Showing 39001 words to 42000 words out of 99210 words

Chapter 14 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8223

kawai yasa nasa ya take ta dan karfi wani irin zafi taji ta tureshi amma ko gizau beyiba saima kara matsota dayayi har suna iya jiyo numfashin juna yace"wlh yarinya kishiga hankalinki inbahaka ba in tattakeki" itama dago kai tayi cikin tsiwa tace" nifa ba tsoronka nakeji ba naga alama mugunta kakeso kamin toh wlh bazan lamunta ba, wannan abinda kakeji dashi nafika jidasu" bakinta nefa kawai ke iya furta wannan amma da za'a tsaga kirjinta tsaf zuciyarta zai fado kasa saboda lugude. Mamaki ne ya kama Aryan lallai yarinyan nan tana buqatar ayi mata factory reset, yaga alama ko tsoronsa bataji, hmmm hmmm hmmm kawai ya fada ya juya ya fice abinsa. Itakuwa tana ganin ya fita ta zauna tana murmushin cin nasara akanshi tafara serving abincinta tanaci tana lumshe ido.


"Ummi dan Allah kibari natafi gidan Ya Aryan kinga fa tun randa aka kai Noor bansake zuwa ba plss ummina" Nana tafada tana marairaice fuska dan ummi taki barinta tatafi gidan amarya. Dada ta cafke kamar da ita akeyi tace" toh me shishshigi mekuma zakije kiyi agidan bayan ba'aso ana damun amarya da ango, yanzu haka sunacan suna shan amarcinsu zaki wanije kikafesu da wannan idanun naki kamar na jamage" me ummi da zatayi inba dariya ba, itakuwa Nana ta wani murguda wa Dada baki tace" Allah yasa kin kusa tafiya kibarmu, ai ko kullum ina hanyan zuwa gidan tunda bakin ciki kikemun" haka sukayita sa'insa da Dada sukaji sallaman Aryan. Kowa a dakin ya fadada fara'ar fuskarsa ganin ango. Zama yayi ya gaida su suka amsa Dada tayi tambayar kawallinta a gajarce yace klau, itakuwa da bakinta baya shuru tace" incedai ka gasa min itada kyau ko, dan wannan jikinnaka nasan kawalli tasha jiki, Allah sarki baiwar Allah, koma dai na bika ne naga ya jikinnata" tafada tana rike haba kamar me tunanin wani abu, su ummi kuwa kunya duk ya rufesu inda Nana kuma ke dariya kasa kasa. Shikuwa ya bata rai jin maganar da Dada keyi babu ko kunya, ummi ce tace" Dada ai karki damu nasan bata cikin wani matsala insha Allah" kai kawai dada ta gyada tace" ehh kuma hakane kinsan yaran yanzu idanunsu ya bude, zata kula da kanta ma"mikewa Aryan yayi ya fice daga dakin yana mamakin wannan tsohuwar. Dada kuwa sai zuba surutai takeyi akan kawallinta.


Yana fita daga dakin ya wuce falon kasa ya zauna, jingina kansa yayi da kujeran,maganan Dada na dawo masa, daga yin aure har an fara tunanin abu ya wakana, kenan nan da watanni tara zasu fara sa ran zuwa gaisuwan aihuwa, shikuma in hakane saidai suyita zaman doya da manja da wannan yarinyar dan bazai taba iya Sonta ba balle har aje maganan hada shimfida da ita. Shi garama ya fita harkan yarinyarnan if not raini zai shiga tsakaninsu komai Daren dadewa dole yasan zata bukaci wani abu daga wurinsa a matsayinsa na mijinta, lokacinne zai nuna mata cewa ya isa kuma dole tayi abinda yakeso. Wani shu'umin murmushi yayi ya shafa gefen fuskarsa.

*******
Yau sati daya kenan kullum Moon dawata matsanacin zazzabi take kwana ta tashi, koda Mahmud ya lura da hakan ya nuna damuwarsa akan sutafi asibiti taki haka ya barta. Kwance take akan gado sai juyi take zuciyarta na tashi kamar zatayi amai. Da sauri ta mike ta wuce bathroom ta dinga kwararo shi, bayan tagama ta wanke bakinta ta tsaya tana kallon kanta a mirror din bayin, sai yanzu ta lura da jikin data kara ga kuma fresh datayi,kamar ta tuno wani abu ta dafe kirjinta da sauri, kusan wata biyu kenan bataga period dinta ba me hakan ke nufi. Da gudu tafito daga toilet din tana kiran lawisa mai aikinta, tana zuwa ta mika mata kudi tace taje chemist din dake kusa dasu tasiyo ma PT. Babu bata lokacin lawisa ta tafi ta dawo, da sauri ta karba ta wuce toilet ta gwada, ihu tayi abayin lokacinda taga result din, kenan yana nufin tana dauke da juna biyu, wani marayan kuka tasaki tana furta wlh bazan haifeshi ba zubarwa zanyi. Tanagama fadin haka ta fice daga bayin ta dau wayarta takira Mama, tana daukawa tasa kuka tafara zayyana mata abinda tagani, kamar dama Mama tasani dan wannan ranan datazo gidanta ta riga taga alaman hakan, wani irin huci tafara yi tace" bandake ja'irar yarinya ya akayi kika bari har wannan Dan banzan yamiki ciki, lallai yazama dole ki zubar dashi bazan bari ki hada jini dashi ba wlh tab wannan ai zubda girma ne, mugama bori akan bamaso yanzu kuma ace wai haryaci nasara akanmu, toh kijini da kyau gobe gobennen zanzo mutafi asibiti ayi me gabadaya kowa ya huta" ajiyar zuciya Moon tayi dan Dari bisa Dari ta yarda da shawaran Mama tunda itama ba son cikin take ba.

*******
Tun bayan breakfast din datayi batakuma saka wani abu a cikinta ba har maghrib, haka kawai taji batada niyyan girka wani abu dama kuma ita kadai zatayi abunta taci shiyasa bata damu ba. Data tuna fadansu na safe saitaji wani nishadi aranta dantayi nasara akanshi," ai in ba haka kikamasa ba kinaji kina gani zai takeki, mutum sai kace mala'ikan mutuwa fuska a daure kodayaushe, mtscheeew" duk wannan maganan ita kadai takeyinshi amma in daga waje kake zaka dauka itada da wani ne. Mikewa tayi ta shige toilet ta dauro alwala jin an fara kiran sallah. Bayan ta idar da sallah tazauna tana tilawa har aka kira sallan isha'i sannan tamike tayi. Koda ta idar wanka tashiga tafito ta shirya cikin kayan bacci me dan nauyi kasamcewar garin da dan sanyi. Har ta kwanta saikuma ta tuna yanzu fa kusan karfe tara da wani abu amma bedawo ba, dakin ta kalla tace" ohh ni nuwaira daki ma kenan da girma balle kuma gida gabadaya kuma aka barni ni kadai aciki saikace tsohuwar mayya. Yanzu fa ko ihu nayi bame mai jina balle akawo mun dauki" tana cikin magana taji kamar kofar bayinta yayi motsi da sauri taja bargo ta rufe daga kafa har kai( Noor tsoro😂) wayarta ta lalubo ta kasan filo tasa kira'a dan karma taji wani motsi, bai jimaba bacci yadauketa.


Karfe 11 pm yadawo, koda yashiga yasamu komai na falon akunne dan haka saida yabi ya kakkashe komai da komai sannan ya wuce daki. Bayan yayi wanka yayi shirin kwanciya saiya tuno da wani aiki dayake dashi kuma gobe zai koma aiki yasa ya mike ya dau jakar system dinshi yafito falon sama dan yafi zama anan in zaiyi aikinsa. Wuta ya kunna ya zauna akasan carpet ya tankwashe kafa yafara aiki shiyama mance da wata halitta agidan. Wuraren 12:30 ya gama abinda yakeyi ya mike ya kashe wutan falon sannan ya haura sama daidai itakuma Noor tafito zata sha ruwa tana mirtsike idanunta da suke cike da bacci, tana lalubar makunnin wutan kawai taji tayi karo da mutum, ganin zata fasa masa ihu da tsakiyar darennan yayi saurin toshe mata baki da hannunsa, ido tashiga zarowa itadai taji gata ga mutum amma koba'a fada mata ba tasan basamude ne duba da yadda tafin hannunsa ya kusan rufe mata Rabin fuska dan girmansa da fadi. Ahankali ya matsa kusada switch din wutan ya kunna, idanunsu ne ya sarke acikin na juna tare sukaji wani irin Shock, da sauri ta zare bakinta daga hannunsa tana jifansa da harara, rabawa tayi ta gefenshi ta wuce tafita, wani kallo yabita dashi karan kansa besan na menene ba amma iya tsayuwan dayayi da ita wani irin yanayi ne ya ziyarce shi har wani kasala yakeji, adaddafe ya shiga daki. Abu kaman wasa fa Aryan dinku yashiga wani hali na tsananin buqatuwa wadda bai taba jin irinsa ba. Gashi dai Noor bawani arnan kaya ne ajikinta ba amma yadda jikinsu ya hadu lokacin daya rufe mata baki ba karamin tasiri yyi akansa ba. Mararsa ne yaji ya fara kullewa cikin abinda bai wuci five minutes ba abu yafara fin karfinsa, da kyar ya karasa toilet ya kunna wakansa shower bayan ya tube amma still, ya kai kusan ten minutes kafin yaji yadan dawo normal kadan, ahankali ya fito yana dafe mararsa dayaji ta kulle gam ya haura saman gado yayi kwanciyan ruf da ciki. Ahaka baccin wahala ya saceshi yana sauke ajiyar zuciya.

Itakuwa tana zuwa kitchen tasha ruwanta har da guzurin wani a jug dan karta fito takara taddashi kamar dazu. Tana shiga daki ta murzawa kofa key sannan taja bargo nan da nan tashige mota sai garin kano.

Asuba tagari.

Washe gari da sassafe yagama shirinsa harya fito amma baiji motsinta ba, da har kaman zai fita saikuma yadawo dan daga shekaran jiya zuwa jiya ya lura da asuban fari take farkawa tafara tilawa amma yau shiru, gudun kar wani abu yasameta azo ayi blaiming dinsa kawai yasa ya nufa kofar dakinta, kwankwasawa yyi amma shiru har ransa yafara baci yace kodai mutuwa tayi,(kai Aryan yada wannan irin fata haka) da sauri ya murda hannun kofan amma yajita akulle, sake bugawa yayi still shiru nan hankalinsa yafara dan tashi karfa wani abu yasamu yarinyar mutane, da wani irin karfi ya take kofan sai gashi ta budu, acan tsakiyan gado ya hangeta kwance ta kudundune acikin bargo tana mutsu mutsu alamar ba lfy. Da sauri ya karaso ya janye bargon yana cewa" ke lfy, meye haka kinmayi sallan asuba kuwa" kamar ma batasan da shigowarsa ba dan ta galabaita sosai, hannunta ya taba yaji zafi rau kamar garwashin wuta, subhanallah ya furta yadan sunkuyo kozaiji metake cewa danyaga bakinta na motsi, itakuwa jin mutum kusa da ita tayi saurin kama hannunsa tana jujjuya kai tana hawaye, be kara dimaucewa ba saida yaga tafara shidewa tana shure shure, yama rasa mezeyi kawai yaji tafashe da kuka tana ammina zan mutu wayyo cikina, pls a taimakamin mutuwa zanyi. Aryan dayagama rudewa dan betaba ganin haka ba yasa da sauri ya dagata daga kan gadon har zai fita saikuma yatuna wani abu, dawowa yayi ya ajeta kan gadon still tana kuka ya dau wayarsa hannu na rawa ya kira family doctor dinsu Doctor Amina, cikin mintina kalilan takaraso da sauri yamata jagora zuwa dakin Noor. Itama ta tsorata da halin dataga Noor din aciki, babu bata lokaci ta fara dubata, ashema bawani matsala bane, allura ta mata sannan tabata wasu magunguna wadda zatasha inta karya. Oga Aryan na tsaye yana kallon duk abinda akeyi,bayan komai ya lafa can kasan makoshi yace" alhaqina ne ya kamaki, jiya nayi nawa gashi yau kina naki" murmushin gefen baki yayi danshi duk tunaninsa irin abinda yasameahi jiya ne itama yasameta. Doc Amina ta juya ta kalleshi tace yasameta afalo, bayan sun fito tace" bawani abu bane, menstrual pain ne kawai saikuma dan zazzabi daya kamata, so She'll be fine insha Allah, yanzu dai daso samune asiyo mata duk wani abun dazata buqata" kallonta yayi cikin rashin fahimta, murmushi tayi tace"ina nufin sanitary pad da su dark chocolate dan ya easing mata pain" gyada kai kawai yayi sannan yace" yanzu babu wani maganin daza'a bata wadda zai kashe pain din gaba daya,I mean tadena jin zafi aduk lokacin dazai zo mata? Doctor amina kuwa tariga tagano cewa shi baima San kan abun ba tace" toh ai Kaine maganinta since you're her spouse " cikin rashin fahimta yace how? Doc tace" ina nufin Kaine kawai zaka iya warkar da ita gaba daya tama dena jin zafi aduk lokacin dazatayi period ta hanyar raya sunnar manzo" sarai yagane abinda take nufi saikawai ya basar yace shikenan nagode. Bayan ta tafi ya zauna yana tunani, wani irin lalura ne za'ace saita hanyar sex za'a magance shi, wannan ma aiba tsari, toh da kafin suyi aure yasukeyi" tsaki yaja ya mike yadan leka dakin yaga tana bacci dan haka ya fice. Abakin gate din gidansu yatsaya sannan yakira Nana yace ta fito, bayan ta fito yace tashiga motar akwai inda zasu, babu musu ta shigo dama a shirye tafito. Abakin wani supermarket yatsaya sannan ya mika mata ATM dinsa, da alamar tambaya take kallonsa, shikuwa ganin haka yasa yace" ki siyo duk abinda mace ke buqata when it's her time of the month" murmushi Nana tayi ta fito amotar, wato dai Ya Aryan girman kansa bazai bari yasiyowa matarsa pad da kansa ba, itama yanzu kara zata masa amma ba kullum zatana wannan aikin ba dole nan gaba yayi dakansa. Haka tashiga tasiyo abubuwan datasan duk wata mace zata buqata sannan ta fito da Leda a hannunta. Tana shiga yaja motarsa yabar wurin bayan ya aje ta agida ya wuce nasa gidan. Shigowarsa yayi daidai da fitowar Noor daga toilet bayan tayi wanka, beyi tunanin ta farka daga bacci ba shiyasa kawai ya kusa kai cikin dakin. Ihu Noor tayi ganinsa alokacin data kunce towel dinta tana share jiki, shikuma babban gamo yayi wadda yasashi kamewa atsaye, jin ihunta yasashi zubarda ledan dake hannunsa ya fita waje da gudu ya bugo kofa. Itakuwa tsugunawa tayi awurin tawani kame jikinta wuri daya duk kunya ya rufeta, ko babanta bai taba ganinta ahaka ba tun lokacin data fara ajiye kulu akirji amma gashi wani katon yagani a araha. Hawaye kawai taji yana bin fuskarta ya akayi tayi wannan sakarcin wayyo ita Nuwairatu.

Oga Aryan yana fita daga dakin ya sungumi jakarsa na aiki ya fice a gidan da sauri dan jinsa yake kamar in ba fita yayi ba ko ina agidan zai rika hasko masa wannan abubuwan daya gani dazu😂😂😂.

*********
Dawowar su Mama daga asibiti kenan itada Moon bayan sun aiwatar da wannan kazamin zunubin, yo kazami mana ciki da ubanshi na sunnah amma ace dan tsabaragen rashin imani ku zubar dashi. Suna Shiga moon tanemi wuri ta kwanta dan tun lokacin da akayi wannan aikin bata jinta daidai. Magungunan da aka bata tasha sannan tanemi wuri tan kwanta ta bingire da bacci. Agidan zata kwana dan kar Mahmud din ya zargi komai sai bayan ta warke zata koma gida tunda Daddy bayanan yayi tafiya.

********
*Gaskiya Naga korafin marubuta da yawa akan rashin comments,babban abin bakin ciki sai dai kaji ance tnx,babu sharhi ta yadda marubuci zai samu kwarin gwiwar ci gaba da suburbudo muku ci gaba,pls readers ku gyara gaskiya.


COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/23/23, 8:06 AM - Reemah: 🌼MIJIN TACE🌼



REEMAH




PG 33_ 34





Wasa wasa yau kwana hudu kenan Noor da Aryan basu kara haduwa ba tun bayan faruwan wannan al'amarin. Kullum hide and seek suke wa juna, ita bata fita sai taji ya fita daga gidan shikuma baya shigowa saiyaji ko'ina tsit babu alamun ta. Gashi next week zasu koma makaranta ta rasa yadda zatayi kuma Anty Jamila tace saita sanar da mijinta kafin tasa kafanta awaje itakuma harga Allah bataso tahadu dashi tunda yaushe yaushe har an fara wannan wasan banzan toh gara tayi taka tsan tsan dashi maganin kar ayi kar afara.

Zaune yake a office dinsa sai faman juyi yakeyi a kujera yakasa tabuka komai, tun ranar dayayi gamo idanunsa suke hasko masa wannan abubuwan, tundaga ranan kuma kome yakeyi nan da nan zasu fado masa su hanashi natsuwarsa,be taba ganinsu ba tunda yake sai ranan. Inhar yakara haduwa da wannan yarinyar toh tabbas za'ayi abun kunya daga baya kuma girmansa yafadi dan haka ya sauwaka wa kansa wannan jarabar. Yana cikin wannan tunanin shareef yashigo, yakara wani fresh da haske sai wani nishadi yakeyi. Zama yayi amma har lokacin Aryan bedawo daga duniyan tunani ba, buga table din shareef yayi firgigit Aryan yadawo hayyacinsa, dariya shareef yayi harda kyalkyatawa yace" kai ango ango, lallai kanwata ta iya mulki, kaganka kuwa har wani fresh kayi kayi bulbul abunka,yanzu badan na shigo ba haka har za'a tashi ma a aiki baka dawo daga duniyar tunanin masoyiya" wani takarda Aryan ya dauka ya jefawa shareef shikuma ya kauce yana dariya. Toh ya akayi shareef din yasan ita yake tunani, kodai yagani afuskarsa ne. Maganan shareef ne ya dawo dashi lokacin dayaji yace" toh kawai ka koma gida mana, kaga nima yanzu zuwa nayi na fada maka gida zan tafi dan babyna na jirana" yakarasa maganan yana wani farr da ido kamar mace. Haushi abunda yayi ya bawa Aryan toh meyake nufi dashi wato shi irin anyi auren soyayya dinnan shikuma Aryan anmasa auren dole ko. Karar kofa kawai yaji alaman shareef yafita dan bazai tsaya jira harsaiya gama wannan tunanin nashi ba. Kansa ya dira saman table din yace" what's wrong with you Aryan " hhhhh tunda wuri haka Aryan, muje zuwa.

*******
Tunda moon takoma gida taketa jin ciwon ciki kadan kadan harya fara mata yadda bazata iya jurewa ba. Suna zaune da mahmud suna hira wadda kusan shine karfin hiran, dan ita daga umm sai hmmm kawai take cewa. Wani sharp pain taji mararta na mata aikuwa nan da nan tafara mutsu mutsu. Cikin rudewa mahmud ya sungumeta sai mota ba bata lokaci ya danna horn mai gadi ya bude masa gate da gudu ya fita cikin tashin hankali dan moon kuka sosai take tana cikinta. Suna isa asibiti aka kaita emergency aka fara dubata, abinda likitoci suka gani shiya tada musu hankali. Daya daga cikinsu doctor aliyu ya fito yana sharce zufa da handkerchief yacewa mahmud yabisa office dinsa. Cikin sauri ya take masa baya har office din, kasa zama yayi danya kosa yaji halinda matarsa ke ciki, kallonsa doctor aliyu yayi yagane tabbas yana cikin tashin hankali dan haka cikin tausasa murya yace" karka damu yallabai zauna muyi magana" da kyar yasamu yazauna yana jiran yaji mezaice masa, " dama kasan matarka na dauke da juna biyu"? Doctor aliyu ya tambayesa, jin tambayar tazo masa a bazata yayi saurin girgiza kai alaman a'a, ajiyar zuciya doctor aliyu yayi yace" a gsky bazan boye maka komai ba, matarka nada juna biyu amma to our greates surprise bleeding din takeyi yasamo asaline daga abortion din datayi, to ina ganin wadda yamata be kware ba dan akwai wasu part na jikin jariri daya rage shine yake barazanar fitowa, toh maganan da muke maka yanzu ana can ana mata wankin ciki sabida gundun karya illatata" tunda doctor aliyu yafara magana bakinsa kawai mahmud ke kallo amma baya fahimtar komai cikin maganganunsa tun bayan ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login