Showing 42001 words to 45000 words out of 136985 words
jin kamar bata biyarshi yasa ya waiga ganin bai ganta ba ya dawo sai dai tsayin da ya ga ta yi ne shi ma kanshi ya so ya bashi dariya, amman ya mazge ya katsa mata wata uwar tsawa yace
"Ke Uban mi kike yi a wurin ba za ki zo mu tafi ba??"
Dije ta yi saurin waigawa sannan ta b'ata fuska tace, "wani abun takaici na gani yanzu wai wani k'atoton banza ne ya yi kwance anata jibgarshi a wofi WALLAHI ya ji haushi shi kam"
Safwan hararar da ya danna mata ce tasa ta yi muk'us ba shiri ta nufo wajen tare da rab'awa ta gefenshi ta wuce, su Surry kansu tuni suka yi gum! har sai da suka ga ya wuce sannan suka sake fashewa da wata sabuwar dariya saboda abinda Dijen ta yi ba k'aramin dariya ya basu ba.
Bayan sun bar wajen ne Safwan d'in ya fisgota da k'arfi ya had'ata da gini tare da d'aga hannu kamar zai daketa cikin b'acin rai ya nunata da yatsa yace
"WALLAHI kada ki kuskura ki janyo in karairayaki cikin Gidan nan, ke shikenan ba zaki natsu ba sai abu kike yi tamkar wata mahaukaciya to bari kiji na sake ganin kin sake irin wannan shirmen jikinki ne zai gaya maki wawuyar banza,, matsa daga nan kina wani kallona da wasu idanuwanki guru guru tamkar idanuwan mota"
Dije ta zunb'uro baki Kai tsaye ya fisgo hannunta cike da jin haushin kwafsawar da take yi masa suka nufi d'akin, sannan ya saketa da sauri suka shiga tare da sallama a bakunansu.
Dije kam sage da hannu ta shiga ta Sami gefe ta rakub'e tana yarfa hannunta,a zuciyarta tana fad'in
_"Shi Kam wannan mugun mutumen har ciki nawa ya ke so ya yi man ne? "_
Tunaninta ya katse ne saboda jin muryar wani d'aya daga cikin Iyayen Safwan d'in da ta jii yana cewa,. "Matso daga ciki ki zauna kinji 'yata"
Dije ta mik'e ta dawo ciki kad'an ta zauna k'asan carpet kamar yanda taga Safwan d'in ya yi, duk da wata zuciyar ta so ace ta hau Kan kujerar ko don ta ji ya laushinta ya ke, don tunda ta k'yalla Ido ta hangosu tasan ba k'aramin dad'in zama za su yi ba, amman firgicin cikin da Safwan ya sake yi mata yasa ta ji duniyar gaba d'aya ma ta fice mata a Rai.
Baba Ali ya sake cewa
"Masha ALLAHU kamar yanda kowa ya sani ne wannan zama mun yishi ne saboda Safwan da Khadija, saboda auren da Ubangiji ya nufa aka yi a tsakaninsu, to Masha ALLAH yanzu Malam Sanda ga gidansu Mijin 'yarka yanda idan ka tashi nemanta kasan ta inda zaka nemeta, Hajiya Balkisu kinga Mahaifin Khadija Malam Sanda wad'annan kuma abokan tafiyarshi ne, Khadija kin ga Mahaifiyar Mijinki Safwan Mahaifinshi kuma tuni ALLAH ya yi masa rasuwa,m sai dai Ni yayanshi tare da wannan k'anenshi tare da sauran 'yan uwanmu Mata da maza da suka rage, shi kam sai dai mu bishi da addu'ar ALLAH Ubangiji ya dad'a masa Rahama a cikin k'abarinshi tare da musulmin duniya gaba d'aya, mu ma idan ta mu ta zo yasa mu cika da imani"
Dukansu suka ce "Ameen Ameen" sannan d'aya bayan d'aya kowa ya yi jawabi tare da neman ma zaman auren nasu albarka, sannan aka ja hankalinsu duka daga shi har ita akan zaman auren tare da nuna masu muhimmancin auren tare da hak'uri a zamantakewar auren duka.
ALHMDLLH shi kanshi Baffahn na Dije yanzu hankalinshi ya kwanta sosai saboda ganin yanda suke Mutane masu karamci, daga nan shi ma ya damk'awa Safwan da Mahaifiyarshi har ma da Iyayen Maza amanar Dijenshi, tare da rok'onsu akan duk abunda ta yi wanda bai dace ba don ALLAH ayi hak'uri da ita da sannu zata dawo dai dai da yanda ake son kowace d'iyar ta kasance, don a fakaice ya yi masu nuni da su yi hak'uri da halayenta don ba ya son ya bayyana k'arara cewa ga laifin 'yarshi, ya fi son idan sun gani a matsayinsu na masu ilimi su fahimtar da ita abunda ya dace su d'orata kan hanya har ta fahimci rayuwar da yanda ake zama cikinta.
Taro ya watse akan cewa gobe tun da sassafe su Baffah'n za su kama hanyarsu ta komawa gida, sannan su Iyaye mazan suka yi sallama da su akan sai goben za su zo su yi sallama da su Baffah'n, Safwan da Hajiyarshi har gindin mota suka rakasu suna yi masu godiya har suka bar Gidan.
Dije kam suna fita ta tashi ta nufi Baffah'nta tana washe baki tace,. "Baffah Kai ma ka ci naman mai yawa ko? WALLAHI baka ga Wanda na ci ba ga abincinsu mai shegen dad'in tsiya"
Baffah ya washe Bakinshi ya ce, "kin samu gidan Aure Dije don ALLAH ki yi biyayya kinji?"
Dije ta d'aga Kai, tana matsa 'yan yatsunta tace,. "Ai ni duk ma aikin da suke so in yi masu zan yi WALLAHI ko don su dinga bani abincina mai dad'i ina ci"
Baffah ya ce,. "Duk abunda Mijinki ya sakaki ki yi masa kinji? haka ma Mahaifiyarshi kin ga dai suna da kirki don ALLAH kada ki yi abunda zai janyo har ace baki kyauta ba"
Dije tace,. ,"Insha ALLAHu Baffah ba Zan yi rashin ji ba ko cen garinmu ai ka ga su ke ja na ai"
Baffah ya ce "Nan ma ai dole su ja ki amman don ALLAH kar ki biyesu ki ce ke dole sai kin rama ki kyalesu da halinsu da sannu zaki ci ribar hak'urinki"
Dije tace "to Baffah amman don ALLAH ka ce da shi ya daina rik'e man hannu WALLAHI Ni bana son inyi ciki gashi yanzu har ciki biyu ya yi mani d'aya nan d'aya a k'auyenmu"
Ta k'are maganar cikin zubowar wasu 'yanmatan hawaye, Baffah zai yi magana kenan sai ga su Safwan d'in sun shigo, dole ya wayance yana fad'in
"Ki yi hak'uri ai ko nan gida ne kamar cen d'in saboda nan da cen duk d'aya ne a wajenki Babu banbanci"
Akafta😛
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Masu buk'atar Littafaina ga su kamar haka:*
*TARTSATSI*
*RUWA DA K'ANK'ARA*
*BAKAN GIZO*
*DIJE K'ARANGIYA*
*BAK'ON YANAYI sai dai shi na kud'i ne da d'ari uku kacal zaki sameshi a complete d'inshi😇*
*Lamba ta 28*
Haka Baffah ya shashantar da zancen aka yi ta fira har aka yi magrib suna tare da Safwan sunata fira duk da ba wani sabawa ya yi da su ba amman ba laifi sun d'an tab'a fira, kiran sallah'r yasa Dije ta yi cikin Gidan tare da matan biyu domin su yi SALLAH, su Baffah kuwa suka yi masallacin da ke k'ofar gidan.
Ko da dare ya yi Hajiya Mama ta saka Dije ta yi wanka da kanta ta nuna mata yanda zata yi kwalliya ba irinta haukarta da ta saba ba, ta d'auko wasu sababbin kayan bacci masu shegen kyau tace ta saka, Dije kam saboda hud'ubar da Baffah'nta ya yi mata sannan da kashedin da Safwan d'in ya yi mata shi yasa ta rage shirme in taga wani abu da bata sani ba sai ta yi shiru ba zata yi ta surutu ba, bakinta alekum ta saka kayan tare da fessesa mata turaren da Hajiya Mama ta yi sannan ta kira Surry tace da ita ta je ta Kai Dije d'akin Safwan, Dije ta zaro Ido waje tace
"Hajiya me zanyi wajenshi Sabida ALLAH Ni kam cikin daren nan yanzu??"
Hajiya ta dafe goshinta tace,. "Ki je ki yi kwanciyarki a cen kafin da safe sai a kaiki gidanki in da zaku zauna da Mijin naki"
Dije ta zaro Ido waje tace,. "Kina nufin gidan nan zan bari???, WALLAHI idan na barshi an cuceni wa zai bani irin abincin da na ci d'azu mai d'an karen dad'i?"
Hajiya Mama ta dafa kafad'arta tace,. "Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHu abincin da zaki ci a cen har sai ya fi na wannan Gidan dad'i, yanzu dai ki je da safe idan kika zo zan yi maki bayanin komi"
Dije ta marairece cikin kuka tace,. "Yanzu tsakaninki da ALLAH d'akin Namiji zaki kaini inje in kwana???bayan nasan ke ma kanki kinsan cewa hakan bai dace ba amman kike k'ok'arin turani???"
Hajiya Mama ta dafe goshinta ba shiri ta kai zaune tace da Surry da ke sunne kai tana k'umshe dariya da ta je, sannan ta janyo hannun Dijen ta zaunar da ita kan gadon ta yi shiru na d'an lokaci sannan tace
"Ai dai kinsan cewa an yi maki aure da shi ko?"
Dije ta d'aga kanta, Hajiya Mama tace
"Masha ALLAH to ai kinga shi baya cikin jerin mazan da aka haramta ki je d'akinsu ko?"
Dije ta yi shiru na d'an lokaci tana tunani tace,. "To Ni dai tsakani da ALLAH Innata ta hanani ko magana in dinga tsayawa ina yi da maza sosai, kuma yanzu idan Baffahna ya ji ai WALLAHI dole ma ne ya dakeni, Ni dai don hasken da ALLAH ya yi wa Qur'ani kada ki bari ya sake yi man ciki na uku"
Hajiya Mama ta zaro ido waje tace,. "Ciki na Uku?????"
Dije tace, "Eh ya yi man d'aya a k'auyenmu yanzu gashi d'azu lokacin da ya zo kirana muje wurinku sai da ya yi man d'aya yanzu haka Ina jin macizai sun fara taruwa a cikina kin gani WALLAHI cikina ya k'ara yin k'ato"
Hajiya Mama ta yi shiru tana nazarin maganganun Dijen sai cen ta nisa tace,. "To ta yaya yake yi maki cikin halan don inji in yi masa fad'a ya daina kada ya sake??"
Dije ta b'ata fuska tare da ciro hannunta duka biyu ta nunawa Hajiya Mamar tace,. "Duba ki gani kowane hannu nawa da kike gani akwai cikinshi d'auke a ciki, gashi ina jin tsoron macizai da yawa idan na haifosu bansan ya zanyi da su ba"
Hajiya Mama ta yi murmushi irin nasu na manya tace "waton hannun naki ya rik'a ko ko ya abun yake ne?"
Dije ta goge hawayenta tace,. "Eh rik'e man ya yi har sau biyu shiyasa Nike jin tsoron ya sake yiman cikin, idan ba haka ba WALLAHI zan yi addu'a in mutu kafin lokacin sai ya san yanda zai yi da macizan idan sun fasa cikina sun fito"
Hajiya Mama ta rik'o hannunta tace,. "Wa ya sanar da ke hakan halan??"
Dije ta goge hawayenta tace,. "Innata"
Hajiya Mama ta yi Yar dariya sannan tace,. "Alhmdllh Innarki ta yi gaskiya sai dai ita baki gano abunda take nufi ba shiyasa, abunda take nufi shine idan har wani daban wanda ba Mjinki ba ya rik'a hannunki to anan ne za ki yi cikin macizan, amman kuma in dai har Mijinki ne ya tab'a hannun anan kam ba wani cikin macizai da zaki yi sai ma lada da zaki samu, ki yi tunani shin lokacin da ya rik'a hannun naki anyi maku aure ne ko kuma kafin ayi?"
Dije cikin sanyin jiki ta ce,. "Bayan anyi addu'ar d'aurin auren ne"
Hajiya Mama tace "Alhmdllh to kinga yanzu gaskiya ta fito saboda haka tashi mu je in rakaki da kaina ki yi kwanciyarki a cen da safe ki zo in baki wani labari"
Dije ta marairece Hajiya Mama ta rik'o hannunta suka nufi d'akin Safwan, Safwan kam yana kwance Kan gadonshi ya zurfafa dogon tunanin abunda yake so ya aiwatar saboda cikar muradin Abokinshi, yana cikin nazarin ne sai gashi ya ji k'wank'wasar d'akin cikin sanyin jiki yace
"Come in!"
Dije ta shigo kanta a duk'e tana zunb'urar baki, ba shiri ya yi zumbur ya mike tare da nunata da d'an yatsa yana fad'in
"Wa ya kawoki d'akin......."
Maganarshi ta mak'ale ne saboda ganin Hajiya Mama a bayanta, cikin sage hannu ya sosa kanshi ya sami gefen gadon ya zauna tare da duk'e kanshi yana feso iska a bakinshi, Hajiya Mama ta zaunar da ita a Kan gadon tace
"Ga Matarka nan sai da safe Ubangiji ALLAH ya baka ikon rik'e 'yar Mutane amana"
Tana k'are maganar ta d'ago fuskar Dije da hawaye suka wanke mata fuska shab'e shab'e tace
"Sai da safe 'yata ALLAH ya baku hak'urin zama da junanku"
Sannan ta fice daga Safwan har Dijen ba wanda ya yi dogon motsi har aka kwashi tsawon lokaci, sannan Dije ta mik'e tsaye zata fita ya yi saurin rik'o hannunta aiko ba shiri jikinta ya d'auki rawa tare da kallon hannun tana k'ok'arin k'wacewa, sai dai kasancewar ba rik'on wasa ya yi mata ba shiyasa bata sami damar k'wace hannun ba, cikin fushi tace
"Wai me yasa kai kake jin dad'in rik'e man hannu ne WALLAHI ka ci sa'a ance ba wani cikin su macizai da zanyi da WALLAHI duk na haifosu kaine na farkon wanda zan sa su ciccije yasin"
Safwan ya mike tsaye tare da sakin hannunta ya d'auko filo ya d'ora akan doguwar kujerar da ke d'akin, sannan ya je ya rufo d'akin ya dawo ya ce da ita
"Kinga wajen kwanciyarki a nan ki kwanta kuma kada ki kuskura inji minsharinki don ba abunda zai hana ni in fiddaki ki kwana waje matuk'ar kika dameni"
Dije ta kalli kujerar ta fisgo filon ta ajiye k'asan carpet d'in ta yi kwanciyarta tana murgud'a Baki, Safwan ya yi saurin kawar da kanshi gefe tare da dafe goshinshi ya yi jarumtar jan k'afafuwanshi ya hau gadonshi ya kwanta, ya d'auki lokaci yana nazari sannan ya yi saurin tashi zaune tare da kiran sunanta a hankali yace
"Khadija!!!"
Dije kam tuni Bacci ya yi awon gaba da ita, ya kirata ya fi sau uku amman bata san ma ya yi ba, jiki a mace ya sauko a hankali ya tallabota tamkar Yar yarinya ya d'orata akan gadon, yana gyara mata kwanciyar ne hular kanta ta sub'uce aiko sai ga himilin gashinta ya hango, don kuwa duk da zirin kitson duka suke a dunkule amman sunyi mata ganwo a baya, don a kallo d'aya za'a gano baiwar gashin da Ubangiji ya wadaceta da shi gashi baki k'irin.
Cike da mamakin ganin gashin nata ya sauko gadon ya kwanta kan kujerar tare da sauke wata ajiyar zuciya, haka ya kwana yanata juye juye saboda tunanin da ya dameshi wanda yasa shi kasa natsuwa.
Dije kam lami lafiya ta yi baccinta duk da zuciyarta cike take da tsoron had'a d'akin da ta yi da shi a matsayinshi na Namiji.
Shiyasa ko da Asuba ta yi ta rigashi tashi ta nufi k'ofar d'akin da nufin ta koma d'akin Hajiya Mama, sai dai ganin d'akin rufe duk da akwai key a jikin k'ofar amman ta kasa yanda zata yi ta bud'e d'akin, don kuwa jawoshi take yi iya k'arfinta amman ko gezau bai yi ba, ganin hakan yasa ta fara bubbuga k'ofar sai ga shi ya tashi firgigit tare da kai kallonshi gareta, cikin d'aga murya yace
"Wai ke me yasa kika cika rashin hankali ne? Me kike son yi ne?"
Ba tare da ta waigo ba tace, "fita zanyi"
Cikin sanyin jiki yace
"Kinyi SALLAH?"
tace "a'a itace zan je inyi"
Ya mike tsaye ya zo bayanta ya tsaya yace,
"Ki jira ki yi SALLAH kafin ki tafin"
Yana kare maganar ya nufi toilet d'inshi ya d'oro arwallah ya fito ya bata umurnin ta je ta yi arwallah a bayin ta yi SALLAH kafin ya dawo masallaci.
Dije kam yana fita itama ta fece zuwa d'akin Hajiya Mama, inda ta taradda ita tana sallahr itama, Kai tsaye ta wuce toilet d'inta ta yi arwallah ta fito ta saka hijabin da Hajiya Mama ta bata ta yi SALLAH da shi jiyan, sannan ta tayar da sallah'rta ba tare da ta tsaya shimfid'a komi ba, tana k'arewa ta fara jero adduointa a bayyane kamar yanda ta saba kullum kamar haka
"ALLAH ka sani Aljannah ka sa Innata da Baffahna da Gambo, Allah ka bani Miji nagari wanda zai dinga siyoman tsiren da Baffah yake siyoman, ALLAH ka sa in zama Likita in dinga yiwa Yaya Usmanu Allura, ALLAH ka sa nice Matar Malam Lawi a Aljannah"
Hajiya Mama da ke zaune tana lazimi ba shiri ta waigo tana kallonta zuciyarta cike da fad'uwar gaba saboda sunan Lawi da ta ji ta ambata.
Akafta😆
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Masha ALLAH Mutanen Dije sannunku da k'ok'arin comments all musamman wad'annan groups d'in:*
*Mata Rahama group*
*D/Auta Novel Fan's*
*Dijen K'arangiya fan's*
*TAURARI fan's 1&2*
*Fadar Ummun fareesa fan's*
*Fatima ce ko zarah fan's*
*Aseela fans group*
*Salmancy fan's group*
*Tamegari Novel fan's*
*K'aramar bazawara fan's*
*Daular Billyn Abdul*
*Kwai cikin k'aya fan's*
*Novels Arena group*
*Maman Maleek group*
*Zauren Uom Mumtaz & Zaratan Mata group*
*Dukanku all ina godiya sosai da dad'ad'an comments dinku kai har ma da wad'anda ban lissafo ba ku sani duk inda kuke HADIZA D/AUTA tana yinku all💋*
*Lamba ta 29*
Cike da mamakin abun Hajiya Mama ta dinga jan carbon tana kallonta har ta kammala jaye sauran 'ya'yan carbin da suka rage ta yi addu'a a gajarce ta shafa ta kalli Dije da har lokacin sai maimaita addu'ar take yi kanta a sama idonta suna kallon rufin d'akin, sai da ta bari ta kammala don kanta sannan tana k'ok'arin yi mata magana Dijen ta janyo jikinta ta k'araso gabanta ta duk'a tare da sunkuyar da kanta k'asa tace
"Ina kwana Hajiya ALLAH ya biya ya saka da gidan Aljannah ALLAH karo maku kud'i ku yi ta cin dad'inku"
Hajiya Mama da ke ta fad'in "Ameen Ameen" addu'ar Dije ta k'arshe tasa ta yi guntun murmushi sannan tace,. "Naji kin fad'i sunan Abokin Safwan Lawi shi miye dangantakarki da shi ne??"
Dije ta yi saurin gyara zamanta ta rufe ido tace,. "Shine ya so ya aureni Babana ya hana kuma bayan yace zai sakani Makaranta har in zama Likita"
Hajiya Mama ta yi shiru sannan tace,. "to ya aka yi shi Safwan aka amince ya aureki??"
Dije ta b'ata fuska tace
"Wai cewa ya yi nace Zan kashe Balan Duduwa bayan Ni WALLAHI ban tab'a cewa haka ba"
Ta k'are maganar cikin zubowar hawaye sannan caraf ta tuno da alk'awalin da Safwan ya yi mata akan cewa in tace itace ta fad'a zai sakata Makaranta, aiko ba shiri ta washe Baki tace
"Laah! Kinga na manta ashe aljanuna ne Suka fad'a ba Ni ba"
Mama ta sake zaro Ido tace,. "Aljanu gareki???"
Dije ta rufe Baki tace
"In fad'a maki gaskiya?"
Mama ta d'aga Kai ba tare da ta sami damar magana ba, Dije ta washe bakinta tace
"Tsakani da ALLAH Ni kam bani da komi amman fa ke kad'ai na fad'awa don ALLAH kar ki fad'awa kowa kinji?"
Hajiya Mama ta yi Yar dariya tace