Showing 111001 words to 114000 words out of 136985 words

Chapter 38 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

2099

ko waiwayensu bata sake yi ba.

Ganin hakan ya sa Safwan ɗin sakin jikin ya mayar mata da martanin sumbar da ta yi masa a leɓenta, sannan ya ɗora kanshi saman wuyanta ya kai mata wani zazzafan kiss ta yi saurin zullewa tare da riƙo hannunshi tana dariya ta ce

"Oya mu je daga ciki kada ka janyo muna abun magana gaban mutane"

Saboda yanda ma'aikatan suke ta satar kallonsu a fakaice ga kuma fiddo da ke tsaye itama, lura da hakan yasa ta hilatoshi suka shige sashenta, wanda shi biye da ita kawai yake amman sam gaba ɗaya ya manta kowa da komi sai ita, yana jin wani daɗi yana huda ko'ina na jikinshi saboda farin cikin ganinta, yau ga shi ga ma'ul hayatynshi Dijengalar Baffah kuma Black cat ɗin shi ada, wadda yanzu ta zamo masa fitilar da yake amfani da haskenta matuƙar yana son ya gane gabanshi.

Surayya da su Husnah da sauran wasu ma'aikatan gidan tuni suka kwashi kayan da Direba yake fitowa suka fara shigarwa sashen Zee, sannan suka koma sashen Dijen inda ita kam tuni ta shige da Mijinta ɗakin da yake mallakinshi a cikin sashen nata ta fara ɗorashi a saiti, don tun shigarsu ya janyota jikinshi ya fara yamutsata tare da aika mata da saƙunan kisses tamkar wani zautaccen mayen ƙarfe, ganin in ta biyeshi za su ɓata lokuta masu yawa yasa ta yi dubarar riƙe hannunshi cikin wani kallo ta ce

"Plss mu je ka yi wanka ku ci abinci kai da Amaryarka kada ta ɗaukeni mai rowa, don na tabbata dukanku kuna buƙatar abincin"

Ta mairaire fuska har da riƙe kunne alamun ban haƙuri sannan ya miƙe tare da dafe goshi yana yi mata kallon mamakin irin wayewar da ta yi masa ta bazata, sannan ya riƙo hannunta ya ce

"Wayo ko? To ai mu je ɗin sai ki tayani wankan don na fahimci so kike ma ki nuna kin fini girma"

Dije ta yi yar dariya sannan ta rufe fuska da hannu ɗaya ta ce

"Ni dai mu je ɗin kada ta ga an ƙyaleta"

Sannan suka je toilet ta haɗa masa komai zata fito ya ce ta jirashi amman daga nesa don baya son ta ɓata masa kwalliyar, ita ko ganin hakan yasa ta yi nazarin kawai ta taimaka masa tunda Surayya ta sanar da ita hakan ma yana ƙara shaƙuwa tsakanin ma'aurata, aiko ta saki jiki ta ajiye kunyar ta taimaka masa sai gata itama ya janyota suka faɗa ruwan ya yi nasarar cire mata kayan ya dinga mammatsewa tare da tanɗewa da lashe abubuwan da ya fi so a rayuwarshi, duk da take jin zafin zafin abunda ya ke yi amman ta nuna masa lalle itama ɗin yanzu ba da bace, da ƙyar ta lallaboshi suka fito toilet ɗin bayan dukansu sun tsalkake jikinsu.

Yana rama sallolin da suka kubce masa ne ta sulale ta wata ƙofar da ke sadata da ɗakinta ta sake yin wani sabon shiri cikin wani danƙareren less bulue black, Wanda aka yi wa ɗinkin riga da siket ya hau jikinta sosai, saboda ɗinkunan takanas Aunty Ummi ta ɗinka mata su Abuja don kawai ta ji daɗin tarbon Angonta, bayan ta kimtsa fess abunta sannan ta sake feshe jiki da turarukanta masu daɗin ƙamshin sannan ta koma wurinshi, yanda ya lalace da kallonta ne yasa ta ƙaraso wurinshi tare da hure masa ido da iskan bakinta ta ce

"It's time for lunch my dear"

Ya rungumota jikinshi yana lakuce mata dogon hancinta ya ce

"Ki godewa ALLAH idan har kinsa Malaminki ya zauce a kanki"

Ta yi wani yarr da ido ta ce "rufani ka saya ai sai ka janyo ace wannan ɗaliba ta wuce gona da iri idan har ta zarta sanin malaminta"

Ya sauke mata wani kiss a goshi sannan ya shirya cikin wasu kayanshi da aka ajiye a ɗakin, sannan ya riƙo hannunta suka fito suka nufi sashenshi da yake tsakiyar na su ita da Zee, inda acen ne ma suka kai komi da suka dafa saboda kawai a nunawa Zee cewa su sun san me suke yi, kuma wannan duk yana cikin shawarar Aunty Ummin da take ta baiwa Dijen akan neman zaman lafiyarta ita da abokiyar zamsnta, har zasu zauna kan diny ɗin Dije ta yi saurin ce wa

"Malam plss ka fito da Amarya ta zo mu haɗu ayi lunch don cikina har ya fara kiran ciroma"

Safwan yana ƴar dariya ya ce "sannu acici to jirani in zo minti ɗaya"

Sannan ya bi wata ƙofa ya yi sashen Zee inda ya taradda ita tare da ƴan uwanta biyun da ƙawarta Ruma da suka zo tarbarta, bayan sun sake gaisa ne ya ke cewa da ita ta zo su je aci abincin, ta nuna cewa ita sam bazata je ba ta riga da ta ci wanda su Ruma suka dafa mata, Ruma ta yi mata signal da ido sannan ta miƙe ta biyoshi ranta a haɗe saboda takaicinshi da take ji a zuciyarta tare da munafukar Matarshi a cewarta, wadda ta sha alwashin ko da bala'i sai ta fiddata gidan ta ƙarfin tsiya, tunda har ita zata nunawa kissa da kitifiri don salon kawo mata reni har da kiranta ƙanwarta wai, haka ta yi ta saƙe saƙen zucinta har suka shiga falon nashi, sai dai hango Dijen da ta yi tana ta Saving abinci a plates kala kala yasa ta ji wani bala'a'en kishi ya taso mata, musamman yanda ta ga har da wani sabon wankan ta sake yi don ta nuna mata cewa sunyi wani abu da Safwan ɗin, tunanin hakan yasa ta ja ta tsaya ta ƙi ƙarasawa wajen diny ɗin, ta rungume hannu tana yi mata wani kallo sai wani girgizar jiki take yi saboda a wuya take ƙiris take jira ayi wadda za'a yi.

Safwan ya ja kujera ya zauna Dijen ta janyo masa abinci a gabanshi tana dariya ta kalli Zee ta ce

"Ƙamshin girkina zai yi maki illa Amarya matuƙar baki yi gaggawar ƙarasowa ki ka fara cinshi ba"

Zee ta yi mata wani kallo sama da ƙasa mai cike da reni sannan ta buga wani uban tsaki tace

"Wahainiyarki ta kiyayi ramata tun wuri WALLAhi, ke ce matsiyaciya wadda abinci ya dama saboda haka ki je ki tambayo wacece Zee kafun ki fara yiwa mutane iyayin tsiya, baƙar munafukar banza annamimiya mai shiga tsakanin mata da mijinta, WALLAhi tun kafin in nuna maki wacece Ni ki kama kanki da ni"

Tana ƙare faɗar maganar ta yi masu wani mugun kallo sannan ta buga wani uban tsaki ta juya cikin fushi ta koma inda ta fito, Safwan kam sai cin abincinshi yake yi ba tare da ma ya nuna damuwarshi akan duk abunda ta faɗa ba, ya ɗago fuskarshi ya kalli Dijen ya wayance tare da faɗar

"Sakin bakin na minene? Ko zaki bita ki bata haƙuri ne? Saki jiki ki ci abincinki in har kina son farin cikina, to ki tattara komi ki ajiye a gefe ki fuskanci gabanki tare da Mijinki da ke kusa da ke, saboda haka dawo nan kusa da ni sai mun fi jin daɗin cin abincinmu"

Dije ta yi shiru sannan ta goge guntuwar ƙwallah da ta cika mata ido
ta dawo kujerar da ya ce, yana dariyar da iyakacinta fuska ya ciko spoon da abincin ya nufo bakinta, ta yi masa wani kallo zuciyarta cike da takaici ya girgiza mata kai ta yi saurin haɗiye kukanta.

Haka suka ci abincin kowane zuciya ba daɗi sai dai ba laifi sun ciyar da junansu sosai, sannan ya ja abarshi suka yi ɗakinshi inda ba ɓata lokaci ya fara saitata a hanya, kafin ka ce me shima ya fara rikicewa tare da zaucewa akan Dijenshi, don kuwa tun haɗuwar fatar jikinsu ya gano akwai banbanci tsakaninta da Zee sosai haka ma akwai tazara mai yawa a tsakaninsu, to balle da ya sami sa'ar shigewa fadar gwamnatinta sai ga shi da fasa wani ihun daɗi yana kuwwa, saboda gaba ɗaya ya zauce mata ni'imarta tasa ya kiɗime babu abunda ke fita bakinshi sai ihu da sambatun daɗi.

Zee kam tana cen su Ruma suna lallashinta ne ta jiyo ihunshi, cike da mamaki ta yi saurin dawowa falon sai dai fahimtar abinda yakewa ihun ne yasa ta dafe ƙirji ba shiri, tare da zuwa ƙofar ɗakin tana dukan ƙofar a haukace tana tsine masu dukansu.

Ganin kamar ba su ma san tana yi ba yasa ta bazama aguje ta yi ɗakin ajiyar fetur ta kinkimo jarkar ta fito da gudu kamar wata mahaukaciya, ma'aikatan gidan suka bita da kallo cike da mamaki duk da duhun magriba ya kawo jiki a lokacin.

Tana zuwa ta fara watsa fetur ɗin ta ko'ina cikin falon da ƙofar ɗakin tana surutan faɗin

"Sai na kasheku dukanku yau yan bura'uba azzulumai macuta, ALLAH ya tsine maku gaba ɗayanku WALLAHI yau sai na kasheku"

Ta yi sashenta aguje gudu ta ɗauko ashana su Ruma suka biyota da gudunsu don su ga abunda yake faruwa, tana zuwa ta kunna ashanar cikin bushewar zuciya ta cillata ƙofar ɗakin.







Wayyo ALLAHna😳🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wuta 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wuta ku yo agaji🏃🏻‍♀️.





Akafta😝








D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Rigiji Gabji wani kaya sai Amalii ina gwanayen wasu ga nawa 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻har ga ALLAH ruwan sharhinku akan book ɗin Ƙarangiya yana faranta man rai ba kaɗan ba, haƙiƙa dole inyi alfakhari da ku saboda ku ɗin nawa ne ba ƙarya,ina miƙa ɗinbin godiyata gareki ƴargata Maman Sultan, irin godiyar da baki ba zai taɓa iya zayyanowa ba, alkhairin ALLAH ya kai maki har ƙasar Niger cikin gidan Baban Sultan akan gadonki wanda kike bacci a kuma gefen da kike kwanciya😝😜*


*Lamba ta 64*


A zafafe Ruma ta yi wani tsalle ta cafke ashanar cikin wani firgici da tashin hankalin da ya ziyarceta, don garin cafke ashanar fetur ɗin da ke malale ƙasa tyles ɗin ya jata ta faɗi tim! A ƙasa, amman duk da hakan sai dai ta yiwa ashanar murzar bala'i duk da zafin ƙunar da ya ratsa hannun nata, cikin fushi ta miƙe ta yo kan Zee zata ƙwace ashanar, Zee ta ƙara yin baya cikin bushewar zuciya da ta yi dacen aka janye mata imani a zuciyar don babu abunda take so irin ta ƙonesu da kowa ma da ke gidan har itama kanta, saboda a ganinta hakan ne kawai zata yi ta cire zafin abunda take ji a zuciyarta, Ruma tana girgiza kai cikin ruɗewa tace

"Kar ki aikata abunda zaki zo ki yi danasani daga baya"

Hawaye suna zuba akan fuskar Zee da idonta suka rikiɗe zuwa jajaye saboda tsallar tsagwaron bushewar da zuciyarta ta yi, ta sake kunna wata ashanar hawaye suna zuba akan fuskarta tace

"Matuƙar na barsu da rai bazan taɓa yafewa kaina ba, ya zama dole su ɗanɗani azabar mutuwa dai dai da cin amanar da suka aikata ma....."

Wani mari ne da ya sauka akan fuskarta ne yasa ta yi saurin sakin guntuwar ashanar da ta kusa cenyewa a hannunta, Ruma ta yi saurin taketa da ƙafa ta murje, a zafafe Zee ta waiga domin taga wace mai ƙarfin halin ce ta mareta, yanda ta ga fuskar Surayya da ke tsaye gefenta tana huci yasa ta yi wata gajerar dariya ta ce

"Wow sannu fa ki ce masu mutuwar yau yawa ne da su? To ki jira ke ma saura kaɗan naki ajalin ya iso ku sa da ke"

Tana ƙare maganar ta fiddo wata ƙwarar ashana kafin ta kyasta ta sake jin wani uban naushi da Surayya ta sauke mata a gefen fuskarta, ba shiri ta saki ashanar ƙasa Ruma ta ɗauke ta fice da ashanar cikin sauri, Zee ko ta yi cikin Surayya suka fara kaiwa juna duka, kafin ka ce damben bala'i ya kacame a tsakaninsu ƴan'uwan Zee ɗin su biyu da ke tsaye suna kallon abunda ke faruwa suna rabon faɗan, sai ga Husnah aguje itama kamar wata zakanya ta rufarwa Zee suka yi ta mazgarta ita da Surayya, sai dukanta suke yi kamar ALLAH ya aikosu tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta koma laƙwas Husnah ta kwashe mata ƙafafuwa ta faɗi ƙasa ba shiri, Surayya ta yi saurin haye ruwan cikinta suna ta duka duk da ƙoƙarin hanasu da ƴan'uwan Zee suke yi, amman hakan bai hanasu yi mata dukan kawo wuƙa ba.

Safwan da Dijenshi kam basu ma san me ke faruwa ba har sai da Surayya ta kirasu a waya ne take sanarwa da Safwan ɗin abunda Zee take yi don a lokacin itama suna sashen Dijen ne wani ma'aikaci ya zo aguje yake sanar da su abunda ke faruwa, shiyasa hankalin Surayya a tashe ta kira Safwan ɗin saboda zuciyarta ta bata cewa Zee ba alkhairi zata shuka ba, tun yanayin da ta ganta lokacin da suka dawo ta yi sashenta cikin fushi, bayan ta gama kiran Safwan ɗin ta sanar da shi abunda aka faɗa masu ne ta ce da su Husnah su kira Aunty Ummi su sanar da ita kafin ta je ta ga abunda ke faruwa, aiko sai gashi tana zuwa ta ji kalaman da Zee take faɗa Shiyasa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kai mata hannu.

Ko da Safwan ɗin da Dije suka fito cike da firgici akan fuskarsu, sai ga wani sabon firgicin da ya sake sakasu ruɗewa saboda ganin gaba ɗaya falon warin fetur ne da wani wanda bai ƙasara bin iska ba malale a ƙasa, Safwan ya kai kallonshi inda su Surayya da ke ta jibgar Zee har lokacin, ya yi saurin katsa masu wata uwar tsawa suka zabura cikin firgici daga su har ita Zee ɗin da ke kwance ligya ligya don ta daku ba ƙarya.

Ya ƙasaro wajensu ya kallesu ɗaya bayan ɗaya ya ɗaga murya a fusace ya ce

"Wai me ke faruwa ne wai??"

Zee ta miƙe da ƙyar ta kalleshi cikin wani kallon reni da kumburarren bakinta da suka fashe ta ce

"Ni zaka tambaya don ni ce zan yi ajalinku dukanku ka sani ka ƙara sani dukanku sai na kasheku"

Tana ƙare maganar ta yi sashenta aguje ko wa ya bita da kallo, cikin fushi Safwan ya bita ƴan'uwan Zee ɗin da Ruma suka biyoshi a baya suna bashi haƙuri, Dije ko ta yi wurinsu Surayya tana tambayarsu mafarin abun.

Safwan yana kaiwa sashen nata sai ga ta sun ci karo da ita da sharɓeɓiyar wuƙarta ta nufoshi gadan gadan da nufin ta soka masa ita, ya yi jarumtar riƙe tsinin wuƙar ya fisgeta da ƙarfi wuƙar ta yankeshi sosai amman duk da hakan bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen kai mata wani wahalallen mari har sai da taga taurari, sannan ya dinga kai mata duka ta ko'ina kamar wani zaki, itama har da su ƙarfin halin kuwar faɗin sai ta kasheshi duk da uban kashin da take sha, don kuwa da ya yi wani ball da ita har sai da ta kai bango, sannan ya damƙo gashinta ya janyota ƙiii ya fito da ita har gindin Motarshi, sannan ya jefata motar ya saka lock sannan ya faɗa cikin zafin nama ya tada motar ya yi wani uban ribas sannan ya fisgeta da ƙarfin tsiya ya fice, bai zame ko'ina da ita ba sai headquarter'r ƴansanda, kai tsaye ya nemi ganin D.p.o ya damƙa masu ita da hannunshi tare da sanar da su cewa Matarshi ce take son kasheshi, su riƙe ta a hannunsu su yanke mata hukunci dai dai da laifinta, suka karɓeta suka jefata ɗakin ajiya suka kulle sannan suka sanar da shi zasu yi ƙwaƙƙwaran bincike akan case ɗin idan har komi ya kammala ta aikata abunda ake tuhumarta da shi to zasu yanke mata hukunci dai dai da laifinta.

Sannan ya baro wurinsu tare da wasu ƴansanda da za su zo yin bincike akan abunda ya faru, shima ya nufo gida saboda damunshi da kiran da ake ta yi, don yaso zuwa ayi masa kanikancin hannun da ya yanke da shi, amman yanda yake jin zuciyarshi ne yasa ko kiran da ake ta yi masa ɗaya bai ɗaga ba, sai na Hajiyarshi ko shi don baya iya ganin kiran yaƙi ɗauka, sai dai bai iya furta ko kalma ɗaya ba sai "to" kawai da ya faɗa, saboda tsananin ɓaci ran da ya cunkushe masa zuciya.

Ko da suka shiga gidan suka taradda kowa a harabar gidan ana jiran zuwanshi, cike da ruɗewa Aunty Ummi ta nufoshi tana faɗin

"Ba abunda ya sameka ko to Alhmdllh mun godewa ALLAH Hajiyarmu ba abunda ya sameshi"

Ya baiwa ƴansandan dama suka shiga ciki suna ta bincikensu, har wuƙar da galam ɗin fetur duk sai da suka fito da su duka, sannan suka fara yiwa mutane tambaya ɗaya bayan ɗaya, don har su kansu ma'aikatan gidan ba'a barsu ba sai da aka tambayesu suka faɗi abunda suka sani, sannan ƴansandan suka bar gidan tare da rahotannin da suka naɗa a wayoyinsu.

Safwan da ke jikin Motarshi tsaye ya ƙaraso wajen Hajiya Mama yana dafe kai ya zauna kan wani ɗan dakalin da aka zagaye wasu flowers, hannunshi da suka hango da ya yi bala'in walshewa da wuƙa kowa hankalinshi ya tashi, Hajiyarmu ta ƙaraso wajenshi ta ce

"Garin ya ya haka ta faru??"

Ya yi shiru sannan ya yarfa hannu saboda jinin da ke ɗiga har lokacin ya ce

"Ni ma bansan abunda yake faruwa ba har sai da Surayya ta sanar da ni"

Hajiya Mama cikin damuwa ta ce

"Ina ita Zainab ɗin?"

Ya yi shiru sannan ya ce, "tana hannun ƴansandan"

Ko wa ya yi shiru yana nazarin abun a ranshi sannan Hajiyar ta ce

"To ka je a yi maka dressing ɗin hannun sannan ka dawo muna jiranka"

Safwan ya miƙe zuciyarshi kamar zata fashe ya kalli su Ruma da ke tsaye dukansu sun sha jinin jikinsu ya ce

"Kada in dawo in taradda ku cikin gidana"

Sannan ya ja Motarshi ya fice aguje, su Hajiya Mama suka yi sashen Dijen suka zauna, inda su ke ta lallahin Dijen da ke ta kuka saboda tunda ta ji abunda Zee ta ce a bakin Surayya hankalinta ya tashi ta fara kuka, sai ga shi kuma ta hango Safwan ɗin yana jan Zee a ƙasa hannunshi sai zubar jini yake yi, akan hakan ta sake ruɗewa tana ta kuka don jin take yi kamar ma ta bar masu gidansu ta koma garinsu tun kafin a kasheta ga banza,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login