Showing 51001 words to 54000 words out of 136985 words

Chapter 18 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

2076

suka zaro ido, saboda mamakin ƙarfin halin Dije a matsayinta na junio a house ɗin, ganin yarinyar ta ƙi karɓa cike da tashin hankali da tausayin Dijen yasa ta rufe bakinta alamun firgici.

Captain ɗin ta riƙe ƙugu tana ƙarewa Dije kallo sama da ƙasa tace,. "Ashe ko yau zan ci Uban Matar aure a makarantar nan sai naga uban da ya ɗauke maki gindin da zaki tunkarata da wannan baƙin gangancin"

Ta yi wata arniyar dariya ta fisge bulalar a hannun Dijen ta yi ta zabga mata bulolin ta duk inda ta samu, Dije kam jin zafin dukan yana ratsata yasa ta yi wani ihu ta yi tsalle ya haye kan Captain, kafin kace me wurin ya cika maƙil da yan makaranta, tsakanin prefet da senios har ma da juneos ɗin ba'a bari ba, don kuwa Dije ta zage damtse sai artabun doke doke take yi tsakaninta da Hause Captain ɗin, in da da ƙyar aka ɓanɓari Captain ɗin a hannun Dijen, don kowa ƙasa ta murƙusheta tanata kai mata naushi aiko gaba ɗaya prefet suka taru kan Dijen sunata jibga saboda takaicin abunda ta yiwa ƴar uwarsu a gaban junios ɗinsu masu ganin girmansu da kuma jin tsoronsu.

Hannatu a gefe sai uban kuka take ci saboda ganin dukan da ake yiwa Dijen, ganin za su kassarata ne yasa ta bazama aguje sai gidan principal ɗinsu tana sanar da ita, aiko a firgice principal ɗin ta nufo Hostel ɗin don zuwa lokacin makarantar gaba ɗaya ta taru wajen ɗauki ba daɗin dukan da prefet ɗin suke yiwa Dijen, don kowa ya kasa karɓarta a hannasu hasali ma wata ɗaya daga cikinsu da ta so a ƙyaleta itama aka hayayyaƙo mata dole ta yi shiru.

Ko da principal ɗin ta zo tuni sun jigatar da Dijen Baffah don kuwa gaba ɗaya sun ji mata raunuka don ko motsin kirki bata iya yi, cike da tashin hankali principal ɗin ta sa aka ɗauketa aka nufi clinic da ita cikin sauri aka fara treatment ɗinta, sannan ta sa aka haɗa assembly na gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba kowa ya hallara prefets ɗin da suka yi aikin kam gaba ɗaya cikinsu ya ɗuri ruwa, don kuwa sai a lokacin ne wasu da yawa suka ji labarin cewa wai matar aure ce, duk da cewa wasu sam basu yarda da cewa matar auren ba ce duba da yanayin karancin shekarunta, don kwata kwata a lokacin Dijen shekararta goma sha huɗu.

Cikin tsananin ɓacin rai principal ɗin ta yi ta faɗa cikin firgici da jin tsoron abunda zai biyo baya, saboda jan kunnen Da Hajiya Mama ta yi tun farkon kawo Dijen akan kada a daketa ko a sakata wani aikin wahala saboda matar aure ce, sannan ta yi hani ga kowace prefet da ta sake dukan juneos ba tare da ƙwƙƙwaran dalili ba, sannan ta tsawatar sosai akan kada a sake yiwa kowa irin wannan dukan da ake yiwa yaran mutane.

Bayan an sallami sauran ɗaliban ne aka bar prefets ɗin inda aka yi bincike aka fitar da waɗanda suka daki Dijen aka yi masu horo mai tsanani sannan aka karɓe ɗankwalayensu sannan aka basu suspension na kwana uku zuwa gidajensu.

Sannan sauran ta tsoratar da su sosai akan kada su sake dukan ƴar kowa uwa uba kuma ita Dijen da ta kasance matar aure inda gaba ɗaya dukansu sunyi mamakin jin cewa wai ita Dijen matar aure.

Hakan da aka yi shi ya janyowa Dije suna a cikin makarantar, sai dai kuma waɗanda abun ya shafa tuni sun k'ulla gaba da sabuwar ƙiyayya a tsakaninsu da ita, inda wasu da yawa sun ci alwashin cewa sai sun ja mata abun da za'a koreta makarantar.



Not editing😻

😝😝😝😝



Akafta😝





D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅*



*Lamba ta 34*



Dije kam bayan kwana biyu ta ji sauƙi sai dai shatin bulolin da suka rage su ƙarasa warkewa kawai, inda ƙawarta Hannatu da sauran wasu da principal ɗin tasa su kula da ita sosai, sun bata kulawa tamkar ƴar uwarsu ta jini don ba ƙaramar gata tasha a hanunnsu ba, don wata prefet ma mai suna Zee Baby takanas ta maidata wurinta tana tarairayarta tamkar ƙanwarta ciki ɗaya, saboda shagwaɓar Dijen da yanayin barkwancinta yasa ta shaƙu da ita aɗan zaman jinyar da tayi clinic na kwana biyu.

Dije kam tana jin ta samu kanta ta fara komawa kan harkokinta kamar kullum, saboda yanzu ɗaurin gindin da ta samu wajen principal ɗin da sauran wasu prefet ɗin yasa take jinta ita wata ce.

A ɓangaren Malamai ma Dijen Baffah ba ɓoyayya bace, don duk malamin da ya shiga ajinsu tabbas sai yasan da zamanta, don kuwa ba laifi tana catching ɗin karatun yanda ake ɓukata.

Akwai wata rana ma wata malamar Hausa ta rubuta masu test cikin ɗoki Dijen Baffah itace ta farkon wadda ta fara gamawa ta miƙa, Malamar sai jinjina mata take yi saboda daman cen akwai jituwa tsakaninsu sosai, don saboda saurin gane karatunta da take yi kafin kowa ya gane.

Bayan an kammala ne aka haɗawa Malamar takardun ta fice wani malami ya shigo, bayan kwana biyu da rubuta test ɗin sai gashi hissar Malamar ta zagayo ta dawo, cike da ɗoki kowa yake murna saboda test ɗinsu da ta fara raba masu, wadda kusan kowa ma na ajin ya canye amman Dije cike da mamaki ta ƙurawa takardar kallo, cen dai ta kasa haƙuri saboda jin Malamar tace duk wanda yake da wani ƙorafi ya faɗa, aiko cikin sauri tace

"Malama naga nan ƙasan tambaya ta biyu kin zagaye mani baki bani marking ko ɗaya ba, gashi kuma na bada amsar karin maganar da kika ce a kawo guda biyar"

Malamar ta zo gaban desk ɗin Dijen ta tsaya ido cikin ido tace da Dijen,

"Karanto karin maganar muji me kika rubuta?"

Dije ta fara kwantawa kamar haka

"ALLAH ya kashe Uwar Ubana lafiya"

Malamar ta ce da ita

"Ƙara dubawa dai ki ga"

Dije ta sake karantawa kamar farko, Malamar tace ta dai sake dubawa da kyau aiko Dije ta ƙara ƙurawa takardar kallo tana karantawa fillah fillah tace

"ALLAH ya kashe Uwar.... Uban......ki lafiya"

Aiko ba sauran Yan ajin ba har ta ita kanta Dujen sai da ta zaro ido saboda ita har ga ALLAH ba haka taso ta rubuta ba, Malamar ranta a ɓace tace

Da sauran abokan zaman Dije wa zai riƙe mata ita?,kusan mutum huɗu ya fito yace "shi, shi," aiko cikin tsananin ɓacin rai Malamar ta kalli Dijen tace

"Daman jira nike yi ki kawo kanki Khadijah yau sai na wulaƙantaki"

Aiko jikin yan ajin yayi sanyi ƙalau saboda ganin yanda take ɗasawa da Dijen amman yau take faɗar haka, aiko Malamar ta sa aka kira sergent ya zo ta karɓi bulalarshi tace da Dije ta kwanta, cikin tsananin tsoro Dijen ta fara roƙonta akan ta yi haƙuri WALLAHI ita ba abunda ta je rubutawa ba kenan kuskure ne, aiko Malamar ta kasa sauraren magiyar da Dijen take ta kwantar da ita ƙasa flat ta dinga zuba mata buloli tun yaran class ɗin suna lissafi har suka gaji suka daina, don kuwa dukan Dijen take yi ba na wasa ba duka irin na fitar hankali har sai da Dijen Baffah ta yi suman ƙarya sannan ne ta ƙyaleta ta daina dukanta ta kwashi tarkacen kayanta ta tsallaketa ta fice.

Hannatu da sauran abokan Dijen suka taso suka talalllabeta suka yi store ɗinsu da ita, aka fara yayyafa mata ruwa ana yi mata fifita, Dijen ta fashe da wani azababben kuka gwanin ban tausayi abokan sai lallashinta suke yi, Hannatu kam itama kukan take yi saboda tsananin tausayin Dijen don ba ƙaramin duka ta ci ba a hannun Malama Ubaidah ba, amman duk da hakan baisa ta kasa turo wata prefet waton sabuwar Captain ɗin House ɗinsu Dijen, akan ta baiwa Dije aiki mai tsanani kullum safiya tare da rakiyar wasu buloli goma kullum ba fashi har na tsawon sati biyu.

Aiko Dije cikin jinyar raunukan ta fara yin aikin kamar gaske sai ko gashi rana ta uku tun Asuba ta saka Uniform ɗinta daga Masallaci bata dawo House ɗin ba ta bi wata ƙofa tayi area classes abunta, akaci nemanta har aka gaji amman ba'a ganta ba dole akasa wasu suka yi aikin tunda ba'a ganta ba.

Sai bayan an dawo school ne prefet ɗin ta ganta ta yi mata faɗa sosai tare da jan kunnenta akan gobe ta sake tserewa linka mata aikin za'ayi, amman duk da hakan bai hanawa Dijen sake fecewa ba wata safiyar haka suka ci gaba da yi har prefet ɗin ta haƙura don kanta, amman kam Dije taci alwashin sai ta rama abunda Malamar ta yi mata komi daren daɗewa.

Aiko sai gashi wata rana Malamar tana yi masu karatu ta ce da Dijen taje Office ɗinsu ta ɗauko mata jakarta da zata ɗauki wani abu, aiko Dije tun daga cen ta yi sa'ar cafke wani ƙadangare ta jefa mata a jakar ta kawo mata, cikin Sa'a aka kirata ga waya da saurinta ta zura hannu da nufin ɗauko wayar aiko ta cafko ƙadangaren, ba shiri ta fasa wata uwar kuwwa ta saki jakar ƙasa, cikin sa'a ƙadangaren ya yo tsul ya fito ya haye ƙafafunta ya yo saman jikinta aguje, ba shiri Malamar ta fara ihu tana cilli da kayan jikinta tsakanin gyalen da dankwalinta har ma da yunƙurin cire doguwar rigar da ke jikinta, sai gashi anyi Sa'a ya fito jikinta da sauri ya fice don shima neman hanyar tserewa yake yi.

Aiko cikin tsananin firgici ta kwashi kayanta jikinta sai rawa yake yi ta zo zata fice taci tuntuɓe ta faɗi sai ga Malama ƙasa ta baje dafe da ƙugu tana yamutsar fuska, cikin jin kunya ta yunƙura da ƙyar riƙe da ƙugunta da ya bugu ta fisgi gyalenta a hannu tamkar wata zararra ta yi waje, inda fitarta ya baiwa ƴan ajin damar fito da dariyarsu da suke ta ɓoyewa, Dije Kam har ƙasa ta kai dafe da cikinta tana wata irin arniyar dariyar muguntar da ta yi, cikin ranta tace..

_"Gobe ma ki sake dukana da wani ƙaramin kai naki sai kace Ladingo ta baki aro😝"_

Yaran ajin ma kowa sai uban dariya yake ci musamman idan sun tuno ihu da kururuwar da Malamar ta yi, musamman dai faɗuwar da ta yi ta baje ƙasa tare da yin zaman yan bori.

Sai bayan sun koma Hostel ne take sanarwa da Hannatu cewa itace ta saka mata ƙadangaren, Hannatu ta rufe baki tace

"Don Allah Ni dai to kar ki bari wani ya ji aje a sanar da ita ki sake shiga uku"

Dije ta yi saurin faɗin

"Tab! Ai WALLAHI duk ta kuskura ta sake dukana sai na yi mata abunda sai ta yi kuka"

Hannatu ta zaro ido waje tace,. "Ni dai Ƙawata ki rage tsokano abunda zai saka ayi ta dukanki a banza don ALLAH"

Dijen ta yi shiru tace

"Ke Ni fa in banda nike son Karatun nan ko to yasin da na jangwalo abunda makarantar nan zata hautsine gaba ɗaya"

Hannatu ta yi shiru sannan tace,. "Wai ni kam Khadijah ke bakya gajiya da janyo abin magana ne??"

Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Cabd'i ai ni idan banyi ba bana jin kaina dai dai yanzu dai mu je ki rakani inyi fitsari"

Suka rankaya gefen wani Pampo Dije ta tsugguna tana fitsarin tace da Hannatu ta je wajen wasu yara da ke cikon ruwa a bokitansu tace da su ita senior ce su bata ruwan tayi tsalki ko taci Ubansu.

Aiko Hannatu ta nufi wurinsu ta sanar da su saƙon Dijen suka bada ruwan jikinsu yana rawa ta kai mata, Dije kam bayan tayi tsalkin ne ta yunƙura kenan zata tashi ta hango wata prefet cikin waɗanda ta janyo aka karɓewa ɗankwali, ta zo da wasu yara da bokitai cike zata ɗibi ruwa aiko ba shiri Dijen ta koma tsugunnen tamkar fitsarin take yi da gaske don bata son ta ganta, aiko Dije tana zuƙunne wajen har ƙafafuwanta suka yi sanyi, kasancewar prefet ɗin cin layi ta yiwa yaran bayan ta cika bokitanta ne idonta ya kai kan Dije da ke tsugunne tace

"Ke don Ubanki zo ki ɗauki ruwan nan mu je"

Dije ta yi kamar bata ji ba ta ƙara shan jinin jikinta, prefet ɗin ta ƙara ɗaga murya tace

"Ke wai don Ubanki ba da ke nake magana ba wai? Zaki taso ki zo ki sai na ci Ubanki"

Yaran suka zaro ido suka ce "laaaah! Ashe ba senior bace ita shine tace in bamu bata ruwa ba zata ci Ubanmu???"

Prefet ɗin ta zaro ido tace "haka tace da ku??"

Suka tabbatar mata aiko cikin sauri ta je ta cafko ƙugun Dije ta janyota har gindin pampon tace

"Yau sai na koya maki hankali don Ubanki ɗauki ruwan mu je"

Dije ta ɓata fuska tace

"Bana ɗibar ruwa ko a gidanmu saboda aljanuna basa bari in ɗora Abu saman kaina".

Prefet ɗin ta yi wata shewa tace,. "Ashe ko yau zanyi bikin cin Ubanki don ko ɗiyar wa ce ke a garin nan sai na cakwaɗaki sai dai a koreni gaba ɗaya in bar makarantar"

Cikin tsoro Dijen ta ɗauki bokitin ta ɗora a kanta sauran yaran suka ɗauko wasu su ma, prefet ɗin tana gaba suna biyarta sai kawai Dije taci tuntuɓe sai ga bokitin ya yi sama ya faɗo ƙasa gaba ɗaya ruwan suka zube ƙasa itama suka jiƙata.

Ba shiri prefet ɗin ta waigo tana ƙarewa Dijen kallo sama da ƙasa tana wassafa irin abunda zata yiwa Dijen ta soshe haushinta da take ji.



Ni dai kam ba da ni ba yasin nayi nan🏃🏻‍♀️don kar ace nasan mafarin faɗan😛




Akafta😅







D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Duniya Rawar ƴanmata na gaba sai ya yo baya zamani adon tafiya ne baya ɓoye baiwata aha💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*

*Sonki a jinin jikina yake my Hannah ina yinki sosai har cikin ɓargona alkhairin ALLAH ya kai maki har gadon baccinki my besty💋*



*Lamba ta 35*



Cikin zafin nama ta kaiwa Dije wani bahagon mari, Dije ta dafe gefen fuskar tare buɗe baki tana faɗin

"Laaa! Laaa! Laaa! Mu kika mara? Ashe ko yau zamu yi luguden dafuwar kanki a kogin burunduƙusuru zunbukur, ayyihuhu kibiyarmu zama daram iso ta hannun damana"

Ta ɗaga hannunta sama kanta ƙasa tana wani surutai kafin kace me sai ga Dije ta yi tsalle ta ɗale prefect d'in tare da cafko gashin kanta da ƙarfi cikin ikon Allah sai ga tsoron prefect ɗaya a hannun Dijen ta raboshi daga cikin ƴan'uwanshi ta jefar, ta sake komawa ta cafko fuskarta iya ƙarfinta ta fara yakuceta ta ko'ina cikin wasu irin surutai da ita kaɗai tasan ma'anarsu, cikin ƙanƙanin lokaci sai ga jini ya fara saukowa tun daga cikin kan prefect d'in yana gangarowa zuwa jikinta, saboda tsoro ɗaya da Dije ta cire mata aiko jini ta ko'ina sai zubowa yakeyi, azabar hakan tasa prefect ɗin ƙwacewa ta arce da gudun bala'i tana faɗin a taimaketa saboda ganin ya firgitata gashi bai daina saukowa ba, Dijen ma haka bata daina biyarta ba aguje itama tana faɗin

"Ai billahillazi yau sai mun kasheki dole ne ma sai mun sha romon kanki a cikin daren yau"

Prefect kam tana gudun ceton rai tana faɗin,. "Ku rabani da ita tun kafin takasheni jini jini ku taimakeni zata kasheni"

Mutane kam kowa ya hango Dije sai ya dare shi ma ya nemi maɓoya saboda ganin abunda ta yiwa Prefect ɗin wanda a duba ɗaya za'a ce aikin baƙaƙen aljanu ne, duba da yanda Dijen take ƴar firit da ita amman ta ci galabar Prefect ɗin da take ƙatotuwa.

Aiko saboda ganin kowa yaƙi yarda ya tunkari Dijen a riƙeta yasa Prefect ta ƙara ƙarfin gudunta ta nufi bakin Gate wurin Baba maigadin Hostel ɗinsu, tana kaiwa ta yi Bayan maigadin tana kururuwar ya taimaketa, Dijen ma itama tana isa ta yi wata irin arniyar ƙara cikin ƙaraji tace

"Murkutus riƙe muna ita a cire shegen kan nan!!!!"

Tayi cikin Baba maigadin da nufin ta cafkota aiko ba shiri Prefect ta some saboda tsananin tsabar tsoron da taji, Maigadin cike da jin haushi ya cira wata ƙatuwar bulalarshi ta doki ya sakarwa Dije har sau biyu, Dije jin azabar saukar bulalar yasa itama ta yi wani tsalle ta faɗi ƙasa tana surutan faɗin

"Ku tafi da ruhinta ga mu nan zuwa ku je ku je fa yanzu a fara dafuwar tarugu da tattasai duka a saka kar a saka gishiri a saka sugar ihu wayyo ALLAHna WALLAHI sai mun kashe duk wanda ya sake taɓa muna goɗiya"

Tana ƙare faɗar haka ta yi ɗif sai yawu take fitowa a bakinta tana furzarwa suna sauka kan fuskarta tana gurnani, ganin haka yasa wasu Prefect suka nufi ƴar'uwarsu suna zuba mata ruwa ta farfaɗo amman duk da hakan jinin da ke fita cikin kanta yasa ya sake bugeta ta tafi luuuu suka rirriƙeta suna kiran sunanta, inda wasu kuma suka nufi Dijen anata ƙoƙarin talallabarta tana ihu tana botsarewa.

Kai tsaye wasu da yawa suma aljanunsu suka fara tashi kafin ka ce me Makarantar ta hautsine da tashe tashen aljanu, sai yarinya tana tsaye sai dai aga ta heta kuwwa ta faɗi ƙasa tana sambatu aiko makaranta ta rikice ko ta ina sai ihu ake yi.

Ana cikin hakan sai ga wani Malami da vice principal sun shigo bakin Gate ɗin Hostel ɗinsu saboda labari yaje garesu cewa makarantar ba lafiya, sai ko gashi sun taradda abunda ya firgitasu agurguje aka ɗauki Prefect ɗin mai suna Rukayya aka nufi clinic da ita don har lokacin cikin mayen bugun jinin take sai mashalo take yi, Dije kam malamin yasa aka kawo masa ruwa a kofi yayi mata addu'a ya tofa mata ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login