Showing 66001 words to 69000 words out of 136985 words
house ɗinsu sai da kowa ya sani, saboda uban kuka da ta ci akan ita bata taɓa iskanci ba amman jini sai fitowa yake yi a jikinta, Wayyo ita ALLAH a taimaketa wani yaci amanarta ya iskanceta bata sani ba, Sis Aysha itace ta janyota zuwa toilet saboda uwar dariyar da taga anael yi mata, cikin natsuwa ta fahimtar da ita komi ta nuna mata ga yanda zata yi ta kimtsa kanta, sannan hankalin Dije ya kwanta amman fa tasha tsokana a wajen mutane ba kaɗan ba, lokacin da ta gama kwanakinta ma Sis Aysha itace ta yi mata gwari gwari akan yanda zata tsallake jikinta.
*Shin wai ina baƙin Turai ne?*
Malam Safwan kam tunda ya tafi Ƙasar ya yi ƙoƙarin danne damuwar da ya tafi da ita domin ya fuskanci karatunshi, sai dai wani gefe na zuciyarshi yana tunano masa Dijen Baffah da shirmenta, wani zubin ya yi dariya wani lokaci kuma ya ɓata fuska musamman idan ya tuno abunda Hajiya Mama take yi masa akanta.
Masha ALLAH kasancewarshi mutum mai tsattsauran ra'ayi yasa baya da wasu abokan kirki sai tsirara ko su just for mutunci kawai don shi miskili ne na gasken sosai, baya shiga shirgin kowa sai wanda ya dace ace ya shiga.
Wannan halin na shi ne ya janyo mata da yawa suka mato a kanshi, inda ko wace ƙoƙarin take yi ace itace ta yi sa'ar ƙulla alaƙa da shi, musamman ma da ya kasance gifted akan karatunshi ko kaɗan baya wasa, don daman cen shi tun asali yana baiwa karatu muhimmanci ko lokacin da ya yi karatun a gida Nigeria bale yanzu da ya shigo cikin fararen fata.
Matan turawan ma da yawa wasu sun ƙyasa ballantana na mu matan na baƙar fata masu zuwa cen karatu, sai dai rashin fuskarshi yasa kowace take ɗar ɗar da shiga sabgarshi don tsoron kada ya yanƙwanasu su ji kunya, amman a hakan sai da wasu turawa suka sami kanshi suka fara mutunci da shi, a cikin baƙaƙen fatarmu namu ma akwai mace ɗaya Zainab wacce ake kira da Zee bab da Namiji ɗaya Auwal da suka sami sa'ar shiga rayuwarshi, waɗanda su kansu yan asalin Nigeria ne sai dai kowane daga cikinsu suna garuruwa mabanbanta, zee Bab yar Gombe ce yayin da Auwal yake ɗan asalin Kano, wasa wasa sai gasu sun zamo aminanshi waɗanda komi zasu yi dole ne sai sun nemi junansu.
Zee Bab kam gurinta na shiga rayuwar Safwan ya cika don kuwa sannu a hankali ta fara nuna masa irin yanda ta damu da shi, kasancewar ba directly ta fito masa ba shiyasa bai hantareta kamar yanda ya saba yiwa sauran mata ba, cikin dabara ta ƙulla alaƙar soyayya da shi mai ƙarfi, wadda ta kai basa shayin nunawa duniya irin yanda suke son junansu ko a gaban ma waye, har suna iƙirarin zasu auri junansu duk runtsi duk da cewa itama Zee ɗin tana da mijinta da zata aura acen gida Nigeria.
Sai dai akasin da aka samu shine ranar da Safwan ya sanarwa da Hajiya Mama labarinta rufe ido ta yi fata fata da shi, akan cewa bata lamunta da ya auri kowace mace ba har sai ya mutunta auren Dije tukunna, shi ko ya nuna mata shi fa ba sonta yake yi ba yanzu ya sami matar aure kuma ita yake so ya aura, don hasali ma ita kanta Zee ɗin bai sanar da ita cewa yana da wata mata ba, saboda rena auren Dijen da ya yi a tunaninshi da ya auri Zee zai korata ta koma ƙauyensu, idan kuma Hajiya ta bashi dama zai cikawa amininshi Lawi alƙawalin da ya yi wa kanshi na duk runtsi sai ya mayar masa da ita ya aureta tunda har ya fishi sonta.
Sai dai kuma gashi Hajiya Mama tana son dakushe masa karsashi, don shi kam sun riga da sun daidaita da Zee akan da ya kammala karatunshi zasu dawo gida Nigeria ayi aurensu kawai.
Akan haka ne ma rashin fahimta ya shiga tsakaninshi da Hajiyar, idan ya kira wayarta ta ƙi ɗauka ya galabaita sosai da mugun fushin ta yi da shi sosai, saboda duk Iyayenshi maza ya yayunshi biyu mata da suke aure duk sunyi ta bata haƙuri akan ta barshi ya yi auren amman ta yi biris da kowa, tace in dai har akan ta goya masa baya ne ya yi wani auren ya ci amanar yarinyar mutane to bazata taɓa lamuncewa da auren ba, jin wannan kalaman nata masu tsauri yasa ya ajiye komi ya nufo Nigeria ba shiri, sai dai yanayin da ya taradda ita ya sa ya ƙara gasgata zancenta dole marairecewa akan neman biyan buƙatarshi, tare yi mata bayanin cewa shi ba zai ci amanar Dijen ba, asali ma so yake yi ya haɗata da masoyinta na asali tunda har ya sami matar da yake so.
ganin ta ƙi amince cewa ne yasa ya kwaso mata mutane suka zo suna bata baki kowa da abunda yake cewa dangane da ALLAH ya ce Annabi yace, ana roƙonta akan ta barshi ya yi aurenshi kafin ita Dijen ta mallaki hankalinta tasan minene auren, da ƙyar aka shawo kanta amman da sharaɗin duk ranar da Amaryar ta tare itama Dijen a ranar za'a kaita gidanshi a matsayinta na uwargida, hankalinshi ya ƙara tashi ya ruɗe gaba ɗaya saboda tsoron Zee taga kamar ya munafunceta tunda bai ce da ita yana da wata matar ba, aikam ba kalar magiyar da bai yi mata ba akan ta janye zancen tariyar Dijen sai daga baya idan Zee ta zo, amman Hajiya Mama tace sam! Bata san da wannan zance ba, dole ba kuzari ya harhaɗa kayanshi da nufin komawa, saboda yanda ita Zee ɗin ta dameshi akan ya dawo ya dawo.
Hajiya ta ce da shi kafin ya bar ƙasar ya je makarantarsu Dije ya ganota, amman don kada ma ta gano ba zuwan zai yi ba ya nuna mata cewa zai je har da cewa ta kawo saƙo, aikam sai ga shi saƙon ma da ta bada akaiwa Dijen aika mata ya yi shi ya fece, zuciyarshi cike da mugun jin haushinta saboda shiga rayuwarshi da ta yi, uwa uba yanzu da ta sanadinta aka hanashi yin abunda yake so, don shi bai ma san da wane kalar idon zai kalli Zee ya sanar da ita cewa wai yana da mata, kuma matar ma irin Dije ai wannan ma shi idan ta sani ya zubarwa da kanshi aji, shiyasa ya ci alwashin ba zai taɓa bari tasan da wannan mummunar maganar ba, har sai idan an ɗaura masu auren da ita idan ta zo ta gani da kanta ta ji da kunnuwanta, akan haka ya tsayu suka ci gaba da zuƙar soyayyarsu hankali kwance, duk da kuma wani gefen na zuciyarshi cike yake da fargabar Zee ta san da labarin kafin aurensu.
***
A cen ƙauyensu Dijen kuma anyi auren Usmanu da Hansai, Dijen ma ta je amman kwananta biyu ta dawo Yola saboda a lokaci ana cikin karatu ne excuse ne aka ɗaukar mata, ƙawayenta kuma su Jummala da Ladiyo ma masha ALLAH zamansu lafiya, sun ajiye shirmen yarinya sun fuskanci zaman aurensu, sai dai Balan Duduwa da kullum tsimayi yake yi zuwan ranar da Dijen zata aiko masa da zakkar, shiyasa lokacin da ma ta zo bikin Usmanu yake ta rawar jiki akan bata wani girma na musamman, ganin hakan yasa ta sake yi masa wata kyautar duk da cewa a lokacin itama buƙace take da kuɗin saboda guntayen matsalolin hidamar auren Usmanun, don ba ƙaramar hidima aka yi ba saboda ko ɗakin Hansai shafe yake fess da broking tyles, Mutane sai zuwa gani ake yi ana sontin sulɓinshi, don kaf garin ɗakinta ne kaɗai da tyles ɗin don Inna cewa ta yi ta haƙura bata so ita kam ta yafe.
*****
Kwanaki suna tafiya makonni su zo su wuce, wata ya wuce shekara ta zo wasa wasa sai ga shekara biyu an laƙumeta ba tare da an tantance ba, bikin Surayya ya zo sai hada hadar bikin ake yi bangaroran biyu, waton gidan ango da na Amarya saboda daman cen angon ne ake jira ya kammala ginin gidanshi, Alhmdllh kuma ya kammala masha ALLAH yanzu haka saura sati biyu ayi auren nasu, Safwan ma kanshi saura shekararshi ɗaya ya kammala karatun da ya je yi ya dawo gida, ayi aurenshi da masoyiyarshi Zainab wadda a yanzu yake jin akan sonta ba gudu ba ja da baya.
Dijen Baffah ma a lokacin tana J.a.s.s 3 zasu yi j.l.c su wuce s.s 1, a lokacin idan kika ga Dijen Baffah ba zaki ce itace ba, saboda yanda maƙerin ƴanmata ya fara ƙereta ta ko'ina ta cike masha ALLAH, kwanciyar hankalin da ta samu ya fito jikinta ya haskaka mata fatarta, don a duba ɗaya zaka gano tsantsar kyawon halittar da ALLAH ya yi mata, uwa uba ga kyawon fuskarta da ya fito ɗas cikin doguwar fuskarta, ga gashinta ya ƙara cika da tsawo saboda gyaran da yake samu sosai, Hajiya Mama kanta idan ta kalli Dije sai ta ji takaicin rashin sanin ciyon kan da Safwan ya nuna akan Dijen, saboda ganin yanda komai da ake so mace ta mallaka na siffar jikin Dije ALLAH ya wadata da abunta, sai dai kawai don ita ɗin tana baƙa amman kuma yanzu baƙin ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, asali ma shine ya ƙara banbantata da sauran mata, don fatarta ta murje luwai luwai ta washe gwanin burgewa, ga ƙirjinta cike fam da dukiyar Fulani kuma a tsaye suke ƙyam! ba alamun zasu ranƙwafa a gaba, saboda girkin kwarya ne da su sun cika fam kuma sun baje a ƙirjinta, duk da ba wai sun gama girman bane amman a hakan ma sai sambarka.
Ana saura kwana takwas bikin Surayya ne su Dije suka kammala zana jarabawar j.l.cn tasu, cike da farin ciki da jin daɗi suka baro makarantar tana ɗokin zuwanta gidan saboda shagalin bikin Surayyar da zasu yi.
Aiko tana dawowa suka ci gaba da shirye shiryensu tare da abokan Surryn yan jami'a, don Surry ta kammala degree ɗinta na farko cikin nasara ba tare da samun matsala ba, Fiddo ce ta yi candy a lokacin.
Ana cikin hidimar ne gaba ɗaya suna babban falo sunata tsare tsarensu ne Safwan ya kira Fiddo, cike da tsananin jin daɗi ta cire wayar daga caji ta ɗauka tana faɗin
"Oyoyo big bros don ALLAH ka zo cikin lokaci plss kasan fa kai ne idonmu"
A cen gefenshi ya ce
"Kada ki ji komi zan zo har ma da Auntynki itama zata zo bikin kuma wajenki zata sauka"
Fiddo ta yi wani tsallen jin daɗi sai dai suna haɗa ido da Dije ta maka mata harara tace,. "Kada ka ji komi big bros bani ita mu gaisa idan kuna kusa"
Zee ta karɓa cike da jin daɗin ganin yanda ƙanwarshi ke sonta tace, "Sannu Sis ki tanadi masaukina insha ALLAHu da ni za'a sha shagalin bikin Surry ki zuba idon ganina kinji"
Fiddo ta yi saurin faɗin "kina da babban masauki big Aunty fatana kawai ALLAH ya kawoku lafiya"
Safwan ya karɓa yace
"Ina Surryn?"
Fiddo ta yi wajen Surry ta miƙa mata wayar cike da jin daɗi ta ce
"Amaryar Yaya Safwan ma zata zo bikin wayyo daɗi"
Diirim! dum! Ba shiri kirjin Dije ya buga, cikin son jin gaskiyar abunda kunnuwanta suka jiye mata aranta tace
_"Amarya? Wace Amarya kuma?..."_
Tunaninta ya katse ne lokacin da Surry ta kara mata wayar a kunne cikin sassauta murya tace, "Yaya Safwan ne"
Gaban Dije ya ƙire ya faɗi ba shiri cikin ɗimaucewa ta ji wani kuka ya zo mata ba tare da ta tantance ba, saboda maimakon ta ji muryar Safwan ɗin sai jin ta yi Zee tana cewa
"Ina fatar zaku tarybeni a matsayin Matar yayanku, kuma ku ɗauki cewa tamkar ma an ɗaura na shigo familynku"
Cikin sauri Dije ta saki wayar ta miƙe da gudu ta nufi ɗakinsu, saboda zuwan wani dunƙulallen abu a ƙirjinta, wanda ya janyo ta kasa juriya bale ta haƙura da kukan bazatan da ya zo mata.
Gareku reader's shin minene wannan abun da ya ziyarci zuciyar Dijen Baffah????????😢
Akafta🤞🏻
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Domin farin cikinku kawai mutanena😅*
*Lamba ta 43*
Dije dunƙule kan gado tana kuka ta ji an dafa kanta cikin sauri ta goge hawayenta ta ɗago fuskata, aiko caraf ta yi ido huɗu da Hajiya Mama fuskarta ƙumshe da damuwa, ta yi jarumtar washe bakinta guntayen hawayenta da suka maƙale suka faɗo, cikin basarwa tace
"Me aka yi maki Hajiyata?"
Hajiya ta sake dafa kanta ta shafo dogon gashinta tace,. "Naji komi Surayya ta faɗa man ki yi haƙuri ki barni da shi ai zai zo garin ya sameni ina jiranshi"
Dije ta yi saurin faɗin
"Ki ƙyaleshi kawai Hajiya Ni na haƙura da duk abunda ALLAH ya ƙaddaro man, haka kuma ma zan yi biyayya ga duk abunda kika umurceni"
Hajiya Mama cike da jin daɗin canjin da Dijen ta samu a wurinsu tace,. "Ki yi ƙoƙari ki nuna masa cewa fa ke ma mace ce duk runtsi kada ki bada wata ƙofa da shi ko yarinyar zasu renaki"
Dije ta ɗaga kanta alamun gamsuwa Hajiyar ta riƙo hannunta tace, " saki jikinki ki koma ku je kuci gaba da shirye shiryenku, ki yi kamar daman cen komai bai faru ba"
Sai da tasata ta je toilet ta wanko fuskarta sannan suka fito tare.
Haka aka ci gaba da hada hadar tare da Dijen duk da zuciyarta ba daɗi amman hakan bai hanata nuna annushuwa kan fuskarta ba, sai dai kuma Fiddo tasha jinin jikinta saboda faɗan da Hajiya Mama ta yi mata akan abinda ta yi a gaban Dijen, duk da ta ci alwashin bazata fasa nuna ƙaunar budurwar Safwan ba ko don Dijen ta ji haushi.
Ana saura kwana huɗu bikin ne Safwan ya diro Nageria tare da budurwarshi, sai dai ita ta yi garinsu sai taga gida sannan ta zo bikin daga baya, a ranar da ya diro gidan da marece za'a je yin wani event mai suna tea party, duka Amarya da ƙawayenta da ma ita kanta Dijen da Fiddo duka sunyi shigar wani yadi milk da kalar cofee, kowacensu ta sha makeup irin na classic ladys masha ALLAH gwanin burgewa, har sun shishiga motoci ne aka manta da agogon Amarya akan stool ɗakinsu, shine Dijen ta fito ta koma cikin sauri da nufin ta ɗauko ta dawo ana jiranta su tafi.
Ta ɗauko agogon ta fito kenan a tsakiyar babban falon suka yi karo har tana ƙoƙarin faɗuwa, cikin sauri ya riƙota ta faɗo jikinshi tare da riƙeta ƙam ƙam don kar ta faɗin, jikinta yana ɓari ta yi saurin kai kallonta gareshi saboda turaren da ta ji ya tabbatar mata da cewa shi ne, ido cikin ido suka kalli juna dukansu a lokaci ɗaya gabansu ya faɗi ras! ras!, Cikin sauri ya saketa duk da bai tabbatar da cewa ita ɗin ce ko ba ita ba, itama kanta ta aro wata jarumta ta yi kamar ma bata taɓa ganinshi ba ta duƙa ta ɗauki agogon da faɗi ta fara taku a hankali cikin wani salon da ita kanta batasan ta iya irinshi ba ta fice, Safwan ya bi bayanta da kallo har ta ɓacewa ganinshi amman bai daina kallon ƙofar ba, cikin wani hargitsatstsen yanayi ya ja jakarshi ya nufi ɗakin Hajiya Mama, don gidan shiru saboda mutane da yawa sun tafi partyn.
Dije kam har ta shiga motar suka tafi ƙirjinta bai daina bugawa ba, saboda ganin bazatan da ta yi masa duk da daman cen tasan da zuwan nashi a ranar.
Sun gudanar da bikinsu masha ALLAH ansha rawa Amarya da Angonta sun gwangwaje tare da abokan ta da yan uwa da abokan arziƙi, Dije ma ba'a barta a baya baya bayan photunan da aka sha kala kala kowace da kalar nata salo ba ƙarya.
Bayan an watse taron ne wani ya biyo Dije har gida saboda tun a cen wajen ta ɗauki hankalinshi sosai, yana biye da komi nata har suka dawo gidan, suna ƙoƙarin kwasar wasu kaya ne a bayan boot ya yi mata sallama.
Ba shiri ta ɗago tana ƙare masa kallo sama da ƙasa sannan ta amsa masa sallamar a yangance, cike da jin daɗi ya yi wani tsadadden murmushi yace
"Khadijah ko?" tayi saurin zaro ido waje tace
"Ni? ko dai wata Khadijar?"
Matashin saurayin yace, "ke dai tawa khadijar"
Dije ta zaro Ido waje ta kinkimi kayan da zata ɗauka ta yi cikin gida don ita sam ma bata kula da Safwan da ke zaune harabar gidan yana chat da Zee ba, Amman shi tun daga nesa ya ƙura mata kallo har ta shige, sai dai kuma ganin wannan matashin saurayin ya bita da kallo ne yasa ya yi saurin miƙewa ya soka wayar aljihu ya nufo wurinshi, wanda kafin ma ya isa sai ga Dije da Fiddo sun zo kwasar wasu kayan, Saurayin ya sake nufar Dijen yana faɗin
"Haba Khadijah ki tsaya ki saurareni mana, WALLAHi takanas wannan zuwan da na yi a nan donki kawai na zo"
Ganin Safwan a wurin yasa ta yi saurin washe baki tace, "ALLAH sarki ka yi haƙuri daman na je ne in ajiye kayan in dawo, to ya kake dafatar ka zo lafiya?"
Cike da mamaki Safwan da Fiddo suka bita da kallo, Fiddo ta yi saurin faɗin
"Malam ina zaka kai zunubin fira da matar aure?"
Saurayin ya zaro ido waje zai yi magana Dije ta yi saurin faɗin,
"No! no! Share da ita wasa ce take yi maka dubanni da kyau, kai kanka ai kasan banyi kama da matan aure ba ko?"
Fiddo zata sake yin magana Safwan ya yi mata alamu da ta yi shiru, dole tayi gum ba shiri saboda bala'in tsoronshi da take yi , Dan Saurayin kam ya bi Dije da wani shu'umin kallo sama da ƙasa ita ko sai wani girgizar jiki take yi tana fesa masa wani murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarshi, sai dai ɗagowar da zai yi a ƙoƙarinshi na son mayar mata da martanin kallonta Karaf yaji saukar naushi a fuskarshi, kafin ka ce me ya fara lallasuwa a hannun Malam Safwan, don kuwa sai da ya ci nasarar haɗa masa jini da