Showing 78001 words to 81000 words out of 136985 words

Chapter 27 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

2120

wurgar da ita a tsakiyar falon yana ƙare mata kallo yana nazarin ma wane hukunci zai yanke mata don ya ji sauƙin abunda ke azalzalar zuciyarshi, cikin takaici ya cakumo gashinta da ƙarfi ya miƙar da ita tsaye, cikin jin zafin da ke ratsa kanta tace

"Don Allah ka yi haƙuri WALLAHi bazan sake ba"

Safwan ya turata baya da ƙarfi ta yi taga taga zata faɗi kuma ya yi saurin riƙota cikin fushi yace

"Kasheni kike so ki yi ne ko kuwa?, Me na yi maki Kika zaɓi ki tozartani cikin mutane?, To WALLAHi tunda har ke baki san darajar aure ba zaki janyo in fiddaki Makarantar da kike kwaɗayi gaba ɗaya, don na fahimci duk wannan rawar kan naki don kin ga an baki damar yin karatun ne, to daga yanzu ba zaki sake zuwa wata makaranta ba da sunan karatu idan ba islamiya, ita ɗin ma anan gidan za'a zo a dinga koyar dake saboda kawai ki san muhimmancin auren da ke kanki"

Dije ta kalleshi ido cikin ido tace,. "Wane aure naji kana faɗa ne? Auren da kai da bakinka ka ce da ni kada in yarda cewa wani yasan kai ne mijina? To Ni yanzu WALLAHi na gaji da wannan wahalallen auren, tunda mai sona tsakani da ALLAH ya bayyana ka barni kawai in auri wanda ya soni tun kafin ka aureni, don ni shi Nike so........."

Wani marin da ya kaiwa bakinta ne yasa ta yi saurin dafe bakinta tana zubar ƙwallah tace, "ko zaka kasheni ba zan fasa faɗar cewa ina son Malam Lawi ba tunda har kai bakasan darajata ba, shi nake so kuma shi nake da gurin zaman aure da shi idan ba haka ba kuma WALLAHi zan koma garinmu gaba ɗaya na haƙura da makarantar bana so"

Ta ƙare faɗar maganar cikin kuka ta durƙushe tana gunjin i kukanta gwanin ban tausayi, cikin wani sabon tashin hankali ya yi durƙuso gabanta har ya so ya shafo kanta, me ya tuna kuma ya yi saurin miƙewa tsaye yace

"Da ace zai amince ya karɓekin da nafi kowa farin ciki, to amman yanzu haka ko da kuɗi aka bashi ke bazai taɓa karɓar ki ba, ko ni nan don Allah ya ƙaddaro da zaki zama matata da ke kinsan baki kai matsayin wadda zan iya rayuwar aure da ita ba, nasan ba abinda ke damun zuciyarki a yanzu face kishi ko? to ki kwantar da hankalinki da anyi aurenmu da Matata Zee zamu bar maki ƙasar gaba ɗaya sai ki ji daɗin karatun naki"

Dije ta miƙe tsaye hawaye shaɓe shaɓe akan fuskarta tace

"Ai Ni ma kasan ba roƙarka na yi nace sai ka aureni dole ba, saboda haka ka barni da shi ka ga idan har bai aurenin ba.."
.
Ya kaiwa bakinta duka yace, "WALLAHi na ji kin sake zancen wani da aurena akanki sai kin gano baki da wayo, wai me kike taƙama da shi ne ba budurci ba? to zan karɓe shi yanzun nan inga ta yiwa mutane wata firiritar tsiya"

Ya fisgota da ƙarfi ta faɗa jikinshi ta fara tirjiya amman hakan bai hanashi cire doguwar rigar da ke jikinta ba, surar jikinta tasa ya ƙara ɗimaucewa a HAUKACE ya fara yamutsata son ranshi, Dije ta na ƙoƙarin kare kanta wajen kai masa duka shi ko yana cen duniyar tsimuwa da muguwar guguwar sha'awarta,don kuwa gaba ɗaya ya susuce sai wasa yake yi da jikinta ta ko'ina yana sauke wani nishin mai bayyana tsantsar kiɗimewarshi akanta, ganin da gaske yake yi zai ci amanarta ta dinga rarumo abubuwa tana kai masa duka da shi, ya yi nasarar rabata da komi na jikinta sannan ya wurgata kan gadonshi, Dije ta firgice iya firgici ta fara ihun neman taimako amman bai ji kunyar rufe bakinshi da nata ba cikin mayen bala'in wutar sha'awarta da ke fisgarshi, cikin dubara ya fara aika mata saƙon da ya fara cin galabarta, ganin haka yasa ya dinga yamutsata iya son ranshi yana wani gurnani tamkar wani ƙaton rago.

Dije ta kasa jurewa ta firgice masa da kalar tata haukar, cikin nasara ta kai hannunta ga laptop ɗinshi dake gefen gadon ta ɗaga ta kwaɗa masa ita a kai, ba shiri ya saketa dafe da kanshi yana faɗin

"La la la ni zaki yi wa rotse?"

Dije ta sauko jikinta yana rawa ta mayar da doguwar rigarta ta buɗe ɗakin ta fice aguje, Safwan ya bita da kallon mugunta yana dariya a ranshi yace

"Komi wayon Amarya....."

Da ƙyar ya samu ya yi control ɗin kanshi ta hanyar kora kwayuj magungunanshi da ruwa sannan ya dinga sakarwa kanshi ruwa har da ya ji zuciyarshi ta yi sassauci sosai akan damuwar da take ciki, sannan ya yi wanka a gurguje ya fito ya nufi inda su Lawi, don lokacin ma har an fara walimar sautin wa'azin malamar da ke yi wa Amarya huɗuba duk ya karaɗe gidan.

Yanayin da ya taradda Lawin ne yasashi saurin washe baki yace, "Abokina ya dai ko har ka fara kewar gida ne?"

Lawi ya yi masa wani kallo sannan ya gyara zamanshi yace, "banji daɗin dukan khadija da ka yi ba gaskiya, yakamata ka fahimci cewa mata suna da wata darajar da duk namijin kirki ba zai taɓa iya ɗaya hannu ya dakesu ba, ka tuna kar garin nan bata da kowa sai kai shin kasan ba zaka riƙe ƴar mutane amana ba me yasa ka aurota??"

Baki sake Safwan yake kallon Lawin cikin mamakin titsiyen da yake son yi masa yace "ka ga malam wannan kuma ba abinda ya shafe ka bane, Khadija Matata ce ina da ikon da zan yi mata koma mine don haka don ALLAH ka daina saka man ido akan duk wani abu da aka ga nayi"

Lawi ya sauke ajiyar zuciya yace, "idan kasan ba zaka riƙe masu ƴa tsakani da ALLAH to ka mayar da ita gaban iyayenta yafi da ka kawota nan ka ajiye kana dukanta, don WALLAHi matuƙar baka daina ba da kaina zan je garinsu in sanarwa iyayenta irin abinda kake yi mata, sannan wannan auren da naji wai zaka sake yi to idan baka ajiye wannan shirme ba tabbas Ni kuma a shirye nike karɓar Khadija a hannunka ko ta halin ƙaƙa"





To fa tsugunne bata ƙare ba kenan🙀😢shin Lawi ko Safwan ina team Dije ku fito ku afafata🤪





Akafta😍






D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Ina yabawa ƙoƙarinku COMMENTERS😉*



*Lamba ta 48*



Safwan ya bishi da wani malalacin kallo yace, "idan har ka ga ka sami damar auren khadija a dai nan wannan duniyar da muke ciki to ka ɗauka cewa bana numfashi ne a doron duniyar, sai ka jira idan har na mutun sai ka yi murna ka garzayo ka auretan, amman yanzu kam WALLAHi bazan taɓa baka damar mallakar macen da na fi so fiye da kowace mace da zan aura ba duniya, kar ka ɗauka cewa wai ka fini sonta to WALLAHi kashi ɗaya cikin goman da nake mata to ko rabi ba zaka kwasa ba, amman bazan taɓa ɗaga mata ƙafa ba matuƙar ta yi man abunda bai gamsheni ba, saboda haka ka kawar da kanka akan matata ka yi gaggawar fito da taka matar don wannan kam ta yi maka nisa, saboda na fahimci cewa idan ban fito na yi maka gwari gwari ba to zaka janyo man abunda zai saka jinina ya hawa, yanzu ga shi daga zuwanka ka firgice mani mata na kasa gano kanta"

Ya kalli Kamal yace, "Aboki ka yi masa wa'azi don ya gano kallon matar aure ma haramun ne balle ya tsaya mayar da yawu da ita yana jin daɗin zancenta, to ka zama sheda WALLAHi ya sake tsaf zan yi masa ALLAH ya isa akan matata"

Kamal yana dariya yace, "banga laifinka ba abokina saboda haka kai Malam ka tsaya iya matsayinka na malam kawai, don kaji a gabanka mijin ɗalibar taka ya kawo ƙararka"

Lawi da ke saurarensu zuciyarshi fess da jin kalaman Safwan, ba shiri wata dariya ta suɓuce masa ya kalli Safwan ɗin yace

"To kai mijin ɗalibata ka ji tsoron Allah ka riƙe man ita amana kada ka bari ɗalibata ta yi kuka matuƙar kana son inci gaba da koya mata dabarun biyayya gareka"

Safwan ya maka masa wata jar harara yace, "kar ma kasa ranka zan bari ka sake ganinta, don ba zaka sake janyo man kwaɓata yin ruwa ba"

Lawi yana dariya yace

"Kwantar da hankalinka nima na kusa angwancewa yanzu haka saura wata biyu masu zuwa insha ALLAHu"

Safwan ya yi saurin washe baki yace "ko kai fa? Ai da ka taimaki kanka gaskiya, zaman tuzururantaka ai ba daɗi ne da shi ba, ka ga ni naji daɗin daushen farko har wani sabon lambun nike son in ƙara ninƙaya a ciki"

Kamal ya yi saurin faɗin, "wai da gaske ne kai zaka auri Zee" Safwan ya washe baki yace

"Insha ALLAHu kwanan nan ma kuwa don bazan koma school ba har sai an shafa fatiha in kwashi matata mu bar maku ƙasarku"

Lawi ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya ce, "Abokina gaskiya zan sanar da kai wannan yarinyar da kake gani yanzu haka da mijinta da za'a haɗasu aure a gida, me zai hana ka riƙe matarka ka barta ta je ta auri zaɓin gidansu? WALLAHi ina jin tsoron haƙƙinshi ya kamaku kai da ita, don abinda ka yi mani ba kowa ne yake da sauƙin zuciyar yafiya ba, ka janye jikinka ka barta ta yiwa iyayenta biyayya ko don dakon jiranta shekara da shekaru da Aminu ya yi saboda kawai yana son aureta"

Safwan ya yi saurin faɗin, "Eh nasan da zancen amman tunda ita bata sonshi ai sai a barta ta auri wanda take so"

Lawi yace "ka dai sowa ɗan uwanka abunda kake sowa kanka yafi abokina, hadisi ne ingantacce kuma ina da tabbacin kasan da shi, saboda haka Ni ina baka shawara ne a matsayina na Abokinka idan kaji ka taimaki kanka, idan kuma ka rufe ido ka ka kasa hango gaskiya to shikenan Ni dai na fita haƙƙinka"

Safwan ya yi wata dariyar gefen baki yace, "idan ka ga ban auri Zee ba to sai in itace da kanta ta ce ta fasa aurena, saboda na riga da na yi mata alƙawari akan zan auretan duk runtsi"

Kamal yace "ALLAH sarki Aminu WALLAHi na tausaya masa"

Safwan ya ɗaga kafaɗa yace, "ka ji da shi ni dai ba gudu ba ja da baya saboda nasan tana sona"

Haka suka yi ta fafatawa har aka gama walimar Safwan ya fito don ya yi sallama da su Zee, Kamal ya biyoshi saboda yana son ta ganshi don tasan yasan komi, aiko sai gata tsaye da Safwan ɗin suna sallama Fiddo ta riƙo masu kayan walimarsu da aka basu ta saka masu a mota, Zee tana yi wa Fiddo godiya suka yi ido biyu da Kamal, ta yi saurin riƙo ƙawarta tace

"Ruma kin ga Mituminki fa"

Ruma ta washe baki tace "laa! Kamal Rai kan ga rai?"

Kamar yana ɗan murmushin yace

"Rumasa'u kwana da yawa"

Tace "sai Alkhairi" ta ƙara da cewa "kai ma ka zo bikin kenan"

Yana dariya yace "Eh gamu munzo ta ya su Zee murna ALLAH ya sanya alkhairi"

Zee ta yi masa wani kallon tambaya sannan tace "Ameen" saboda mamakin ya aka yi yasan tsakaninta da Safwan ɗin, shi ko don ya tabbatar mata da yasan komi yace,.

"Ashe haka aka yi kenan Abokina ya yi wa wani Abokina ƙwace?"

Zee ta yi saurin kallon Safwan tace, "Abokin yaya Aminu ne fa"

Safwan ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinshi yace, "ALLAH ya baiwa mai rabo sa'a idan Abokin nashi ne mijin ai sai ku daidaita kawai"

Zee ta zaro ido tare da ɓata fuska ta ce

"Haka ma zaka ce?"

Yace "eh to ai addu'a ce nayi ko?"

Ta turo baki tace, "to in fa Kuma addu'ar ta faɗa kanshi fa?"

Ya yi saurin faɗin "sai in ɗauki na annabawa ALLAH ya bani wata madadinki"

Kamal ya yi saurin faɗin, "ALLAH ai ya baka kuma sai dai in bazaka gode wa irin baiwar da ya yi maka ba"

Zee ta yi saurin kallonshi tace, "wa ya ba shi ɗin ?"

Kai tsaye kamal yace, " kyakkyawar Matarshi mana ko baki ganta ba"

Zee cikin firgici tace

"Tsaya Kamal don kana taya Aminu kishi kada ka ce zaka ɓata man rai, wace mata ka aura masa bayan ni da zai aura kwanan nan? A gaskiya bani son muguwar fata"

Ta ƙare maganar tana harararshi, Kamal ya yi yar dariya ya kalli Safwan da duk ya diririce alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskarshi yace

"Kai Abokina to ka yi mata bayani da bakinka mana don naga kamar na shiga hurumin da ba nawa ba"

Safwan cike da jin haushinshi yace, "kai da ka yi mani waliccin auren ai sai ka yi mata bayani da bakinka don sai tafi saurin gamsuwa dai dai"

Zee ta washe baki ta ce "ƙyaleshi my cuddle bear nasan kishi ne yake taya Abokinshi bayan ni na riga da na yi masu nisa sai dai haƙuri"

Kamal ya yi mata wani kallo cike da jin haushin irin cin amanar da zata yi wa Abokinshi yace, "ita dai gaskiya idan ta tashi fita tafin hannu ya yi kaɗan da ya kareta, haka duk wanda ya ci amana to ya sani akwai lokacin da ranar sakamako zata ziyartoshi, ni kinga tafiyata fatana kawai ita Uwargidan ALLAH ya bata haƙurin sammakon da za'a yi mata"

Yana ƙare faɗar haka ya wuce abinshi, daga Safwan har ita Zee suka bishi da wani kallo mai ƙumshe da harara, ran Zee a jagule ta kalli Safwan ta ce"

"My hero Wai me yasa a ko'ina sai an samu yan adawa ne?, Ji don ALLAH yanda yake wani zaƙewa sai kace shine Aminun?"

Safwan ranshi a ɓace yace, "shareshi kawai hassada ce zo muje ki yi sallama da Hajiya mu je in raka ku gida tun kafin wannan magulmacin ya ɓata muna tsari"

Ya yi gaba Zee tare da janyo hannun ƙawarta amman sai Ruma ta ce da ita su je kawai ita zata jirasu, suna shigewa Ruma ta yi wurin Kamal zuciyarta cike da son jin gaskiyar abunda yake son sanar da Zee, ta nemi izinin ganinshi na ɗan lokaci suka keɓe gefe, Ruma ta zama serious bayan sun ƙare ɗan barkwancin da suka saba tace

"Kamal don ALLAH ka sanar da ni gaskiyar zance shin da gaske Man ɗin Zee yana da aure?"

Kamal ya yi yar gajeruwar dariya yace, "tunda kince ALLAH to ba wani kwana da zan tsaya yi maki, tabbas Safwan yana da Mata asali ma yanzu haka shekararshi biyu cikin ta uku da aurensu"

Ruma ta zaro ido waje tace, "Kamal kasan dai bamu irin wannan wasar da kai ko?, tsakaninka da ALLAH na roƙeka ka faɗa mani gaskiyar lamarin, saboda WALLAHi Zee ta mato sosai akan wannan guy ɗin idan har ta ji wannan magana nasan ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba"

Kamal ya karkace baki yana dariyar gefe idonshi suka kai ga Surayya da ke ta ɗaukar hotuna da Ƙawayenta ya yafitota da hannu, ta nufoshi tana dariya kasancewar tasanshi sosai saboda tare suka yi karatu da Safwan a garin, asali ma kamar gidan suke dukansu har da Lawi a lokacin da suka yi karatun jami'arsu.

Tana zuwa ta gayar da shi a mutunce bayan sun gaisa ya ce da ita, "Surayya ki yi mata bayanin gaskiya saboda ta ji da kunnuwanta, shin da gaske Safwan yana da aure ko kuwa?"

Surayya ta washe baki tace, "ALLAH sarki ƴar uwa da gaske kuwa Yayanmu yana da aure kuma yana bala'in son Matarshi, haka itama kuma tana sonshi sosai"

Diirim! dum! Shine abunda zuciyar Ruma ta yi saboda maganar ba ƙaramin bugun zuciyarta ta yi ba, nan take ta fara tausayin ƙawarta cikin canzawar yanayinta da ya koma kalar damuwa ta ce

"ALLAH sarki ko zaki iya nuna mani matar in ganta don ALLAH"

Surry tace, "bari in dubota don tun ɗazu ma ban ganta ba"

Surry ta yi cikin gidan zuciyarta cike da fatar ALLAH yasa ma auren ya wargaje kowa ma ya huta, sai dai duk bulayin neman Dijen da ta yi bata ganta ba, dole ta dawo da nufin sanar da ita cewa bata ganta ba, sai ga shi ma ta taradda su duka har da Safwan ɗin suna sallama da juna, saboda Ruma bata nuna komi ba nufinta sai sun je masaukinsu ta sanar wa da ƙawarta gaskiyar zancen.

Cikin tsoro Surry ta yi saurin komawa cikin gidan ta laɓe, har suka fita Gate ɗin gida Safwan ya bi su a baya sannan ta fito tana sauke ajiyar zuciya.

To sai dai abu kamar wasa har dare anata neman Dijen Baffah ammsn ba'a ganta ba, tun ana ɗaukar abun wasa har kowa hankalinshi ya fara tashi don kuwa anyi nemanta ko'ina gidan kaf ba'a ganta ba, Hajiya ta firgice sosai sai kiran Safwan take yi akan ta ji shin yana tare da Dijen ko kuwa, amman bai ɗauka ba saboda bai ma san ta kirashi ba don wayar a silen take, sai bayan ya gama firarshi da Zee ne Suka yi sallama yana kan hanya ya ga tarin miss calls na Hajiyar da su Surry da wasu ƴan uwansu duka, cikin tashin hankali ya dannawa Hajiyar kira sai ko ta yi caraf ta ɗauka, ba tare da ta jira jin abinda zai faɗa ba ta ce

"Ina khadija kuna tare da ita ne?"

Safwan a firgice yace "A'a WALLAHi Ni tun ɗazu rabon da na ganta"

Hajiyar ta yi saurin faɗin ka yi gaggawar nemota duk inda take, saboda an duba kaf gidan nan ba'a ganta ba, kuma jikina yana bani kai ne ka yi mata abunda ya janyo ta bar gidan, WALLAHi ka ji na rantse matuƙar baka nemo man ita ba to ko kada ka kuskura ka tako ƙafarka cikin gidan nan".

Kitt! Ta kashe wayar zuciyarshi cike da tashin hankali ya furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un"

Cikin ruɗewa ya nufi tasha saboda cen zuciyarshi ta hasko masa zata nufa, saboda cewar da ta yi masa bata son karatun ita garinsu zata koma, sai dai kuma duk iya binciken da aka yi tashar babu sunan Khadija Umar a cikin jerin list ɗin mutanen da Motarsu ta tashi ranar a tashar, ya fito a gigice ya nufi wata ƙaramar tashar da ake shiga Mota nan ma ba wani alamun ta je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login