Showing 102001 words to 104042 words out of 104042 words

Chapter 35 - MASARAUTAR JORDAN

CHN   

30 Oct 2025

3194

Office d'in.
     
  Tunda ya fito ya tsare Ni da ido, gabana ke faduwa, kukan da nake toshewa ne na shiga yin shi sosai.
Kauda kanshi yayi sannan yaje gurin Ghaniyu yayi mishi magana, fitowar Likitan da ya karbi apple a hannun Ablah yazo zai magana, Ashraf ya hana shi yace yaje yace yaje ya sami Dr Fu'ad.

Nannah ya gayawa mutuwar Husnah, a fusace ta mike, shi kuma ya bar gurin zuwa dakin da gawarta take ciki,
Ina cikin damuwa Nannah yazo zata kara min, dan d'aga hannun tayi zata mare ni na riƙe hannun.

Sosai ta nemi duka na, na hana faruwar, haka Rigima ya kaure a tsakanin mu, fitowa da gawar na kurawa Yarinyar ido, naje kan gawar na sake wani Irin kuka, me mugun cin rai.

Rike hannunta nayi nace.
"Wani irin laifi nayi haka da nake fuskarta hukunci haka, Ya Allah na tuba ka yafe min zunubi na."

Fitowar Nurse daga d'akin gaggawar, tace.
"Yallabai d'ayar ma ta cika."

Ji nayi zan fad'i yayi maza ya sake jikin gadon ya rike Ni, gam nake rigarshi ina sauke ajiyar zuciya, kafin nace.
"Alhamdulillah."
Cak naji hawayena ya kafe, tabbas lokaci yayi da zan bar Ashraf, dan Natashah tana cikin mawuyacin hali itama, haka suka fidda yaran, muka nufi gidan.

Anan aka kira masu wankar gawa, suka musu shi kuma Ashraf ya kira su Ummi ya gaya musu, zazzaɓi ne ya rufe ni. Dakyar yasani a gaba naje naga gawarsu, nayi musu addu'a. Sannan na fita, wani irin dangana nake ji a raina, sai dai bana jin zan cigaba da rayuwa a jordan.
Tun daga ranar ban kuma ganin Ashraf ba, har sai dasu Ummina suka zo naga idanunshi, abinda nake gani a cikin idanunshi yana kara rikita min lissafi, domin kuwa k'iyayyar da ban san da ita ba yake nuna min, Ummi da Umma suka zo sai Abba, Dudu yana Ukraine yana karatun da matar shi.

Kwanansu Ummi biyar suka dawo, ana gobe zasu dawo Abba na yakirani, naje inda yake duk suna zaune na zauna a gefen Umma. Kallona suka yi sannan Abba yace.
"Kuyi hakuri! Allah zai baki wanda suka fisu! Sannan na fahimci kina cikin damuwa, kiyi hakuri ki cinye jarabawarki, Insha Allah komai zai zo karshe."

Nasiha suka min, mun jima muna hira, kafin muka yi sallama, har zan fito naji Muryan Ummi tana cewa.
"Alhaji idan zaman ba me yuwa bane ta dawo gida kawai, na gaji da fitina, nima ina son Y'ata, ta bar mata D'anta."

"Amma Mariamah me yasa zaki d'aga murya ne! Idan kuma taji fa"

"Ai gwara taji, lokacin da nayo cikinta waye ya tayani sai wasu banzaye su samin yarinya a gaba."

Ni dai nabarsu ban san ya suka kare ba, sai da asuba da zasu tafi. Dake jirgin biyar da rabi na asuba, suka samu, ta shigo min, munyi magana sosai wanda naji du duniya bani da sama da Ummina.

Iyayen Natashah sun zo sun dauketa, inda suka tafi da ita domin sai da suka yi uwaka ubanka da Y'ar Uwarsu. Tunda Yaran suka rasu Ashraf ya fidda min wani iskanci, da bakar magana idan yazo shashina, sai ya wucce dakin yaran yaje ya zauna, yayita tuna yaran. Idan naga ya jima sai na biyo shi, koran kare yake min.

Yau ne dai da ya fara min na dakatar dashi.
"Ban san laifin da nayi ba kake min wannan tozarcin, Ashraf ban maka dole ba, kuma kai baka min dole na zauna da kai ba. Dan haka rayuwa yana da zab'in shiga ko fita. Amma ba damuwa gani na da kake a rayuwarka ya saka ke ganin na cutar da kai idan na fita daga rayuwarka, sai kayi farin ciki."

Ina gama fad'ar haka na fita na bar dakin na koma nawa nayi kuka sosai, yanzun nake jin mutuwar yaran, had'a kayana nayi dana Ablah. Sannan na dauki wata memo na rubuta mishi sako.
_Nagode sosai da irin abinda ya faru_

Daga haka na ajiye biron na dauki Ablah,na goya sannan naja akwatina nafito bayanan, duba agogo karfe goma, na koma na duba jakata, na debi kudi na zuba, sannan na fito na bar cikin gidan a hankali na bar Masarautar baki d'aya.

★★★
Oman.....
Tunda suka dawo da ita sai yau Allah ya nufa ta bude idanunta, akan likitan da yake dubata. Sake lumshe idanun tayi kafin ta bud'e tare da juyar da kanta gefe.
"SAFINAH!! Ki koma zasu kashe miki yaranki, SAFINAH ki koma zasu kashe miki yaranki."

Alluran barci suka mata, sannan likitan ya fito, ya sami Iyayenta yace.
"Wacece SAFINAH? Toh ita mara lafiyar take kira ta koma zasu kashe mata yara."

Shiru duk gurin akayi sannan ya kara da cewa.
"Insha Allah zata tashi, sai dai kamar taci wani abu wanda ya haifar mace da kumewar jini a cikinta bayan ta haihu jinin ya taru, mun same nasarar fidda jinin."

Yana gama musu bayani ya fita.....

★★★
A cikin ɗakin ya kwana, har ya makara ma, fitowa yayi bai ji motsin ta ba, dan haka yayi wuccewar shi. Abinda Ya bashi mamaki yana murɗa kofar yaji shi a bude, juyawa yayi ya kalli kofar ta. Sannan ya fita zuwa masallacin sai da garin yayi haske, sannan ya dawo gidan a gurin Ammyn shi ya tsaya suka gaisa, shiru yayi kan a sunkuye kallon shi tayi cikin kulawa tace.
"Kayi hakuri! Allah zai maida maka masu alkhairi."

D'ago kai yayi ya kalleta sannan ya mik'ewa yayi, ya bar falonta. Halayyar shi na baya yake son dawo da ita, duk yadda kaso mishi magana dakyar yake cire kai ya kalle ka, koda ya shiga gurin Zoyah ya sameta tana ta barci fita yayi ya koma gurin SAFINAH, koda ya shiga ya samu bata fito ba, dakin yaran ya koma, ya kwanta a kan gadon su.

Yana tuni ana gobe zasu rasu da yazo kwantar dasu suka fara rigima, akan ya goyesu, aikuwa ya dauke su, kowa ya dauka sai daya ta fara ihu, a haka SAFINAH ta same su dams yazo daukar Ablah ce, kuma ba shiri suke dashi ba, har zata fita Aamih tace.
"Ummina kice Appa ya goyi,"
Da sauri na bar dakin tana jin lokacin da suka saka dariya har Aanih nacewa.
"Appa! Ummu tayi nauyi bazaka iya daukar ta ba," cikin dariya yace.
"Ai Ummunku bata da nauyi kamar ku haka nake daukar ta."
Aikuwa suka saka ihu.
"Yeeeeeeee! Appa muje ka dauketa a gaban mu"
Narke fuskarshi yayi dan baya don zuwa gurin SAFINAH dan kartace yazo da laluransa, shine ya lallaba yaran suka kwanta, a jikin shi, sai da ya tabbatar sun yi barci, sannan ya fita a falo suka had'u tana sanye da rigar barci sau daya ya kalleta, ya kauda kanshi, dan ganinta sai haka ba karamin d'aga mishi hankali yayi ba.

Kwallar da suke sauka ne ya an karar dashi halin da yake ciki.
*Taya SAFINAH tabari aka kashe mishi yara?!* Wannan shine tambayar da kullum yakewa kan shi, kuma har yanzun bai da me bashi amsa,

A sannu barci yayi gaba dashi, me cike da mafarkai marasa tushe, farkawa yayi yana jin sautin kuka, yunkurin mik'ewa yayi wani irin barci ya kuma ɗaukar shi, dakyar Allah ya bashi ikon farkawa. Tashi yayi zaune yana kallon d'akin yana son tuna abinda ya gani ya manta dan haka, ya tashi ya bar dakin. Yadda ya wucce falon haka ya dawo ya samu, anan ne zuciyarshi ta fara girgiza,. D'akinta ya shiga ya same komai a nutse.

Da azama ya buɗe ban daki, yaga ko dingon ruwa babu, bai gamsu ba, sai da ya fito zuwa kitchen yaga babu SAFINAH babu labarin ta.

Bai tsaya ba ya wucce gurin Ammyn shi, yace.
"Ammyn ina SAFINAH ta tafi."

Baki sake ta kalle shi, sannan tayi sannan tace.
"Ina zan san inda taje, kaine ka yarda da ita ai nasan komai akayi sai ta nuna maka cewa ita din Karuwa ce."

"Ammyn ba shi na tambaye ki ba, ina matata tashiga?! Wallahi wani abu ya sameta dake da Zoyah sai na baku mamaki, ya kuke so nayi ne? Ammyn me kuke bukata na baki ki rabu damu "

Fita yayi daga cikin gidan cikin lokaci ƙalilan kowa yasan Sultan na niman matar shi, cikin awa gudu aka birkita garin jordan, har babu inda ake wuccewa sai ka buɗe motarshi, tashin hankali yayi yawa.
Da farko ya zata tana kusani sai tayi fushi sai yaga ba haka bane abun dan har an dauki lokaci ba a ganta ba, tsabar bai yarda ba da kanshi yaje gidan Ghaniyu da kanshi yaga bata nan, a nan ne fa yasa aje tasha jirgin sama, da ta jirgin kasa. Sai na Safa safe, aka shiga niman SAFINAH, har Airport sai da aka je niman nimanta da hotonta ba a sameta ba, sosai ya gigice tun safiya ake abu d'aya ko ruwa bai saka a bakin shi ba, cikin wuni guda Ashraf ya koma, wani zararre. A sanadin haka sai da yasa aka rufe masu tsaron gidan shi tare da, zuba wasu.

Gidan shi kuwa yaki magana da kowa, karshe da Zoyah ta dame shi da tambayar ganganci, kiran wani daga cikin masu tsaron gidan yace.
" A kai ta gidan su, shi zai nimeta"
Kallon Nannah tayi ko zata yi Magana amma ta wani dauke kai kamar bata gurin haka suka fita da ita ta juya yaje har gaban Nannah tace.
"Wallahi mu zuba dake."

Haka suka kad'ai keyarta....

★★★
"Maah kice SAFINAH ta je karsu kashe mata Yaranta,"
"Toh Natashah za a gaya mata!"

"Maah Ammyn bazata gama da duniya lafiya ba, Ammyn tacutar Da SAFINAH! Maah kice SAFINAH taje kar su cutar mata da Yaranta."

Iya wannan shine abinda Natashah ke fad'a, kuma idanunta na rufe maganar, duk hankalin iyayen ta a tashe, ga jaririnta madara ake bashi, sakamakon bata da ruwan nono, idan kaga ta sai ka zubda hawaye tsabar tashin hankali.

Alhamdulillah book 2 ya kare, cikin yardan Allah,

Ga dai abubuwa sun faru ba a san yaushe suka faru ba,
Tsakanin Nannah da Zoyah akwai alaka me karfi!?
A cikin Nannah da Zoyah wacece tayi nasaran bawa Yaran SAFINAH guba?
Me Natashah ta sani! A pagen baya Natashah ta rike hannun SAFINAH zata mata Magana Nannah ta fincikota! Me take son Sanar da Safinah?
Kalmar dake Yawo a bakin Natashah, SAFINAH taje karsu cutar mata da Yaranta, iya shi take fad'a, kenan Akwai wani kulli da tasani.

Na cire muku Abinda baku yi nazarin shi ba.

Duk abinda ke faruwa Sabida Ashraf ne! Sannan Nannah da Zoyah sun taimakawa juna..... Meye silar taimakon......


Book 3 na hanya......

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login