Showing 33001 words to 36000 words out of 136985 words
ziyartota, duk nacin da Lawi ya yi akan yana so ya yi sallama da Dije bai sami wannan damar ba, saboda ganin yanda Safwan ya keta hidimar d'aukar pic's d'inshi da su Dijen.
Sai da aka gama ne ya samu ya yi wa Dije sallama tare da mika mata wata envelope idonshi jawur tamkar ya yi kuka, don shi ya kuduri aniyar ba zai jira ayi auren Dijen da shi ba, da nufin tun da sassafe ya had'a inashi inashi ya bar garin, don shi Safwan ya ce ba ranar zai tafi ba ya yi gaba shi zai biyoshi ta baya.
Dije tana kuka suka yi sallama da Lawi ta tura envelope d'in da ya bata a jaka ta nufi gida,. Kai tsaye ta shige toilet ta bud'a envelope d'in saboda ta matsu taga me ke ciki gashi bata son Inna ta gani.
Aiko sai gashi tana budawa taga wasu Yan hannu da zobe masu bala'in kyau sannan da bandur d'in kud'i sababbi kal yan d'ari bibbiyu, Dije ta zaro ido tare da goge hawayenta cikin sauri ta rungume kud'in da sauran kayan ta fashe da kuka gwanin ban tausayi, sai dai ita bata san duk abunda take yi Inna tana hankalce da ita, shiyasa lokacin da taga ta dad'e bayin ta biyo sawunta sai ko gashi ta ganta durk'ushe kasan bayin tana ta kuka, cikin tausayawa ta isa wurinta ta tadata Dije ta yi saurin yunkurin b'oye kud'in sai ga takardar kud'in ta yage kud'in sun zubo shaaaa! A k'asa.
Ku yi hakuri da kuskuren da kuka gani yau ban yi editing ba🤦🏻♀️
Akafta😉
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*
*Lamba ta 22*
Daga Inna har Dijen gaba d'aya zaro Ido suka yi suna kallon kud'in, cikin firgici inna ta yi saurin fad'in
"Dije me nake Shirin gani yau Ni Hasiya?"
Dije ta yi saurin duk'atawa tana ta tattara kud'in har ta kammala sannan ta mik'awa Inna tace,. "Karb'i kyauta ce aka bani"
Inna ta tak'i karb'ar kud'in ta tsuke fuska tace,. "Gaya man duk fad'in garin nan waye mai arzik'in da har zai iya baki wad'annan mak'udan kud'in sababbi k'al da su haka?"
Dije ta saka hannu ta share hawayen da har lokacin basu daina zubo mata ba tace,. "Malaminmu D'anbirni ne ya bani wai tashi gudunmuwa ce yace ko Daddawa a siya man"
Inna ta maka mata wata jar harara tace,. "To WALLAHI Ni ba ruwana in har Baffah'nki ya ji wannan magana,sawunki a likkafa ki tattara kayanshi da kud'inshi ki je ki Kai masa salun alun ba wanda ya ji ba wanda ya gani"
Dije ta sake fashewa da wani sabon kuka tace,. "Ni dai Inna ina son awarwaron da zoben, don ALLAH ki bari in mayar masa da kud'in kawai don ALLAH Inna"
Ta k'are maganar cikin marairecewa gwanin ban tausayi, Inna ta karbe kud'in da awarwaron da zoben ta janyo hannunta suka fito tana janye da hannun Dijen har d'akinta, sannan ta samo wata leda baka ta zuba kud'in da kayan ta k'ulle jabau! Ta mika mata tare da had'e fuska alamun ba wasa tace,. "Karb'i kije ki mayar masa da kayanshi yanzun ba sai anjima ba"
Dije ta karb'a har ta fito ta dawo tace,. "To Inna ki bari in cire kayan Makarantar in saka na Gida"
Inna ta taso mata kamar zata daketa tace,. "Bazan bari ba nace ba za'a bari ba zaki je ko sai na sab'a maki ne yanzu Nan??"
Dije ta fice tana tafe tana gunguni har ta kai wani lungu ta bud'e ledar ta cire awarwaron da zoben ta k'ulle ledar ta nufi gidan Inna Gambo, sai da ta samu wani waje cikin dabara ta b'oyesu d'akin Gambon sannan ta fito ta nufi gidan Maigarin, sai dai rashin sa'ar da ta taka tun kafin ta isa daga nesa Maigarin da ya hangota ya bada umurnin a hanata zuwa wurinshi, saboda yaci alwashin daga Dijen har Baffah'n ba zai sake shiga cikin shirginsu ba, sai dai ita kam ta nace akan ita bazata koma ba don wurin Malaminsu ta zo ba wurinshi ba, Maigari kam ganin rigima zata b'alle ne a tsakanin Dijen da wani yaronshi yasa yace a kyaleta, kai tsaye ta nufi k'ofar d'akinsu Safwan ta fara rafka sallama sai dai ta yi har ta gaji ko sau d'aya bata ji an amsa mata ba, cike da k'unar rai ta fad'a d'akin da k'arfinta sai dai wayam ba kowa d'akin, tana k'ok'arin fitowa ne ta ji ta yi karo da mutum da sauri ta ja baya tana sosa goshinta da kan Safwan ya buge, Cikin tsoro ta rab'a ta gefenshi ta fito jikinta yana rawa ta fara fad'in
"Don ALLAH ka yi hak'uri wajen Malam na zo na yita sallama banji an amsa ba shiyasa na shigo in ga ko lafiya"
Safwan ya maka mata wata Uwar harara sannan ya rungume hannu a K'irji ya ce,. "Lafiya kike nemansa? ba naga kunyi sallama ba ko Mahaifin naki ne ya amince zai bashi aurenki ne shiyasa kika zo yi masa albishir? "
Dije yanayin fuskarshi da tambayoyinshi sun sakata daburcewa, cikin rawar murya tace
"Kyautar da ya bani ce na zo kawo masa kayanshi sabida gidanmu ance bazan karb'a ba"
SAFWAN ya yi wani mere yace,. "Sai Kuma aka yi rashin sa'a shi ya bar garin gaba d'aya ya koma gida, cen zaki bishi garinsu ki kai masa ko yaya?"
Dije ta zaro ido tace,. "WALLAHI na koma da su sai sun janyo man gagarumar matsala, don ALLAH ka karb'a ka ajiye masa idan ka koma sai ka bashi abunshi kace na gode sosai ALLAH ya had'a fuskokinmu a aljannah, kuma ka yi masa albishir insha ALLAHu nice Matarshi a Lahira idan munje cen"
SAFWAN ya galla mata wata jar harara da jajayen idonshi da suka rine lokaci d'aya yace,. "Zaki bar wajen nan ko sai kin janyo na karairayaki a kaiwa kwad'ayayyen angonki sauran k'asusuwan???"
Dije ta yi saurin ja da baya tace,. "Don girman ALLAH ka karb'a WALLAHI dukana za'a yi gidanmu idan na koma da su"
Safwan ya buga mata wani uban tsaki ya shige d'akinsu tare da fad'in,.
"Idiot!!!"
Dije kam sanin idan ta koma da su gida akwai matsala ta lallaba ta jefa ledar kud'in cikin d'akin ta zank'ara da gudun tsiya, Maigarin da mutanenshi suna ganin fitowarta da gudu suka bita da kallo, Maigari ya mike tsaye jikinshi yana rawa yace
"Bari in je in dubo yaron Mutane kada ta kasheshi mu shiga uku, tunda shi har yanzu bai tashi barin garin ba duk da kyamar garin da yake yi"
Sauran mutanen su ka biyoshi baya har zuwa d'akin sai dai ganinshi da suka yi kwance yana latsar waya ne yasa hankalinsu ya kwanta, sannan suka koma suna ci gaba da yi da Dije da Baffah'nta, inda wasu suke ganin laifinshi akan abunda ya yi wa Maigarin yayin da wasu suke ganin hakan da ya yi shine dai dai.
Bikin yana saura kwana Uku aka gyarewa Dije d'akinta ram! gidan Inna Duduwa,Wanda Balan ya ci gado ga Mahaifinshi da ya mutu, don asalima d'akin Mahaifiyarshi ne da ta yi zama ciki lokacin da Mahaifinshi yana raye, don yanzu haka tana wani k'auye tana aurenta da yaranta biyar bayan Balan.
Biki sai kankama yake yi Bala da abokanshi da kawayen Dije Su Jummala sai shagalin bikinsu suke ta yi, don ana saura kwana biyu ne aka shirya wani bikin tauri a k'ofar gidansu Balan, inda yan tauri suka baje sai nuna k'warewarsu suke yi, sun burge iya burgewa in da bikin wasar taurin ya d'auki lokaci har cikin dare anata fafatawa da zaratan jaruman Yan taurin.
Ko da safiyar JUMU'A ta waye aka shiga hada hadar hidimar d'aurin auren a k'ofar gidansu Dijen, don tun kafin aje masallacin JUMU'A aka fara shimfida sabbin tabarmomi da ledar buhu manya manya aka malale k'ofar gidan ko'ina, ko da aka ta so mutane ta ko'ina sai b'arkowa suke yi zuwa k'ofar gidan Baffah'n Dije Malam Sanda, Baki na nesa da na kusa Kai har na manyan biranen da Baffah yake abun arzik'i da su sai da ya gayyatosu zuwa daurin auren shalelenshi Dijengala.
Cikin bak'in da ake zuwa daurin auren har da wasu fararen dattijai na hango tare da motocinsu na alfarma, inda kai tsaye hankulan mutanen k'auyen ya karkata kansu saboda alamun hutun da ya bayyana a jikinsu, nan take za'a banbancesu da mutanen garin saboda kamarsu daban da take ko da ko a cikin duhu.
Wani Dan'uwan Baffah'n shine zai yi waliccin Dije, yayin da wani kanen Baban Bala zai karb'arwa Bala auren Dije, soron Gidansu Dije nan ne aka yiwa wad'annan bak'in alfarmar masauki akan saman sababbin tabarmin da Baffah'n ya tanada don kawai wannan Rana.
Kai tsaye Liman ya nemi ganin waliyyin Ango da waliyyin Amarya duk suka hallara, Baffah kam bakinshi kamar gonar auduga saboda tsabar farin cikin ganin wannan Rana mai d'inbin tarihi a wajenshi da Dijenshi, saboda auren Dijen yana daga cikin abubuwa masu muhimmanci a rayuwarshi, don yasa a ranshi ko yau ya kwanta dama shi gurinshi ya cika tunda har ya auradda 'yarshi guda mace da ALLAH ya albarkaceshi da ita a doron duniya.
Kafin kace me sai ga Liman ya fara hud'ubar aure cikin ikon ALLAH sai jin aka yi mai sanarwa fad'in auren ya fara shelar shewa an d'aura auren NANA HADIZA wadda aka fi sani da suna DIJE tare da Angonta MUHAMMADU SAFWANU JABB'I YOLA.
Durum! dum! dam! dum! dum! Haka naji gaban Baffah yana ta luguden fad'uwa tare da sauran mutanen da ke wajen da ma ita kanta Dijen da ke bayi tana ta gurzar kuka na tashin hankali.
Oh! oh! rigiji Gabji 😳 Ni kam taya aka haifu a ragaya😱🤔 HAJIYA DUDUWA kar ki zargeni don ni ma bansan komi ba🙌🏻🏃🏻♀️
Akafta👻
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*LUV U SO MUCH ALL MY FAN'S💋Ina jin dad'in yanda ku ke kaunar book din Dije K'arangiya yawanku ya kai bazan iya lissafoku ba amman ku sani ina yinku sosai all my guys👍🏻*
*Lamba ta 23*
A zabure Baffah'n ya mik'e cikin sabon tashin hankali marar misaltuwa ya nufi wurin k'anen Mahaifin Bala yana fad'in,. "Daman shi haka sunan Balan na gaskiya yake?"
K'anen Mahaifin Bala yayi d'an murmushin yak'e yace,. "An samu akasi ne Malam Sanda don ba da Bala aka d'aura auren ba"
Baffah'n yana jin haka ya rud'e tashin hankalinshi ya k'ara k'aruwa cikin zaro Ido waje ya nufi wurin Liman ya shak'o wuyanshi yace,. "Da wa ka d'aurawa 'yata aure ne?? mugu azzalumi ai WALLAHI sai na yi shari'a da kai matuk'ar baka yi gaggawar kwance wannan mugun auren ba"
Cikin masifa Baffah'n Dije ya shak'e Liman tare da kai masa wani azababben naushi mutane suka rirrik'eshi, kafin ka ce me wuri ya hautsine hargitsi tare da gutsuri tsoman jama'a, saboda ruwan bala'in da Baffah yake ta zubawa cikin d'aga murya yana hargowar cewa,. "Ai WALLAHI in duk garin nan za su taru a kaina bazan lamunta ba sai an kwance wannan bak'in auren da aka k'ullawa 'yata, Ni na haifeta kuma nace ba zan bada ba shin auren dole ne ko ita kad'ai ce 'ya mace a garin nan"
Kai rigima fa tun ana ganinta a wasa sai ga abu tana shirin zama Babba, don kuwa Baffah sai zillo yake yi akan sai an barshi ya daki Liman, ana cikin rigimar ne sai ga sak'o daga Maigarin ya aiko duk kowa ya hallara a k'ofar gidanshi, Baffah'n kam har kowa ya tsiyaye aka barshi shi kad'ai k'ofar gidan yanata sauke ruwan sababi, Inna da sauran matan da ke cikin Gidan suka fito sunata bashi baki.
Maigarin ya yi ta aikowa da sak'on neman Baffah'n ya kai sau uku sannan ya nufi gidan Maigarin har lokacin bai daina sambatun fad'anshi ba tamkar wani tabab'b'e sabon kamu.
Abun mamaki k'ofar gidan Maigarin cike dank'am da d'an'adam maza da mata yara da mayan, sai dai kuma idan aka yi la'akari da yanda kowa yake son ya ji k'waf to hakan ba abun mamaki ba ne ba saboda ba Baffah'n kad'ai ba wasu da yawa suna son su san shin ta yaya aka haifu a ragaya?, Baffah'n da idanuwanshi da ba abunda ke cikinsu a lokacin face tsagwaron tashin hankalin da yake ciki jin yake yi gaba d'aya kowa haushi yake ba shi, yana muzurai zuciyarshi awa garwashin wuta saboda tsabar k'unar da take yi masa, ba tare da ya zauna ba ya tsaya k'ik'am yana huci tamkar wanda ke shirin kai naushi.
Maigarin ya kalleshi da kyau yace,. "Malam Sanda ka zauna wannan taron ba don kowa aka yi shi ba face donka da kuma 'yarka Dije"
Baffahn ya makawa Maigarin wata jar harara yace,. "Me kuma zan zauna a fad'a man yanzu? wanda ya wuce muguwar kullalliyar da kuka k'ulla kuka rufeni kuka baiwa 'yata Mijin da ba Ni na zab'a mata ba???, Sai na gani da Ni da ku wa ye yake da ikon auradda ita??don ku ma sani wannan auren k'addara mai cike da bak'ar manufar tamkar an kwanceshi an gama"
Ya k'are maganar cikin huci tare da zabgawa Liman wata muguwar harara sannan ya yi kyafci, Maigarin ya k'ara cewa da shi
"Da kasan irin ta'adin da 'yarka ta shirya idan anyi auren da wanda kake son ta aura d'in,to da baka tsaya gaban Mutane kana wannn shirmen ba, Kai godiya ya dace ace ka yi wa Mutane ba wai ka tsaya kana yi wa mutane karatun hauka ba"
Aiko cikin nasara maganganun Maigarin sun saka Baffah cikin shakku da tsoron abunda zai fito akan wani aikin ashsha da Dije ta aikata ko take Shirin aikatawa, saboda yasani sarai ba son auren take yi ba haka ma yasan wacece ita da ayukanta, shiyasa cikin sanyin jiki ya ja k'afafuwanshi zuwa kusa da wad'annan manyan alhazawan bak'in fuskar ya zauna.
Maigarin ya kalli Safwan da ke cikin manyan kayanshi da suka fito da zallar kyawunshi na Bafillacen usali, ya yi shiru na d'an lokaci sannan Maigarin yace da shi
"Yi masa bayani da bakinka don ya san cewa muma ba ma cikin mutanen da zasu cutar da wasu ma bale shi"
Safwan ya gyara zama tare da yin gyaran murya yace,. "To a zahirin gaskiya yau kwana shida da 'yarka ta iskeni har d'akina tana sanar da ni cewa muddin ba'a aura mata Abokina ba to ko ita duk ranar da aka kaita gidan Mijin da ka zab'a mata zata kashe kanta shi ma ta kasheshi, ta hanyar saka masa shinkafar b'era su ci dukansu su mutu murus daga shi har ita"
Aiko ba Baffah'n ba har ta mutanen da ke wajen sai da suka fara salatin fad'in "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un"
Cike da fad'uwar gaba Baffah'n yace,. "Wannan k'azafi ne aka yiwa Dijeta don kuwa sam k'wak'walwarta bazata yi wannan tunanin marar amfani ba, dududu duka Dijen guda nawa ta ke? da har za'a ce tasan da wannan mugun tunani kai ina da sake WALLAHI"
Ya mike tsam! da nufin barin wajen Safwan ya yiwa Bala wani kallo k'asa k'asa aiko sai ga Bala da mik'ewa tsaye yana fad'in,. "Baffah ka tsaya ka ji gaskiya ce ake fad'a don Nima bakina da nata tace dani duk ban janye aurenta da Ni ba sai ta kasheni ta kashe kanta, shine na zo wajen wannan Abokin wanda take so d'in na nemi alfarmarshi akan ya aureta Ni na hak'ura ko don mu shawo Kan matsalar, to Abokin ya tafi kuma an yi ta nemanshi a waya amman ba'a sameshi ba, shine sai shi wannan bawan ALLAHn ya karb'i tayin aurenta ga waliyyanshi anan su ne suka karb'i aurenta wajen Baba Buba"
Cewa da D'an uwan Baffah'n Wanda shine ya bada auren Dijen ga Safwan, cike da tsananin firgici Baffah'n ya koma ya zauna dab'as yanata jero salati, tare da godewa ALLAH da har hakan bata kasance ba.
Cikin zubowar wasu hawayen takaici ya kalli SAFWAN yace,. "A matsayina na Mahaifin Dije na rok'i alfarmar ka sauwake mata, don ko auren da Balan yanzu na janyeshi ba za'a sake zancenshi ba har duniya ta nad'e, ina yi maka godiya sosai na gode da taimakonka amman don girman ka taimaki rayuwata da ta 'yata ka sauwak'e mata yanzu ba sai anjima ba"
SAFWAN cikin sauri ya duk'e kanshi tare da yin nazari na d'an lokaci, sannan ya d'ago da jajayen idanuwanshi da a take suka sauya zuwa tashin hankali, ya shafo dan k'aramin gemunshi sannan yace
"Ka yi hak'uri Baba wasiyyar da Mahaifina ya bar man kenan lokacin da zai rasuwa, akan cewa duk runtsi kada in zamo mutum mai auri saki, ballantana irin wannan auren da ko ina ba'a je ba ya haneni da yin irinshi tun lokacin da yana ray...."
Zancenshi ya katse ne saboda ji yo sautin Dije da aka yi tana fad'in,. "Ai billahillazi daga kai har Balan sai kun san da ni kuke zancen, Ni za ku ci wa amana ku yi man k'azafi da raina ban mutu ba??????"
SAFWAN da Balan suka yi saurin kai kallonsu gareta, cikin sabon b'acin rai Safwan ya mik'e ya kalleta ido cikin ido yace
"Ni zan yi maki k'arya?? Yanzu kina nufin kin manta lokacin da kika zo kina fad'a man maganar?"
Dije ta fashe da kuka tace,. "Ai WALLAHI sai dai in aljanuna ne amman Ni kam bansan ma na yi ba"
Safwan ya kalli Maigarin yace,. "Baba ai kasan lokacin da kuka je ganin ya nake bayan ta fita wurina aguje ko?"
Maigarin yace,. "Tabbas hak'ik'atul amri ba ma Ni kad'ai ba har ma da su Malam Tsalha duk mun ganta da idanuwanmu lokacin da ta zo"
Safwan ya ce "to ai a ranar ne take sanar dani wannan magana, har ma ta rok'eni ta ce da Ni don ALLAH ka da in fad'a har sai bayan sun mutun ita da Angonta, Ni kuma ganin zata je ta yi aika aika yasa lokacin da shi Balan ya zo neman Abokina ban ja da tsauri ba na amince a d'aura da Ni, saboda haka ina b'ukatar a bani Matata yanzu mu kama hanyar garinmu saboda mu yi saurin isa gida tare da Iyayena da suka yo tattaki tun daga Yola har wannan Gari domin kawai su karb'a mani aurenta"
Baffah ya mike cikin wata sabuwar