Showing 30001 words to 33000 words out of 99210 words

Chapter 11 - MIJIN TACE Complete Hausa Novel

Reemah   

13 Jul 2025

8230

irin kayan da su ummi suka dawo dashi, datayi tambaya sai suka ce mata na wata yar uwarsu ce a saudiyya. A makaranta kuma data ga Noor da hijab da niqab sai abun ya kara kulle mata kai danta tambayi Noor saitace mata wai dilka ake mata. Bata kara cewa komai ba tasan sarai komai da lokaci zai bayyana.


Oga Aryan fa tunda yaga su ummi sun dawo daga Dubai da wannan kaya tukuru'u sai hankalinsa yakara tashi, lallai ba wasa akemasa agidannan ba. Shi ko amafarki betaba ganin inda akayiwa namiji auren dole ba amma gashi akansa za'a fara. Bakin ciki kamar ya kasheshi.


Moon kuwa babu abinda ya ragu sema wadda ya karu cikin rashin mutuncin datakeyiwa Mahmud. Kuma tanayine danta samu goyon baya dari bisa dari daga wurin mahaifiyarta. Shiko Mahmud ba karamin damuwa yake ciki ba kuma be taba fadawa iyayensa ba. Yanzu ko sha'awarsa ta motsa Indai ba danne Moon din zeyi ba to saidai ya mutu amma ko ajikinta.



Yau sati biyu kenan da akeyiwa Noor gyaran jiki kuma sosai ta canza dan jikinta kamar wani kwai, ga tsumin da Hjy Balaraba kebata wani lokaci saita rika jin wani feeling na taso mata saita rasa yadda zatayi. Yanzu sun fara exams wadda by the end of next week zasu gama. A yanzu kam Noor tafara zargi akan wannan gyara da ake mata dan ita a iya saninta amare kadai akewa wannan irin gyaran. Toh amma meyasa babu wadda yamata maganan, kuma ai ita batada wani saurayi balle ace har ansa mata rana.


Su Anty Jamila kam shiri akeyi bana wasa ba. Komai na gidan amarya ya gama haduwa saura aje a shirya mata su. Yanzu kam su Hanan sunsan da maganan bikin dan Anty Jamila ta fada musu kuma ta gargade su akan fadawa Noor hakan yasa suka ja bakinsu sukayi shiru, amma ba karamin tausayi Noor tabasu ba, a wannan zamanin yaushe ake wani yayin auren dole, yo auren dole mana tunda ita amaryar bata sanda bikinta ba.



Agurguje


Yau saura sati daya biki mutani har anfara cika a gidan ummi hakazalika bangarensu Anty Jamila dan anan Abuja za'a daura auren. Mutanin saudiyya suma wasunsu harsun fara zuwa, mutanin Adamawa ma haka duk anfara zuwa. Kankace me gida ya fara cika saikace gobene bikin. Aryan tunda yaga haka saima yadena kwana agidan, yakoma sabon gidansa yana kwana dan har ankai jeren Noor sun Anty umaima da sauran yan uwa. Saidai part dinsa komai shi da kansa yayi. Ummi ba tace masa komai ba duk da tana sane yadena kwana agidan. Su Dada da hajja mahaifiyar ummi anhadu sai gwaranci sukeyi, ita Dada tana Hausa itakuma hajja tana larabci, haka ake musu dariya insuka fara hiransu kamar sunajin mesuke cewa.


Anty Aisha da lubna tunda sukaji labarin auren Aryan suka fara sabon bori akan lallai saisunkawo cikas a wannan bikin. Anty Aisha sai kumburi takeyi tana fashewa akan meyasa Aryan zai auri wata ba yarta ba(🙄🙄ba zance komai ba fans din MJIN TACE su zasu baki amsa).



Yau Noor zata koma gida tama riga tagama kimtsa kayanta. Da rana su Hanan dakansu sukazo suka dauke ta. Tunda su ka shigo gidan take mamakin yadda aka canza abubuwa dayawa na gidan, ga mutane ko ta ina hayaniya na tashi. Tunda su ka shigo falon mutani suka fara guda, gabanta ne taji yayi ras, Allah yasa de bada ita akeyi ba. Anty Jamila ce takama hannunta zuwa falon uncle saif. Mamaki ne ya kamata ganin daddynta suna hira da uncle saif din. Da gudu ta fada jikinsa ta rungumeahi tana jin dadi. Shima Daddy rungumeta yayi, sun dauki kusan two minutes kafin suka zauna. Daddy yakamo hannunta Noor da kyau cikin nasa yace "Nuwaira" ahankali ta furta na'am. Ya kara matse hannunta cikin nasa yace" lallai kincika 'ya tagari me bin umurnin iyayenta kuma nasan duk alfarmar dana nema awurinki bazaki taba cemin a'a ba" jikin Noor duk yayi sanyi dukda batasan inda maganar Daddy ya dosa ba. "Noor na miki miji kuma yau ya rage kwana biyar kacal da daurin auren ki" dammmmm haka Noor taji gabanta ya fada, kenan duk zarginta yazama gsky, inna lillahi wa inna ilaihí raaji'uun. Wasu zafafan hawaye taji yana gangarowa daga idanunta, Daddy yayi ajiyar zuciya yace" Noor kin amince da zabin daddynki"? Kusan minti biyu shiru kafin ahankali tadago da jajayun idanunta ta kalli daddy ta bude baki ahankali tace".........



COMMENT AND SHARE


REEMAH✍️
10/14/23, 7:19 PM - Reemah: https://chat.whatsapp.com/HKRxGHXg9gP6uOdVkfTL6j


🌼MIJIN TACE🌼


REEMAH



PG 27_ 28



Ahankali tace " na yarda Daddy na" sai kuma ta rushe da kuka me sauti, Anty Jamila ta taso takamata suka fita daga falon, Daddy yabita da kallon tausayi yana mejin zafi azuciyarsa. Suna shiga daki ta kwace jikinta daga rikon da Anty Jamila tamata ta kwanta saman gado tana kuka mecin rai. Su Hanan dama sunsan hakan zata faru, da kyar suka rarrasheta tayi shiru.


Abangaren su ummi kuwa anata shirin shagalin daza ayi, kama daga su Arab night, su mother's day,dinner da kuma walima. Suna zaune a daki sun baje wasu kaya masu kyau itada kannenta biyu mata Anty ounaisa da Anty Raihana suna dubawa. Nana ce ta shigo tana ta bori dan yanzu takeda labarin cewa yayanta ne zeyi aure. Wuri tasamu ta zauna kusa da Hajja tace" yanzu ummi dama Ya Aryan ne zeyi aure ina matsayin kanwarsa kwaya daya amma ace ko labari banda shi"? Dariya su Ummi suka fashe dashi dan yadda tayi da fuskarta ita adole tana fushi, ummi ba komai yasa tayi hakan ba dande kawai karta fadawa Noor cewa auren yayanta za'ayi itakuma Noor ta zargi wani abu shiyasa. Fushin Nana be wani lasting ba ganin uban kyawawan kayan da aketa budewa, su Arabian gowns ne masu kyau wadda kudinsu sun fallasa Kansu da Kansu. Wani royal blue abaya Nana ta daga tace" ummi wlh wannan kayan inama ace ta Noor ce daba karamin amsarta zeyi ba" ummi ta juyo ta kalleta, ko de tasani ne? Amma babu alaman hakan a fuskarta. Haka sukayita bude kayan suna yaba kyawun dayayi, Dada da Hajja sun juya nasu side din suna gwarancinsu na fama sai faman kyalkyata dariya sukeyi idan dayansu yafadi wani kalma me ban dariya.


Agefen ango kuwa abokansa daga Saudi su Muhsin da abokansa biyu ne suna hira wadda shikuwa jinsu kawai yakeyi ko kala bece musu ba. Muhsin ya kalleshi yace" wlh Aryan tsab wannan banzan halinnaka zai bace, bari akawo maka amaryarka I bet you saita maida kai MIJIN TACE, cos you'll be heads over toes for her" dariya wa'nnan biyun suka fashe dashi, Aryan wani dogon tsaki yayi shi duk abun duniya ta issheshi, shi meyasa ma becewa Abba bai amince da wannan auren ba, ai kowa yanada freedom of speech dinsa. Knocking sukaji akofa, Muhsin yatashi yabude, Nana ce tsaye abakin kofa se turo baki takeyi ita zata zo ta nunawa Ya Aryan fushinta akan cewa meyasa be fada mata aure zeyi ba( wannan 'ya kodai tamance da halin yayannata ne), yadda Muhsin ya kafeta da ido kuma yaki bata hanyan wucewa ne yasata tsarguwa. Aryan na lura da yadda Muhsin din yake kallon Nana daka mata tsawa yayi yace " what are you doing here" afirgice dukkansu suka juyo suka kalleshi kamar ma bashi yayi maganan ba ya maida idonsa kan wayarsa yana latsawa, da sauri Nana ta juya aguje tabar wurin azuciyarta tana cewa" toh ni nasa ummi tace ka dawo nan gidan sai bayan biki dazakazo kana wani haurawa kamar flour, garama kayi auren ka ficewa mutane agida". Wani shu'umin murmushi Muhsin yayi yajuyo ya shiga falon yana kallon Aryan yace" Nana has grown so much, she looks cute how I wish nima na samu chance" harara da Aryan ya watsa masa ne yasashi tuntsirewa da dariya yace"Allah yasa ba kaibane babanta, ina iya zuwa wurin Uncle yanzu kuma nasan ba hanani zeyi ba" tsaki yayi ya mike ya shiga dakinsa yana banko musu kofa. Dariya daya daga cikin abokan Muhsin yayi me suna Lukman yace" this guy is really funny".



Yau su Anty Jamila suketa shirye shirye za' a kawo lefen Noor, wasu kuma zasu kai lefen Ya Shareef. Tunda safe aketa girke girken tarban baki. Sai karfe sha biyun rana aka fara kawo lefen Noor, yan uwan ummi mata biyu da kuma yan uwan Abba sukuma kusan rai bakwai, motocine manya manya range rovers guda shida kowani mota dauke yake da akwatuna guda four. Basu gama parking ba sukaji horn alaman wata motarce zata shigo, mamaki ne yakama mutanin dake wurin ganin wata dankareriyar mota kirar latest Mercedes benz fara uban ubansu an nadeta da fulawowi jajaye ta shigo. Driver din daya tuko motar ya fito ya mikawa Anty ounaisa key din motan. Bayan angama shigar da akwatuna daddaya har guda 24 kowa ya hallara afalon tarban baki ana kallon kaya. Babu wadda beyi santin kayan dake cikin akwatinnan ba, kayane ingantattu tsadaddu kyawawa masu daukan ido. Bayan angama duba kaya su Anty ounaisa suka nemi akawo musu amaryarsu suganta. Babu musu Anty umaima ta mike ta fice daga falon zuwa dakinsu Noor. Tunda ta hangeta ana tsantsara mata makeup taketa furta masha Allah tabarakallah. Light makeup ne amma bakuga yadda ta hadu ba, wani sea green lafaya take sanye dashi yayi mata kyau sosai. Anty umaima takamo hannunta suka fito harzuwa cikin falon. Suna shigowa hankalin kowa yadawo Kansu. Duk da kan Noor akasa yake be hanata ji ajikinta cewa ita ake kallo ba. Saida suka karaso har gaban Anty ounaisa sannan ta zauna akasanta. Kamo hannun ta Anty ounaisa tayi tadan ja gelen zuwa baya dan fuskarta ya bayyana da kyau" tabarakallah ahsanul khalikeen" su Anty ounaisa suka furta lokacin dasuka ga fuskar Noor. Kunyane ya kama Noor ta duke kanta tanajin bugun azuciyarta na tsananta. Muryar Anty ounaisa yana mata yanayi da wadda tasani amma kuma tamance da wa dan bata kalli fuskar Anty ounaisan ba. Rafar five hundred guda biyu ta ajewa Noor akan cinyarta ta kuma kamo hannun Noor ta dunkula mata key din wannan hadaddiyar motar dasuka shigo da ita dazu tace" wannan kyauta ne daga garemu yan uwan megidanki, Allah Ya baku zaman lfy ya kauda sharri atsakaninku" kowa a falon ya amsa da Ameen. Sun kara kusan mintuna ashirin kafin suka tafi. Makullin motan Noor ta mikawa Anty Jamila ajiya. Bayan ta koma dakinta tacigaba daga inda ta tsaya wato sana'ar kukanta dama karfin hali kawai tayi da bata fashe musu da kuka a falon ba.

Acan gidan Amaryan Ya Shareef ma hakan ta kasance, ankai lefe, akwatuna masu kyau guda goma sha biyu. Murna akan fuskar wannan ahali ba'a magana dan suna da yakinin cewa yarsu tayi dacen gidan miji.

Har I yau mama batada labarin bikin Noor Dan Daddy da yan uwansa babu wadda ya fada mata, shi Daddy ma cewa yayi sai bayan bikin kafin ya sanar da ita. Yau Moon takawo mata ziyara sai kwanciya take tayi ga kuma bala'in kwadayi har Mama tafara zargin kode Moon nada shigan ciki ne. Moon na cikin cin Apple Mama ta shigo falon tace" ke Moon anya ba cikine da ke ba"? Sai shegen kwadayi kike tayi tunda kikazo Allah yasa ba abinda nake tunani bane. Da sauri Moon ta mike tace" Mama dan Allah karki kara min wannan mummunan fatan, ni ban shirya aihuwa da wannan mutumin ba, wlh inma shine zubar dashi zanyi" dariya Mama tayi tace" yawwa ko kefa ai shine magana, ina ke ina hada jini da wadda aka miki auren dole dashi " haka suka cigaba da hiransu.


Washe gari akayi mother's day agidansu ummi. Dayake farfajiyar gidan nada matuqar girma, kwararrun designers aka kawo suka decorating ko ina gwanin sha'awa. Taron mata ne kawai dan haka maza basu zo ba. Nana ta kira wayar Noor yafi so akirga amma switched off dan tunda aka fadawa Noor maganan aurenta ta kashe wayarta. Sunyi taro lfy antashi inda gobe kuma zasuyi Arab night.


Yau Thursday, agefen su Anty Jamila kuwa shirye shirye akeyi na henna party din Noor. Kwararrun masu lalli aka kawo. Hanan da Hanifa sune kadai kawayen Noor saikuma wasu yan uwansu sa'anninsu. Noor aka fara wa lalli, inda aka tsantsara mata Jan lellenta me kyau babu ko digon baki. Farar fatannan nata ya bala'in haska lallen yai kyau sai tashin kamshi take, dan tunda tadawo take kan hayakin turare wadda Hjy balaraba tabata. Kowa saida yayi lallin har kusan karfe sha dayan na dare ana kan lalle, wasuma har sun fara bacci. Ranar Friday ne za'ayi dinner din Ya Shareef inda Noor kuma sai Saturday bayan daurin aure da daddare.


Su Anty Aisha sunyi iya kokarinsu naganin sun ruguje duk wata shirin da akeyi amma ko fuska basu samu ba a gidan ummi. Yan uwa gaba daya sun San halin anty Aisha shiyasa babu wadda ya sake da ita. Itakuwa Lubna ganin babu abinda zasu samu agidan illa disgrace yasa taja mamanta suka bar gidan suna bakin cikin kubucewar Aryan daga tarkonsu.

Su ummi sunyi taron Arab night dinsu da daddare, inda da kyar aka shawo kan Aryan ya taho wurin taron. Farar jallabiya dakuma hiram yasa mai matuqar kyau ash colour abokansa kuma suka shirya cikin jallabiya kawai, kowannensu da rawanin larabawa suma sunyi kyau. Muhsin sai faman Satan kallon Nana yake, itama data lura da hakan sai ta dena sakin jiki awurin taron harga Allah ya burgeta amma ganin idon Boss Aryan bazaisa tayi wannan gangancin sakewa da Muhsin dinba dukda cewa dan uwansu ne.

Washe gari

Agidan amarya Na'ima kuwa, kwalliya aka mata me kyau dan na'ima itama akwai kyau masha Allah. Shiri tayi cikin wata princess gown purple colour anyi shirin zuwa dinner. Bini bini tana waya da Ya Shareef ana hiran love kawayenta sai zolaya suke mata itakuma tana basu amsa bako kunya.

Ango shareef shima ya shirya cikin dakakkiyar shaddarsa light purple yayi kyau Masha Allah. Agidansa ya shirya dan tun ana sati daya da bikin yakoma kwana awurin dan baki har cikin dakinsa suke kwana. "Aryan pls get up and get ready now, meye haka pls dude ka tashi mana" Aryan dake zaune yana latsa wayarsa dagashi sai guntun wando da singlet kaya kawai zesa danya riga ya yi wanka. Su Muhsin suma suna cikin abokan Shareef tunda beda aboki sai Aryan shiyasa suma suka masa kara. Su sunma gama shiri cikin shadda light blue wadda anko sukayi Aryan kawai ake jira. Da kyar ya mike shima ya dau goggagun kayan nasa ya Sanya. Yayi kyau sosai kamar shine angon, ya shareef ya kalleshi yace" Allah sarki ango ango, gobe muma war haka muna shirin zuwa naka" suka fashe da dariya suna zolayarsa, ko ajikinsa dayaga zolayan bame karewa bane yace" seriously guys, in baku dena ba zan fasa tafiya and I mean it" haquri suka shiga basa. Bayan ya gama shiri duk suka fito daga harabar gidan. Motocine masu ji da nera guda biyar manya manya suka jera Kansu suna jiran ango. A wata farar Bugatti din Shareef suka tafi shida Aryan. Su Muhsin da abokansa biyu kuma suka shige na bayansu, saikuma bodyguards asauran motoci ukun suka fara tafiya zuwa inda za'ayi taron.



Noor ne zaune tagama shiri tana jiransu Hanan su gama shirinsu. Wani material royal blue kowaccensu tasaka da alama anko sukayi. Kayan ya bala'in fitting Noor, ga dankwalinta da tayi simple dauri dashi yayi kyau, fuskarta ba makeup amma annurin fuskar amare ya kawata fuskartata. Tulun gashinta yana cikin dan kwalinta bata bari ko tsini daya ya fito daga ciki ba. High heels ne akafarta fari me kyau. Suma su Hanan sunyi kyau kowa da irin tata kwalliyar gwanin sha'awa. Muryar Anty Jamila sukaji tana kiransu su fito. Kowa yariga ya fito lokacin da suka fito daga dakinsu yayinda wasuma harsun tafi. Amotarsu suka tafi inda Noor dakanta take tuki har suka iso babban hall din daza'ayi taron. Ko ina ya hadu sai tashin music akeji.


Motar amarya ne ya shigo inda hankalin kowa ya koma Kansu. Har gaban motar Ya Shareef ya tafi ya bude wa amaryartasa dakansa. Ahankali suka tako har entrance din hall din suna rike da hannu juna kowa nata santin irin kyawun da sukayi. Su Noor kuwa sun iso su hanifa suka tafi wurin amaryarsu itakuma Noor ta tsaya a jikin motar tana rera kukanta, kenan itama gobe zata zama matar wani. Dayake wurin akwai dan duhu shiyasa bata ga wucewarsa ba. Shikuwa Aryan motar dasukazo aciki ya shiga ya zauna. Sheshshekan kuka yakeji kasa kasa shi ya Sanya ya dago kai ya kalleta. Juya baya tayi ta manne da kofar motan tana kukanta tsakani da Allah. Tsaki yayi ya mayar da kansa ya kwantar ajikin kujeran motan yana tunani. Har kusan mintuna goma amma bedena jin kukanta ba. Fitowa yayi ya zagayo har inda take ya kafeta da ido kamar yaso ganeta amma kuma fuskarta na manne da glass din motar."wai meyasa Ku mata bakuda wuyan kuka ne, Ku abu kadan kesaku kuka, mukuma damuke cikin damuwa kullum muceme, mtscheeew" tunda ya fara magana tayi shiru tana sauraransa kamar taso gane muryarsa, daga kai tayi karaf idanunta suka sauka acikin nasa, sunkai minti biyu suna kallon junansu, shi ya fara janye idanunsa sannan itama tayi kasa danata, haka kawai taji yayi mata kwarjini, share hawayenta tayi ta juya zata tafi taji yace" nonsense " juyowa tayi ta murguda masa baki hadi da harara, dayake akwai reflection na haske kadan awurin yasa yaga abinda tayi masa, tana ganin ya nufo ta tajuya zata gudu cikin rashin sa'a takalminta ya goce, harta gama sallamarwa zata jita akasa sai kawai tajita a hannun mutum. Shima karan kansa besan ya akayi yayi saurin tarota ba, kusan thirty seconds amma besake ta ba, wani irin yanayi ta tsinci kanta acikin da sauri ta zare jikinta daga rikon dayayi mata tana turo karamin bakinta gaba. Bakin ya kama yaja da dan karfi tasaki kara tace"mug.." Bata karasaba jin ya kama hannunta ya murguda abayanta. Ihu tayi da Sauri yasaketa yabar wurin kamar mara gsky😂😂. Da Sauri itama ta shige hall din. Anriga anfara taron, wuri ta nema

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login