Showing 87001 words to 90000 words out of 104042 words
musu.
D'akin ya biyo ni, ina tsaye a jikin, jin hannunshi a tsakanin k'uguna, ya janyo Ni jikinshi, cikin damuwa yace.
"Don Allah ki yafe min! Nayi kuskure sosai kuma a shirye nake na gyara."
Janye jikina nayi daga gare shi, nace.
"Yanzun da ka fahimci mata suna suka tara ko!? Ashraf kenan! Ni kawai ka sallame Ni, tunda ban isa mace ba kuma ban kai mace ba, Ni ba yar mulki bace, asalima Ni ba yar kowa bace, na shigo rayuwarka, dan haka kaja tsuman rayuwarka nima na riƙe nawa don Allah ka rabu dani."
Girgiza kai yayi cikin damuwa yace.
"Wallahi bazan iya ba! Kece rayuwata! Wannan silent din da kike min yana cutar da ruhina, don Allah ki barmu, mu rayu a duniya d'aya. Wallahi na gaji na gama hakura da abinda ya faru, ke kawai nake buƙata."
Murmushin gefen baki nayi sannan nayi magana kasa kasa, nace.
"Kai da kake da sabuwar budurwa dal kai ka fasata me zakayi da second hand"
Janyo Ni jikinshi yayi cikin nutsuwa yace.
"Kowacce mace da irin halittar amma taki halittar dabance."
"Heyyy! Ashu! Ai haka ne yasa kayi sati guda a cikin gida kamanta da shanyar ka da ka zuba a rana. Ka dame sabon rami ka manta da wasu tsofin ramuka."
Juyo Ni yayi jikinshi na rawa, Yace.
"Wallahi ba haka bane, bai dace na fita ba barta bane shi yasa na zauna "
"Sabida su a gaban iyayensu ka auro su ko!? Ni kuma a layi ka auro Ni, babu daraja dan ina sonka na sabawa kowa nawa, Ashraf kaje kawai idan naga yuwar zama da kai, zan nime ka."
Ƙamar wanda aka watsa mishi wuta haka yake cira, riko hannuna yayi na zame tare da girgizar mishi kai na, nace.
"Please kafita min."
"Don Allah Safinah kiyi hakuri, wallahi bazan kuma ba."
"Wallahi zaka kuma, ai nima haka nayita binka ina baka hakuri kaki saurarona, karshe nima da na fara,a nan d'akin kayi amfani da karfin ka, kabiya bukatar ka, dake Ni ba yar kowa bace, idan nayi abu jikinka na rawa zaka kira Ummina ka gaya mata, Ashraf jeka Ni bana son ganin ka Don Allah idan na hucce zan nime ka......"
Dafe keyarshi yayi cikin tashin hankali, ina gama gaya mishi haka na shige ban daki na saka kuka, Wallahi ina masifar son Shi. Bana jin zan iya dakatar da kaina dole ya biya kuskuren shi, sai dai son shi da kewarshi suna damuna, sosai sai da nayi kuka na koshi sannan na fito abuna, baya d'akin sai dai wani takarda da ya bar min, ɗauka nayi na bud'e.
_Idan na isa dake ki shirya zamu wucce Paris da karfe biyu na rana, Ablah da Yayi ta zasu zauna a gurin Ammyn na_
Sau shida na karanta sannan na ajiye....
[16/03 10:44 PM] My 2nd Mtn: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*
Oum Muwaddah
4️⃣1️⃣
Mik'ewa nayi na shiga had'a kayana, Ina cikin saka kayana naga jakar da Sophia ta kawo min ɗauka jakar nayi na d'an dib'e wani garin daka, da kuma nakiyar Sudan, sai garin kuka wanda aka had'a har da kanunfari da aya tare da marzan kwaila. Tsimi wanda aka jefa dabino me hula a cikin.
Sai wani d'an karamin abu kamar bushashen jijiya, anyi rubutu a ciki.
_Didih wannan gindin ayi ce, koda ke baki bukatar Abbansu Ablah, ki jika da ruwan zafi yana jika kici ki b'oye dan iskokai suka d'aukewa sai ki sha Insha Allah zaku raya daren cikin amincin Allah_
Wani roba na ciro a kayan naji yana kamshin, ina duba saman robar.
_Didi wannan sabulun tsarkine babu wani abin cutarwa dan Nice na hada, sabulun cussion na baby care, sai garin Jujuba magarya, sai d'an sabulun zaitun, sai lalle, da farin miski dashi nake amfani babu matsalar komai_
'
Shiru nayi cikin raina ina jin kaunar Sophia da Nanah Asma'u, bud'e wata leda nayi naga zunguru (Bani mantawa ina da shekara tara zuwa goma, Kakata tana saka min zunguru idan zata mana lalle sallah, a lokacin kuka nake sabida ina son me yankar salate, wannan zunguru malamai likitanci a musulunci sun nuna amfanin shi, yana kariya sosai ga farfaɗo da kwayoyin halittar mace da suka suma, sannan yana kare mace daga sharrin jinn, Please koda bazaki yi ba ki gwada akan yara, balle kuma minti nawa ne, ni idan na daura lalle karfe goma, Insha Allah sha biyu na dare nake cirewa, sabida jinina yana rike lalle, na sunan Zainab sai da nayi wata uku kafin ya fito, dan haka ko a yatsu muyi yana da fa'ida, 😏🙄🤭 gaskiya duk wanda ya karanta book ɗin bai dauki wani abu ba, wallahi ya cuce ni eh dagaske nake)
Ciro zunguru nayi na shiga kuncewa sannan naga yar takarda.
_Inji Hajja wai ki maida lalle abin yinki sabida yana maganin abubuwa dayawa Please didih_
Wasu itace na gani wanda yake cikin wasu roba, wasu itace na gani da takardar su.
_Ki sami kaza guda ki cire kominta ta sama sai ki sakata ta dahu da itace. Sannan kiyi peppe soup ɗinta, karki rabata ki barta haka da kanta inda kika bila zata had'e abu me muhimmanci shine ruwar miyar sannan kici namar har da kashin Allah de best_
Ajiyar zuciya na sauke tare da tattara kayan na ajiye, duk sai na dawo zanyi amfani da shi, sabulu. Na dauki abinda zan iya ɗauka na rufe shi a wardrob.
Sai da na zuba kayan wani tunani yazo min.
Shifa rayuwar aure babu abinda yake rike dashi sai hakuri, da addu'a. Duk wani abinda zai je ya dawo matukar karike Allah kaine asama, sannan kayan mata bai hana namiji ya tsula miki tsiya, kuma abinda na fahimta shi namiji komi kankantar shi, (🙄🤣yana bukatar kulawar mace, balle kuma wanda ya manyanta, malaman Musulunci sun ce, idan kana da baligin yaro Magana ta gaskiya iyayen shi, suyita tambayar shi a siyasance sau nawa kayi mafarkin mace, kusan me yasa na sako haka sabida mu iyaye mata muke kashe yaranmu, Duk wani namiji na duniya zaka samu da zaran asuba tayi babu abinda yake buƙata kamar mace, sabida a lokacin nau'in halittar su tana tafasa, shi yasa wasu Mazan da zaran sun dawo sallah Asuba sai sun had'e da matar, wani muka kafin tafiya masallaci. Toh tun a kananun kananun su ake saka ido akansu,ina basu kulawa har lokacin aurensu, haka zai rage yawan matsalolin da muke fuskanta, sannan Idan har kika bincike shi baya jin wannan yanayi da asuba Don Allah, ki nema mishi magani kar ya auro yar mutane azo ana uwaka ubanka)
Sannan dole muyi hakuri dasu, tabbas abinda Ashraf yake min banda Ummina tana danne min zuciyata wallahi tuni na cire shi a rayuwata, amma bana son fushin Ummi shi yasa nake bawa Allah zab'i akan alamarina, dan na fahimci duk abinda zanyi inda ba Allah bane ya bani shi Kayan mata bazasu kwace Ni ba. Dan haka na tattara kayan zai maida sai na tuna Hausar malaman bahaushe da yake cewa.
_Dole kwalliya ta biya kud'in sabulu, sannan kowa yaci ladar kuturu tilas ya biya da yatsa, akan tauna tsakuwa dan aya taji tsoron, ya zama dole nayi amfani da su kodan rama cuta ga macuci..._
Murmushi nayi sannan na saka kayan a cikin jakar.
A raina nasaka koda zamu cigaba da zaman doya da manja, sai na sanya shi ya zubda hawaye a kaina, sannan ya kuma nunawa duniya wacce ni, sannan ya dauk'ak'a kimata a idanun duniya, ya gayawa duniya dame nafi sauran matan, amma dole sai nisance shi, dole sai naja layi a tsakanin mu. Dole nayi nisa da Ashraf, yadda zai gane darajata yayinda ya bud'e idanu yaga nisan tazarar dake tsakinmu a lokacin zai fahimci ni ina daraja ko bani da ita, dole na juya mishi bayan, yadda shi zai fahimci ni d'in Y'ace, dole na sadaukar da farin cikina domin samun dai-daituwa da Ashraf, Ni na fahimci kuskurena zuwa da nayi ba tare da izinin iyayena ba na kuma amince ya aurene, duk namijin da yasameka a bakagas dole yayi maka gani gani, tunda na nuna ina mutuwar Son shi, taya bazai juyani kamar boxes d'in shi ba, duk wata nasara da Allah yabawa Ashraf yasameta ne ta hanyar kusanci na dashi, sannan duk wata nasara da miji ko mace zasu samu a rayuwarsu, toh dole sai da taimakon juna, da zaran d'aya ya mike tabbas d'aya zai kasara, sannan tausayi shima wani tubaline da yake aure ......✍🏼
😫😪😤😰 Kuyi hakuri bani da lafiya sosai, 👏🏼🙏🏻
number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*
4️⃣2️⃣
Tausayin da soyayyar da na nunawa Ashraf ita ce, ta jamin komai. Domin da ita yayi ta amfani yana min iskanci son ranshi, dan haka nima na farka a giyar son shi dole na rama abinda yayi min.
Sai da nagama had'a kayana sannan na shiga wanka, ina fitowa yana shigowa.
Kauda kaina nayi, na shiga shafa mai, zama yayi yana kallon yadda na tsuke fuska. Sai duk ya diririce ya shiga inda-inda, ganin zaman shirun ya dame shi sai ya fara magana.
"SAFINAH! Ko zaki takura ne akan tafiyar na tafi da Zoyah."
Juyawa nayi na kalle shi na wasu mintina, sannan na cigaba da abinda nake yi, kallon bag d'ina Yayi, sannan ya dauke su ya fidda su falon sannan ya dawo ya same ni a kwance, daga Ni sai towel zama yayi a bakin gadon, yana kallon cinyoyina da suke masa dakuwa (🤣😂 Su Malam Ashraf an jima ba a haɗu ba)
Had'iye yawu yayi, yana jin abu na taso masa. Ƙoƙarin danne Kwadayin shi yake, hannunshi ya kai tsakanin cinyoyina yana shafa su. Banza nayi da shi a raina ina cewa, *zaka ji dashi*
Jin yana shirin wucce iyaka, bansan lokacin da na mike zubur ba, fuskana a daure nace.
"Don Allah ka rabu da ni, kaje ka tafi da matar ka, Ni da kake zaman banza dani ka barni na zauna lafiya."
Rike hannuna yayi cikin damuwa yace.
"Kuyi hakuri! Naga kamar na takura miki ne shi yasa nace ko zan tafi da Zoyah ne! Bawai dan na b'ata miki rai bane."
K'asa-k'asa nace.
"B'acin rai na nawa kuma! Hmm dake Ni ba yar dangin nace shi yasa ake nuna min iyakata kaje bani zuwa."
Duk sai ya shiga damuwa, ya rasa yadda zai dani, ga lokacin sai tafiya yake dan haka ya mike waje ya fita, ashe Dudu yakira ya gayawa abinda ke faruwa..
Ina kwance wayata ta fara kara ina dubawa naga Dudu .
Tunda muka gaisa ya shiga kawo min kabili da ba'adi, na dakatar da shi.
"Dudu kenan kace ya kiraka, toh bari na gaya maka wani abu, wallahi babu inda zanje ya tafi da matar shi, na tab'a gaya maka abinda yake min? Ko na tab'a kawo maka karan shi, tunda kaji nayi magana toh ya kure nine dan. Haka bani zuwa ko ina."
"Toh kiyi hakuri Didih ya gane kuren shi wallahi ya damu sosai."
Kashe kiran nayi dan shima haushi yake bani, shigowa yayi ya zauna tare da narke min kamar zai fasa kuka a raina nace.
" Baka ga komai ba"
Ciro wayar shi yayi ya, can ya manna a kunne yace.
"Ummi gata nan"
Mik'a min wayar yayi na watsa Mishi harara sannan na amshi wayar, tun kafin tayi min fad'a na fashe da kuka. Shiru tayi bata ce min komai, jin ina sauke ajiyer zuciya tace min.
"Ki tashi ku tafi Allah ya jibanci al'amuranki"
"Toh Ummi shi baza a mishi magana sai dai idan ya cuce Ni, Ace nayi hakuri.,"
Murmushi tayi wanda naji sautin shi sannan ta ce.
"Waye ya gaya miki ba a mishi magana!? Kina so na mishi fad'a ko!? Toh share hawayenki zanfi mishi fad'a shikenan."
Kamar tana gabana na gyad'a mata kaina.
"Ummina! Kawai kice ya dawo dani gida na gaji da nan d'in."
"A'ah SAFINAH! Ki zauna a d'akin ki."
Cikin wani irin kuka nace.
"Wallahi Ummi bana kaunar zama kusada shi ne."
Shiru tayi ta rasa yadda zatayi dani, kuma ta fahimce halin da nake ciki Indonesiya samu ne na samu sarari.
"Ki cigaba da addu'a, zaki ji saukin halin da kike ciki."
Nasiha tayi min sannan na mika mishi wayar shi.
Fita yayi daga d'akin, ya jima kafin ya shigo ya same Ni, ina saka kayana, zuwa yayi ya rungume ni ta baya yana fad'in.
"Kiya hakuri! Nasan nayi laifi amma Insha Allah zan gyara."
Share shi nayi nasaka d'an kunne na, abinda na Fahimta Ummi tayi mishi magana dan naga jikin shi Yayi sanyi.
Ina gamawa na saka gyalen rigar da nasa, na nad'e shi. Sannan na durkusa zan dauki takalmina ya rigani dauka, sannan ya ciro min, tare da d'aga kafana ya samin, yana gamawa ya mike tare da riko hannuna, a hankali na zare hannun fuska ba walwala nace.
"Ba sai ka rike min hannu ba nagode"
A raina kuwa jin haushin rantsuwa da nayi ne nake gashi nan zan bishi, muna fitowa falo naga Mujaheeda tare da Ablah sai kuka take, amsar ta nayi na zauna na bata nono muna gaisawa da ita, ina gama bata muka wucce part din Nannah, tana zaune jikokin suna kwance a jikinta, dan yanzun wani irin so take musu ko Natashah da take da cikin bata damu da ita ba, sai biyun.
Muna shiga duk muka zube a capter, muna gaisheta, kallon agogo tayi sannan tace..
"Kai da zaka fita karfe biyu sai yanzun zaka fita biyu da ashirin."
Raina nace.
*Allah ya haɗa shi da dai dai dashi ce*
Sosa kanshi yayi sannan yace.
"Na tsaya saka hannu ne a wasu takardun da aka kawo min ne, insha Allah yanzun zamu tafi."
A raina nace.
*Ji karya*
Shigowar Natashah wacce tayi fayau sai uwar kayan nono da uwar hanci, a hankali ta taki har inda nake, ta zauna tare da kallon shi tace.
"Maman Ablah! Baki da kirki rabonki da kizo duba ni har na manta"
Murmushi nayi mata sannan nace.
"Ran gimbiya ya dad'e! Nima ina cikin hidindumu ne amma ya jikin naki, ku ai matan so ne kuma y'ay'an dangi duniya tasan daku mufa yan karere ne dan haka idan Allah ya nufa zamu dawo tare zanzo na duba ki."
Tunda na fara magana Nannah da Ashraf suka zuba min ido, suna jin maganar da nake gaya musu magana a wasa.
"Kai Maman Ablah! Ai kinfi karfin karere, tunda ina ganin shigar Sultan shashinki tun karfe d'aya bai fito ba sai biyu da ashirin, ko Sultan"
Shiru yayi kamar baya gurin, a raina nace.
*Ikon Allah! Ni ina rena kulawar da nake samu ashe idanun wasu na kaina*
Mik'ewa yayi yace..
"Ammyn zamu tafi."
Nima mik'ewa nayi sannan nace.
"Nah zamu tafi, Tashah zamu tafi."
"Allah ya dawo daku lafiya! Hmm SAFINAH, dan tsaya."
Fita sukayi da Natashah, Ni kuma ni kuma na zauna.
"Kiyi hakuri, da abinda ya faru dukda nasan mun miki rashin adalci, amma Don Allah karki ce zaki guje shi, a yanzun tallafawarki yake nima, idan kika juya min baya, duk wahalar da akayi ya tashi a banza, a cikin mata dari dakyar ake cire goma masu Irin halinki, idan da za a cire goman nan ayi tankad'e dakyar za asamu d'aya me irin halin sak, SAFINAH badan Ni ba kodan Yaranki Don Allah ki zauna da shi mana"
Shiru nayi ban ce mata komai ba, dan itama haushi take bani, duk damuwar su yara da shi Ni babu wanda ya tab'a tunanin ina cutuwa ko bana cutuwa, ban san me yasa a duniya sai namiji yaci karen shi ba babbaka da zaran an ga, kafara yunkurin zaka kwaci kanka sai kowa ya fara cewa yaranka da kai kanka, bayan kai ma basu maka adalci ba, babu wanda zai dakatar da ni, dan lokacin da yayi min babu wanda ya dakatar dashi.
Mik'ewa nayi cikin sanyin murya nace.
"Sai mun dawo."
Haka na fita nasame shi da Natashah, tana mishi rigima. Kanta a bisa kafadar shi, yana ganina ya zame kanta a kafad'arshi, yana kallona ina zuwa muka rungume juna, nace.
"Gasu Ablah! Koda ban dawo ba ki rike min su da amana, shine iya abinda zan baki."
"Insha Allah, zaki dawo kuma zan rike su kafin ki dawo."
"Nagode"
Nace mata, sannan muka rabu, shiga motar muka yi ita kuma ta juya zuwa cikin gidan, tunda muka fita daga