Showing 93001 words to 96000 words out of 136985 words

Chapter 32 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

2105

kuma ke baki san yanda ake rufe sirrin miji ba to ki tona ɗin sai inga da ni da ke waye zai jiyo kunya?"

Wasu hawaye suka zubo mata akan fuska tace, "WALLAHi ALLAH baka kyauta man ba, yanzu shikenan zata gano na iskance"

Ya yi shiru yana saurarenta tana kuka tana soki burutsun zantukkanta, har suka je bakin gate ɗin gidan sannan ta sake fashewa da wani sabon kukan, cike da mamakinta da fargabar da ta cika masa zuciya ya yi parking ya fito suna gaisawa da ma'aikatan gidan, Dije kam kasa motsi ta yi har sai da ta ji yo muryar Fiddo tana yi wa Safwan Oyoyo.

Sannan ta muskuta da ƙyar ta fito tana goge hawayen da suka ɓata mata fuska, ganin yaran wata yayarsu Safwan ɗin sun nufota suna faɗin

"Oyoyo sannu da zuwa" yasa ta washe ta taryesu da murnarta ta ɗauki ƙaramin yaron, ko kallon Fiddo da shi bata yi ba ta fara taku a hankali cikin ƙarfin hali ta shiga cikin gidan, Safwan ya bi bayanta da kallo cikin tausayawa halin da take ciki a zuciyarshi, Fiddo ma shi ta bi da kallo tana faɗin

"Ai WALLAHi yayanmu duk abunda Hajiya ta yi maka ka fanshe akanta, kana ga fa tunda ta bar gidan nan bamu sake ganin fuskar Hajiya ba, kullum zancenta ɗaya ne ALLAH ya dawo da wannan ƴar ƙauyen lafiya, ita bata ko ta jin taka sai ta ɗiyar wasu haka kawai ta zo ta ƙwace muna fada a wurin Hajiya, yawwa ina zancen da ta ji muna yi da kai....? shikenan fa ta hau akan cewa wai ni da kai ne muka haɗa kai muka sa ƴar ƙauyen ta bar gidan, duk rantsuwar da nasha yi mata fa bata yarda da ba hannunmu ba"

Safwan ya bita da kallo mai cike da harara yace, "to wai ke wa ma ya tambayeki wannan uban surutun da kike yi? Yarinya dai gata na dawo da ita to kuma yanzu me yayi saura?"

Fiddo cikin tsoron yanayinshi da taga ya canza a lokaci ɗaya yasa ta sha jinin jikinta ta ce "ka yi haƙuri big bros Bari in shiga ciki kafin ka ƙaraso"

Da sauri ta shige ta barshi yana tunanin ya shiga ko ya bari sai dare ya sulalo ya shige ɗakinshi?, Wata zuciya tace da shi ya shiga kawai ya roƙeta yafiya ya sauke nauyin, ya mazge ya ja ƙafafuwanshi ya shiga gidan cikin fargaba, yana ta rokon ALLAH a zuciyarshi akan kada yasa Hajiya ta ja abun da tsauri.

Sai dai yanayin da yaga ta tarbeshi ne yasashi shan jinin jikinshi amman a hakan ya ƙoƙarta yace,

"Don Allah Hajiyarmu ki yi haƙuri WALLAHi......."

Ta yi saurin ɗaga masa hannu tace, "ajiye ban haƙurinka ni ba shi nake buƙata ba, yarinya dai gata ta dawo hannuna to kaji da kanka kawai don ALLAH"

Safwan zai fara yi mata magiya ta katsa masa tsawa tare da bashi umurnin fita ɗakin, ya miƙe ba shiri ya fice cikin ƙunar zuciya, Hajiyar ta bugawa Fiddo da ke tsaye wata uwar harara itama ta fice sum sum, ta kalli Dije da ke zaune tana sharar ƙwallah ta ce

"Ke kuma jeki ɗaki ki jirani kafin in zo"

Dije ta miƙe a hankali ta fara ɗingisa ƙafa Hajiya ta bi ta da kallo har ta shige, cikin tausayawa ta dawo da kallonta ga Yayarsu Safwan ɗin tace

"Ummi ki kirashi kawai yanzu tunda har mun samu ta dawo lafiya, gobe idan ALLAH ya kaimu tun da sassafe sai ku kama hanya, saboda bana son ma yasan ke ce kika tafi da ita, don nasan halinshi bana don ya dameki akan sai an bashi ita"

Aunty Ummi ta yi shiru sannan tace, "Hajiyarmu naga kamar yanzu yana son Matarshi fa ki yi haƙuri ki yafe mashi don ALLAH Hajiyarmu"

Cikin tsananin ɓacin rai tace "eh nasani Kuma a sanadiyar hakan ma ne nike son nuna masa cewa ko shege yana da ranar shi, saboda haka ki yi abunda nace da ke kawai umurni na baki ba shawararki na nema ba"

Cikin sanyin jiki Ummi ta ɗaga waya ta kira wani mai suna Garba, bayan ya ɗauka tace da shi gobe tun da sassafe ya zo ya ɗaukesu ya yi driving ɗinsu ita da yaranta zuwa Abuja.

SAFWAN kam yana fitowa kiran Ruma yana shigowa wayarshi, ganin mai kiran har yaso kar ya ɗauka ganin ta dameshi da kiran ne yasa ya ɗaga, cikin Muryar kuka Ruma tace

"Don Allah ka zo Zee tana cikin mawuyacin hali kuma ba wanda take kira sai sunanka, plss ka zo WALLAHI tana unconscious we need your help seriously kuma urgent plss and plss"



Wata sabuwa🤦🏻‍♀️






Akafta😉









D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Ku yi haƙuri ku yi haƙuri ni ma ba haka na so ba😢*



*Lamba ta 55*


Cikin wani sabon tashin hankali tare da kiɗimewa ya koma wurin Hajiyar, yana sanar da ita halin da Zee take ciki tare neman izininta akan komawar da yake son yi Gomben, ba tare da wata damuwa ba ta ce da shi ALLAH ya tsare, har ya fito ya dawo yana sosa kai yace

"Khadija fa? Don Allah zan bata saƙo kafin in tafi"

Hajiyar tace da shi tana ciki ya yi saurin shigewa ɗakin zuciyarshi cike da tunanin abubuwa da yawa a ranshi, sai dai yanayin da ya taradda ita ne yasa gwiwowinsa suka yi sanyi, cikin mutuwar jiki ya ja ƙafafuwanshi ya isa wurin da take kwance tana ta cisgar kuka, ya yi saurin duƙawa gaban gadon tare da ƙoƙarin ɗago fuskarta amman ta ƙi ba shi damar hakan, cikin damuwa ya ce

"Haba khadija yanzu kuma me aka yi maki?don ALLAH ki yi haƙuri ki yafe mani abunda na yi maki, Ni ma ba da son raina ba na kasa controlling kaina ne shiyasa, ban san me yasa na sake aikata maki abunda na yi ba duk da nasan zan cutar da ke, plss ki yafe mani don ALLAH, plss ki ɗago fuskarki ki ce dani kin yafe mani don ALLAH"

Dije taƙi ɗago fuskar haka ma ta ƙi daina kukanta, yana cikin magiyar ne kira ya sake shigowa wayarshi, cikin sauri ya fiddo wayar ya duba ganin Daddyn Zee ne da kanshi yasa ya yi saurin ɗagawa, cikin muryar kuka mai haɗe da tashin hankali Daddyn Zee ya ce da shi

"Don Allah ka zo ƴata zata rasa ranta a sanadinka, plss ka bi yo jirgi urgently ake buƙatar ganinka, don ALLAH ka taimaki rayuwar ƴata ka zo"

Ya ce "insha ALLAHu zan zo soon" sannan ya kashe wayar ya miƙe jkinshi yana rawa ya kalli Dije da ke ta kukanta, cikin damuwa ya ce

"Ni zan je Gombe yanzu Khadija ki yi man addu'ar dawo wa lafiya kinji?"

Yana ƙare maganar ya duƙo da kanshi saitin fuskarta ya sakar mata da wani kiss a kumata sannan ya fice da saurinshi, daga nan inda take tana ji yo shi yana yin sallama da su Hajiyar, haka kawai ta ji kamar ta tashi ta bishi ta sanar da shi ta yafe masa, amman wata zuciyar ta gargaɗeta akan kada ta yi hakan saboda kunyar idonsu Hajiya da Aunty Ummin da ke falon, sai dai a zuciyarta ta yi masa fatar ALLAH ya dawo da shi lafiya, saboda bata fahimci ko wanene ya yi kiran nashi ba, ammsn taji rashin son tafiyar har cikin ranta.

Tana kwance ɗakin ne Hajiyar ta shigo ta yi toilet minti biyar a tsakani sai gata ta fito ta ce da ita ta biyota toilet ɗin, cikin fargaba Dije ta miƙe ta tako a hankali saboda zafin da take ji yana ratsata, sai dai ganin fuskar Hajiyar a haɗe ya sa ta yi saurin gyara tafiyar cikin ƙarfin hali, Hajiyar ta maka mata wata uwar harara ta ce

"Ki cire komi naki ki shiga cikin ruwan nan ki buɗa ƙafafuwanki da kyau su ratsa jikinki, ki yi haka har sau uku duk kika tara ruwan kinga wannan maganin ki zuba a cikin sannan ki sake shiga, idan kuma baki yi yanda na ce da ke ba to ni zan zo da kaina in yi maki, tunda ke Kika janyo wa kanki duk abunda ya yi maki, to ai ga shi nan ya barki da jinyar jiki shi ko a jikinshi"

Cikin fushi ta fice toilet ɗin tana ta ƙananan faɗa, Dije ta bi ruwan da ke cike da bahon wankan har turirin ɗimi suke yi, amman saboda gudun ta zo ta yi matan kamar yanda ta faɗa ya sa ta yi saurin cire kayanta ta shige ruwan zafin ta zauna, ruwan suna shiga jikinta tana yarfa hannu tare da cije leɓe har suka dallashe, sannan ta fara jin ƙarfi a jikinta ta yi hakan sau uku kamar yanda Hajiya ta ce sannan ta yi wanka ta fito, sai gata tana takawa da kyau duk wani zafi da take ji ya rage sosai, bayan ta shirya ta ci abinci ne Hajiyar ta zaunar da ita ta ce

"Gobe idan ALLAH ya kaimu Ummi zata je da ke Abuja, zaki zauna a cen ki ci gaba da karatunki a cen, insha ALLAHu zata riƙeki kamar yanda na yi maki a nan, fatana kawai ke ma ki ɗauke ta tamkar yanda kika ɗaukeni, don duk da kinsani amman dole in ƙara sanar da ke cewa itace gaba da Safwan shi yake bi mata, ki yi haƙuri da duk abunda ya yi maki da sannu zai hankalta har ya dawo ya baki matsayin da nike ta yi maki fata a wurinshi, sai dai ki iya mu'amala da kowa saboda yanzu da da cen inda aka fito ba ɗaya ba, kina da aure kuma Mijinki yana sonki ko da ko bai faɗa ba, saboda ki riƙe masa amanar kanki kuma ki riƙe mutuncin aurenki, ALLAH ya baku haƙurin zama ki dage ki yi karatunki don shine gatanki ko don ke ma ki tallafi iyayenki da hannunki"

Dije ta yi shiru tana sharar ƙwallah tace "ALLAH ya bamu haƙurin zama"

Ummi da Hajiya ta ce "Ameen"

Tun cikin daren ranar Hajiya ta haɗa mata kayanta tsaf! Asubar farin Garba ya zo ya ɗaukesu suka kama hanya sai fatan sauka lafiya ake ta yi masu, bayan tafiyarsu ne Hajiya Mama ta riƙo kunnen Fiddo ta ce

"Ke kuma WALLAHi ko da wasa na ji kin sanar da shi cewa ga inda Matarshi ta ke, to ki sani daga ranar kin bar gidan nan, don kuwa ƙauyensu Baabah Kulu zan kai ki cen ki zauna har sai an tashi aurenki a dawo da ke nan"

Fiddo ta zaro ido waje tace "Haba Hajiya wannan mugun ƙauyen? Ai WALLAHi ni ko yini ɗaya ba zan iya yi a cen ba bale har in yi rayuwa a cen tab! Mutuwa, Hajiya garin da ko toilet ba bu daji ake kashi kike so in je inyi rayuwa a cen?"

Hajiyar ta sunne dariyarta tace, "to idan ba kya so ki ceci kanki kawai a wuce wurin, amman WALLAHi duk ranar da naji kin faɗa masa inda take to a ranar zaki bar garin nan ki je cen"

Fiddo ta yi saurin shigewa ɗakinsu tana zancen zucinta tana faɗin, "to ni me ma zai sa in faɗi inda take tunda har ma ba wani damuwa ya yi da ita ba, kuma ma ni daga ALLAH ya rabamu da ƙaya ai godiya yakamata inyi wa ALLAH ba wai faɗa masa ba, don ni har kuɗi ma zan iya badawa akan kada ya gano inda take"

Ta faɗa gadonsu cike da jin daɗi tace"ALLAH ya raka taki gona WALLAHi Ummu ta gayar da Aysha"

***

Safwan kam a kiɗime ya isa Gomben kai tsaye Asibitin ya nufa don ko Lawi bai nemi rakiyarshi ba, sai kuwa ga shi zuwan ya yi rana don kuwa ko da ya je numfashinta sama tana kiran sunanshi cikin dusashiyar muryar da ta sha ciyo na faraɗ ɗaya, mahaifiyarta da Daddynta da sauran Yan uwanta da Aminu da ƙawarta Ruma duk kuka suke yi, ganin Safwan ɗin da ta yi ne yasa ta yi saurin kiran sunanshi da ƙarfi ta some, ai kuwa ɗakin ya ɗauki kuka saboda tsammaninsu ko ta rasu, shi kanshi Safwan ɗin kwatanta tashin hankalin da ya shiga abu ne babba, saboda ganin yanda ta rame lokaci ɗaya sai karen hanci da ya fito idanuwanta duk sun zurma, hankalinshi bai kwanta ba har sai da likitoci suka rufu a kanta tare da yin nasarar zuƙo numfashinta, cikin dawowar numfashin ne ta fara nishi sama sama tare da sauke numfashin da sauri da sauri, Mahaifin Zee ya zo gabanshi ya duƙa hawaye suna kwaranya akan fuskarshi ya ce

"Ka taimaki ƴata ta dawo cikin natsuwarta"

Aminu da ke tsaye ranshi a ɓace ya fice ɗakin, Safwan ya ɗago Mahaifin Zee ɗin ya miƙe cikin kwantar da murya yace

"Ka yi haƙuri Alhaji Insha ALLAHu ALLAH zai bata lafiya"

Muryarshi da ta ji yo yasa ta yi saurin faɗin sunanshi, Likitan ya ce ya matso kusa da ita ya bashi wuri ya matsa jikin gadon, Zee ta yi saurin riƙe hannunshi ƙam ƙam tana zubar da wasu hawayen takaicin kanta ta ce

"Me yasa ka yi man ƙarya? Me yasa ka amince da ni bayan kasan kana da matarka wadda ka fi so fiye da ko wace mace?, a hakan ka so in aureka in je inyi auren boranci? Ina sonka my man amman ka sani ko da zan mutu ba zan aureka ba, na yafe maka abunda duk ka yi mani ALLAH ya haɗa fuskokinmu a al..ja..n...n...ah"

Sarƙewar da numfashinta ya yi ne yasa ta sake somewa, Mahaifiyarta ta fashe da wani uban kuka, Ruma da ƙawarta da sauran matan da ke ɗakin suma suka kwantsama kukan, da ƙyar likitoci shawo kansu wajen fitar da su ɗakin suka dawo kan Zee ɗin suna ta aikin neman ceton rayuwarta.







Wayyo Zee Baby😢




Akafta🥰









D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*Addu'o'inku da kullum kuke bina da su ba ƙaramin faranta man zuciya suke yi ba🥰, na gode 🙏🏻sosai Mutanena Alkhairin ALLAH ya kai maku a ko ina kuke👍🏻 muna kyawon tare🤝🏻*



*Lamba ta 56*



Likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu amman numfashinta sai sama da ƙasa yake yi, wani likita ya ce da Safwan ɗin ya yi mata magana cikin daɗaɗan kalamai, ko da ALLAH zai sa ayi nasarar ceto ranta cikin mawuyacin halin da take ciki, saboda tana sonshi idan ta ji muryarshi kuma ALLAH ya shiga cikin lamarinta aka yi dace za'a yi nasara.

Safwan riƙe da hannun Zee ɗin da har lokacin take riƙe da shi jabau!, yana hawayen tausayinta ya ce

"Plss my precious ki tashi gani a kusa da ke, ke ma kinsan ina sonki kuma bazan iya rayuwa babu ke ba, plss and plss for give me i apologies for you and everything else, ki tashi ki kalleni ido cikin ido in sanar da ke a shirye nike da aurenki a kowane lokaci, kinsan na yi maki alk'awali kuma insha ALLAHu bazan saɓa ba, ki tashi ki kalli Man ɗinki ki ido cikin ido ki ce kin yafe masa plss my dream"

Ya ƙare maganar cikin wata muryar kuka saboda yanda yaga har lokacin numfashinta ya ƙi daidaita, saboda yana jin tsoron ace ƴar mutane ta mutu ta sanadinshi, ganin anƙi samun abinda ake buƙata ne yace da likitocin su bashi minti biyu, saboda sun san kan aikinsu yasa suka bashi haɗin kai wajen ficewa dukansu, Safwan ya miƙe ya yi sunkuyo saiti da fuskarta ya buɗa bakinta ya saka nashi ciki, cikin wani salo ya fara zuƙo numfashinta a hankali tare da yi mata kalamai masu sanyi tare da kiran sunayen da suke faɗawa junansu cikin wata murya mai tsada, cikin nasara Zee ta dawo hayyacinta tare da fara zubar da hawaye gefe da gefen fuskarta, sannan ta ƙura masa ido ko ƙiftawa bata yi saboda ganin take yi abun kamar almara ko a mafalki, Safwan ɗin da ko hannunta bai son taɓawa ko acen ƙasar Turai wai shine yau da tsotsar bakinta, cikin mayen sonshi da ke fisgarta ta riƙe hannunshi gam ta ce

"My man me yasa ka yaudareni?"

Ya yi saurin ɗora hannunshi akan lebenta yace, "ki bar zancen plss a shirye nike da aurenki a duk lokacin da kika tashi"

Zee ta washe baki cikin farin furucinshi ta ce, "duk da ka yaudareni amman still har yanzu ban daina sonka ba, me yasa so yake makaho ne? me yasa zuciyata ta ƙi karɓar ƙiyayyarka da na yi ta cusa mata?, Haƙiƙa ka yi nasarar samun sarautar zuciyata You are my prince chrmn and my everything shonah"

Safwan cike da tausayinta yace "na yi kuskure ki yafe mani albarkacin son da kike mani ko don ceto lafiyarki, saboda ko da ina son a yi muna auren yanzu kin ga sai an jira kinji sauƙi tukunna, don kin san ba za'a yi aure kina cikin ciwo ba"

Zee ta yi saurin share hawayenta ta yunƙura da nufin ta shi zaune amman ta kasa, dole ya riƙata ta tashi zaunen tare da taimaka mata ta jingina jikinta da filo tana binshi da kallon ƙauna, cike da jin daɗin ganin nasarar da aka samu ne Safwan ɗin ya leƙa ya kira likitocin, abun mamaki sai ga Zee sun taradda ita zaune tana share hawayenta jefi jefi.

Cikin sauri wani likita ya kira Iyayenta suka shigo cike da jin daɗin albishirin ɗin da ya yi masu, mamaki fal zuciyoyinsu saboda ganin yanda ta ke zaune har da su dariyar ƙarfin hali, dukansu har likitocin sun gasgata ba ƙaramin so Zee take yi wa Safwan ba, Aminu kanshi da ya dawo ya taradda ita zaune ana bata tea tana sha ya jinjina lamarin, take yanke ya sallamawa kanshi barin Zee ko don ta samu abinda take so, saboda a yanzu ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya yi abunda ALLAH bai tsara a cikin rayuwarshi ba, haka wani bai isa ya auri matar da ba ta shi ba, don da tuni ya aureta saboda dakon sonta da ya yi ta yi a zuciyarshi tun tana ƙarama.

Kowa sai murna yake yi kan haka ne ma mahaifin Zee ya ja hannun Safwan ɗin suka fita, cike da jin daɗin ganin ƴarshi ta fara dawowa hayyacinshi yace

"Duk da bansan me ya haɗaka da Zainab ba amman jikina ya bani cewa kai ka janyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login