Showing 75001 words to 78000 words out of 136985 words
wannan da kike gani ba kowa ba ce face ƙaskantacciyar ƴar aikinmu, dubarta da kyau ki gani bagidajiya ce usuli ƴar ƙauyen ƙayau, ta nace akan dole sai yaya Safwan ya aureta bayan kuma shi ko kaɗan baya sonta"
Ta janyo hannun Zee ta yi wa Dije wani kallo ta buga mata ƙaton tsaki tace, " mtsss! Mayya kawai"
Zee tana yi tana waigenshi zuciyarta cike da ƙunar baƙin cikin da Dije ta sakar mata, sai wassafa yanda zata shaƙe Dijen take yi a ranta har sai ta ɗauke numfashi sannan ta saketa, har suka isa ɗakin Hajiyar suka zauna bata san ma sun je ba, sai da ta ji Fiddo tana gabatar da ita ga wata Auntynsu sannan ta dawo hankalinta ta fara sunne kai tana gayar da su.
Safwan kam shigewar su Zee ciki yayi dai dai da dawowar natsuwarshi, ya kai kallonshi ga inda yake tsammanin ganin Dijen sai dai kuma wayam bata nan, ya wara idanuwanshi a masifance domin ya hango ta ina zai ganta ya sauke fushinshi akanta, sai dai kuma bata ba dalilinta a falon duka, a harzuƙe ya yi wurin Surayya yace
"Ina magen yarinyar cen ta tafi???"
Sury cikin firgici tace
"WALLAHi Ni ma bansan inda ta je ba yayanmu"
Safwan ya kaiwa iska duka sannan ya bar wajen ya sake dawowa ya ce da ita, "to ki yi gaggawar dubo man ita yanzun nan idan ba haka ba WALLAHi yau daga ke har ita sai kun san dani kuke zance"
Cikin rawar jiki Surry ta miƙe ta yi ɗakinsu domin ta gani Dijen tana cen ko kuwa, sai dai ta duba ko'ina Dijen bata gidan take ta sanar da shi yana huci ya yi wurin Hajiya, sai dai tuno ɗakin da mutane yasa ya ja ribas dole tare da furzo iska mai zafi a bakinshi yana wani bubbuga kanshi alamun ta saka shi a tension da yawa.
Yana nan tsaye sai ga Fiddo ta fito tare da su Zee tana ganinshi ta yi saurin zuwa wurinshi tace, "big bros WALLAHi yau idan ka kama yarinyar nan ka ci ubanta da kyau da kyau, don ni kaina yau sai na tayaka mun ci uban shegiya......"
Kallon da Safwan ɗin ya yi mata ne yasa ta yi saurin cewa da su Zee "Aunty ku zo mu je ku ci abincin kafin mu je wajen da za'a yi event ɗin"
Zee ta yatsina fuska ta kalli Safwan tace,
"Barshi kawai Ƙanwata ni yanzu ma zamu koma gida"
Safwan ya yi saurin zaro ido cikin wani sabon tashin hankali ya marairece fuska yace, "Sorry Unique ke ma kinsan ke ce dream ɗina safe da rana, ke ce wadda nike mafalkin aure a kowane lokaci, wannan yarinyar ba kowa ba ce a wurinmu face ƴar aiki kamar yanda kika ji Fiddo ta sanar da ke tun farko"
Zee ta yi masa wani arnen kallo mai cike da ma'anoni sannan ta nufi hanyar fita ƙawarta ta riƙo hannunta, cikin wayancewa ta ce da Fiddo mu je ki kaimu wajen da za'a yi bikin, Fiddo cike da damuwa ta ce "to ku yi haƙuri ku ci abincin mana kunga kun kwaso tafiya ga shi ko ruwa ma baku sha ba"
Ƙawarta Ruma ta yi murmushi ta ce "ok to mu je mu ɗin ai sai mu yi sauri mu kammala"
Fiddo cike da jin daɗi ta kai su ɗakinsu da ta riga da ta shirya shi tsaf saboda tarbonsu, ta nuna masu toilet sannan ta fito zuwa kwaso masu kayan abincin, Safwan da ke tsaye jiki ba kuzari damuwa fal ranshi yace
"Zo nan ki ji"
Fiddo ta ƙaraso wajenshi cikin sassauta murya yace,. "Don Allah ki yi duk yanda zaki yi ki nuna mata cewa ba wani abu tsakaninmu da yarinyar cen, don WALLAHi idan bata amince ba yau sai na ci uban yarinyar nan a gidan nan"
Hajiya da ke bayansu cikin shirinta na fita zuwa bikin ta ce,
"Wa za'a ci wa Uba kuma a gidan nan yau?"
Safwan ya gyara tsayuwarshi tare da sosai kai yace,
"Wata ce Hajiyarmu"
Hajiya ta ce "ALLAH ya taimakeka to tunda ba Khadijah kake nufi ba don WALLAHi idan har da ita kake ka kuskura naji ka daketa akan wata sai na baka mamaki"
Tana ƙare faɗar haka ta sa kai ta tafiyarta, Safwan da Fiddo suka bita da kallo har ta wuce, sannan ya nufi ɗakinsu Fiddon ranshi a matuƙar ɓace saboda jin haushin taka masa burkin da Hajiya Mama take yi akan Dije.
Yana shiga ya taradda Zee dunƙule tana kuka ƙawarta tana lallashinta tana bata baki, tana ganinshi ta yi saurin zuwa ta cakumo rigarshi cikin kuka tace
"Daman abunda ka shirya man kenan Shiyasa ka matsa akan in zo bikin ƙanwarka??, To na zo na gani tabbas kana da matar da zaka aura ƴar Uwarka ALLAH ya baku zaman lafiya Ni na haƙura na bar mata ALLAH ya bani dangana, amman ka sani sonka shine ajalina idan ka ji saƙon mutuwa to shine sila"
Safwan ya dafe goshinshi cike da wani takaici da ruɗewa yace, "ki yi haƙuri my fiance na gaya maki yar aikin gidan nan ce, tukunna ma ina wadda na taɓa sanar da ke an so a haɗamu aure da ita to ai itace wannan"
Ta yi masa wani kallo mai cike da tuhuma tace, "eh kam lalle yar uwar taku ce yanzu ta zama yar aikin naku ko? Hmm! To bari ka ji bazan ja abun da tsauri ba na haƙura na bar mata kai kawai"
Tana ƙare faɗar maganar ta fisgo gyalenta da ƙarfi zata fita ya yi saurin riƙo hannunta cikin damuwa yace "plsss Zee ki fahimceni mana, wallahil'azim a shirye nike da in aureki a kowane lokaci, ki bani dama domin in tabbatar maki da hakan idan kin aminta yanzu ma kafin mu koma ayi auren kawai mu tafi abun mu cen mu zauna idan kinsan hakan zai kwantar maki da hankali"
Zee ta kalleshi zuciyarta cike da jin daɗi tace, "promise?"..
Yace "promise"
Sannan ta rufe fuskarta tana dariyar jin daɗi, Safwan ma ba shiri ya mayar mata da martanin dariyarta zuciyarshi fess saboda ganin ya tufke abunda Dije ta warware masa.
Fiddo ta shigo ta ajiye kayan abincin tana wasar bakin jin daɗin ganin Zee ta washe tace, "masha ALLAH Auntynmu har naji daɗi da kika saki fuskarki, yayanmu ba shi da wata matar da zai aura a yanzu face ke, don wannan munafukar yarinyar da kika gani itace take sonshi sai dai shi ko kaɗan ba ya sonta, ta yi masa haka ne a gabanki don kawai ta haɗaku faɗa, daman gurinta bai wuce ki yi zuciya ki bar mata big bros, to don ALLAh Auntynmu ki bata kunya kada ki bari ta rabaki da yayanmu kinji"
Zee ta washe baki tace, "na gode ƙanwata ina jin daɗin yanda kike sona ke da yayanki, kuma insha ALLAHu bazan taɓa nuna damuwata akan wani abu da zata sake yi ba, matuƙar ba my soul ne ya nuna kulawarshi akanta ba, to agaskiya anan kam bazan taɓa jura ba don Ina kishin inga wata mace ta raɓeshi bayan ni WALLAHi"
Fiddo ta fara zuba masu abincin tace, ",kwantar da hankalinki don ba ma zai kulatan ba saboda daman cen itace kawai da baƙin nacinta"
Haka dai Fiddo ta yi ta basu kulawa tana wanke zuciyar Zee daga tsatsar da Dije ta sakawa ruhinta, har suka ƙare komi cikin kulawar Fiddo sannan suka ajiye motarta da suka zo da ita Safwan ya ɗaukesu suka tafi bikin.
Shigarsu hall ɗin ke da wuya Safwan ya hango Dije tsakiyar fili tana ta cashewa abunta, zuciyarshi a take ta zo wuya saboda ganin yanda ƙaton hall ɗin ya cika ya batse tsakanin maza da mata.
Fiddo ta wuce da su Zee tana ta gabatar da ita ga ƴan'uwa da abokan arziƙi, sai dai abinda bata sani ba mutanen da yawa wadañda basu san da zancen auren ba sunyi mamakin auren da Safwan ɗin zai sake yi, bayan ga Dije dake hannun Hajiya kuma itama tana amsa sunan Matarshi.
Safwan kam cikin dubara ya fice ya sa wata ƙawar Surayya ta kira masa Dijen, sai dai cikin rashin Sa'a Dijen ta ƙi biyo ƙawar Surryn saboda gargaɗin da Hajiya ta yi mata akan kada ta biyewa Safwan ɗin ya daketa a banza, ƙiri ƙiri tace da ƙawar Surryn Hajiya tace kada ta fita ko'ina, dole haka ƙawar taje ta sanar da shi, aiko ya ƙara hawa akan fushin da Dijen ta saka shi, ya yi ƙwafa ya koma hall ɗin
Sai dai rawar da ya ga tana ta cisga ne yasa shi dafe goshinshi ba shiri, ranshi a ɓace ya kasa haƙuri ya nufi wurinta gadan gadan da nufin kai mata wani bahagon mari, tana hangoshi ta yi saurin ficewa filin ta nufi wurin Hajiyar tana haki, ya wayance ya fara zubawa Surry likin kuɗi daga nan ƴan'uwa suka cika filin suna yi masa liƙi yana yi masu shi ma, ta ko'ina sai zubo kuɗi ake yi har sai da mc ya bada umurnin kowa ya koma ya zauna abar Amarya kawai a tsakar fili.
Ganin hakan ya baiwa Zee damar fitowa ita da ƙawarta suka fara watsawa Surry farfaru bugun Abuja, Hajiya Mama ta ciro kuɗi a jakarta ta miƙa wa Dije tace itama ta je ta watsa, cikin jin daɗi ta karɓa ta isa wurin ta fara mannawa Surryn kuɗin sannan ta dawo tana mannawa Zee cikin murya ƙasa ƙasa tace
"Da kin daina wannan zaƙewa tunda dai har yanzu baki riga da kin shigo familyn ba, amman kuma ba komi a hakan ma muna godiya, sai dai kuma ga shawara ki adana sauran kuɗinki don rabawa malamai su ji daɗin yi maki addu'ar ƙwato zuciyar wanda ake yi dominshi"
Saboda salon yaudara irin na Dije tana liƙa mata kuɗin fuskarta a sake take maganar, wanda bai ji ba ba zai taɓa fahimtar cewa wai wata baƙar magana ce take faɗa mata ba, don shi kanshi Safwan ɗin ya yi mamakin ganin Dijen tana wasar baki ga Zee, uwa uba ma har da su watsa kuɗi don a ɗauka cewa bata san zafin kishi ba.
Har aka watse taron Zee maganganun Dije suna yawo cikin kwanyar kanta, sai dai idan ta tuno da zancen aurensu da Safwan ɗin da ya zo mata da shi sai ta ji wani sassafci a ranta, duk da tasan cewa itama za'a sha fama da ita kafin a janye zancen auren wani da ke kanta.
Dije kam har aka shiga bacci bata bari sun haɗu da Safwan ba, saboda ma tunda ya fita raka Zee gidan ƴan'uwasu da suka sauka a cen, bai dawo gidan ba har sai da dare ya tsala sannan ya dawo ya shige zuciyarshi cike da jin daɗin shima ya kusa angwancewa, sai dai wani sashe na zuciyarshi yana ingizashi akan ya koyawa Dije hankali kafin ya bar garin, amman yana jin tsoron abunda zai janyowa kanshi wajen Hajiya Mama.
Ranar juma'a ranar ce ta kama ta ɗaurin aure kuma ayi walima, haka ranar ce kuma Malam Lawi ya diro garin tare da wani abokinsu da ke cen Gomben, saboda gayyatar da Safwan ɗin ya yi masu, cike da jin daɗin gani junansu kowa yake ta ɗokin ɗan'uwanshi, sai firar yaushe gamo ta ɓarke a tsakaninsu ihunsu kawai ke tashi a ƙofar gidan bayan sun dawo ɗaurin auren.
Kasancewar a harabar filin gidan ne za'a yi walima shiyasa aka kafa rumfuna manya manya aka ƙawataa wurin sosai.
Dije ta fito zata je cen wajen ne idonta ya kai kan malam Lawi, cikin sauri ta zaro ido cike da jin daɗin ganinshi ta nufi wajensu fuskarta a washe take faɗin
"Rai kan ga rai Malam? ashe ina da rabon sake ganinka a duniya?"
Lawi cike da mamaki ya bi ta da kallo tun daga sama har ƙasa saboda ganin yanda gaba ɗaya ta sauya kamannu kamar ba Dijen da ya sani ba, wadda ko a mafalki da siffarta ta ƙauye yake hangota, sai dai kasancewar yasan cewa da da yanzu ba ɗaya ba ne, saboda yanzu igiyoyin aure sun yi masa shamaki da ita, auren ma na Abokinshi Safwan, shiyasa ya wani basar ba tare da wani sakin jiki ba ya ce
"Amarya kinsha ƙamshi ya garin? da fatar kina lafiya?"
Dije ta washe baki cike da jin nauyinshi tace, "Malam saukar yaushe haka babu sanarwa?"
Lawi ya kalli Safwan ya ga yanda gaba ɗaya yanayinshi ya canza ya yi gajeren murmushi yace, "wannan kuma laifin angonki ne tunda shine bai sanar da ke ba"
Dije ta kai kallonta gareshi ta yi ɗan murmushin yaƙe sannan ta ce
"Bari in je in dawo Malam ai da nasan kana nan da tun ɗazu ka sha tarbata"
Lawi ya bita da kallo yana wani murmushi cen kuma me ya tuna ya yi saurin kawar da kanshi a gefe yana wassafa siffarta cikin bular doguwar rigar da ke jikinta, ta yi mata kyau ɗagwasgwas ta zauna a jikinta, ga ɗankwalin rigar da ta yafo gaban kanta gaba ɗaya a buɗe yake har ana hango kwantaccen gashin kanta da yasha gyara ya kwana, ga sajen gashin ma ya kwanta luf luf a gefe da gefen fuskarta, girarta ma cike tafi da gashi gazar gazar da ta ƙara Ƙawata mata fuskar, duk da bata yi wata doguwar kwalliya ba amman yanayin tsarin shigarta ta burgeta sosai.
Daga shi har Safwan sun faɗa tunanin da su kaɗai suka san me suke tunawa, tunaninsu ya katse ne lokacin da Dijen ta dawo tana murmushi tace
"Malam zo mu je falon baƙi ka ci abinci ko?"
Abokinsu da suka zo tare da Lawin ya kalli Dije cikin murmushi yace, "Au Wai abun ƴar wariya ce daman?"
Dije ta waigo tana dariya tace, "yi haƙuri idona ne suka rufe ruf WALLAHi a duk wurin bana hangen kowa sai malamina kawai"
Ba Safwan da maganar ta daka a ƙirji ba har shi kanshi Lawin ba shiri ya waigo, saboda maganarta ba ƙaramin dukan zuciyarshi ta yi ba.
To fa wata sabuwa 😝
Akafta😅
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*My fans bakina ba zai iya misalta farin cikin da kuka sakani ba, naso in zayyano sunayenku to amman yawanku ya kai ba zan iya lissafoku duka ba, amman na gode 🙏🏻na gode🙏🏻 sosai Alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke💃🏻ku daɗe ku yi ƙarko mutanena👍🏻*
*Lamba ta 47*
A harzuƙe ya taso da nufin kai mata duka sai ga motarsu Zee ta kunno kai harabar gidan, cikin sauri ya nufi motar yana washe baki saboda jin daɗin ganinta, Dije ta kai kallonta gareta take wani ɓacin rai ya ziyartota, amman a hakan ta kalli Lawi ta yi wani murumushi tace
"Zo mu je Malam"
Lawi ya yi shiru sannan yace da abokin nasu mai suna Kamal yace, "zo mu je Abokina don wannan tafiyar dole ne a buƙaci rakiyarka"
Kamal kam sai kallon motarsu Zee yake yi mamaki fal ranshi yace da Lawi, "Abokina baka gane wannan yarinyar ba ne?"
Lawi ya kai kallonshi ga motar inda Safwan da Zee suke tsaye jikin motar suna fira kowanensu cikin farin cikin ganin ɗan'uwanshi, Lawi yace
"Kai ne idon gari Abokina ban gane su ba gaskiya"
Kamal ya ce, "budurwar Aminu ce fa wadda ya susuce kanta kullum yana dakon ta kammala karatun da take yi ayi auren amman Mahaifinta sai ja masa rai yake yi, ko kallon zumuncin da ke tsakaninsu ba ya yi, ya fifita son zuciyar ƴarshi akan na kowa"
Lawi yace, "Eh kam sai yanzu na tuna amman kasan ni daman bansan yarinyar ba ai labarinta kawai nake ji"
Dije tana tsaye tana saurarensu ba tare da ta ma nuna tasan wani abu da ke faruwa ba, cikin dariyar yaƙe tace
"Ai kam dai yanzu sai dai Aminu ya yi haƙuri saboda ita ce matar da Malam Safwan zai aura tare suke karatu a cen ƙasar wajen"
Daga Lawi har Kamal suka zaro ido cike da mamakin jin wannan zance a bakin Dije, haka kawai Lawi ya tsinci kanshi da cewa
"To ke har kin amince kenan?"
Dije ta yi shiru tana yar dariya mai cike da takaicin da ke cin zuciyarta tace, "ku zo mu je mu barshi ya ji daɗin firar don kada mu takurashi"
Suka wuce Safwan da hankalinshi gaba ɗaya yana kansu saboda tsabar kishin da ke cin zuciyarshi, ya bisu da kallo ranshi a matuƙar ɓace yace da Zee
"Zo mu shiga ciki ku gaisa da Hajiya"
Zee ta bishi da kallon mamakin me ke damunshi tace, "my man what's wrong with you?? Ko na yi maka wani abu ne?"
Safwan cike da ƙunar rai ya shafo kanshi ya ce
"No! no! kada kiji komi mu je kawai"
Yayi gaba Zee ta bishi da kallo ƙawarta ta riƙo hannunta suka shiga cikin gidan, suna shiga suka yi kiciɓis da Fiddo ya ce da ita ta kaisu wajen Hajiyar idan sun gaisa abasu muhalli a wajen walimar, sannan ya barosu ya nufi ɗakin baƙin da zuciyarshi take ta azalzalarsa akan ya je ya ga wace irin wainar ce ake toyawa, ai kuwa sai ko ya taradda Dijen ta gama zuzzuba masu abincin tana miƙawa Lawi lemun da ta zuba masa a cup, daga ita har shi murmushi ne kwance a kan fuskarsu, idonshi a rufe yana zuwa bai wata wata ba ya fella mata wani wahalallen mari har sai da ta saki cup ɗin saboda tsabar tsoronshi da kuma azabar da ta ziyarceta, cikin wani masifar ƙarfi ya fisgo hannunta suka fice Kamal da Lawi suka bisu da kallo, cikin tsananin ɓacin rai Lawi ya dafe kanshi zuciyarshi sai tafasa take yi saboda zafin marin da Safwan ya yiwa Dije ya ji shi har cikin ranshi.
Kamal ya kalli Lawi yace, "wai wannan guy ɗin mi ke damun ƙwaƙwalwarshi ne?, Ko da yake banga laifinshi ba fa don ko ni nan ina da irin wannan mata WALLAHi dole ne na yi kishinta, amman kuma yasan yana sonta zai tsirowa kanshi auren Zee da rana tsaka?"
Lawi ya yi shiru saboda ɓacin ran da yake ji yasa ya ma kasa furta wata kalma a bakinshi, sai shafa ɗan ƙaramin gemunshi da yake yi yana nazari.
Safwan kam bai zame ko'ina ba sai ɗakinshi da Dijen, yana shiga ya saka key tare da