Showing 87001 words to 90000 words out of 99210 words

Chapter 30 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8203

iya tsugunawa ta dauko takardar saboda girman cikinta.Kurawa takardar ido tayi, an masa ado da flowers masu kyau, haka kawai ta tsinci kanta da sha'awar bude takardan, tana budewa taga hoto aciki amma an kifeshi to the other side, bata bude hoton ba sakamakon hand writing dinsa data gani a page din, handwriting dinsa nada matuqar kyau da daukan hankali kamar typing akayi ba rubutu ba, kalaman soyayya ne wadda a saman page din an rubuta sunanta aka drawing love da flowers, takardan kansa kamshin turarensa yake. Bayan ta gama karatun ta dau hoton tana dokin ganin hoton wanene acikinta, daram damm dammmm haka taji zuciyarta ta buga, kamar amafarki take ganin hoton Ammi, cikinta ne taji ya murda mata sosai batasan lokacin data saki kara ba, Aryan dake toilet yafito da sauri dagashi sai shorts, yana karasowa inda take tsugune idanunsa yakai kan hoton dake hannunta, dafe kansa yayi yace"YA ILAHI" har wani rawa jikinta keyi kamar mazari, nan da nan kuma tafara fidda numfashi sama sama da alama tafara fita hayyacinta, tsaab mutuwar amminta yadawo mata sabo fil, fuskar amminta lokacin datake mutsu mutsu akasa tana neman agaji har numfashinta ya tsaya cak komai ya dawo mata, cikin fitar hayyaci tafara ambaton"ammina ammina, Ya Aryan ammina" tuni kuma ta fashe da kuka harda jijjiga, Aryan fa lokaci guda kuma yabi ya rude ya susuce, tsoronsa kar wani abu ya sameta da kuma abinda ke cikinta, da sauri ya sungumeta zuwa kan gado, sannan ya dau jallabiyarsa dake kan sofa ya sanya, hijab ya dauko ya samata ya dau key din motarsa suka fice daga dakin. A rude ya ke saukowa daga step, baima san step biyu yake tsallakewa at a time ba, back seat din motarsa yasata yayiwa motar wuta yakama hanyar asibiti, wani wawan driving yakeyi hatta mutane kauce masa suke, inda yasan halin dazata shiga kenan in taga hoton Ammi da bai yi sakacin barin hoton hakaba, yana isowa asibitin yafito da sauri yana kwalawa nurses kira, attendants ne suka fito suna gungure gado me tyre, aguje yabi bayansu, Noor fa kaman wasa ta gama galabaita ga kuma cikinta dake wani irin juyawa, abun ya hadu mata biyu, kirjinta sai sama da kasa yake alamun dambe take da numfashin tana kokarin fuzgoshi, bayan an shige da ita emergency room wata nurse ta dakatar da Aryan kafin ya yarda ya tsaya awaje sai kai da komowa yake, duk wadda yagansa alokacin saiya tausaya masa, karfa wani abu ya sameta, she's just seven month pregnant, inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Yana juyawa yayi turus da Daddy dake rike da hannun wata yarinya mai tsananin kama da Noor, kuma tabbas yaga hotonta tareda Ammi kenan suna nan kusa dasu kenan, baigama tunani ba ammi tafito daga wani consultation room fuskarta dauke da damuwa, zufa ne ya shiga tsatssafowa daga gefen fuskar Aryan, kwalla na kwance acikin idanunsa, Daddy yayi mamakin ganinsa, baima san yadda zai fara tambayarsa meyakeyi a nan ba gudun kar Ammi taji abu ya baci, shidai Aryan kwata kwata ma ba wannan ne a gabansa ba, yasan Daddy bazaiso suyi maganar anan ba tunda shima a tunaninsa Aryan ma baisan yasan cewa Ammi na raye ba. Ita kam Ammi tana ganin Aryan sai nata damuwar ya kau tausayin halin data gansa aciki ya kamata, bata taba ganin ingarman namiji kamarsa ya shiga irin wannan hali, lallai koma wani irin abu ne toh babba ne. Suna cikin kallon kallo dasu Daddy doctor tafito daga kofar da Aryan yabawa baya yana facing su Daddy, da sauri ya juya Yana kallonta, zufa duk ya rufeta itama duk da Ac din dake dakin, " Mr Aryan, gsky akwai matsala" cikinsa ne yayi kulululu jin wannan furucin na doctor, hawayen dake makale a cikin idanunsa ne yasamu daman gangarowa, tausayinshi duk saiya kama mutanen dake wurin," your wife is in a serious condition, her blood pressure is rising, ka guma premature labour ya kamata" ba Aryan kadai ba hatta Daddy saida ya girgiza dajin maganan doctor din, meyayi zafi haka da Noor ta shiga wannan halin, shine tambayar dake yawo a zuciyar Daddy, zubewa yayi on his knees agaban doctor din yana hawaye kamar karamin yaro labbansa na kerma alaman yanaso yace wani abu" plss doc, save my wifey, she's my life ,I iii can't live without her plsssss" Ammi dake tsaye saitaji jikinta yayi wani irin sanyi, haka kawai taji zuciyarta na dukan uku uku, zataso taga wanene wannan matar tasa, hannu doctor tasa ta dafe kafadar Aryan tace" don't worry,she's gonnan be OK, yanzu dai we can't live her to give birth herself, dole ne kawai mu operating dinta to avoid further complications" a yanzu babu abinda yafi buqata kamar ran matarsa, koda kuwa zai rasa twins dinsa ne yasan Allah ne me bayarwa kuma zai basu wasu masu albarka. Mikewa yayi still yanajin kafarsa na shaking, nurse ce ta kawo wani paper na information din operation din da za'ayiwa Noor din, hannu na rawa ya signing papern, nan da nan aka fara shirya Noor zuwa dakin theater, Daddy da bai iya tsayuwa awurin ba ya shige toilet ya fashe da kuka kamar karamin yaro, meke shirin faruwa ne, suna cikin jarabawa musamman shi, yanzu idan Ammi ta hadu da Noor cikin wannan halin ya zaiyi, mezaiyi ya fahimtar da ita, Ya Allah.

Aryan na tsaye har aka fitar da Noor akan gadon asibiti an canza mata kaya zuwa wani uniform blue daidai guiwarta, tana kwance flat akan gado idanunta akulle, tayi wani fari fat an sanya mata oxygen to normalise her breath, yana ganinsu ya iso gefen gadon ya kamo hannunta, duk da idanunta ba a bude yake ba amma kamar tasan shine, damtsen hannunsa ta kama da karfi sosai, hannun yayi wani sanyi, gashi yanzu hoto kawai na shirin daukar ran matansa inaga kuma sun hadu ido da ido, fatarsa kawai shine ayi mata cs din lfy, Ammi da sunaina sun shiga wurin Doctor ana duba sunaina saboda ciwon mara daya addabeta tun jiya da daddare, ashe period dinta ne,irin yara masu fara menses da wurine. Basu fito ba har aka shige da Noor dakin theater,wani kujera ya samu abakin kofar ya zauna ya dafa kansa dake masa ciwo sosai. Daddy ma yafito idanunsa duk sun kumbura sunyi ja abunka da farin mutum har fuskarsa tayi jaa,bawan Allah. Zama sukayi akujera daya da Aryan babu mai cewa uffam. Ko lokacin da su Ammi suka fito, sunaina kadai aka kai gida, itakuma Ammi ta zauna anan asibiti, duk yadda Daddy yayi da ita ta tafi amma ta kiya, tace saitaga matar wannan matashin, babu yadda ya iya haka ya kyaleta, zama tayi kusada Aryan tana masa magana kasa kasa, jiyake kamar Noor dinsa ne ke magana saboda muryarsu Sak iri daya, shidai baice komai ba, addu'a kawai yake azuciyarsa. Lokacin sallan zuhr yayi still basu fito daga operation room dinba. Hannunsa Daddy yakama kamar karamin yaro suka tafi masallaci, basu dade da tafiya ba doctor ta fito tana nemansa, Ammi ce ta mike tayi magana da ita,"are you her mum" doctor dinta tambayeta, batayi tunanin komai ba tace ehh,nodding kai tayi tace" dama jini muke buqata, ban sani ba ko blood group dinku yazo daya da nata, are you O- "? doctor din ta tambayi Ammi, da sauri Ammi ta gyada kanta alamar ehh, what a coincidence, bata Santa ba amma ikon Allah jininsu yazo daya, basu bata lokaci ba aka gwada jinin, within fifteen minutes aka debi jininta, su Aryan sundawo basu ma nemi Ammi ba, babu wadda yake hayyacinsa dagashi har Daddy. Can cikin theater kuwa anyiwa Noor alluran pain relieve, amma ko ajikinta sai kiran Aryan take, kowa na mamakin wannan soyayyar dake tsakaninsu, taki natsuwa sai juyi take da kafarta ita lallai akira mata Ya Aryan dinta, wata nurse ce ta fita ta sameshi awaje yana kai da komowa, apron da hulan theater ta mika masa ya sanya suka shigo tare, idanunta na kan kofa tana ganinsa tafara miko masa hannu tana Baby love, ta basa tausayi duk ta galabaita ta fita hayyacinta, ba tareda bata lokaci ba aka fara mata aikin, hawaye ne ke gudu a kumatunsa ganin yadda ake fede matarsa ba imani injishi😂😂, baby daya aka fara fiddawa dan karami dashi fari tass da sauri aka nadeshi cikin towel wata nurse ta karba, dayan babyn aka fitar shima baby boy kamar wancan girmansu daya in akwai bambamci ma kadan ne, fari tasss Masha Allah, kamar wancan ma wannan aka nadeshi cikin towel, aka dinke Noor wadda by now jikinta yayi lakwas. Aryan yama rasa mezaiyi, farin ciki ko akasin haka, yana farincikin successful operation din matarsa, ga kuma bakin cikin halinda take ciki. Tsaf aka gyara babies din aka sanya su cikin incubator duk da sunada dan girman su daidai gwargwado, at least kowannensu yana weighing 2.3kg, Noor batayi wasa da abinci ba ai dole yara sufito da girma wannan inda sun kai watanninsu ai dole nema ayimata cs dan bazata iya aihuwa dakanta ba. Itama aka gyarata aka kai VIP room na hutu kamar dakin amarya komai tsab tsab. Daddy dake waje da Ammi bayan ta fito daga dakin da aka debi jininta sunyi tsuru tsuru suna jiran afidda Noor daga dakinta. Kiran Ammi akayi awaya ta fita lokacinne kuma aka fitar da Noor daga theater, da sauri Daddy yasa aka shige da ita kafin Ammi ta dawo. Da kyar Daddy ya lallaba Aryan ya koma gida yayi wanka ya canza kaya he looks tattered. Can Ammi tadawo tace" naga yaron ya tafi an fitar da ita ne"? Gyada kai Daddy yayi, sujudush shukur Ammi tayi tana godiya ga Allah, taso shiga dakin amma Daddy yaki yace doctors sunce tana buqatar hutu, haka ta haqura ta ce zata tafi gida amma anjima zata dawo.

Aryan kuwa yana isowa gida yayi wanka sannan yasamu ya dan huta, wayarsa ce tafara ringing yama mance yabarta agida. Har kusan ten missed calls ummi tamasa dan dama haka takeyi, kowani awa daya take kiran Noor taji ya lafiyar jikinta, toh data kirata dazu ba'a daga ba yasa hankalinta tashi musamman kuma data kira Aryan har ten missed calls shima bai daga ba. Yanzu ma data kirashi tana tunanin zuwa gidan ne in bai daga ba amma kuma Alhamdulillah sai yanzu ta sameshi, cikin tashin hankali take tambayarsa lfy, bai boye mata komai ba ya fada mata abinda ya faru amma banda maganan Ammi, tundaga waya tafara masa fada akan meyasa bai kirata ba tun kafin su tafi asibiti har saida aka gama komai, ummi bata san cewa shima ba'a cikin hayyancinshi suka tafi hospital din ba. Nan da nan labarin aihuwar yafara zaga dangi na nesa dana kusa. Su Anty Jamila kan kace me suna asibiti amma anki barinsu suga babies saidai Noor itama din saidai abakin kofa zasu tsaya dan ba'ason hayaniya. Aryan ma yanzu ya dawo asibitin, kwata kwata bashi a hayyacinsa Ummi dataso yimasa fada insuka hadu a asibitin saikuma ta fasa saboda ganin yanayin dayake ciki. Suna wannan yanayin, labari ya iskosu Lubna ma ta sauka tahaifi danta namiji kuma suna lfy, anyimata Allah ya raya amma babu wadda yaje duk suna nan ana dokin ganin twin babies. Babies din are doing fine ma kamar ba bakwaini ba, ana sa ran nan da kwana biyu ma a ciresu a kwalbar in mahaifiyarsu ta farka kuma babu damuwa ana iya sallamansu.

Wuraren karfe bakwai bayan maghrib Daddy na asibitin duk suna zaune a agaban dakin dasu twins din Anty Jamila dasu Ummi dasu Nana su Ya Shareef su Na'ima duk suna zaune wasu suna tsaye har yanzu Noor bata farka ba. Sallama sukaji gaba dayansu suka dago suna kallonta, rike take da basket din ruwan zafi ga su bread da kayan tea, Daddy salati yafara a zuciyarsa, shikenan magana ya kare, Anty Jamila zumbur ta mike tana murtsuke idanunta, ita kanta Ammi dataga Anty Jamila awurin sai ta rude, su Ya Shareef kowa bakinsa abude yake kallon matar dake gabansu, Aryan duk wannan ba shine agabansa ba, iyanzu hankalinsa yafara tashi meyasa har yanzu Noor dinsa bata farka ba gashi anki barinsu su ganta, bini bini ya mike yana lekata ko ta farka. Anty Jamila ragab ta samu wuri ta zauna tana ambaton inna lillahi wa inna ilaihí raa ji uun. Sallallami kawai ke tashi from every angle, Ammi ta karaso inda Anty Jamila ta zube ta riko hannunta, a tsorace ta fizge hannunta dan har yanzu bata yarda da abinda idanunta ke ganemata ba, Hanan da Hanifa suka taso zuwa inda su Anty Jamila ke zaune, dafa Ammi sukayi dukkansu biyun idanunsu sun cicciko da kwalla, mikewa Ammi tayi ta rungumosu ajikinta sai suka fashe da kuka, babu mai rarrashin wani, Anty Jamila ma ta mike ta rungumesu atare sai suka cigaba da kukan. Ummi da Nana na tsaye suna kallon ikon Allah, kenan ammin Noor tana raye,wani iko sai Allah,da sauri Aryan dake tsaye ajikin kofar dakin Noor ya juyo yana kwalawa nurses kira akan ta farka, mutanen dake wurin kowa ya juya da sauri zuwa kofar dakin, nurse da doctor ne suka shiga dakin, kowa na lekenta ta kofa masu farinciki nayi masu hawaye nayi, Ammi ta kosa taga wacece aciki, acan ciki kuwa, Noor ta farka amma ba'a bari ta mike ba saboda aikin dake jikinta sai ta releasing air kafin tafara motsawa, suna fitowa aka basu daman su shiga amma two at a time, Aryan bai bari ta karasa magana ba har yana bangajeta da sauri ya kusa kai ciki, Noor ba ganinsa ta fashe da kuka, rungumeta yayi yana jin wani sanyi, sai yanzu yakeji kamar an sauke masa wani gamu a zuciyarsa. Kuka takeyi yana bubbuga bayanta yana rarrashi, sauran mutane awaje sun kagu su shiga su ganta amma Aryan baima da niyyar fitowa, Daddy bayaso Ammi ta hadu da Noor yanzu gudun abinda zai biyo baya. Kusan thirty minutes kafin Aryan ya fito, su Anty Jamila da ummi suka shiga, haka suka dinga shiga suna fitowa kafin daga karshe Daddy shima ya nufi hanyar shiga, ga mamakinsa sai ga Ammi abayansa itama zata shiga, ya riga yasawa ransa komai yazo karshe dan haka ba tareda musu ba suka shiga tare. Noor na kallon kofar,Daddy kawai ta gani bataga matar dake bayansa ba, har ya iso bakin gadonta ta kafeshi da gajiyayyun idanunta, ahankali Ammi tafito daga bayan Daddy, suna hada ido da Noor kowannensu yaji zuciyarshi ta buga. Noor na kallonta amatsayin gizo take mata, itakuma Ammi tana mamakin ganin Noor, kenan itace tabawa jini dazu ,kenan yartace ta aihu, kenan wannan matashin shine mijin Noor dinta. Kuka Noor ta fashe dashi ta kankame rigar Daddy tana cewa" Daddy ka taimaka min banaso na mutu yanzu, ance in lokacinka ya kusa mutanen dasuka mutu suna zuwa maka a matsayin fatalwa, Daddy banaso na mutu yanzu babies dina da Ya Aryan wazai kula min dasu" kamo hannunta Ammi tayi da sauri ta fizge, tsabar tsoro batama lura cewa in fatalwar gaske ne jikinsu bazai mannu ba, itakawai kallon fatalwa takewa Ammi. Matsawa Daddy yayi yabawa ammi space, wani kallon zamu hadu dakai Ammi tayiwa Daddy da sauri ya juya ya fice adakin yana dan sakin ajiyar zuciya. Noor fa taki Ammi ta tabata, da kyar Ammi tasamu ta kwantar da hankalinta bayan ta kira sunanta, shiru tayi tana kallon idanun Ammi, so take ta gasgata abinda take gani, mintsilin Ammi tayi har saida tace aushh, da gaske fa amminta ne agabanta, amminta bata mutu ba. To ya akayi haka bayan a idanunta ta daina numfashi. Rungume juna sukayi suka fashe da kuka, duk sauran suna tsaye bakin kofa suna kallonsu cikeda burgewa. Farin ciki double double kenan, ga Ammi tadawo Allah zai kawo musu karshen Mama, gakuma aihuwar da akayi masu, a ranan Ammi ce ta kwana da Noor taki kowa ya zauna da ita sai amminta, hatta Aryan jan ido tayi masa a haka bai haqura ya tafi ba, abakin kofar dakin ya zauna yana dan gyangyadi, Ammi na zaune bakin gadon Noor itakuma tayi bacci anyi mata allura dan haka basuyi wani hira ba duk da Noor taso suyi, shafa kanta takeyi ahankali, har yanzu Noor bata canza ba akwai surutu. Yau Allah ya nuna mata gashi ta zama kaka. Saidai kuna tana ta zuba ido kozata ga autan maza suhail har yanzu bata ganshi ba. Gobe zata tambayi Daddy.


Cikin ikon Allah washe gari aka samu Noor ta releasing air kamar yadda ake buqata in akayiwa mutum operation. Tea mai kauri doctor tasa aka hada mata, Tass ta shanye saboda yunwar dake addabarta, babies ma Masha Allah sunyi lfy babu wani damuwa, karfe goma aka fitar dasu, amma ba'a bari anyi jagwalgwale dasu, Aryan aka bawa na farkon Ummi kuma ta karbi dayan, sunyi matuqar kama da Aryan kamar shiyayi kaki ya fiddasu, kwantancen gashin kansu sak na babansu kalar ne kawai na mamansu baki wuluk dasu, eye colour dinsu ma irinna Aryan ne irin sharp brown dinnan. Sai mamulan hannu sukeyi alamun suna iin yunwa, lokacin kuma Noor tayi bacci bayan ammi ta taimaka mata tayi wanka. Kamar jiya yau ma kowa na asibitin, tuni Dada ta dau hanyar Abuja itada sauran matan gidan su matan Alhaji Jibril da matan kanne da yan uwa. Abun ba'a magana mutum zai dauka biki ake a asibitin. Bayan asr aka sallamesu, Ammi ta nemi alfarmar abata Noor tayi wankan jego agidanta, ba haka Aryan yaso ba amma yana jin nauyinta dan haka ya yarda. Tare suka tafi gidan ammin bayan sallan maghrib kowa ya tafi gidansa amma banda su Hanan da Anty Jamila. Dada na saukowa garin Abuja tace lallai saidai akaita gudan Ammi tunda anan akace ankai Noor. Karfe tara saiga Aryan da ledoji niki niki ya kawo, har dakin Ammi ya shiga, babu kowa adakin sai Noor dake kwance kan gado ga twins dinta agefe sai tsala ihu suke amma ko ajikinta, Dada ce ta fito saga toilet hannunta rikeda zaninta under skirt ne kawai ajikinta sai zanin rigar, ta fitone

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login