Showing 99001 words to 102000 words out of 104042 words

Chapter 34 - MASARAUTAR JORDAN

CHN   

30 Oct 2025

3168

dashi hannunshi kaikayi yake mishi. Zan dauki kowacce iskanci amma abinda duka, dan baka isa ka tab'a Ni da rana da dare ka biyo NI kana min dan murya ba, Allah kayi kadan.
Tun daga lokacin da baki ya taba lafiyata sai ya daina shigo min, ranar da yake guna ma baya shiga, tattara shi nayi na watsa gefe.

Hhhhhh mayen mata dagaske zuciya yayi akan babar shi, ganin munyi kwana uku bamu hadu da Natashah ba, bayan Sallah la'asar na shiga gurinsu. Zoyah da Nannah suna zaune ana gulmar. Suna ganina suka firgice, Salam kawai nayi musu, sannan na wucce inda zai sadani da shashinta, tana kwance da katon ciki a gaba.

"Sannu Kyautar Allah! Irin wannan zungurerren cikin ko sojoji biyu zaki haifa mana."

Tashi tayi ta zauna tana murmushi, gashinta da ya barbazu take tattarawar.
"Maman Ablah! Ai nazata kinyi fushi dani ne baki gani na kenan kinki zuwa."

Tashi nayi na amshi bam din hannunta na daure gashin ta, sannan na zauna kusada ita.

Mik'ewa tayi zata kitchen nace.
"Dawo Ni na koshi, indai ba wahalar da sojojina zaki yi ba."

"Wallahi ba sojoji bane yan mata ne, irinsu Aamih."

Can sai gata da katon bowl me dauke da ya-yan itace ta ajiye min a gabana, sannan ta zauna a kasan capter.

Kallon kofar da nashigo tayi, sannan ta kalle ni, akwai magana a bakinta, sai dai kamar tana cikin tsoro, dafa kafad'arta nayi cikin kwanta da hankali nace.
"Banzo dan na sanyaki damuwa ba, ya hanaki zuwa gurina ko?! Gashi Ni nakasa hakuri na biyo ki. Amma tunda kina lafiya zan koma yanzun."

"A'ah Maman Ablah, kawai nice bana son fita. Amma Insha Allah zaki ganni."

"Toh shikenan tunda kince haka, amma."

Mun jima muna hira kafin na mike zan bar gurinta, mik'a min kayan fruit din tayi. Amsa nayi tare da godiya.

Inda nabar Nah da surukarta suna zaune, haka na ficce abina.

★★★
Da dare ina zaune nasaka laptop a gabana ina aiki. Zama shirun ba dad'i shine na nemi aiki da wata gidan jarida amma a Internet. Bai sani ba na nemi aikin kuma, kuma iya editing kawai suka dauke Ni nake musu.

Kuma zasu biyani kudi me kyau, dan haka na amshi aikin hankalina kwance, yanzun ma sun turo min da editing labarin da zasu yi amfani dashi shi. Ban ji shigowar shi ba, sai rufe min laptop din da aka yi.
Ban d'ago kai na mishi magana ba na buɗe abuna na cigaba da aikina.
"SAFINAH! Natashah bata gaya miki nace kar na kuma ganinta a shashinki ba, kenan kar na kuma ganin ki a shashinta."

"Ai kace yanzun mun shiga zamanin da za a hanaka walwala kenan?! "

Dake hankalina yana kan aikin da nake, na bashi amsan ashe yaji haushi na, daukar system din yayi zai buga da bango.
"Wallahi kana bugawa, na gama zama da kai har duniya ta tashi. Wallahi da ka fasa min shi gwara ka sallame ni, zai fi sauki akan ka fasa."

K'arban abina nayi sannan na cigaba da cewa.
"Ba zai yi kaki sauke hakkin da ya rataya akanka bayan ka hanamu walwala da juna sannan kayi tsammanin zan zauna bakin cikin ka ya kashe ni, bana fatan cigaba da zama cikin wannan kuncin rayuwar, kaje ka zauna da matar so da kuma Nah, sai dai kasani idan bakayi a hankali ba, hakkinmu Allah bazai kyaleka ba, kaje mun Barka da Allah."

Duk yadda yaso ya kuntatta min naki sabida na gama fahimtar shi na kuma san halin su.

Saima nice ke kuntatta musu, domin a gabansu zai gaya min magana baki kula shi, a bayan idanun su kuwa fasa juna muke, kuma har zuwa wannan lokacin bai shigowa dakina. Nima kuma bai dame Ni ba, dan baya gabana. Sai dai nasaka a raina matuƙar na haife cikin jikina, sai na bashi mamaki, dan ajiye mishi jaririyar zanyi na koma gida abuna na gaji da iskancin Nah da Zoyah, sun juyar mishi da hankali, baya gane me kyau ko mara kyau, shi dai burin ya ci min mutunci.

Bayan wata guda.....
Ina ƙoƙarin fidda su Aamih, su tafi makaranta, sai ga Zoyah. Dan har yaran sun fito, saura shi, yana dakin Zoyah. Nazo wuccewa, sai da nazo wuccewa kawai tazo zata bangaje Ni nayi maza na kauce sharrinsu ya koma kansu, ta fadi a gurin, ta fasa ihu.

Fad'uwar ba wata babba bace, amma tana kaiwa ƙasa sai ga jini.

Ashe yaji muryan ta, shine ya fito a guje.

Gani na a tsaye ya sashi yiin kanta yana tambayarta, cikin kuka take gaya mishi ai nice na tureta, gashi nan na zubda mata cikinta da tasamu, dan na tsaneta.

D'ago jajjayen idanunshi yayi akaina banji komai ba, sai ma kauda kan da nayi....


*Don Allah kuyi hakuri tun jiya rabonmu da wuta! Shi yasa zaku pagen dan mitsitsi idan muka samu wuta zuwa dare Insha Allah zan yi 48🤔 Wannan labarin yayi tsayi da yawa, da alamu sai mun shiga book 3 kenan Allah yayi mana jagora yasa mu dace duniya da lahira*
[20/03 2:30 PM] My 2nd Mtn: number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*

4️⃣8️⃣+4️⃣9️⃣

  Juyawa nayi zan bar gurin dan ban ga alamun faduwar da tayi ne ya zubda cikin, kawai dai akwai abinda ta shirya ne kuma zai koma kanta.

        Fincikoni aka yi lokacin guda aka sauke min wani mari akan idanuna, sai da na daina gani baki d'aya na tafi zan fadi akan cikina.
"SAFINAH!!!!" Ya kwala min kira, lokacin guda ya ture Zoyah a cinyarsa, kafin ya iso na fadi akan gwiwata, na dafe kasa da hannuwana biyu.

              Wani irin b'acin rai nake ji, lokaci guda. Mik'ewa nayi tare da juyawa zan bar gurin, ta kuma fincikoni zata mare Ni ya shiga tsakaninmu.

   "Ammyn ki Kyaleta! Ba ita kadai bace da ciki a jikin ta."

    Cikin fusata tace.
"Ita Zoyah ba cikin ne da ita ba, ta zubda mata,  Muhammad ka farka Yarinyar nan bata kaunar cigaban ka, amma baka fahimci haka ba, kamar yadda ta zubda mata cikinta itama sai na zubda nata, idan kuwa baka son faruwa haka sai dai ka saketa na gaji da ganin SAFINAH a karkashin inuwarka."

             Zubawa Nannah ido nayi cikin bakin ciki nace.
"Wallahi Nannah ke butula ce ke, idan Ashraf ya sake Ni sai ki zau.."

      "Shuuuuu" abinda naji kunne na na cewa kenan, yayinda na taune harshena. Sabida karfin marin Ashraf yayi min. Sauka kwalla yayi daga idanuna na dama, inda ya mare ni na kura mishi ido bakina yana rawa nace.

    " Ni ka mara?!"
   Kallon hannunshi yake kamar yaga sabon halitta.
"ASHRAF Ni ka mara?!"
   Dan duk abinda muke yi akan idanun Yaran, lokacin da ya mare ni, k'amk'ame juna suka yi tare da fashewa da kuka. Suna kirana,
  Lashe bakina nayi cikin murmushin takaici na taka gaban Nannah na tsaya, har numfashinmu yana dukar juna na kalli cikin ƙwayar idonta nace.
"Ki zuba ruwa kisha! Abinda kike son gani ya faru ince muyi rigima, Nah ya mare Ni sabida ke! Hmm zaki girbi abinda kika aikata."

   Sake fincikoni yayi, yana hucci bance mishi komai ba. Na saka kai zan koma cikin shashina, naji Muryan Nah tana ce mishi.
"Ka rabu da ita, dan wallahi bata da mutuncin."

    Nakai makura bana wasa ba, iya geji na kai, bana son na tanka mata har mu sake samun matsala da ASHRAF. Ga kuma Zoyah a gurin, shima barin gurin yayi har na shiga, na rufe koma na manta da yaran suna waje a dunkule guri guda.
             Ganin Ablah ce kawai akan kujera yasani kiran su, basa ciki. Komawa nayi da nasan komawar zata iya zame min matsala da ban fita kiran su ba, dan da na barsu a gurin rayu suke gurin Natashah ina fita naji suna saka dariya tare da magana.
"Ai karuwa ce! Sai da ta gama lalacewarta, sannan suka nacewa Ashraf. Suma Yan biyun shegune, dan haka  Ablah ce kawai aka same...."

      "Toh tsohuwar banza! Tunda nake ban tab'a bin wani namiji ba kuma da kike cewa na nace mishi, toh shi ya shiga rayuwata, Nah wai ke har kina da bakin zagina bayan ke kika lalata min rayuwa, bayan na cika miki burinki kika guje Ni. Wallahi tunda kika iya butulce min har abada babu wanda bazaki butulcewa ba, kuma Nagode da sheganta min Yarana, wacce bata san ciwon kanta ba, ke Zoyah kike idan baki bi a sannu ba wallahi sai kin gane kuranki."

           Dariya suka saka sannan Zoyah tace.
"Kee Safinah kike ko? Toh ai bani da ciki, munyi ne dan mu hadaku kuma haka yayi aiki, ashe ana tsoron komawa cikin wahala shi yasa kika ki biye mishi."

      Dariya suka saka sannan Nah tace.
"An ce miki karuwa! Ai duk Yar Arziki bata barin gaban Iyayenta ta shiga duniya ba, Yaran da suka san darajar iyayensu zama suke a inda iyayensu suka ajiye su amma kum"

        Ji nayi jikina na rawa, ban san, ya akayi ba sai gani na nayi a gaban Nannah, kamar dama sun shirya hakan eh shirine kam tunda sun san  nashiga ciki kuma, na fito toh meye ya fito dani? Yarana hujjar ya isa har ina kare kaina?  Yadda nake jin kamar na rufe ta da duka, tsakanin Nah da Allah ya dungule hannunta zata daki cikina nayi baya, ta dan gefen shashinmu anyi adon gurin da wasu tukwanen flower, shi Nannah ta raruma ta buga min, a bayana. Lokacin da najuya da sauri dan karsu tab'a lafiyar cikin, ina isa bakin kofar na tura yarana sani duk cikin gidan na jingina da kofar, a hankali nasaka key na rufe. Zamewa nayi na zauna a kasa, wannan bala'in har ina.

    Ina son nayi kuka, amma ganin Idanun Yarana ya hanani, badan komai ba sai dan su zama masu ƙarfin zuciya, kar su zama komai na rayuwa tsoro yake basu, amma a zuciyata kuka nake me kona zuciya da ruhi.

        Buɗe musu hannu nayi suka zo da gudu na rufe su a ciki.

            Wannan tashin hankali da me yayi kama, matan nan ta hanani sakat. Sai naki koda fita bakin barandar tunda na fahimci bazata bar gurin ba, burinta ta zubda cikin.
        ★★★
Kamar zararre haka ya isa gidan Ghaniyu, yana isa ya fito yana tafiya kamar wanda ya sha abin mayye,  buga gidan yake kamar zai balle musu kofa. Ghaniyu na buɗewa ƴa faɗa jikin shi, ya sake kuka kamar ƙaramin yaro,
"Subhanallahi! Sultan!! Me ya faru, ina Safinah meye ya sameta?!"

    Cak ya tsayar da kukan sannan ya kalli Ghaniyu ya girgiza mishi kai sannan yace.
"Marinta nayi."

"Akan me?! Kuma me ta maka ?! Har akwai abinda zata ka daketa?!"

           Yana kuka take bashi labarin abinda yake faru, kallon renin hankali Ghaniyu yayi mishi.

   "Ai haka ne?! Ina ga ka sake ta kawai ta koma ƙasar ta, zai fi saukin wannan cin mutuncin, an hanaka shiga gurinta tayi hakuri, sannan yan, dan nayi magana abisa kuskure shine ka mareta, toh idan kuma fitar da kayi su suka cutar da ita, waye gatanta! Don Allah doka fitan min a gida wallahi idan hakkinta ya kamaki sai kun gane kuranku."

             Sai da Ghaniyu yayi mishi tass sannan suka tattauna akan abinda Nannah tayi yace .
"Wallahi bazan b'oye maka ba Ammyn bata kyauta ba! Domin ita Uwace taya zata rike ka da wani abinda babu hujja, sannan dan rashin imani har kana marinta dan tace ka zauna da Ammyn idan ka rabu da ita, kai idan akawa Yarka haka zaka ji dad'i, Wai tukun kama da Imani ma kuwa, kamar yadda ka hana Natashah walwala ita Safinar haka kake son ta zauna karya motsa, a waje kai sarki ne a gidan ka mata biyu sun birkita maka lissafi. Indai har ka iya zaro masu laifi toh wannan karon ina bukatar kayi bincike, abinda ke faruwa zaka yi "

          Sun tattauna sosai sannan yayi mishi Sallama, har zai fita Ghaniyu yace.
"Majnun angon layla, idan ka kuma a daina kuka idan aka toshe layla."

Banza yayi dashi, sai da ya tadda motar shi, ya d'aga mishi hannu..

    ★★★
Wato su Nannah basu bar gurin ba sai da Ashraf ya dawo gidan, sannan suka bar gurin.

....... A dakin Natashah tana can tana fama da ciwon tun jiya, idan ciwon yayi mata sai ya saketa, har ta fara barci, wayarta ta ciro takirani, ina bakin kofa naji karar wayar dakyar na mike naga Natashah, da sauri na dauka.
"Natashah lafiya?!."
"Maman Ablah! Bani da lafiya kizo."

Kashe kirar tayi, idan hankalina yayi dubu ya tashi, a hankali na mike sannan nacewa yarana.
"Ku nutsu karku fita yanzun Zan dawo."

Gyad'a kansu sukayi na fita da sauri. Na same su, duk suna falon a zaune, ciki na shiga naga itama Natashah ta fita hayacinta, da sauri na fito na gaya mishi, amma yayi banza dani. Sai da nace mishi.
"Toh wallahi idan wani abu ya same yar mutane sai na gayawa Iyayenta"

Ina gama faɗar haka ya biyo NI da sauri, kayanta na ciro nasaka mata. Sannan na ciro duk abinda zata bukata, sannan muka nufi waje da ita, yana sakata a mota ta riko hannuna.
"SAFINAH!!"
Da mamaki na kalle ta sabida bata taɓa kirana ba, sannan ta cigaba da cewa..
"Don Allah idan na haihu! Ki rike abinda na haifa na bar miki duniya da lahira, idan kuma Maah ta karba don Allah ki saka ido akan babyn, SAFINAH ki yafe min."

Fincikoni Nah tayi na fito daga cikin motar, gaba na faduwar, ina ji ina gani suka tafi da ita Asibiti, wanda yake cikin masarautar, sabon Fad'uwar gabana ya kamani lokacin da na nufi cikin gida naga kofana a bude. A hankali nake jin nauyi a kirjina har na isa falon abinda idona ya gane min ne ya bani tsoro da tausayin kaina da rayuwata

Allah sarki Ashe ganina dasu kenan na karshe, rungume su da nayi dazun shine na karshe......✍🏼


Kuyi hakuri Don Allah, rashin wuta muke fama dashi



number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a 500fs  +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
   *Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150₦ ne idan kuma Kati ne Transfer 200₦ ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode Masha Allah*

5️⃣0️⃣
   Ganin har lokacin Aamih tana aman kumfa, na shiga cikin kitchen da mugun gudu na dauko mangyad'a na d'ura mata, komawa kan Aanih nayi, itama na juye mata, ita Maryamah tana amai, Husnah shiru, banga Ablah a falon ba.
      "Ablah!!!!!!!"
  "Ummu"
       Naji muryan ta, a sukwane na juya, jikina na rawa.
Ganinta nayi rike da wani apple,  kuka ne ya kwace min, na janyo ta sannan na dauki wayata, tsabar rawan jiki, dakyar na sami Number shi, yana ɗauka na fashe da kuka.
"Kazo yaran suna cikin hatsari, kowani lokaci zasu iya mutuwa."

         Kashe wayar nayi yi ina kuka, bai yi cikakken minti biyar ba sai gashi. A gigice shida Ghaniyu, suka dauki yaran. Ni kuma na dauki Ablah har na kwace apple din sai na saka kuka kuma baci zata yi ba, dole na bar mata, muka bi bayan su.

              Tunda muka shiga motar nake kuka, ina kallon yaran.
     Har muka isa asibitin aka shiga dasu d'akin gaggawa, haka su Dr Fu'ad suka yi takaiwa da komowa.

              Zuwan wani likita dan kasar Lebanon, yazo wuccewa ya kallemu. Har ya tafi sai ya dawo yasaka hannun ya amshi, kuka tasaka tana ihun ya bata abinta, tafiya yayi da apple din, babu wanda yayi Wani yunkurin, dan muna cikin tashin hankali.

     Jaririn Natashah aka fara fito mana da shi, yaron me kyau kamar Ashraf.
Muna cikin wannan halin Dr Fu'ad, ya fito tare da kiran Ashraf zuwa Ofishin sa, yana shiga yace.
"Fu'ad ya jikin su?!"
      Girgiza kai Dr Fu'ad yayi sannan yace.
"Kayi hakuri! D'aya ta rasu"
    Zaman dirshan yayi a Office d'in, tasirin kiran sunayen Allah ya rike shi, kafin ya d'ago kai yayi yace.
"D'ayar fa?!"
 
  "Sakamakon bata mai da akayi ya karya ƙarfin gubar, tana nan sai dai ta jikata sosai."

     Bai kuma ce komai ba yafito  daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login