Showing 27001 words to 30000 words out of 136985 words

Chapter 10 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

2125

don Ni na dad'e da sanin hakan"

Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki ta kalli Maigarin tace,. "Don Allah ka yi man iyaka da shi tun kafin ya kassarani"

Maigarin gano inda ta dosa yace,. "Ai kuma tunda kince baki sonshi shikenan zance ya wuce, amman ki sani don yace yana sonki kin amince masa ba shi zai sa ki yi ciki ba, don haka kai yarona ka bata hakuri kuma a kiyaye faruwar hakan a gaba tunda dai ita tace bata sonka"

Lawi ya mike Dije ta yi saurin kallonshi tace,. "Ina zaka je kuma bayan baka bani hak'urin ba?"

Ya fuske yana saka talkamanshi yace,. "To ki taso mu je daga cen sai in baki hakurin in kina so"

Dije ta mike ta bi bayanshi har zuwa wani k'aton kututturen icce da ke gefen k'ofar gidan Maigarin ya zauna, Safwan ya bisu da kallo ya yi mere ya shige d'akinsu sai dariya yake kyakyatawa.

Dije ta yi tsaye kikam tana girgizar jiki tace,. "Bani hak'urin Ni dai in tafi inda zan je kar aga na dad'e"

Lawi ya kai kallonshi ga su Maigarin ganin basu kallonshi ya washe fuskarshi yace,. "Ai dai nasan kina son kije Makarantar gaba da primary ko?"

Dije ta saki baki sake tace, "Eh kai zaka kaini?"

Ya yi saurin fad'in

"Tabbas in har kin amince kin aureni to Ni na yi maki alk'awali Ni zan kaiki kiyi Makarantarki har ki yi degree ki zama likita kina yi wa marasa lafiya allura"

Dije ta zaro Ido cikin jin dad'i ta yi saurin zaunawa kan iccen tace, "Don Allah da gaske kake yi zaka kaini in yi likita ???"

Yace "me zai hana in har zaki aureni"

Dije ta yi shiru sannan ta ce "Ni ba Wai aurenka ne matsalata ba bana son ne ince ina sonka don WALLAHI na tsani in haifi macizai saboda tsoronsu nike ji sosai, akwai ranar da muka je daji muka ganshi WALLAHI har suma sai da na yi acen aka kwasoni aka kawoni gida"

Ta k'are maganar cikin zubowar wasu yanmatan kwallah, Lawi ya yi saurin fad'in

"To ya isa daina kuka Ni na hak'ura ko baki ce kina sona ba in dai har kin yarda zaki aureni shikenan Ni kin gama mani komi, Ni ko zan kaiki ki yi karatu har ki fito matsayin babbar likitar Mata"

Dije ta washe Baki cikin tsananin jin dad'i tace,. "Aiko WALLAHI na amince kai Ni gobe ma ayi auren muje in fara karatun Likitancin"

Lawi ya zaro Ido waje yana dariya yace,. "Masha ALLAh lalle Ni Lawi dangata ne"

Dije ta rufe fuska tace,. "WALLAHI ina son inga ina yiwa mutane allura nasan sai sunyi ta kuka"

Lawi ya tuntsure da dariya yace,. "Au to mugunta ma za ki yi ashe ba taimako ba??"

Dije tace "duka biyun ai Ni ina da tausayi wani zubin fa in naga ana kuka nima sai inji ina yi"

Lawi bakinshi a washe yace,. "ALLAHu Akbar ashe haka Dijen take da imani ban sani ba?"

Dije ta rufe fuska tace,. "Ni dai yaushe za'a yi auren in fara zuwa karatun likitar?"

Lawi ya sassauta murya yace, "to ai ke sai kin gama wannan da kike yi sai kije ta gaba sannan ki fara ta Likitar"

Dije ta zaro Ido tace,. "Cabd'i ashe abun da wahala? To yanzu ita ta gaban wannan da muke yi mi ye sunanta??"

Lawi yace,. "Secondary". Dije ta yi saurin maimatawa tace,. "Sakandari?"

Ya ce,. "Eh".

Tace "shekara nawa ake yi a gama to?"

Yace "shekara shida ce itama kamar primary"

Dije ta zaro Ido cikin sanyin jiki tace,. "Anya ko Baffahnah zai barni in yi karatun kuwa??"

Lawi cikin farin ciki yace,. "Me zai hana ke dai kawai kice masa kina son akai ki idan har ya amince ko kina cikin karatun sai a yi muna aurenmu ki je kici gaba a gidana"

Dije ta rufe fuskarta cike da jin kunya ta tashi ta zank'ara da gudu aguje ta nufi gida cikin tsananin farin ciki, Lawi ya bita da kallo yana dariyar shirmenta musamman da ya tuno da zancen zai lalatata ya yi mata ciki don ba ya da imani.



Dijelawis asha luv lfy🤣


Akafta😛






D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN K'ARANGIYA GA JINJINAR BAN GIRMA👍🏻😝*


*Lamba ta 18*



Da tsallen jin dad'i ta shiga gidansu sai wasar Baki take yi, Inna ta bita da kallon mamaki wadda ta fita tana kuka yanzu kuma itace ta dawo tana wasar Baki, aiko sai da ta zauna daf da Inna sannan ta kwanta saman cinyarta tana rufe ido da tafukan hannayenta, Inna ta shafo dunbujen tulin gashinta da kullum ba'a wuce yi mata tsoro hudu a saman Kan nata, saboda bala'in jin zafin kitso ne da ita gashi gashin a cikenshi yake da kuma tsawonshi tubarakallah, don ko shartar gashin za'a yi mata idan an kwance sai duk makota sun sheda, saboda kururuwar da zata dinga yi tana kukan wayyo ita zafi, shiyasa kullum kitsonta tsoro hudu ne don ko shi d'in sai Inna ta ajiye bulala a gefe sannan ake yinshi tana kuka har da su majina shabe shabe, saboda in ta kawo mata reni kai tsaye ta ke mazgarta da bulalar, shiyasa in dai har ranar kitson ta zagayo to ko Baffah dole ne sai ya siyo mata wani Abu a matsayin cin hanci don kawai a samu ta natsu a yi kitson lami lafiya, amman da ta canye abun sai a koma tarxomar da aka saba kullum.

Tana shafar gashin kan nata tace,. "Yau kuma me ya saka 'yar Baffah farin ciki irin haka??, Ke da kika fita da kuka to me ya sakaki wannan murmushi da kike ta yi?"

Dije ta tashi daga kwancen ta rufe fuskarta tace,. "Inna mun shirya da D'anbirni har ma ya yi man alk'awali zai sakani Makarantar Likitoci in dinga yiwa mutane allura"

Inna ta zaro ido waje tace,. "Au kin amince zaki aureshin yanzu??"

Dije ta rufe fuskarta alamun jin kunya tare da d'aga kanta, Inna ta bita da wani kallon yaron man kaza tace

"Kina sonshi kenan?"

Dije ta mik'e da sauri zata shige d'aki tace,. "Ni WALLAHI fa bana sonshi amman zan aureshi saboda ya kaini Makarantar koyon Likitanci"

Har zata shige ta dawo baya tace,. "Kin ga shikenan Ni sai in dinga yiwa mutane allura ba har sai an tafi zuwa birni ba"

Inna ta maka mata harara tace,. "To sai aka ce da ke in har kin aureshi a nan garin zai zauna da ke ko?, to bari kiji garinsu nisa ne dashi ke asali ma sai anyi kwana biyu ana tafiya kafin aje cen d'in, kin ko ga Baffahnki ba zai tab'a bari ki yi auren ba saboda nisan da ke tsakaninmu da su"

Dije ta dawo tare da kumbure fuska tana dire diren kafa tana fad'in,. "Ni WALLAHI Inna ina son in zama Likita don ALLAH ki ce da Baffah ya barni in aureshi don ALLAH"

Aikuwa caraf sai ga kunnen Baffah da ke shigowa tare da Usman, cike da mamakin abunda ya jiyowa kunnenshi ya k'araso idonshi akanta yace,.

"Me naji kina fad'a ne???"

Dije ta isa wurinshi da sauri ta rik'o hannunshi tana share yan guntayen kwallar da suka zubo mata tace,. "Baffah D'anbirni yace dani idan na aureshi zai sakani Makarantar likitoci in zama babbar Likitar Mata don ALLAH ka barni in aureshi WALLAHI ina son zama liktanya Baffah don ALLAH kaji?"

Ta k'are maganar tare da d'aga kanta ta kalleshi cikin marairecewa, Baffah ya k'wace hannunshi da ta rik'e ya tureta gefe ya wuce yana fad'in

"Ke wace irin yarinya ce da kullum shirmenki k'aruwa yake yi? Sai ana murna anga sauyi sai kuma ki k'ara tsunduma ruwa? To bari kiji ni zan ganshi da kaina in sanar dashi cewa ba Zan bashi ke ba, tunda har baiji kunyar zaunar dake ya sharara maki wannan k'arya ba, ke kuma da yake ba wayau ne da ke ba kika amince da zancenshi na yaudara, to WALLAHI na sake jin ma kin tsaya da shi kunyi magana sai kinsan d'anjaki dukiya ne, tunda ke kwakwalwarrki bata hasko komi sai shirme mara tushe bale makama, ke Makarantar ma kin daina zuwa daga yau sai nagani in akwai wanda ya isa yasa ki koma"

Haka ya yi ta sababin fad'a Dije kam ta rabe jikin gini sai kukanta take sharba, Usman ya maka mata wata jar harara yace

"Wawuya kawai mara hankali ke in banda wauta irin taki ma me 'yanbirni irinsu zasu yi dake ne? Da har zaki yarda da karyar da ya shinfida maki??ke da ko wanka har yanzu baki iya ba sai bak'ar jik'a jik'ar daud'ar da kike yi kullum, har sai Inna ta gaji da kazantarki ta yi maki a hakan za ki je birnin?? ALLAH yasa ma Baffah ya hanaki sake zuwa Makarantar da gaske muga ta iyayin bacci da Littafin Boko a karkashin filo"

Ya buga mata wani uban tsaki ya shige d'akinshi, Dije ta bishi da harara tare da murgud'a Baki tace,. "Ai billahillazi in na zama likita ko zaka mutu bazan yi maka allura ba"

Usman har zai shige d'akinshi ya waigo yace,. "ALLAH ma ya tsareni da allurarki WALLAHI, kuma yarinya ta jira idan har taga ta zama Likitar sannan"

Dije ta bi k'ofar da kallo tana harare harare sannan ta yi tsugunne tana wasa da kare tana zane k'asa tana rubuta,

_WALLAHI Ni sai na zama likitar nan_

Ta goge ta sake rubuta

_Idan ba haka ba daji Zan koma da zamana acen kuraye da sauran namun daji su cenyeni tunda har ba'a sona._

Haka ta lalace a wurin ta yi ta shirmenta har sai da Inna ta fito ta korata ta shiga d'aki.

*****

A bangaren Lawi kuwa tana tafiya ya nufi wurinsu Maigarin Baki har kunne yake sanar da su cewa Dijen ta amince, Maigarin ya yi masa wani kallo yace

"Yaro man kaza to bari kaji gaskiyar lamarin Mahaifinta ya tabbatar man da cewa ba zai baka aurenta ba, don haka kaje ka nemo wata in har sha'awar aure a cikin garin namu kake yi, ka duba da kyau Akwai sa'o'inta da yawa a garin har ma da wad'anda suka fita, duk Yar da kake so ka nemota Ni zan shige maka gaba har sai ka sameta, matuk'ar ba wannan masifaffiyar yarinyar bace"

Lawi murnarshi ta koma ciki, cikin sanyin jiki yace

"Idan har ba zan sameta ba a bar zancen wata kawai Baba"

Yana kare fad'ar maganar ya mike ya nufi d'akinsu zuciyarshi sai hasko masa fuskar Dije take yi lokacin da take rufe fuskarshi alamun jin kunyarshi, don kuwa saura k'iris ya rage ya ci k'asa saboda wani uban tuntuben da yayi, cikin yamutse fuska ya shiga d'akin ya fad'a kan katifarshi ya baje tare da d'ora hannu a saman goshinshi yace

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil!"

Safwan da ke ta game a wayarshi da ko caji har sai sun kaita babban garin sun samo sannan su yi ta maneji har lokacin da ya sake cenyewa, shiyasa suka fara shawarar saka Generator su huta da zirga zirgar kai cajin da suke yi.

Ya yi saurin kai kallonshi gareshi ganin yanayin da ya ganshi yasa ya ajiye wayar ya tashi zaune yana kumshe dariyarshi yace

"Yanzu Kai don baka da imani shine kake so ta yi ciki?? To WALLAHI Ni babu ruwana idan ka janyo ta haifi macizai"

Ya k'are maganar cikin shekewa da wata arniyar dariya tamkar ba Safwan ba, saboda ba k'aramin dad'i ya ji ba akan wannan wasar kwaikwayon da Lawi ya yi da Dijen, Lawi ya mike zaune cikin damuwa yace

" Seriously WALLAHI ina son yarinyar sosai, bansan ta ya zanyi in shawo kan Mahaifinta ba, har in samu ya amince ya bani aurenta"

Safwan kam sai kallonshi yake yi da gabanshi da ke ta fad'uwa da sauri da sauri, cikin dakiya yace dashi

"To ita yarinyar ta amince da kai ne halan?"

Lawi ya dafe kanshi yace, "bana jin yarinyar yanzu saboda na fahimci ta inda zan shawo kanta cikin sauk'i in janyo ra'ayinta a kaina, don ko yanzu na gano tana sona k'urciya ce kawai tak'i bari ta gano hakan, amman Mahaifinta ne matsalata don yanzu Maigari yake sanar dani wai yace shi ba zai auradda d'iyatai gareni ba saboda munyi nisa, to Ni WALLAHI idan zai amince sai in dawo nan garin da suke karkashinshi in nemi aikina a nan, idan na samu sai in zauna nan din mu shimfida rayuwar aurenmu Ni da Matata"

Safwan ya yi masa wani kallo yace,. "Su Kuma iyayenka da sauran danginka sai ka yi ya ya dasu??"

Lawi ya yi saurin fad'in, "Zan dinga zuwa Ina dubosu ai WALLAHI ya fi man da dai ace in rasata gaba d'aya"

Safwan ya buga wani uban tsaki yace

"Lalle akwai alamun tabin hankali a Kwakwalwarka tunda har zuciyarka take hasko maka hakan shine dai dai, yanzu akan mace macen ma wannan kucakar yarinyar ace zaka rabu da kowa naka akanta?? WALLAHI ka yi kuskure don tun wuri ka ajiye wannan shirmen banzar, ko ka manta cewa Kaine fitilar da Mahaifinka da mahaifiyarka da kannenka suke haskawa su ji sanyi?? Ka yi nesa da su ta ya ya kake ganin zasu dauki hakan a matsayinka na mai taimakonsu???"

Lawi ya furzar da iska a bakinshi yace, "ba zaka gane ba ne Abokina WALLAHI ina mugun son yarinyar, nima bansan ya aka yi har ta sami irin wannan mazauni a zuciyata ba kada ka ga laifina plss!"

SAFWAN zuciyarshi sai dakan lugude take yi muryarshi a sarke yace,. "Yanzu kai duk matayen da ke duniyar nan ka rasa wadda zaka so sai wannan bagidajiyar??"

Lawi ya maka masa harara yace,. "Plss abar zancen na godewa ALLAH da har ya b'oye maka abunda ni na hango, wanda a birnin ma ire irenta ne suke d'aga kai suna hurar hanci suna tak'ama, don WALLAHI wannan yarinyar da ka ke renawa ta shiga birni ruwan birnin suka wanketa tas tasha jar miya to WALLAHI ba k'aramar mace za'a yi ba"

SAFWAN cikin fushi yace,. "Da bak'in??"

Lawi yace,. "Ni bakinta bai dameni ba don asali ma bak'inta mai kyau ne idan fatarta ta sami man shafa pure wanda zai gyarata sosai WALLAHI sai ka sha mamaki idan ka ganta wata rana"

Safwan cikin sanyin jiki yace ,. "Shi kuma kauyancin fa ka yi ya ya da shi haka kawai ka sakata Mutane ta dinga kwafsawa???"

Lawi ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yace,. "A tsarina tun fil'azal kai ka sani bana son wayayyiyar mace, nafi son macen da komi sai na d'orata akan hanya, wadda duk tarbiyyar da na bata akanta zata hau ta yi tafiya har a cimma nasara a gaba"

SAFWAN ya maka masa wata jar harara kamar ya dakeshi yace,. "To dai ita wannan yarinyar bazata tab'a yi maka abunda kake so kuma kake ta hasashe ba"

Lawi ya yi saurin fad'in "Saboda mi?"

Kai tsaye SAFWAN yace,. "Saboda ba zaka aureta ba"

Lawi ya zaro Ido waje yace,. "Au! don kai kake so ka aureta kenan ko ya ya??"

SAFWAN ya yunkura kamar zai dakeshi yace,. "ALLAH ya rabani da wahala WALLAHI, Kai din ma bazan barka ka aureta ba"





Tofa🤔 Kai ko MALAM SAFWAN banda hana ruwa gudu fa😕





Akafta😊







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*Masu comments da masu share bani da bakin godiya gareku sai dai ince ALLAH ya biyaku ya saka maku da alkhairi, naga comments dinku all kuma na gode sosai dukanku I love you gabza gabza😉*


*Special gift for you my..... HAJIYA DUDUWA Ina yinki sosai wlh💋*


*Lamba ta 19*


Lawi ya bishi da kallo har ya fice sannan yace,. "WALLAHI ka yi kad'an ka hanani abunda nike so, don son Dije cikin jinina yake kuma aurenta kamar nayi na gama don haka ka zura ido ka yi kallo"

SAFWAN ya dawo da kanshi yace,. "Ka rok'i ALLAH ma akan ka bar garin nan lami lafiya ba tare da ka janyo anyi cikin macizai ba"

Lawi ya mike ya fito shima tare da dafa kafadarshi yace,. "Stof jocking my man WALLAHI da gaske nike son yarinyar, don ALLAH ta wace hanya ka ga zanbi in shawo kan matsalar??"

Safwan da kanshi yake duk'e ya d'ago da jajayen idanuwanshi ya d'orasu kan Lawi yace,. "To be sincere Abokina wannan yarinyar ba ajinka bace, kuma kasancewar iyayenta gidadawa ne zaka sha matuk'ar wuya idan kace ala dole itace zaka aura, shawara d'aya zan baka akan ka bi komi a hankali in matarka ce zaka aureta komi tsanani kuwa, amman idan ka tsaurara to garin neman gira zaka fa rasa Ido, baka ga auren baka ga Mutuncinka da mutane suke gani a garin nan, don yanzu kafin aje ko'ina ma shi kanshi Maigarin zai ga kamar baka ji maganarshi ba, tunda har ya fad'a maka gaskiyar abunda Mahaifin yarinyar yace, tare da guje maka aibin da ke tattare da auren yarinyar"

Lawi ya yi shiru sannan yace,. "Wai Abokina ko dai sace yarinyar nan zan yi ne?, Idan muka yi aure na dirko mata ciki acen sannan in dawo masu da ita, nasan izuwa lokacin dole ne ma su hak'ura su janye tsattsauran ra'ayinsu akan kin aurena"

SAFWAN ya bishi da wani kallo baki sake yace,. "Lalle baka cikin hayyacinka to bari kaji kasan ALLAH WALLAHI duk inda ka kaita ka b'oye Ni sai na zakulota na dawowa da iyayenta 'yarsu, don tun wuri ma ka ajiye wannan bak'in kudurin naka tun kafin zuciya ta debeka ka aikata abunda daga baya zaka zo kana danasani, Ni in bancin k'ulafuci irin naka ma me aka yi aka yi wannan bak'ar magen?? Wadda ita kanta har yanzu bata san me ye duniyar ba, to kaje ka aikata duk abunda kake so tunda har ni baka d'aukeni Abokin kwarai Mai baka shawarar gari ba"

Yana kare fad'ar maganar ya tafi abunshi ya bar Lawi da tunanin zuci mai cike da neman mafita akan matsalar auren Dijen Baffah da Inna Hasiya kanwar Usmanu Mijin Hansai.

***

A bangaren Dije kuwa tsawon kwana biyu ta daina kula kowa a gidan, don Baffah yace da ita bazata sake zuwa Makarantar bokon ba, shiyasa ta k'ara shiga kunci kullum ta shige d'aki tanata kukanta har sai INNA ta fara balbalin fad'a sannan ta yi shiru, don tun tana yin banza da ita har ta fara shiga damuwa akan kuncin na Dije, don Baffah in ya fita gonarshi sai gaf da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login