Showing 33001 words to 36000 words out of 104042 words
bayi basu tsira ba.
Shi kanshi Ukshe sai da ya tattara jikokinshi mata, yasa aka tsallaka dasu Saudiya, sannan zuciyarshi tasami nutsuwa, duk wasu manyan fada sai da Bilal yasa aka sauke mukamansu, daga cikinsu har da Uzaif da Ammar.
A fujajjan suka fara niman Ashraf.
(anya zasu same shi🤔🙄)
★★★
Oman...
Natashah sun dawo, cikin nan ko wata uku bai yi ba, aka kusan cika daki da kayan baby. Tsakaninta da Aamih da Aanih hantara da kyara, tun can ma yaran sun san ba sonsu yake ba, balle yanzun da kakar tayi banza da al'amarin su sabida laifin Uwar su, yaran sun koma abin tausayi. Musamman da wannan cikin ya bayyana a jikin Natashah kiri kiri, Nannah ta fara cire su. Bama kamar Aanih wacce ta dauko duhun fatar SAFINAH, shima ba can ba.
Me kula da Yaran ta gaji da Irin abinda akewa yaran dan haka ta kira Ashraf bayan, ta gaya mishi, katse kiran yayi kawai.
Amma cikin Natashah yana shan kulawa na musamman.
Kwana biyar tsakanin sai ga Ashraf yayi musu dirsn mikiya.
Basu yi tsammanin ni shi ba.
Dai dai Nannah tana make Aanih tare da gaya musu magana.
"Banda dole ce tasani amsar ku, ina zan yarda da shegu a jikokina."
"Allah Ammyn ki mai da su gun Uwarsu tunda musul."
Had'iye maganar ta tayi sakamakon hango shi da tayi a tsaye, yasa kananun kaya amma ya rufe fuskar shi da hirami, sabida badda kafa.
Yaye hiramin yayi tare da shiga falon Ammyn ya durkusa a gaban Yaran ya kwashe su.
Tashin hankali ne ya bayyana a fuskar Ammyn, tare da kaico da abinda ta furta, har ya kai baƙin kofa sai kuma ya tsaya tare da cewa.
"Me kika gayawa Iyayen SAFINAH da suke shirin hanani aurenta."
Cikin b'oye abinda aikata tace.
"Me zakayi da wannan yarinyar, da ta girmeka!? Jan iska yayi sannan ya kauda kanshi yana cewa.
"Ammyn! Meye yasa baki je nima na da kanki ba!? Meye yasa kika cusa mata soyayyata a zuciyarta,!?"
ajiye yarana yayi tare da sake murmushin nasara, dan tayi shiru ne.
"Kinbi badaru zuwa Nigeria saboda son kai Irin namu na larabawa, kika nemi Abdul ya saki jiki dake dan ki cimma burinki akan shi yaki sakin jiki dake, sai kika yi amfani da soyayyarta da tayi miki kikayi kawata mata duniyata ko ba haka ba."
Yayi watsi da hannunshi baki É—aya, idanunshi sunyi jajjur.
Sannan ya cigaba da cewa.
"Ke Mahaifiyata ce! Karki bari Ni nayi Magana da yawa dan nasan shirinki akan SAFINAH dan haƙa bana s."
Kira mishi mari tayi cikin borin kunya ta shiga cewa.
"Ni zakawa sharri, sun kitsa maka ƙarya da gaskiya kazo kana min rashin kunya."
"A'a! Ammyn akan gaskiya nake. Ai ke kinfi kowa sanin mace bata da daraja a cikin masarautar indai ba jinin sarauta bace, ita ce take tsira ita ma saboda kar a tab'ata ya zama rikicin masarautar, Ammyn kin sayi kimar SAFINAH tun bata san ciwon kanta ba, kika bawa iyayenta kudi dan ya zama fansa ga duk abinda ya sami yar su, Ammyn nifa soyayyata nakewa Yaki ba kowa ba, Ammyn tunda na iya barin Al'ummanta ki gaya min waye bazan bari ba, shekaru ɗai-ɗai har Ashirin da shida, rabona da naganki, inda da gaske ke Uwace bazaki taba barina a cikin wannan shekaru uku ba, yanzun kin same ni a sama, kin juyawa yarinyar da ta gama wahala dani, kema sanin kanki duk cikin al'ummar duniya babu wanda ya kai bakin fata tsayuwa akan ra'ayinsa, shi yasa kika zaɓi Safinah, sannan kika hora musu yar su da rashin jin maganar su, Ammyn kin min Illar so, kin karya min zuciyata da abinda kika aikata, sannan ai na san da cewa baki son alaƙata da Safinah, babu yadda zaki iya ne yasa kika nema min aurenta, sannan kika fara jawota taga Natashah dan zuciyarta ya karaya dani. Ammyn kenan, ki tsaya a iya matsayinki na wacce ta haifeni amma akan SAFINAH zan iya faɗa da kowa indai zaka min iyaka da ita, Ammyn babu ruwan ki da ita. Idan tazo a surikarki ta nemi rena min ke, wulakanta ta akan ki, dan Uwarta tafi takowa, amma karki shiga tsakani na da Ita dan haka zai sani tsanarki, sannan zanje na dauke ta mu tafi inda bazaku sake ganinsu ba.."
Tana bala'in kaunarshi bazata iya barin shi ya juya mata baya ba, amma indai tana raye sai ta hana SAFINAH farin ciki kamar yadda ta hana itama, sai tasa shi ya wulakanta ta kamar yadda yace, sai ta gigita rayuwarta, kamar yadda yayi mata yau ita ma haka zata mata.
.... Tattara yaranshi yayi har ya kai bakin kofa sai ya juya yace.
"Amadadin ki zame min haske ranar sai kika zame min haske makafi, ina tunanin inuwar giginya tazo gidanmu inda nake ashe na nesa kasha dadi ne, Ni ya dace nasamu soyayyarki amma nine kike farautar soyayyarmu."
Daga haka bai kuma ce mata kome ba yasa kai ya fita a ranar ya biyo jirgin Lagos.
★★★
Duk abinda duniya ya taru yayi min katutu, abinda Ashraf yake nufi dani duk rana da wani yasani sunana matacciya, dan Wallahi bindige Ni Abba zai yi, kusan sati d'aya kenan, ni nakira shi dan mu fahimci juna yaƙi ɗauka, nayi mishi text Ni reply. Abin ya dame mu sosai.
Ga aurena da naji an saka nan da sati hud'u mugun tashin hankalin da kashiga ba iyaka, wannan karon Ummi da kanta take min gyaran jiki.
...... A dame na kalli Ummi sannan nace.
"Ummi nifa bana son Alhaji Nuhu, wallahi bai min ba"
"Hmm! Haka zakiyi hakuri dashi, tunda an rigada an gama kome."
"Don Allah Ummi kayi wani abu."
"Babu abinda zanyi da, dan bazaki ja min magana ba."
Shiru nayi cikin kuka nace.
"Don Allah, Ummina wallahi bazan iya mishi biyayya ba"
"Kome zakiyi kiyi amma aure ba fashi."
Fita tayi daga d'akin Ni kuma zuciyata ta dibe Ni ga amsa tayin Ashraf, tare da amincewa.
Yana ganin sakon ya kirani.
"Ina dauka na saka. Mishi kuka ina gaya mishi abinda ke faruwa.
"Kizo idan suka ganmu a tare babu yadda za suyi damu."
"Wallahi tsoron su nake ji, don Allah kazo."
" Na gaya miki ki san yadda zaki fito, Ni kuma nasan abinyi."
Lallai na tabka kuskure, amma banga laifina na biyewa Ashu ba sabida su kansu iyayena sun san shi nake so amma sabida Nannah karta zarge su zasu hanani muradin zuciya ta.
Sun gaza mana adalci toh taya bazan biye mishi ba, dukda nasan abinda yaƙe don muyi babu kyau amma bani da zaɓin da ya wucce in bashi haɗin kai tunda Allah ya gani na gayawa Ummina bana son Alhaji Nuhu, amma taki fahimta ba mamaki idan suka ga abinda muka aikata jikinsu yayi sanyi, dan in ba haka muka musu ba, wallahi bazasu taɓa fahimtar girman yadda muke bukatar junanmu ba.
Goge kwalla nayi ina niman hanyar da zan fita zuwa gurin Ashraf, tunanina ne yatsarshi lokacin da nayi zurfi cikin niman mafita, karshe dai kamar zanyi hauka a dakin sabida babu wani mafita.
Tura mishi sako nayi nace.
*Ban san ta yadda zan fita ba,*
*Kiyi cewa Ummi zaki wanke kanki, Ni kuma zan biyo ki duk inda kike.*
*Hmm! Ni ina tsoron karka min irin abinda kayi min na baya, kuma ina tsoron Allah ina tsoron halinmu na maza, kana ribanta dani zaka juya min baya*
*Shima na farko sabida bana tare dake ne da ina tare dake wallahi babu wanda ya isa ya musguna miki idan zaki yarda dani ki cire tsoron wani a ranki idan kuma zuciyar bata aminta ba shi kenan nagode*
Duk sai na rude na shiga kiranshi dakyar ya dauka kamar zan yi kuka nace.
"Ashu! Me yasa kake bani wahala ne? Dan kaga na damu da kai!"
Dogon numfashi ya sauke cikin kasaita yace.
"Ni yadda na damu dake ko wallahi ko Ummi haihuwar ki tayi Ni kuma numfashinmu a tare yake bugawa"
  *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Insha Allah*
Oum Muwaddah......
16.
  "A'ah Ashu tsoro nake ji bana son na zama sanadin da iyayena zasu tsane. A halin yanzun ya dace na gyara gobe na, amadadin haka sai bata musu nake."
    "Didih"
Naji muryan Yarana, hawaye ne ya zubo min cikin tashin hankali nace.
"Mariamah!!!"
   Â
"Zaki yi yadda nace ko na maida musu yaran?"
  Â
  "Wai meye yasa kullum kake bani matsala ne haka, kasan girman iyaye kuwa!? Da kake son na bata musu kaje da abinka kawai Ni ba zanzo ba."
   "Ba damuwa karki zo, kiyi zamanki ma. Ni da nake da daman auren mata hud'u, balle ke gaba da zama."
    Kashe kiran nayi tare da g
Cillar da wayar, na cigaba da kuka tunda shine abokinsa hirana, sam ban san wani irin son kaine yake dawainiyya da Magabatanmu ba tunda nace Ashu nake so ya kamata su duba lamirina bawai su zuba min ido nayita abinda bai dace ba.
  Kifa Kaina nayi akan pillown ina kuka sosai.
   Da dare na je har falon Abba na sameshi shi yana kallon network news, zama nayi can gefe kaina a sunkuye,wasa nake da harshen gyale na, hawaye ne ke zuba daga nuna.
Â
Gyara zaman shi yayi Cikin nutsuwa sannan ya rage ƙarfin maganar da ake a tv.
"Safinah! Ba munki miki abinda kike so bane! Sai dai munyi dubi da irin rayuwar da zaki shiga ne,"
    Zuciyarki da kwalkwarki baza su iya daukar kasadar dake cikin masarautar Jordan ba, tunaninki da nazarin ki bazai dauki bukatar alummar cikin masarautar ba, SAFINAH ina ganin kiyi hakuri da Alhaji Nuhu, shine mijin da ya dace dake. Ba Ashraf ba, idan kuma aka yi dubi da rayuwarku da bambanci domin duk wanda aka daura shi shugaban al'umma sai ya take gaskiya dan wata dalilin shin zaki iya jure masifar da tasa uwa tafiya tabar d'anta? Zaki iya jure masifar da ya raba miji da mata!? Indai zuciyarki tana da adalci bazata rabamu dake ba, SAFINAH ki zauna damu hankalinmu zaifi kwanciya muma zamu fi samun nutsuwa ace kina kusa damu, badan ina Mahaifinki ba sai dan abokin shawaranki."
    Kukana ne ya tsananta, dakyar na mike tare da gyad'ana. Kuka nake me mugun cin zuciya.
 A haka na isa d'akina na kwanta, duk inda naso abin ya kasance yaki yuwa har Dudu da Umma nasamu, da maganar. Ita Umma yasameta su akan su bar i mu auri Ashraf.
 "Maman Safinah! Yarinyar nan tafi ku gaskiya tunda tace muku Ashraf take so kubarta takoma hannunshi, ita Kuma uwar Ashraf ɗin idan har ta cika Uwa dole taso abinda d'anta yake so ba wai tace muku. Ku raba abinda Allah ya haɗa ba, Safinah ba Yarinya bace amma tunda tace muku shi ta zaba a abokin rayuwarta kamata yayi kubata shi."
  "A'a! Amnah ki kyaleta kawai son zuciyarta ce kawai amma ita ba tsara Ashraf bace, kuɗi! Mulki! Nasaba! Uwa uba d'auk'ak'a, shi ba sa'anta bane, tayi hakuri Allah ya Kawo miji tayi biyayya kawai."
"Maman Safinah! Zaku sak'e tura ta cikin wani irin hali kodan Albarkacin yaranta ku kyaleta ta koma kansu, Bazawara ce ita addini ya bawa daman zaben Abokin zamanta ku iyayenta naku addu'a da bincike, kuna son kanku."
"Don Allah Amnah ki bar maganar nan ta auri Nuhu."
"Toh tabbas duk abinda ya biyo baya kune sila sabida tsoron karta kwace dukiyar ta, takwace mana."
"Ni kam fita daga d'akin korafin yar dakinki bai karbu ba."
Hmm duk yadda muka zata ba haka ba ne, domin kuwa Abba shi bai ja ba, Ummi ce ta kafe kai da fata. Kuma taki sauraro kowa.
Gaba bikin yana karatowa, dan haka na kashe wayata na zuba musu.
Sosai Al'amarin ya zafafa. Dan haka yau laraba na fito wanka daure, taje kaina nayi sosai sannan, na ciro pant da bra dina na saka. Zuciyata ta gama raya min abinda, ina gamawa na zauna sai da na busar da gashina sannan na fito daga d'akin sanye da hijab har kasa, Ummi na zaune tana haÉ—a wani tsimi na shiga mika min tayi na amsa ba musu na shanye. Sannan nace mata,
"Ummi zanje Salon!"
Zuciyata ke bugawa kamar zata fito, tsabar tashin hankali musamman da ta tsare Ni da manyan idanu, wai na shiga ruÉ—ani.
Had'iye yawu nayi tare da b'oye halin da nake ciki.
"Kina da kuÉ—ine ko na baki?!"
Dan karya zargi wani abu sai na ce mata.
"A'a Ummi dama ina tunanin ko zaki bani ne."
"Ki bud'e wancan sif É—in zaki ga kuÉ—in ki É—auki yadda yayi miki Allah yayi miki albarka,ya kareki daga sharrin mutum da aljan"
Tausayi tabani na kasa motsawa, sai da tayi min magana a karo na biyu naje na É—auki kuÉ—in.
"Allahumman Amin, Ummina Kiyi hakuri dani."
Murmushi tayi sannan tace.
"Allah ya jibanci alamarinki"
"Amin Ya Allah, Ummina sani na dawo."
Da sauri na fita naje na ɗauki wayata ina fita daga gidan. Sai da nayi tafiyar kafa, Kafin na kirashi kamar jira na yaƙe sai gashi ya kirani, cikin juriya na dauka.
"Assalamu alaikum"
"Waalaikumun Salam! Kin fito ne!?
"Eh gani a Bayan layinmu"
"Ok ga wani toyota nan zai dauke ki."
"Ok"
Juyawa nayi motar tayi parking a gabana, drvn motar ya fito ya bud'e min na shiga, sannan ya tadda.
Bamu tsaya a ko ina ba sai wannan gidan da ya kaini, suna filin gidan shida yaranshi da ma'aikatan gidan yaranshi na wasa da yan kuikuiyom kare, sai dariya suke, a hankali na zaro kafana na fito a ina kallon girka girkan karanukan gidan wani suke kaÉ—ai min wutsiyar su. Kallon agogon wayata nayi, naga sha biyu saura.
Watsewa ma'aikata ya riko hannun yaranshi, murmushi yayi min.
"Barka da zuwa Mrs Hashim"
Ban ce mishi kome ba, tunda muka shiga ya kawo min abin sha, yaga ban taba ba.
Murmushi yayi sannan yace.
"Nafi karfin ciyar dake maganin barci dan biyar buƙata ta, idanunki biyu komai zai faru."
D'ago fuskana nayi me cike da damuwa nace.
"Ashraf!?"
"Shhhhhi!? Kamar yadda kika bani ciwon kai, get ready da hukuncina dan na rantse sai na rama kome da aka min yau sai na sauki fansata."
Gyad'a kaina nake idanuna na cike da kwalla. Na cin amanar iyayena,
Hawa jikina yaran sukayi cike da murna suka shiga bani labari sai na manta da kukan da nake, na cigaba da biye musu, tashi yayi ya barmu, nan wanka yayi cikin farar jallaɓiya sabuwa kal da ita, sai farin hula malam tab'ani kasha hadisi. Sannan yayi wasa da turare kafin ya fito.
Sumbatar yaranshi yayi sannan ya kalle Ni tare da kashe min ido, yace.
"Ke kinyi katuwa! A can zan baki naki rabon. Kishiga kiyi salla da wanka ina zuwa ki tabbatar kin kintsa kome kafin nazo."
Tura mishi baki nayi tare da dalla masa harara, lumshe idanu yayi sannan yace.
"Zaki biya"
Haka ya fita ranshi fari nawa baki, ji nake kamar na gudu dan abinda nake shirin aikawa babban kuskure.
Me kula da yaran ce ta shigo ta kama hannunsu suka shiga wani daki, daga nan ban kuma jin duriyarsu ba, nima Dakin na wucce ina shiga naga wata rigar barci tare da wani turare.
Ban daki na shiga nake nayi wanka sannan na fito daure da towel, na zauna akan stool na shiga gyara gashina, sannan na É—auki rigar na kalla sai kunyar kayan ce ta kama Ni, dakyar na saka. Sannan na daura hijab dina akai.
Salla na gabata, ina cikin addu'a ya shigo da katon leda, har guda biyu ya ajiye a gabana.
Daura kanshi yayi akan cinyata, tare da sauke ajiyar zuciya.
"Alhamdulillah! Na kusan cika cikekken namiji kamar kowani namiji."
Dariya ya bani sosai sannan