Showing 30001 words to 33000 words out of 136985 words

Chapter 11 - DIJE ƘARANGIYA

09 Apr 2026

2126

magriba yake dawowa, kuma da ya dawo yake yin arwallah ya nufi masallaci sai isha yake dawowa, sannan shigowarshi gidan ke da wuya zai fad'a wanka don ko da zai kammala sauran abubuwan tuni Dije ta yi bacci, shiyasa baya sanin halin damuwar da take yini da shi ganin hakan yasa Inna ta fara yi masa korafi akan sabon sauyin da Dijen ta shiga, cikin tashin hankali ya nufi d'akin Innar inda take ta baccinta tana sauke ajiyar zuciya, cikin tausayi Baffah ya kalli Inna yace

"Gobe idan ALLAH ya kaimu na amince ta koma Makarantarta amman da sharadin bata ba wannan yaron, idan ta amince shikenan don shima zan je in fad'awa Maigari ya ja masa kunne sosai akan 'yata, don kada in zo in saki baki ya yi mani sakiyar da babu ruwa don Yan birnin nan ba kunya ce da su ba"

Yana kare maganar ya juya zai fita cikin damuwa yace,. "Ni dai WALLAHI ALLAH banji dad'in zuwan bak'in nan garinmu ba, haka kawai muna zamanmu lafiya su zo muna da wani tsirfin tsiya"

Inna ta bishi baya cikin sanyin jiki tana k'ara zayyana masa irin kuncin da Dijen ta saka kanta akan rashin zuwanta Makarantar.

Aiko tun Asuba Inna ta yiwa Dije albishir da zuwanta Makaranta, cike da d'oki Dije ta je ta d'ora ruwan zafin wanka ta sullo wankanta tas, ta shirya cikin uniform d'inta da suke cikin rigar filonta da kullum take matashin kai da su, sunsha karin guga fess da su sai wasar Baki take yi ta nufi d'akin Baffah da ke zaune yanata laziminshi da ya zame masa jiki kullum, ta durk'usa har k'asa cikin wani sabon ladabi tace

"Ina kwana baffah"

Ya kalleta cikin jin dad'in ganin yanayinta yace,. "Lafiya Lau Makarantar za'a je ne?"

Dije ta washe baki tace,. "Eh nagode Baffah da ka yafe man WALLAHI baka ji yanda naji ba kwana biyu da bana zuwa, har mafalkin Makarantar nake ta yi"

Baffah ya tashi daga kishingidar da yake ya zauna da kyau yace,. "Idan har kina son in barki kici gaba da zuwa to ki yi man alk'awali ba ki ba sake kula Yaron nan, idan kuma kika kuskura na ji ance an ganki da shi to ko ki sani ba ki ba sake zuwa ko k'ofar Makarantar nan, in kin amince shikenan ki tashi kije idan kuma kinga ba zaki yarda da hakan ba to ki je ki cire tufafin ki yi zamanki gida tunda ba da karatun za'a tambayemu cikin kabari ba"

Dije ta yi saurin fad'in

"Na yi maka alk'awali Baffah in kuma na sab'a ka ce man shegiya"

Baffah ya yi saurin runtse idonshi yace,. "Kinga haukarki ko to kar in sake jin kin Kira kanki da suna shegiya kinji ko??"

Ta d'aga kanta alamun gamsuwa .





Akafta😝




D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*COMMENTERS GA JINJINAR BAN GIRMA👍🏻*


*Lamba ta 20*


Sai da ta yi masa alk'awali sannan Suka yi sallama ta fito ta nufi Makaranta, tana tafe tana wasar baki musamman idan ta tuno watarana ita Likita ce, sai wassafa yanda zata dinga soke Mutane take yi suna ihu, ita kad'ai sai faman murmushi take yi bisa hanya har ta isa makatantar, inda ta taradda Malam Safwan zaune bakin barandar ya duk'e kanshi ya lula zuzzurfan tunani mai zurfi,don har ta kawo wurinshi ta gayar dashi bai ma san ta yi ba, ganin ya kyaleta yasa ta murgud'a masa Baki ta wuce abunta, tana gaf da shigewa class ne ya ankara da ita aiko cikin sauri ya d'aga murya yace

"Hey!"

Taso ta share amman dai ta waigo don tana da tabbacin da ita yake, amman duk da haka sai da ta nuna kanta tace

"Ni?"

Ya d'aga mata kai sannan ta dawo zuciyarta cike da tsoron laifin me ta yi masa kuma?, Aiko tana zuwa gabanshi zata yi kneel down ya yi saurin girgiza kai yace,. "No! no!"

Dije ta mik'e cike da mamakin sauyawarshi ta kura masa kallo sai da ya yi shiru sannan cikin yaren hausa yace,. "Me ya hanaki zuwa Makaranta kwana biyu"

Dije ta zaro ido waje saboda tsananin mamakin da ya bata bakinta yana rawa tace,. "Malam ashe daman cen ka iya hausa?"

Hararar da ya maka mata ce yasa ta yi saurin rufe Bakinta tace,. "Sorry ser"

Ya sake maimaita tambayarshi Dije kam nan take ta bata fuska tace, "Baffahna ne ya hanani zuwa"

Cike da mamaki Safwan ya yi saurin cewa,. "Saboda mi?"

Dije wasu hawaye suka gangaro mata tace,. "Saboda Abokinka yace yana so ya aureni shine ya hanani zuwa Makarantar, yanzu haka ma sai da na yi masa alk'awalin bazan sake kulashi ba sannan ya barni na tafo, don ALLAH Malam ka ce dashi ya yi hak'uri ya daina yiman magana har sai na kare Makaranta, don WALLAHI ina son karatun bana son a hanani zuwa kuma gashi ma ina son ya kaini Makarantar Likitancin da yace zai kaini"

Ta k'are maganar cikin zubowar wasu ruwan hawayen, Safwan ya yi shiru yana nazarin maganganunta sannan cen ya d'ago da kanshi ya kalleta cikin sanyin jiki ya ce "kina so ki yi karatu mai zurfi bayan kuma kinsan hakan ba al'adar garinku bace, ko akwai wadda ta tab'a zuwa Makarantar gaba da primary a garin nan?"

Dije ta girgiza masa kai tace,. "Ko d'aya duka aure ake masu, yanzu haka ma cikin kawayena Hansai da Ladiyo da Jummala duk suna da Miji da an tashi aure kawai za'a yi masu"

Safwan ya yi saurin zaro ido yace,. "Cabd'i jam! To ke ba'a yi maki Mijin bane?"

Ta rufe fuskarta tace,. "Ai Ni ba wanda ma ya tab'a cewa yana sona sai mutum biyu"

Cikin kureta da kallo tare da had'e fuska yace,. "Su waye Mutum biyu din?"

Dije ta rufe fuskarta tace,. "Kunyar fad'a nake ji WALLAHI"

Shi kanshi gano wannan firar bata dace da Malami da dalibi ba yasa yace,. "Ok to je ki shiga class amman Kika kuskura naji kince da wata na iya Hausa I will purnish you"

Dije ta dafe bakinta tana k'umshe dariyar da ta zo mata tace,. "Ba zan fad'a ba ai"

Safwan yana shirin sake yi mata magana ne ya hango Lawi zai shigo Makarantar ya yi saurin fad'in,. "Oya go to your class"

Dije ta tafi tana ta k'umshe dariyarta saboda gargadin da yayi mata ya bata dariya, don ganin renin wayon nashi ma ya yi yawa ashe ma ya iya hausa amman kullum yake ta zuba masu zallar turanci, sannan zagin da tasha yi mashi da Hausa ita da su Lanti ashe duk yana ji amman yake yi kamar bai san me suke fad'a ba, sai dai laifi kad'an zai sa ya yi ta harararsu yana muzurai, k'arshe ma haka zai k'are karatun ba tare da sun fahimci komi ba.

Lawi kam tun daga nesa da ya hango Dije yake ta sauri sai gashi kafin ya k'araso har ta wuce, cikin damuwa ya isa wurin Safwan ya zauna ya na bin class d'in su Dijen da kallo, Safwan ya yi masa wani kallo ya yi wani mere yace

"To yarinyar nan dai ka d'aga mata k'afa don yanzu ta ke sanar dani Mahaifinta ya hanata zuwa Makaranta ne saboda kai, idan har da gaske kana sonta to ka barta ta yi karatunta, don an gargad'eta a gida duk ranar da aka sake ganinta da kai za'a cireta daga school d'in gaba d'aya"

Lawi ya yi saurin fad'in

"Innalilahi wa'Inna ilairraji'un kai wannan bala'i da me yayi Kama?? WALLAHI kwana biyun nan da ban ganta ba jinsu nayi tamkar shekara biyu, Abokina ka taimaki rayuwata WALLAHI mutuwa zanyi idan har ban auri yarinyar nan ba"

Safwan ya yi saurin mik'ewa tare da buga wani uban tsaki ya barshi a nan ya shige Ofishin Malammai, Lawi ya bishi da kallon mamaki sannan ya yu shiru yana nazarin mood d'in abokin nashi akan matsalar, da kullum baya bashi goyon baya akan soyayyarshi da Dijen, asali ma sai Kara dakushe masa karsashi yake yi kullum safiya, a ranshi yace

_"shin wai shi baya da imani ne da har ba zai taimakeni na samu abunda yafi soyuwa agareni ba?, Ko don shi har yanzu bai San zafin son bane?"_.

Ya furzar da iska mai zafi a bakinshi ya mike ya nufi office d'in ranshi a b'ace, saboda damuwowin da suka yi masa yawa ga rashin goyon bayan Safwan akan masoyiyarshi Dije, ga kuma wata bakuwar matsalar da aka kunno masa da ita, don rashin magana da Dije a wurin ba k'aramin purnishmen ne aka bashi ba, yarinyar da har gizo take masa a ido baya da wani mafalki a Yan kwanakin nan sai nata, lokaci d'aya a rabashi da ita irin haka ai an ci da zalinshi.

Ranar har aka tashi ba wata walwala ko wata huld'a mai k'arfi da ta shiga tsakanin Abokan biyu, abun takaicinma lokacin da aka tashin k'iri K'iri Dije ta ki tsayawa ta ji uzurin Lawi da ke son yin magana da ita, saboda tsoron a ganta aje a fad'awa Baffanta Safwan kam ba k'aramin dad'i hakan ya yi masa ba, ya sake girmama lamarinta saboda ganin ashe rashin kunyarta da sauk'i tunda har tana jin maganar iyayenta.

Lawi kam ko dakinsu bai nufa ba ya isa wurin Maigarin cikin damuwar da ta kasa boyuwa akan fuskarshi, Maigarin ya kalleshi cikin tausayawa don yasan labarin gizo baya wuce na koki, amman duk da hakan sai da ya wayance yace dashi

"Yarona lafiya Na ganka haka? ko wani abun ne ya faru cen Gida? "

Lawi ya kara sunne kai yace,. "A'a Baba akan dai matsalar nan ne"

Maigarin ya ce,. "Wace matsala Kuma? Ko ta Yar Gidan Malam Sanda?"

Lawi ya d'aga kanshi yace,. "Eh ita to yanzu abun ya Kara rikicewa saboda ko magana ma an hanata tsayawa ta yi dani"

Maigarin ya yi shiru sannan yace,. "Ka yi hak'uri yarona Ni zan ga Malam Sanda duk yanda muka yi zan neme ka"

Lawi ya mike tare da yi masa godiya ya yi d'akinsu, zuciyarshi cike da takaicin bala'in da ya janyowa kanshi yana zaman zamanshi.

Maigarin kam bai yi k'asa a gwiwa ba dakanshi bayan magrib ya yi tattaki tare da mukarrabanshi suka nufi gidansu Dije, cike da mamaki Baffah'n ya shimfida masu tabarma suka zauna tare da yi masu sannu da zuwa.

Bayan an k'are gaggaisawa ne Maigarin ya yi gyaran murya yace,. "Malam Sanda nasan zaka yi mamakin abunda yasa na yo tattaki zuwa wajenka?, To ba komi ba ne akan matsalar Bakon yaron cen ne da Yar wajenka Dije, a zahirin gaskiya yaron nan dai na gano ba k'aramin so yake yi mata ba, shiyasa nace bari in zo in jaddada maka zancenshi da muka yi a kwanakin baya, shin har yanzu kana kan bakanka akan bazaka baiwa mutumen nesa yarka ba Koko ya abun yake?"

Baffah kam Nan take wani sabon b'acin Rai ya ziyartoshi amman cikin dariyar yake yace,. "Ranka shi dad'e ina mai jin kunyar sanar da Kai cewa na yiwa Dije Miji, kuma insha ALLAHu wata mai kamawa Zan auradda Dije ga Bala dan Gidan Mariganyi Mamman jikan Inna Duduwa"





To fa rigiji Gabji😳 lalle akwai kwacagiya😝




Akafta🤣







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*


*Lamba ta 21*


Gaba d'aya jikin kowa na wurin ya yi sanyi sai cen Maigarin ya yi jarumtar fad'in,. "A komi ALLAH Ubangiji yasa hakan shine alkhairin"

Ya yunkura ya mike tsaye yana saka talkaminshi yace da abokan tafiyarshi,. "Ki tashi muje sai mu yi masa bayani idan har ALLAH zai sa ya fahimcemu"

Haka suka bar k'ofar gidan kowa jiki ba kuzari saboda ganin duk girman Maigarin ya zo neman abu wajen Baffah amman ya rufe idonshi ya kasa yi masa wannan alfarma, shi Kam Baffah ko a jikinshi hasali ma hankalinshi kwance ya nad'e tabamar ya shige cikin gida, inda kai tsaye ya kira Usman ya ce ya je ya kira masa Balan Duduwar, sannan ya shige d'aki abunshi Inna ta bishi da kallon mamaki jin aiken da ya yi na neman Bala, cikin sanyin jiki ta bishi d'akin tace

"Malam ALLAH dai yasa lafiya?? Naga Maigari ya zo wajenka kuma ga shi na ji yanzu ka ce a kira Bala"

Baffah ya yi saurin fadada fuskarshi da murmushin yace,. "Abunda kike so ne za'a yi maki tunda na hango hakan shine mafita akan matsalolin da suke son kunno man kai cikin gida"

Inna ta bishi da kallo Baki sake tace,. "Ka yi man bayani yanda Zan gane Malam"

Baffah ya fito d'akin tare da d'auko buta ya fara sabuwar arwallah har ya k'are ba tare da yace kanzil ba, sannan ya mike ya kalleta yace

"Wata mai kamawa Zan yiwa Dije aure da Balan Duduwa tunda har yana sonta"

Inna ta zaro ido waje tace,. "A'a Malam gaggawa fa aikin shedan ce, ka bari abi komi a hankali kar a zo ayi abu don neman mafita wata sabuwar matsalar ta bullo"

Baffah ya kalli Inna shekeke sannan ya nufi hanyar fita yace,. "Alkhairi muke fata kuma shi zamu gani"

Ya fice ranshi a b'ace Dije da ke k'ofar Inna ta k'araso wajen da Innar take tsaye cikin kokwanto tace,. "INNA naji Baffah yana zancen aurena da Balan Duduwa da gaske yake yi ko wasa???"

Inna ta maka mata wata Uwar harara ta nufi madafi tace,. "Ki jira idan har ya dawo sai ya amsa maki tambayar da bakinshi tunda ai ba Ni kika ji na fad'a ba"

Dije ta ja buta ta yi bayi tana gungunin cewa,. "Ai na rantse da ALLAH ni Malam Danbirni zan aura cabd'i! Haka kawai in aureshi ya hanani zuwa Makarantar koyon Likitanci hum! lalle ma ko"

**

Baffah Kam tare da Bala da Usman suka yi sallahr Isha sannan suka garzayo gida, Baffah yasa Usman ya shimfida masu tabarma a zauren gidan, sannan yasa aka kawo masa tuwonshi ya yi wa Bala tayi Bala cike da jin nauyin surukuta yace,. "Alhmdllh"

Baffah ya kalli Balan yace,. "Naji labarin cewa kana son Dije ko?"

Bala ya sunne kai cike da jin kunyarshi, Baffah ya ce

"Magana zamu yi mai Muhimmanci saboda auradda ita nike son yi idan har kashirya aurenta to ka fito da karfinka Ni zan aura maka Dije duk lokacin da ka shirya"

Cike da tsananin farin ciki yace

"Na gode Baffah" Balan kam bakinshi ya kasa rufuwa saboda tsabar murnar ganin nesa ta zo masa kusa, cikin jin nauyi ya nunawa Baffah amincewarshi tare da godiya akan wannan karamci da ya yi masa, sannan ya yi masa alk'awalin zai turo iyayenshi kurkusa ayi komi a gama cikin kankanin lokaci.

Haka suka rabu zuciyarshi cike da farin ciki uwa uba ma da Baffah'n ya bashi damar ya fara zuwa zance wajen Dijen don su fahimci juna kafin lokacin auren ya zo.

Baffah kam bai shigo Gida ba har sai da ya tabbatar Dije ta yi bacci don ba ya son ta janyo abunda zai sa ya jibgeta a banza, don tunda ya dawo masallacin ya ga yanda ta makure jikin gini tana sharar hawaye yasan akwai magana, don baya raba d'aya biyu yasan taji zancen aurenta Balan shiyasa, sai dai a mamakinshi ko da ya shiga cikin Gidan ya taradda ita idonta biyu jikin ginin har lokacin tana gyangyadi, jin shigowarshi yasa ta yi saurin mik'ewa ta nufoshi tana fad'in

"WALLAHI Ni Baffah ban son Bala ba zan aureshi ba"

Baffahn ya yi mata wani kallo yace,. "Baki sonshi wa kike so??"

Dije ta yi saurin kamo gefen dankwalinta tana wasa dashi tace,. "Ni Baffah ba wanda nike so WALLAHI Ni gurina kawai inje Makarantar gaba in zama likita"

Baffah ya zaro Ido waje yace,. "Au shirmen ya kitsa maki kenan ko? To ai kwanan nan zanyi maganin abun, ai WALLAHI ko bani so dole ne in auradda ke cikin gaggawa tun kafin su kaini ga maganar banza"

Yana kare maganar ya shige d'akinshi zuciyarshi cike da jin tsoron sharrin wad'annan bak'in Yan bokon ga Yar guda gudar yarshi Dije, wadda ko kuda baya so ya tab'a masa ita matuk'ar yana da ikon hakan.

Dije kam ranar kwana ta yi tana sharbar hawayenta saboda sam sam ita bata son auren kacakam ballantana auren Balan, idan son damunta ne ace ta yi karatu mai zurfi ta zamo abar alfakhari cikin kauyensu, amman ina kash tasan gurint sam bazai tab'a cika ba muddin ta auri Bala, don dama ace Lawi ne da zata sakawa ranta cewa gurinta zai cika komi daren dad'ewa.

Ko da Safiya ta waye da d'ar d'ar ta shirya don ta zaci Baffah'n ya hanata zuwa Makaranta, amman sai gashi bai hanata ba har da yi mata ALLAH ya kiyaye, saboda yasan Shirin da yake yi akan auradda ita d'in cikin kankanin lokaci.

Dije sukuku ta zo Makarantar Lawi ya so ya yi mata magana amman tuno irin gargadin da Maigarin ya yi masa akanta yasa ya yi k'ok'arin kawar da kanshi gareta, don ko da aka tashi ma sai da kowa ya watse Makarantar sannan shi ya nufo masaukinsu, don gaba d'aya ma shi zaman garin ya gundureshi jin yake yi kamar a saman kaya yake, Alla Alla yake yi su kammala service dinsu su bar Garin, don akan hakan ma har abokin nashi ma sun fara zaman doya da manja dashi, gashi shi ma Maigarin yace ya zame hannunshi idan shi zai iya ga fili ga mai doki.

**

Cikin wata d'aya aka kammala neman auren Bala da Dije inda aka kawo komi na auren Rana kawai ake jira ta zo a sha shagali, izuwa lokacin Dije ta saduda dolenta saboda ba tirjiyar da bata yi ba akan auren amman Baffah'n kam ya kafe ba gudu ba ja da baya, don ita kanta Innar ganin akan auren Dije zasu samu matsala da Baffah'n shiyasa ta zubar da makamanta ta fara shirye shiryen auren Dijenta.

Ana saura sati d'aya bikin Dije suka zana jarabawar kammala primary, kowa sai murna yake yi inda shi Kuma Lawi yake cike da bak'in cikin rasa Dijen da yayi, Safwan kam ko kad'an bazaka gano yanayin da yake ciki ba, asali ma shi hankalinshi kwance yake ta d'aukar photuna da su Dije da sauran yaran Makarantar, Dijen ma ba wata walwala akan fuskarta don kuwa a kallo d'aya zaka gano sauyawar da ta yi, don kuwa gaba d'aya ra zabge sai Ido da karan hanci don izuwa lokacin har wata natsuwar dole ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login