Showing 15001 words to 18000 words out of 99210 words

Chapter 6 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8219

akan faffadar kirjinsa wadda yake sumul kamar bayan kwai babu alaman gashi. Take wani irin feeling ya taso mata. Duk abinda takeyi Aryan na ankare da ita dan tun shigowarta yaji motsi amma be motsa ko kadan ba. Hannun ta takai kan kirjinsa da zummar yimasa wani abu ya cafke da sauri, tsananin bakin ciki da haushi hadi da takaice yaji ya ziyarce shi akanta, take wani irin tsanarta ya darsu a zuciyarsa, me ma zai mata yaji sanyi azuciyarsa, wani mugun kallo ya watsa mata da lumsassun sexy eyes dinsa wadda ya dan fara canza kala, hankadeta yayi harsai da tafadi akasa. Mikewa yayi ya nufi kofar dakinsa ya murza key dan yau insha Allah saiya koyawa Lubna hankali kila akansa bazata kara taba namijin daba muharrraminta ba. Itako shu'umar mikewa tayi still bata daddara ba wani irin tafiya na daukan hankali takeyi ita adole she's looking sexy dinnan duk tunaninta biye mata zaiyi shiyasa ya sanya key akofar. Murmushinsa mai tsananin kyau yayi sannan ya raba ta gefenta ya wuce cikin closet dinnsa ya sanya singlet ya dora ash jallabiya akai sannan ya zaro wani skin belt dinsa daga ma'a daninsa, abayansa ya boye belt din ya fito daga closet din. Mamakin ganinsa da kaya ajikinsa Lubna tayi, kenan yanada ulterior motive shiyasa ya kulle dakin. Baya ta fara ja kadan kadan shikuma yana jara matsota har yazo inda take. Bata ankara ba taji belt atsakiyan skin din bayanta. Wani irin zafi taji ya ratsata wadda tunda take bata taba jin irinsa ba. Ihu ta kurma gaba daya gidan ya amsa.

Su ummi suna falo suka jiyo ihun Lubna, a zabure Anty Aisha tamike tana waige waige kozata kara jin ihun, aikuwa takara ji na yanzu ma yafi na dazu, da gudu suka nufi dakin aryan dan anan ne ihun ke fitowa. Suna zuwa sukaji ihun Lubna da kyau alamar jibganta akeyi, Dada ta kama handle din kofar amma tajishi akulle. Babbuga kofar suka farayi amma bai bude ba.

Saida yamata duka black and blue tayi laushi sosai dan ba karamin fasa mata jiki yayi ba. Ko kwakkwaran motsi bata iyayi sannan ya wuce ya shige toilet ya wanko fukskarsa ya fito. Abakin kofa ya ganta tana kokarin bude kofar amma babu key. Tana jin motsinsa takara kurma wani ihun tana ataimaka mata zai kasheta. Wayansa ya dauka a side drawer din gadonsa sannan ya dau key din motarsa da key din dakin, kwallo yayi da ita aikuwa ragab sai gata ta bugu da dressing mirror dinsa goshinta ya fara fidda jini. Ko kallonta baiyi ba dan zuciyarsa wani irin tafarfasa yakeyi shi inta shinema wannan dukan dayamata kadan ne.

Anty Aisha sai kuka takeyi wai zai kashe mata tilon 'yarta. Sukuwa su ummi ko kala basu ce da ita ba harda Dada. Itakuwa Nana wani irin farin ciki takeji yau Ya Aryan ya gyara wa Lubna zama. Suna wannan tunanin ne suka ji anbude kofar dakin. Yana fitowa ko kallansu baiyi ba yasa kai zai fice ummi tace"dakata Aryan,where do you think you're going"? Baiso ummi ta tsayar dashi ba, bai tafi ba kuma bai juyo ya kallesu ba. Dada ce tace"ummu sulaim kyaleshi yatafi duk abinda yamata ita tajawo wa kanta" yana jin maganar Dada ya fice abunsa. Anty Aisha da gudu ta shiga dakin ta tadda Lubna acan gefen dressing mirror ko kwakkwaran motsi batayi. Da gudu ta yo kanta tana kuka. Su ummi ma suka shigo inda duk jikinsu yayi sanyi. Amma ummi tayi mamakin ganin irin shirin da Lubna tayi, kenan abinda tasa kenan yasa ta sanya jalbab akai? Hmm. Da kyar suka taimaka wa Anty Aisha ta mikar da Lubna har wurin motar ta. Babu wadda yabita acikinsu sai ummi dan Dada tace babu inda zata hakama Nana. Asibiti suka wuce da ita suna zuwa aka shigarda ita emergency.


Noor da Hanifa da Hanan sune a kitchen yau ana girki. Dama haka Anty jamila ta koyar dasu, duk ranan weekend suke abincin gidan acewarta bata yarda ta aurar da 'ya miji ya dawo da ita sabida rashin iya girki ba. Hadadden chicken biryani suka hada da fatoush salad da kuma brazilian lemonade. Noor itace ta hada snacks inda tayi meat pie dasu samosa. Ko ina a kitcehn din sai tashin kamshi yakeyi. Sunayi suna taba hira gwanin sha'awa. Suna gamawa suka shirya akan dinning sannan suka wuce dakinsu dan lokacin sallan zuhr yayi. Wayan Hanan ne yayi kara ta dauka tana wani kashe murya ta fice daga dakin. Dariya su Noor suke mata itada Hanifa. Bayan sallan zuhr suka hallara a kan dinning dancin lunch. Sosai sukayi santin snacks dinda Noor tahada musamman meatpie din wadda yaji wadataccen nama acikinsa. Bayan sun gama ci suka koma falo aka kunnan tv, su uku kawai aka bari a falon. Wani romantic indiam film ake nunawa inda Noor tamaida hankalinta sosai kamar me daukan darasi. Nuwaira kenan.

Tuki kawai yakeyi amma harga Allah bemasan ina zai tafi ba dan wani irin tukukin bakin cikine ke cinsa aciki. Kanwar bayansa itace babu kunya takeso yayi iskanci da ita? Lallai 'yan matan nigeria daban suke da matan saudi. (Hakane?). Asokoro ya wuce inda ake gini gidansa, anyi nisa sosai aginin inda ake matakin roofing din gidan. Sosai gidan ya hadu tunma kafin akarasa. Wani masallaci dake kusa da gidan ya wuce yai sallan zuhr sannan ya dawo site din yana kallon yadda ma'aikata keta aikinsu cikeda kwarewa.


Su Lubna kuwa angama dressing ciwonta an maida ita wani special room. Hannunta daure da bandage dan har karaya ta samu ga goshinta daya fashe shima an daura masa bandage. Anty Aisha tayi kuka harta godewa Allah. Ummi nata rarrashi amma ko kallon ummi batayi ba. Sosai abinda Aryan yayiwa Lubna yataba ta kuma ta dau alkawari saita dau fansa akansa. Dago kai tayi ta kalli ummi tace"wlh ummu sulaim dani kuke wasan dake da danki badai 'yartawa ce bayaso ba, to bazan taba bari yayi aure ba inhar ba Lubna zai aura ba. Dukan nan daya mata ba'a banza zai tafi ba saiya jishi ajikinsa" ummi baki bude take kallon Anty Aisha, murmushi ummi tayi tace"Allah yabaki sa'a Aisha, da Allah kike zancen kuma seya shayar dake ruwan mamaki, kuma inhar auren Lubna ne da Aryan wlh wlh ko bayan raina Aryan ya auri 'yarki bazan yafemasa ba" tana kaiwa nan ta fice. Driver dinta ta kira babu dadewa ya iso suka bar asibitin. Anty Aisha ko sai bombomi take tama mance dawani magani data karbo daga wurin boka Gangaran.

Ummi na isowa gida tawuce dakinta anan tasami Dada da Nana suna hirarsu kamar ma babu abinda yafaru. Kallonta sukayi ko tambayar ya mai jiki basuyi ba, ummi tace" Nana dama kinsan halin Lubna shine baki taba fada min ba? Nana tace" ummi to kona fada miki ai babu abinda zai canza, dadin abun shine abba da Ya Aryan basa sonta ba shi kenan ba" ajiyar zuciya mai nauyi ummi tayi alokacin wayarta yayi kara. Abba ne, amsawa tayi sannan yake tambayarta abunda yafaru dan yanzu Aisha takirashi take fada masa Aryan yawa Lubna duka. Duk abinda ya faru tafada masa. Yasan dama hakan zai faru, Allah ya kiyaye gaba kawai shima ya fada sannan sukayi sallama. Ko sallan zuhr ummi batayi ba toilet tawuce ta dauro alwala sannan tazo ta fara sallah.


Sai 10:00pm yadawo guda lokacin yasan kowa yayi bacci. Yana shigowa ya wuce dakinsa, har zai shiga yaji muryan ummi abayansa. Tsayawa yayi sannan yajuyo asanyaye ya dube ta" magana nake so muyi dakai. Dakinsa ya bude mata sannan suka shige. Abakin gado suka zauna, ahankali ummi takami hannunsa cikin nata tace" Aryan baka taba min karya ba kuma nasan bazaka taba yi ba, menene ya faru tsakaninka da Lubna "? Beyi zaton wannan tambayar daga wurin ummi ba amma kawai bari ya fada mata. Babu abinda ya boye cikin abinda Lubna ta dade tanayi masa itada Anty Aisha wadda hakan yasa ko gidansu bayaso yana zuwa. Ajiyar zuciya tayi tabbas babu namijin kwarai wadda zaiso yasamu irin Lubna amatsayin mata. Shafa kansa tayi batare data cedashi wani abu ba kawai ta mike tafice. Tana fita shima ya mike ya rage kayan jikinsa sannan ya wuce bathroom. Shower ruwan sanyi ya sakarwa kansa. Ya dau kusan twenty minutes kafin ya kashe ya hada ruwan zafi cikin jacuzzi dinsa ya shige. Saida yayi thirty minutes a toilet din kafin ya fito. Kananan kaya kawai yasa sannan yayi sallolinsa yadda yasaba ya haye kan gado babu bata lokaci bacci yadaukeshi.



Washe hari ummi tahada breakfast tabawa driver yakai asibiti dan Nana tace babu inda zata. Itama ummin babu abinda takeso yakara hadata da Anty Aisha shiyasa bata tafi ba.

Da driver ya kaiwa Anty Aisha abincin haka tasa yadawo dashi afadinta wai bata buqatar wannan guban. Koda ya dawo dashi basuyi mamaki ba harda Abba dan dukkansu sunsan halin Anty Aisha.

Wunin ranan gaba daya Aryan yayi shi ne adaki sallah kawai ke fitar dashi.


Washe gari...


SHARE AND COMMENT



REEMAH✍️
10/8/23, 5:36 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH


PG 17_18

Yau su Noor zasu fara test, tun jiya da daddare take karatu kuma ba laifi tashiryawa test din sosai. Sanye take da normal wear dinta na makaranta tayi kyau sosai sai baza sassayan kamshi take. Babu makeup a fuskarta face lipgloss da tozali amma hakan bai hanata fita one in ten ba.

Kasancewar tun first week din data fara zuwa school su Nana ke koya mata mota, yanzu kuma har tana iya tuka motar amma kuma bata zuwa wuri mai nisa. Hanan ce ta tuka su suka tafi makarantar. Suna parking motar a parking space kowa ya wuce faculty dinsa.

A entrance din faculty dinsu suka hadu dasu Nana da yasmeen. Kamar yadda tayi tsammani test din yayi sauki dan karatu bana wasa tayi ba. Sai nine suka fito daga test din, Karfe sha biyu zasu kara rubuta wani. A resting area suka yada zangonsu kafin time din next test din yayi. Shima ba laifi bai bata wahala ba.

Suna fitowa Nana tace" Noor dan Allah yau kibini gidanmu wlh sosai ummi keso taganki, ko ban kawo mata hirarki ba take tambayata ke fa" cute smile dinta tayi tace" to shikenan amma bari na Sanar dasu Hanan sai na kira habibty (Anty Jamila) itama na fada mata"hakan tayi indasu Hanan sukace lallai saidai sutafi tare da ita. Bayan sallan zuhr suka wuce gidansu Nana.


Ummi ta karbesu hannu bibbiyu kuma tamkar gidansu haka suka sake babu wani matsala Noor saitaji kamar agidansu take sabida yadda ummi tasake da ita sai nan nan take da ita tana tambayarta me takeso abun har mamaki yabawa su Hanan, sunyi hira da Dada inda anan kawance ta kullu tsakanin Dada da Noor har wani kawalli take kiranta. Sai 5: 30 suka shirya zasu tafi. Kyaututtuka sosai ummi tahada musu.

Parking motansa yayi ya fito, sanye yake da suit royal blue, suit din mai tsayi ne irinna Koreans dinnan ya kai masa kusan guiwa kuma yanada igiyoyi daga gaba qn hadasu a baya. Bakin wandon suit ne ajikinsa sai black toms masu shegen tsada da kyau. Kyau kuwa nabarku da tunaninku. Dan fadin kyawun dayayi inna tsaya zayyanawa bata lokaci zamuyi.

Nana dasu ummi ne sukarakosu har gaban entrance din gidan. Suna fitowa shikuma yana shigowa yaci karo dasu ya koma da baya. Idanunsu ne ya sarke dana juna, sunkai kusan one minute suna kallon juna bama susan magana akeyi dasu ba. Hanifa ce tadan bugi kafadar Noor sannan ta sauke kanta. Gaidasu ummi da Dada yayi yai wucewarsa ko ta kansu bai kara bi ba. Murmushi ummi tayi a zuciyarta tace" Allah ya tabbatar da mafi alkhairi". Sai da suka ga tafiyansu Noor kafin suka koma cikin gida.

*******


Jikin Lubna yadanyi kwari ba laifi saidai tsamin jiki da kuma ciwon hannunta dana goshi wanda yake mata zafi. Ita ko tunanin abinda yafaru ma bata sonyi, amma ta dau alkawarin cewa Aryan saiya san ita ya daka. Anty Aisha ma abinda take kissimawa a zuciyarta kenan dan sunyi magana da Abba inda yace mata tacewa 'yarta tafita harkan Aryan inko bahaka ba duk abinda yabiyo baya ita tajawa kanta. Kenan Abba yana bayansu ummi da Aryan, lallai yanzu za'a fara wasan. Sai da yamma aka sallami Lubna suka koma gida tacigaba da jinya.

*******
Tunda ya shigo daki yake tunani" meyasa Allah keta hadasa da wannan mara kunyar yarinyar, shi wlh ko ganinta bayasonyi dan itace mace ta farko data bude baki ta zage shi abainan jama'a, har aka kira sallan maghrib sannan ya fito bayan yayi wanka ya canza kayan jikinsa.

Su Noor suna zuwa gida suka yi wanka suka ci abinci. Suna zaune ana hira Hanifa tace"Hanan kinga wani ikon Allah ashe dama abokin Noor yayan kawarta ce" tafada tana dariya hadi da kallon Noor wacce ke aika matada sakon harara. Hanan ta dara tace" wlh nifa na fara tunanin kila Allah neke nuna musu wani sign, kinga wani irin kallon da sukewa juna dazu kuwa" "wlh Ku fita harkata zan muku rashin M, Allah ya kiyaye mezanyi da wannan basamuden, nidan cakwas nake buqata ba wadda zai rika jibgata ba" dariya suka mata sannan suka bude wani dan jakar da ummi tabawa Noor, wow kawai suke fada, wani golden bracelet ne aciki mai dan karen kyau. An kawata jikin bracelet dinda yan kananan stones. Ita karan kanta Noor sosai bracelet din ya burge ta, karba tayi ta gwada a tsintsiyan hannunta aikuwa das yamata kamar dama dan ita akayi shi. Haka suka cigaba da santin abubuwan da ummi tabasu suna kara jin matar azuciyoyinsu.

*******

Yarage wata guda da auren Moon sosai Daddy yake narka kudi wurin siyan ingantattun kayaki wa Moon,mama batada ko labari akan abinda akeyi, amma itama data ga babu sarki sai Allah tafara saukowa daga saman gajimaren data hau. Mai gyaran jiki ta kira daga Maiduguri kasancewarta yar can aka fara gyara Moon. Moon batada wani walwala duk abinda ake mata kallonsu kawai takeyi amma bawai dan tanaso ba.

Yau su Mama suna zaune a falon itada Moon sukaji horn kamar na babban mota. Mai gadi ne ya wangale gate, wani babban motan daukan kaya ne yashigo ya paka a tsakiyan compound din gidan. Wasu samari ne su uku suka fito daga motar suka bude bayan motan. Kayane birjik ancika motan fam, su kayan kitchen ne da abubuwa dai wadda ake siyawa amarya amma banda furnitures, su Mama suna tsaye abakin kofa suna kallon ikon Allah, Daddy fa dagaske yakeyi ga dukkan alamu. Moon bata tsaya awurin ba tafashe da kuka ta wuce dakinta tacigaba da ruskan kukanta.

A BQ suka jera kayan wadda yacika daki da falon BQ din fam, ajiyar zuciya Mama tayi tashige ciki abinta. Babu yadda zatayi saidai ta rungume qaddara ayadda tazo mata, wani gefe na zuciyarta kuwa tsinewa Noor takeyi,gashi tunda ta tafi batama da numberta balle takirata taci mata mutunci.


*******
Su Noor sungama test inda suka fara shirin exams nan da one week inda a kirge zasu gama ne ana yan kwanaki da bikin Moon wadda batama da labarinshi. Tana Library tana karatu wayarta ya dau kara, Daddy ne ke kiranta, gaida shi tayi sannan ya Sanar da ita gobe zaizo abuja yaganta, murna wurin Noor ba'a magana. Sai bayan sallan asr suka bar makarantar.

Anty Jamila da Ya shareef suna zaune a falon suna hirar akan kudin sadakin Ya shareef dinda aka kai gidan matar da zai aura Na'ima. Su Hanan suka shigo suka tarar dasu zaune afalo,zuwa Noor tayi ta zauna kusada Anty jamila, anan take labarta musu sa ranan auren Ya shareef, murna wurinsu ba'a magana. Su Hanifa har anfara magana akan shagalgalun daza'ayi da bikin. Noor ce tace " habibty gobe daddy zaizo insha Allah"Anty jamila dama daddy ya riga ya kirata kuma ya sanar da ita zuwan nasa tace" ba damuwa Allah yakaimu, gobe ai babu lectures kinga kenen zamu shiga kitchen tare muyi girki" haka suka cigaba da hira abinsu suna tattaunawa akan bikin.



********
Rana bata buya saidai uwar 'diya taji kunya, su Noor sun gama jarabawarsu ta first semester, murna sosai awurinsu Noor dasu Nana. Har wani get together suka shirya wa kansu su biyar, Nana da Noor, yasmeen, Hanan dakuma Hanifa.

Restaurant mai tsada na 'yayan manya suka booking, kowaccensu sanye take da kaya mai kyau ox blood colour. Doguwar riga wadda yasha adon tsones masu kyau da walwali Noor ta sanya. Necklace irin me stones manya manyannan shima ox blood tasa, takalminta mai dan tsini yayi kyau akafarta yazauna gwanin sha'awa. Ganin kyawun Noor sai wadda ya hadu da ita kawai abun ba'a magana. Yan biyun anty jamila suma sosai sukayi kyau.
Yasmeen a gidan su Nana ta shirya, karfe bakwai zasu tafi shiyasa kowacce ta dauki time dinta ta shirya da kyau, gsky dukkansu sunyi kyau saikace makarantar gabadaya zasu gama ba first semeter 100lvl ba. Ummi ce tacewa Aryan saidai ya kaisu Nana inda zasuyi taron nasu. Haka kuwa akayi bayan sallan maghrib suka fito suka shige motarsa. Wani irin kallo ya watsa musu dukkansu biyun ya tabe bakinsa yace"where are you guys going to" cikin in ina Nana tace" dama yaya da ma dama.."tsawa yadaka mata yace" will you tell me or saina hanaku tafiyan" kuka Nana tafarayi instead ta fada masa inda zasu tsaban tsoronsa daya kamata. Itako yasmeen tama riga ta fidda rai tasan halin Ya Aryan sarai. Juyowa yayi yace"ke ina zaku"ya tambayi yasmeen, a dan firgice tace" cilantro" bai kara magana ba yafigi motarsa yafice daga gidan. Sun iso cikin restauramt din daidai su Nana ma sun iso. Kafin ya barsu suka fito daga motan yace"i'll be here kuma hour daya kawai na baku" kai suka gyada da sauri kamar wadda suke Allah Allah sufita amotar. Da sauri suka karaso wurinsu Noor sannan suka shige. Shidai Aryan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login