinsu hani'an. Ammi tadawo kwana da ita in case koda yaran suna buqatar wani abu da daddare.

Ana gobe suna, su anty umaima sun iso daga kano, gidan Ammi yacika makil da jama'a, wasu kuma suna gidan Ummi, wasu na gidan Anty Jamila. Noor tasha kwalliya cikin wata atamfa Holland blue mai ratsin black and white anyi masa adon flowers yasha stones agaban rigan,kayan dinkin riga da Zani ne amma skirt rapper yayi mata kyau sosai kamar bamai jego ba saita zama wata yar sweet sixteen da ita. Zaune take kan carpet ta baje kafa tana shan farfesun kan rago wadda yasha kayan hadi sai tashin kamshi yake, ga kuma chips din ta agefe da kwai sai tea kakkaura( kai Noor Allah yasamu adanshinku). Anty Jamila na dressing yara wadda akayi musu wanka sai tsala kuka sukeyi ana gasa musu cibi dan ya riga ya fadi tun jiya. Sallama sukaji, da sauri. Noor ta dago tana kallonsa, yayi bala'in kyau cikin wani half jumper blue colour yasha aiki mai kyau, ga hulan zanna bukar daya zauna das akansa kamar akan akayita, tundaga bakin kofa akejin kamshin turarensa wadda nan da nan ya mamaye dakin, wani irin murmushi ya sakar mata tareda winking idonsa daya, batasan lokacin data sauke kai kasa tana sakin murmushi ba, Anty Jamila da tuni tagama shirya yara tazauna tana kallon ikon Allah, ko ma ya san da ita adakin, shi kawai matarsa, ikon Allah. Karasa shigowa yayi saiga su Ya Shareef dasu Ya muhsin suma sun biyo bayansa suna jan akwatuna bibbiyu ahannunsu. Can saiga Nana da hanan suma sun shigo da daddaya, baki sake Noor ke kallon jerin akwatuna kamar na amarya. Bata gama tunani ba saiga Hanifa da yasmeen suma sun shigo da guda daddaya. Sallamansu Anty ounaisa da su Anty laila suka jiyo daga bakin kofa, wani tsalle Noor tayi ta mike zata karasa bakin kofa kafin su ida shigowa aikuwa unluckily ta harde kafa, da sauri Aryan ya tallabota ta fada saman wide chest dinsa, kallon juna suka shiga yi kamar yau suka fara ganin junansu, sun mance da mutanen dakin sun shagala da kallon juna, kit kit kit sukaji ana daukansu hoto, da sauri ta dago daga kirjinsa tana boye fuskarta atafin hannunta, shima shafa keyarsa yayi dan borin kunya, Ya muhsin ne ya sheke da dariya yace" lallaima Aryan, you've got some nerves, wannan irin rashin kunyan har gaban su abla hmmm" saikuma yakara fashewa da dariya su Ya Shareef ma suka dauka, su dai matan babu abinda sukace saima wuri dasuka samu suka zauna aka fara bude akwatunan da aka kawo. Da sauri Noor ta fice adakin shima yabi bayanta. Kayane sosai nagani na fada kamar na amarya, akwatuna guda takwas ne, hudu na Noor, hudu na babies, atamfofi su leshi gasu materials su abaya, kamar dai yadda akeyiwa amarya. Abun ba'a magana. Suna budewa ana hiran yaushe gamo, inda Ya muhsin yaja Nana suka bar dakin, Ya Shareef ma yaja Na'ima suka fice kowa yanemi nasa lungun ana shan love. Su hanan kuwa an zagaye baby, kowa na fadin sunan da za'a bawa yara suna ta argument tsakaninsu.


A garden din gidan su Noor da Aryan suka zauna,hira sukeyi gwanin sha'awa inda yake fada mata yadda yayi missing dinta atare dashi, gashi Ummi tace mai bazata dawo ba sai tayi arba'in. Itama harga Allah tayi kewarsa amma babu yadda ta iya, tana tsoron yiwa Ummi jayayya ne kawai. Haka yayita zuba shagwaba tana rarrashinsa, har ya bata tausayi, da kyar yake iya bacci dan ya riga yasaba dajinta ajikinsa itama kuma haka amma ita tana baccinta me kyau ma. Saida aka kira sallan zuhr sannan takoma cikin gida shikuma ya tafi masjid. Bayan sallah, masi lalle tazo tayiwa Noor kunshi.


Washe gari ranan suna, tunda safe karfe tara motoci suka fara hallara a gidan kamar biki akeyi. Manya manyan matan Abuja su kawayen ummi dasu Anty Jamila ga kuma matan abokan Daddy, Abba, da uncle saif duk sunzo da 'ya'yansu mata. Mai jego taci kwalliyarta anyi mata jan lalle yayi dark maroon sosai ga kuma bakin design din da aka mata yayi kyau Masha Allah, gashin kanta yasha gyara saboda tsayinsa yahana ayi mata kitso ga kuma tsantsinsa. Taci wanka cikin white shadda da akayi masa aiki da golden zare, an kashe mata dauri mai step step, ga gold jewelry din da Aryan ya siya mata ta sanya yayi kyau, babies ma sunsha kwalliya cikin kaya iri daya white and gold colour na baby boys. Kowa na santin yaran amma ba'a bari ana daukansu ana jagwal gwala su, suna kwance cikin baby bed dinsu duk mai son ganinsu zai zo ya tsaya ya kallesu ya dan shafa su shikenan. Anty ounaisa ce ta shigo dakin hannunta dauke da wani golden tray an rufeshi da gold linen. Ajewa tayi gaban Noor, sannan ta dauko twins din ta daura mata saman cinyarta, bude tray din tayi ta fidda Ajwa(dabino ne da ake samu agarin Makkah da madina), sai ruwan zamzam, sai wani dan kwalban turare mai hegen kyau kana ganinsa kasan ba karamin kudi gareshi ba, sai kuma alkyabba uban ubansu white and golden colour da takalman jarirai guda biyu, suma golden colours sunsha ado.kamar na sarauta, cup ta dauko ta tsiyaya tabawa Noor ta shanye tas sannan tabata ajwan shima ta cinye shi, turaren ta dauko ta mikawa Noor tace ta fesawa yaranta, batayi musu ba ta fesa musu nan da nan dakin ya hade da kamshin turaren saiyabada wani irin kamilin kamshi mai sanyin shaka, takalman jariran aka sanya musu akafa saiya tafi da kayan dake jikinsu, alkyabban Anty ounaisa ta dauko sannan ta ratayawa Noor bayan ta kwashe yaran daga cinyarta. Masha Allah tabarakallah, saiga Noor tafito kamar wata matan sarkin saudiyya, tayi hadu sosai sosai. Mikawa Hanan da Hanifa yaran Anty ounaisa tayi sannan tace subi Noor abaya su sauko kasa wurin jama'a za'ayi hoto. Haka kuwa akayi, kowa na zaune a babban falon kasa ana hira ana dan motsa baki da kayan ciye ciye, tunda suka ji karan takalma ana saukowa ahankali, idanun kowa ya koma kansu, Masha Allah Masha Allah kawai kakeji afalon, wasu kuma suna kyasawa musamman yan matan dake falon yaran abokan Abba dasu uncle saif. Tafito kamar shining star tayi fice cikinsu, babu wadda ya kai kwatan kwacin haduwar datayi,yasmeen na bayanta tana gyara mata alkyabbar, su Hanan kuma suna bayan yasmeen suna rikeda babies. Har suka karasa saukowa babu wadda ya kyafta sai kallon su ake. Ammi dake zaune kujeran gefe ta kafe Noor da ido kawai taji hawaye nabin gefen fuskarta, yau Allah yacika mata burinta daya barta da ranta hartaga wannan rana. Yau gata ga jikokinta, Allah sarki suhail dinta inama yana raye, taso yaronnan kamar me saboda shi kadai Allah yabata namiji. Sai da tabi kowa dake zaune afalon manya ta gashshesu. Kafin aka mike aka take mata baya zuwa harabar gidan wadda yasha decorations da balloons masu kyau. Mazaje suna waje ana hira, can na hango baban jego tareda Ya Shareef suna hira. Tunda yaga sanyin idaniyarsa yarasa natsuwarsa, har wani rufewa Muhsin ido yake kar agane masa mata. Buge hannunsa muhsin yayi yana tabe baki,shi dakeda Nana mezaiyi da second hand din Aryan, bugu Aryan yakai masa shikuma ya kauce yana dariya. Itama kallonsa takeyi, ya hadu sosai shima sanye yake da alkyabbar irin nata, ga kuma shadda fari irin nata shima yasha aikin golden zare, takalmin kafarsa da hulan kansa kadai abun kallo ne. Sun shagala wurin kallon junansu, ahankali yake takowa har gabanta, bude mata hannunsa yayi alamar ta hugging dinshi, ba musu kuwa ta karaso jikinsa ta kwanta luff, tare suka sauke ajiyar zuciya, Aryan harda wani lumshe ido ya furta "ALHAMDULILLAH YA RABB". Kowa baki galala ake kallonsu, ko irin nauyin dumbin mutanen dake wurin basuji kunyarsu ba, daga sama sukaji muryar Dada tana cewa" ahap ai in wannan ne kar Ku wani ji mamaki, fiye da haka ma sai suyi, kunma gode rasa kunyar bai sumbaceta ba" ta karasa maganar tana jifan Aryan da harara, shi hankalinsa ma ba'a kanta yake ba. Anty ounaisa ce tayi magana" kai Aryan banason rashin kunya, kai ko nauyin mu baka ji dalla saketa mugani" turo baki yayi kamar karamin yaro da aka raba da bakin nono ya dan saketa amma still suna manne da juna, abinda yayi ba karamin burge yan matan dake wurin yayi ba, saisukaji inama inama sune. Allah sarki har na tausaya muku in wata acikinku tashiga hannun boss Noor😂😂

Inda aka tanada na zaman iyayen babies suka zauna sannan aka miko musu babies din, hoto aka shiga daukansu kit kit kit kamar ba gobe, kowa na zuwa adaukeshi hoto taredasu yadda kasan celebrities. Masu abinci kala kala aka gayyato,inda aka dafa both local and continental dishes kowa yaci yasha abun sai son barka. Matsowa Aryan yayi kusada kunnin Noor yayi mata kus kus aciki, saigani nayi tayi murmushi da alama wani abu yafada mata wadda yayi mata dadi sosai. Mc na cikin magana akan iyayen babies kawai mukaji dirowar motoci acan compound din gidan inda motoci suka parking. Yadda suke shigowa gidan saika dauka yan gudun hijira ne suka gudo daga hannun kidnappers. Ban sha mamaki ba dannan san su waye babu shakka yan gidan MIJIN TACE NE. Aikuwa ban gama rufe baki ba saiga su ANTY ASHANTY DA TAWAGARTA sun kuso kai, sunci anko ansha kwalliya kamar za'aje dinner party😜, can saiga MOM SANI ITAMA DA BATALIYARTA kowacce acikinsu tasha no red skirt(no respect/ google)😂😂, su AMMEY LAYLA su Anty yusrah ma da su Mrs Isa duk sun zo, sauran mutan gidan MIJIN TACE MA na hangosu ana dambe da security wai sai lallai anbarsu sun shigo da kulolin abincin dasukayiwa Noor niki niki kamar za'a shekara anaci😂. Dafe goshi Aryan yayi ya ce" kai Allah sun iso kenan, yanzu zasu hana mutane saqat" murmushi Noor tayi kawai tana kallonsu, can kaji DJ yasanya wakar BUGA na kiss Daniel, su Mom sani harda kwasan shoki ana shigowa fili, Anty Ayshu da Ammey layla sun kame kan high table( special guest of honour)😂.

Su Mrs Isa kuwa saida aka kwasa da Dada dan dama bawani shiri suke ba, matar tacika sa ido dan kawai taga Mrs Isa da dan atemaki wadanta( high heel) shikenan tahanata saqat wai tayi hankali kar ta gurde kafa😂. Kowa yaci yasha anyi rawa an gode Allah. Sai ana gab da ganawa baban jego ya amshi mike sannan ya yafara magana" NUWAIRA, NOORIE!!! SHE IS THE BEST THING THAT HAS EVER HAPPENED TO ME, SHE GAVE ME ETERNAL HAPPINESS, ITACE JIGON RAYUWATA, TABANI ABINDA KOWANI DA NAMIJI YAKE BURIN SAMU DAGA MATARSA WATO 'YA'YA, I DON'T KNOW HOW TO EXPREESS MY PROFOUND GRATITUSE TO RABBIS SAMAWATI FOR THE GIFT OF NUWAIRA, BUT SURELY DO I KNOW THAT BAZAN TABA BARINTA TA KASKANTA ARAYUWA BA, I PROMISE TO BE HER SOULMATE FROM NOW TILL THE HEREAFTER, THANK YOU SO MUCH UMMU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login