Showing 78001 words to 81000 words out of 99210 words
ya faskara dan ko ajikinta,bama ta zama inda suke. Kusan four days kenan da tafiyar Abba amma kullum sai anyi fada tsakanin Lubna da Nana danba raga mata Nana keyi ba duk da ta girme mata a shekaru nesa ba kusa ba, badan wasan datakeyi amakaranta ba da yanzu ta graduating harma tafara aiki.
Cikin kwanakinnan Aryan yasa Noor agaba da tambayoyi da suka shafi Ammi, hakan ba karamin tayar mata da hankali yake ba,idan yayi mata alqawarin bazai kara ba ,the next day zai dauko same topic, sam Noor taki fada masa abinda Mama tayi. Tayi rantsuwa ita kadai zata fighting battle dinta, wannan fadan tsakaninta ne da Mama ba ruwan kowa ciki kuwa harda Baby love dinta. Shiko Aryan tunda yagane akwai abinda Noor ke boye masa yasa yafara bincike har ya hiring private investigator, sannan shima yacigaba da bincike akan Mama, ga kuma sirrinta daba kowa yasani ba sai ita dashi dakuma Allah wadda har yanzu babu wadda yasanarwa.
ISTANBUL TURKEY
Awani katafaren gida mai tsananin kyau yaji komai na jin dadin rayuwa ya hadu sosai Masha Allah. Acikin garden na hango wata mata fara sol tana sanye da turkish gown maroon colour ta sake gashin kanta wadda yasauka har waist dinta, tanada matsakaicin jiki shape dinta mai daukan hankali, wasu fararen tattabaru take zubawa tsabar shinkafa inda suketa rububi suna ci. Wata karamar yarinya ce kyakyyawa zata kai kimanin shekaru tara, kamanninsu daya da wannan matar da alama yarta ce ta fito da gudu tana kiran sunan Ammi, juyowa matar tayi amma bishiyar lemu dake garden din ya hana na gano fuskarta, yarinyar sanye take da school uniform da alama dawowarta kenan daga makaranta, cikin wani irin daddadan murya tace" welcome back my little princess " chuckling yarinyar tayi ta ware hannayenta alaman mamanta ta dauketa, haka kuwa akayi daukarta tayi suka wuce ciki. Na jima tsaye a wurin na dauka zasu fito amma har na gaji da tsayuwa na fice abuna batare da gano fuskar daya daga cikinsu ba.
****************
Yau zasu koma makaranta dan haka da sassafe suka gama shirinsu tunda tare zasu fita. Wayar Aryan ne yayi ringing ummi ce ke kiransa, bayan ya dauka suka gaisa sannan suka danyi magana kafin ya katse kiran. Juyowa yayi ya kalli Noor dake gyara jakarta yace" honey zamu biya gidan ummi mu dau Nana driver dinta yayi tafiya " gyada kai kawai Noor tayi sannan ta kammala shirinta suka fito. Har suka iso gaban gate din gidan suna jiran Nana amma shiru bata fitoba, sauka sukayi su biyun suka shige gidan. Afalo suka tadda fada ne ya kacame tsakanin Nana da Lubna harda dambe, Nana badai karfi ba, Lubna ta daku harta godewa Allah. Suna jin sallamarsu Lubna ta dago suka hada ido da Aryan dake bin kowa na falon da kallon mamaki. Bai san suna gidan ba dan babu wadda ya sanar dashi kuma tun da suka dawo daga Adamawa bai kara zuwa gidan ba sai yau. Da gudu lubna taxo ta shige jikin Aryan tana kuka batama lura da Noor dake tsaye agefensa ba. Shock ma yahanashi motsawa, baiyi expecting haka ba. Wani irin kukan kura Noor tayi ta bangaje Lubna daga jikin Aryan tana huci, a sukwane ta nufi Lubna dake kwance akasa ta haura ruwan cikinta tafara kikkifa mata mari left and right, da sauri Anty Aisha da ummi suka karaso wurinsu, sunyi sunyi su dage Noor daga jikin Lubna amma sun kasa. Aryan dake tsaye ya kame awurin yama rasa me zaiyi yaji muryan ummi tana kiran sunansa, firgigit yadawo sense dinsa ya matso inda Noor take ya sanya hannunsa acikinta ya dagota sai wutsil wutsil takeyi da kafa tana cewa abarta taci kaniyar yar iska, sai sambatu takeyi kamar me shafar aljanu. Lubna da tun tuni ta sume sabida wani one blow seven die din da Noor ta bata a kai, kuka Anty Aisha takeyi tana cewa Noor takashe Lubna, shiko Aryan dakin Ummi ya wuce da Noor wadda still bakinta baiyi shuru ba. Suna shiga ta kwace jikinta daga rikonsa tana zabga masa uban harara tace" wlh daka barni da yar banza dani take zancen, ni dama tunda sukazo gidana itada mamanta nasan ba alkhairi bane sudin" ta karasa maganar tana fashewa da kuka abun yayi mata zafi, yaza'ayi wata ballagaza tazo ta rungume mata babynta agabanta. Lallai ta taro match. Ganin yadda take kuka kamar ana yanka naman jikinta ya sanyashi matsowa kusa da ita ya rungumota amma ta fizge jikinta daga nashi shima ta hau balbale masa ruwan masifa saikace shidinne ya rungumo Lubna. Shiyama rasa wani karfin haline yasa Lubna rungumeshi, ko dai da biyu ta yi hakan sabida ta batawa Noor rai, aiko in hakane saiyayi maganinta. Duk yadda yaso fahimtar da ita, Noor fa tace sam batasan wannan zancen ba, wai ai inda baiso ba, bangajeta zaiyi lokacin data rungumeshi, daga karshe ma tace ya fita ita bacci zatayi tama fasa zuwa makarantar. Haka yafita jikinshi asanyaye, koda yasauko babu kowa afalon, can cikin guest room yaji muryan Anty Aisha tana surfe ummi da ruwan bala'i, da sauri yashiga dakin. Lubna na jingine da head board din gadon tana kallon mahaifiyarta tana yiwa ummi fada kamar itace ta haifeta, gefe kuma Nana ce wacce ke tafarfasa sabida ummi tahanata maidawa Anty Aisha martani. Rai a matukar bace ya karasa shigowa dakin, ga batawa babynsa rai dasukayi, ga kuma cin fuskar da akeyiwa mahaifiyarsa acikin gidanta. Suna ganinshi Anty Aisha ta yi tsit Lubna kuma tasha jinin jikinta dan ta tuno abinda tayi dazu, harga Allah bada gangan tayiba, kawai dai bakin wahalan datasha ahannun Nana ne yasata guduwa zuwa wurinsa neman ceto kuma bata lura da Noor dake tsaye agefensa ba. Wani kallon takaici yake binsu dashi inda Ummi taja hannun Nana suka bar dakin ranta duk ajagule. Nuna Anty Aisha yayi da yatsar hannunsa kamar wata tsararshi cikin kakkausan murya yace" before sunset banaso naga kafar kowannenku cikin gidannan, bansan da wani dalili kuke zama cikin gidan ba amma ina mai tabbatar muku idan na dawo na sameku bazaiyiwa kowannenku dadi ba" yana gama fadin haka ya sauke idanunsa kan Lubna ya harareta sannan ya juya ya fice. Tsaki Anty Aisha taja wadda da Aryan yana wurin ko motsa bakinta bazata yiba tace" aikin banza, bari inga abinda ya isa yayi, nida gidan dan uwana wata shegiya bata isa tasa nabari ba," ita dai Lubna batace kala ba duk tabi ta damu hukuncin da Aryan zai yanke in ya dawo ya samesu, ina zasu tafi yanzu bayan kowa ya gujesu tunda yagane cewa tana dauke da ciki.
Acan dakin Ummi kuwa, yana fita adakin Noor tabaje saman gadon ummi tafara sharar baccinta kamar ba ita tagama balbali ba. Ummi da Nana suka shigo dakin inda takeyiwa Nana fada akan raini data keyiwa Anty Aisha da Lubna, kamar zata fashe da kuka tace" ummi nikam gsky haqurinki yayi yawa, ana cutarki ne, idan ita hata girmama mahaifiyarta ba yaza'ayi ni in girmamata" juyawa tayi da gudu ta fice daga dakin ta wuce nata, ajiyar zuciya ummi ta sauke tashige toilet still Noor na bacci ba ta farkaba.
Kusan sau goma yana kiranta amma ba'a picking ba, duk yabi ya damu, baiyi tunanin har haka take kishinsa ba, murmushi yayi lokacin daya tuna irin super dindatayi da dira akan Lubna Allah nema ya takaita al'amarin da babu abinda yafaru. Still yakara kiranta amma bata dauka ba, tunaninsa baikai ga cewa bacci takeyi ba. Yana cikin wannan Shareef ya shigo yana waya da Na'ima yana 6a66aka dariya da alama wani abun dariya take fada masa, yatsina fuska Aryan yayi, shi yana cikin halin damuwa babynsa na fushi dashi ga wani gario anan sai dariya yake kamar zautacce. Bayan ya gama wayar ya zauna suka gaisa sannan suka fara tattaunawa akan wani babban project dasuke shirin farawa. Karar shigowar sako yaji awayarsa amma baibi takanshi ba har suka gama maganarsu da Shareef saikuma ya mance bai duba sakon ba, ya mike ya dau suit dinsa ya fice daga office din. Parking lounge ya nufa ya dau motarsa yabar harabar companyn.
Daddy ne kwance akan gadonsa yana waya, sai zabga uban murmushi yake da alama wadda yake waya dashi ba karamin mutum bane awurinsa kuma da alama macece. Jin motsin mutum yasashi saurin katse wayar ya maida kasan pillow dinshi yayi kamar yana bacci, lekowa Mama tayi tana kallonsa bata karasa shigowa dakin ba, tabe baki tayi tace"mutum kenan kullum yana kwance safe rana dare baima da lokacin matarsa" juyawa tayi ta banko masa kofar dakin tana jan guntun tsaki. Bude idanu Daddy yayi yayi wani irin Murmushi wadda shi kadai yasan ma'anarta. Fidda wayarsa yayi daga karkashin pillow, wani hoto ya tsurawa wa ido yana murmushi yace" I missed you, komai ya kusa zuwa karshe insha Allah ".....
TOH FAH
WACECE WANNAN MYSTERIOUS MATAR DA YARTA???
ALLAH YAKAIMU GOBE RAIDA LAFIYA.
COMMENT AND SHARE
REEMAH✍️
11/1/23, 8:16 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j
🌼MIJIN TACE🌼
REEMAH
PG 57_ 58
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯S͟W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯
This page is dedicated to Mom Sani. Zanyi missing dinki yar uwa. Allah ya sada mu cikin alkhairi mutuniyar arziki.
Kamar yadda Aryan ya fada, karfe biyar motarsa ya danno kai cikin gidan ummi. Su Anty Aisha sunajin parking din motarsa suka fara kame kame, sun san halin Aryan sarai, bawani mutunci gareshi ba. Yana shigowa direct dakinsu ya nufa, ko sallama baiyi ba ya shiga dakin dasuke. Wani irin kallo ya watsa musu nan da nan ido ya raina fata. Lubna da gudu ta mike ta nufi toilet zata shiga, da azama yabi bayanta ya cafko gashin dokinta, wani ihu tayi saboda ya hada da suman kanta. Jawota yayi ya hurga ta tsakinyan dakin, tangal tangal tayi zata fadi da Sauri Anty Aisha ta kamota gudun kar wani abu ya sameta asirinsu ya tonu.
Noor na dakin ummi tun da taji karar motarsa tafara zagaya dakin tana jiran taji shigowarsa yazo ya bata haquri amma har kusan ten minutes ko motsinsa bata jiba kuma tasan ya shigo cikin gidan, basai Noor tafara kumbura ba. Fitowa tayi daga dakin ummi daidai ummi ma tafito daga dakin Abba sukaci karo," Noor lfy ina zaki"? Ummi ta tambayeta, sakin fuskarta tayi karta gane wani abu tace " Ummi dama kitchen Zani" kamo hannun ta tayi suka sauka kasa, anan suka fara jiyo hayaniya a guest room inda su Lubna suke. Basu gama karasowa ba saiga Aryan ya jawo hannun Lubna ya hurga ta waje ragabbb ta fado tsakiyan falon, da Sauri ummi ta taho wurin Aryan ta rikeshi tana masa magana kasa kasa, Anty Aisha tafito fuuuu daga dakin sai sakin ashar take tana bombomi. Sallama sukaji abakin kofa, Noor ce dake tsaye tana kallonsu sai faman kyalkyala dariya take ta hango Abba tsaye abakin kofa shida wani mutum batasansa ba. Anty Aisha dake masifa ta juyo ta kalli kofa, wani uban salati ta saki ta sanya hannu akai batasan lokacin data juya zata shiga daki ba, Aryan yayi saurin shan gabanta. Daddyn Lubna ne ya taho tareda Abba. Takaici tab kwance afuskar Abba, ga tsananin bacin rai kamar ya hadiye zuciya atake. Bai ce dasu uffam ba ya karasa shigowa falon ya zauna akan cushion ya cire hularsa yana fifita kansa. Daddyn Lubna kuma ya karaso inda Lubna ke zaune dirshan akasa sai faman share zufa take. Ita duk damuwarta ba mutanin falon bane face Aryan, in yaji abinda ta aikata ba makawa nan take zai rufeta da dan banzan duka. Ummi ce ta wuce kitchen ta fito da ruwa da drinks akan tray, akan center table din falon ta ajiye shi, ruwa ta tsiyaya a cup ta mikawa Abba, hannunsa na kerma ya karba, bai iya kaiwa bakinsa ba kawai ya sakeshi akasa, kansa ne ke wani irin bugu kamar zai tarwatse, kanwarsa uwa daya uba daya ta gama dasu, ta lalata sunan family dinsu. Kunyar Daddyn Lubna duk ya mamayeshi tunda ya sanar dashi abubuwan da suka aikata. Bai tsaya a iya nan ba, hatta zamansu a gidan honorable duk babu wadda baisani ba, ga kuma cikin Lubna wannan ma bashi bane ya dame shi ba tunda yasan halin Lubna, amma Anty Aisha gode gode da ita ace tana aikata zina? Wa iyazubillah. Aryan da Noor sukayi saurin zuwa wurin Abba suna tambayansa lfy, Anty Aisha da Lubna sun gama shan jinin jikinsu babu makawa asirinsu yagama tonuwa. Daddyn Lubna ne ya fara magana" assalamu alaikum, Ku gafar ceni mun zo batare da sanarwa ba, naga kamar Alhaji yana cikin wani yanayi dan haka nizanyi magana game da abinda yake kasa amma kafinnan muna da baki da zasuzo" yana gama magana wayar Abba yayi ringing, mikewa yayi ya fice daga falon, minti kadan sukaji sallaman Abba gefensa kuma Baffa ne da Alhaji Jibril mai bin Abba. Lallai akwai babban abinda yafaru, basuyi tsammanin ganin Baffa agidan ba musamman ma da basu dade da dawowa daga Adamawa ba. Gaba daya in ka kalli fuskokinsu zaka gane cewa ba lfy ba. A three seater cushion Baffa da Abba suka zauna, two seater kuma Alhaji Jibril neda Daddyn Lubna, Aryan kuma na zaune a one seater. Baffa ya bukaci kowa agidan ya taho falon. Babu musu kuwa duk suka nemi wuri suka zauna,Noor kuma ta haye sama ta tasshi Nana daketa baccin huce haushi. Saukowa sukayi suka nemi wuri kusa da kafan ummi suka zauna. Anty Aisha da lubna sun kame a tsaye sun kasa zama, wani tsawa baffa ya dakawa Anty Aisha ba shiri ta zuba akasa, tun ba yau ba suna tsananin tsoronsa musamman ita Anty Aisha, Lubna ma ta nemi wuri ta zauna kusada mahaifiyarta. Baffa ne ya fara magana, duk abinda yafaru tsakanin Daddyn Lubna da Anty Aisha na sakinta dayayi da kuma cikin dake jikin Lubna da kuma zamansu a gidan Honorable Musa duk ya fada, babu abinda ke tashi sai salatin da ummi keta zubawa, Nana da Noor kuwa sai zabga murmushi suke, wannan lamari ba karamin dadi yamusu ba, ita Nana tana murmushin asirinsu ya tonu, Noor kuma tana murmushin cikin dake jikin Lubna, ko ta halin 'ka'ka ai tasan Aryan bazai taba kallonta ba, dacan ma tana kishine saboda bata san halin lubna ba. Sosai Anty Aisha ke kuka kamar na Allah amma babu wadda kukan ya taba, taso tayi musu akan alakarta da Honorable amma Abba ya katse ta ta hanyar playing discussion dinsu dashi da Honorable a wayarsa, abun ba dadin ji inji ustaz. Bayan Baffa yagama magana sannan ya yanke hukuncin cewa abinda addini ya ce ayiwa duk wani mai zina shi za'ayiwa Anty Aisha da Lubna, if possible kuma in aka kama wannan samarin da Lubna ke hulda da su za'ayi filing case akansu tunda ba lallai iyayensu su yadda ayanke wa yayansu hukuncin da addini ya ce ayiba. Shikuma Honorable sun barsa neda Allah, danko duk magidanci mai zina hukuncinsa kisa ta hanyar jifa, toh ammafa a wannan kasar duk wannan ba damuwa bace, sai aga magidanci na zinace zinace da yayan mutane amma instead ayi masa hukuncin daya dace saima abasa goyon baya. Tun daga nan gidan duniya Allah zai fara nuna masa sakayyan abinda ya aikata. Itakuma Lubna Baffa yace saita haife abinda ke cikinta, kuma bayan ta aihu za'ayi DNA test agwada samarinta wadda jininsa yazo daya da abinda ta Haifa za'a daura mata aure dashi,kuma bayan ta aihu tas za'a zaneta bulala dari kamar yadda shari'a yace ayi tunda ita budurwa ce. Anty Aisha kuma zai tafi da ita can Adamawa, acan za'a yi mata hukuncinta na jifa har lahira(wa iyazubillah, Allah ka tsare mana imaninmu). Wani irin ihu Anty Aisha ta kurma nan da nan tafara bori akasa kamar mai sabon hauka, bawai batasan hukuncin dake kanta bane a matsayin matar aure mazinaciya, saidai tsoronta jifannan nanne daza'ayi mata har lahira, wani irin radadi ne zataji kafin rai yayi halinsa. Rokonsu tafara yi tana cewa laifin Lubna ne data hadata da honorable (kuji fa). Sai yanzu bakin Lubna ya budu , kallon mahaifiyarta tayi da jajayen idanunta tace" amma mommy Allah ya isa tsakani na dake, wlh nikam banyi sa'ar uwa ba, kaicona da halin ki mommy, duk fa laifinki ne, tun ina shekara goma sha hudu kikafara introducing dina to porn videos kikace karna baki kunya a idanun mijina gara na fara koya tun yanzu, da banyi aure da wuri ba kuma ni nasan inada karfin sha'awa shine nafara bin maza, ko dana fada miki sadiqboii ya kawar da budurcina ai cewa kikayi ya naji abun da dadi ko akasin haka, banyi mamaki ba saboda nasan dama tuntuni kina burin nasan maza, ko lokacin danaji wa'azi nayi kokarin barin wannan abun na gagara saboda na saba, ko sau daya baki taba tsawa tarmun ba saima bani goyon baya dakike shine yau zakice laifina ne, Allah ya isa wlh Allah ya isa" kowa afalon jikinsa yayi sanyi jin furucin Lubna, tabbas Anty Aisha ba uwa ta gari bace, babu da ko 'ya aduniya dazatayi addu'ar samun mahaifiya kamarta. Sai yanzu Lubna tasamu daman yin kuka, wani irin kuka mai radadi takeyi, saida kowa yaji tausayinta banda Aryan, Noor kuwa itama jijikinta yayi sanyi, dama batasan labarinsu ba sai yanzu. Aryan ne farko ya mike yabar falon yakoma garden din gidan yacigaba da latsa wayarsa,message yayiwa Noor amma dayake wayarta baya tare da ita bata gani ba. Haka taro ya tashi bayan Alhaji Jibril ya rufe taron da addu'a, su Baffa suka wuce hotel shida Alhaji Jibril inda gobe zasu wuce Adamawa da Anty Aisha, Lubna kuwa mahaifinta ya nemi alfarmar zai koma da ita gidansa acan zata aihu sannan ayi aurenta da uban dan dake cikinta, Anty Aisha daketa sambatu kuma aka koreta zuwa dakin dasuka sauka kafin gobe. Ummi jiki asanyaye ta mike ta haura sama, Nana ma duk tausayin Lubna takeji, ashe duk ba laifinta bane laifin mahaifiyarta ne. Sai falon yarage daga Noor sai Abba da ya dafe kansa yanajin wani irin radadi azuciyarsa, kenan hukuncin kisa ya hau kan tilon kanwarsu, inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Ahankali