Showing 114001 words to 117000 words out of 136985 words
don ganin ƴansandan ma yasa ta ji wani tsoro ya sake kamata.
Ko da Safwan ya dawo an ɗaure masa hannu da bandeji bayan an ɗinke masa ƙatuwar yankuwar da ya yi, ya shigo ya zauna idonshi akan Dijenshi da ke sharar ƙwallah idonta sun yi ja saboda kukan da ta sha, cikin sanyin jiki ya ce
"To ke me kike wa kuka kuma yanzu?"
Aunty Ummi ta ce "dole ta yi kuka tunda bata taɓa ganin irin wannan bala'i ba a rayuwarta, wannan matar ƙaddara ai babu mai fatar ALLAH ya haɗashi da ita bale ta zowa mutum a matsayin kishiya"
Ta ƙare maganar cikin yin wani kalar mere kamar wata yarinya, Hajiya Mama ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce
"Yanzu dai abunda ya faru ya riga da ya faru fatanmu kawai ALLAH ya taƙaita wahala kuma ya tsare gaba"
Safwan ya dafe kanshi da ke ta sara masa ya ce, "ai kuma yanzu sai dai ta bi wasu shanun don nikam WALLAhi saki uku ringis zan dannawa shegiya, don bana fatar ko a hanya in sake haɗuwa da ita bale ta sake zama gidana"
Surayya ta yi saurin faɗin, "hukuncin da ya dace ita kenan baƙar arniya mai zuciyar kafuran farko"
Hajiya Mama ta maka mata wata harara Surayya ta ce,. "Haba Hajiyarmu yanzu da ace ta kashe muna su ai da mu ta bari da shiga uku, don duk hukuncin da za'a yi mata ba lalle ne ya zama dai dai da abunda ta aikata ba"
A harzuƙe Husnah tace "Ni WALLAHI na ma so mun illata shegiya kafin Auncle ya zo"
Aunty Ummi ta ce "ai WALLAHI da ace ina kusa sai na ja shegiya na damalmala kanta cikin fetur ɗin sannan in fito da ita tsakar gidan nan in ƙyasta mata ashanar sai ta ci wutar ƴar shegiya"
Hajiyarmu ta yi saurin faɗin "to kenan da ke da ita duk hukuncinku ɗaya in har kika aika wannan shirmen, yanzu dai abu ɗaya ya rage ka kira Mahaifinta ka sanar da shi abunda ke faruwa"
Safwan ya ɓata fuska ya ce "Ƴan'uwanta da aka yi a gabansu miye amfaninsu da ba zasu sanar da su abunda yake faruwa ba?"
Hajiyarmu ta ɓata fuska ta ce, "kaine ke da haƙƙin sanar da su ba wasu ba, saboda haka ka kirasu yanzu ka sanar da su abunda ke faruwa"
Safwan cike da jin haushi ya ɗaga waya ya kira Daddyn Zee ba tare da jiran komi ba ya ce
"Na saki Zee saki biyu a bisa sunnah da in ana yin ɗari duk sai nayi mata, don haka ayi gaggawar zuwa a kwashe mani tarkacen kayanta cikin gidana"
To fa 😳😳😳kai ko Malam Safwanu saki haka da sauri 😔
Akafta🙌🏻
D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Am sorry fo you my FANS😊 jiya kun ji Ni shiru ko? To ku yi haƙuri yanzu gani tare da ku😸fatana kawai ku biyoni mu je🏃🏻♀️*
*Lamba ta 65*
Yana ƙare maganar ya kashe wayar cikin fushi ya miƙe zai bar falon Hajiya Mama ta kira sunanshi a hankali cikin wata murya mai cike da alhini, ba shiri ya waigo ta ce da shi ya dawo ya zauna, sannan ya dawo ya zauna sai wani cika yake yi alamun a wuya ya ke sosai, Hajiya Mama ta sake kiran sunanshi ta ce
"Abunda na ce ka aikata kenan? Me yasa kai a koda yaushe baka iya dafa mutum cikin ruwan sanyi ba?, Nasan Zainab bata kyauta ba amman shi mahaifinta laifin me ya yi da har zaka yi masa wannan cin fuskar?, Yanzu idan kai ne a matsayinshi wani ya kiraka ya saki ƴarka irin haka wane irin hali kake tsammanin zaka shiga?, To bari ka ji banji daɗin abunda ka aikata ba, don Mahaifinta komi lalacewarshi ya gama maka komi tunda har ya ɗauki ɗiyarshi ya baka, don haka ka sani laifin wani baya shafuwar wani, saboda shi mutum daraja gareshi mussaman wanda ya ke sama da kai irin haka, saboda haka ka dinga kwatanta adalci akan duk wanda mu'amala ta haɗaka da shi, don da ace ka yi cuta gara ace kai ne aka cuta, don yanzu wannan abun da ka yi masa har abada ba zai taɓa mantawa ba, tabbas kam ƴarshi bata yi abunda ya dace ba amman ka sani kai ka yi abunda ya fi wanda ta aikata muni"
Safwan da su Aunty Ummi Suka kallota cikin mamaki ta ce
"Eh tabbas haka ne don ita da makami ta yi niyya kasheka cikin fushi, kai kuka ka yi amfani da dafin harshe ka caki ubanta da mummunar maganar da dole ne ta daki zuciyarshi, ko baki ji ance dafin harshe ya fi na takobi zafi ba?, to bari ka ji yanzu wannan raunin da ta ji maka a hannu zai iya warkewa har wurin ya koma tamkar ma ba'a yi, amman dafin abunda ka yi wa mahaifinta ka sani har abada ba zai taɓa goguwa a cikin zuciyarshi ba, saboda haka ka daina yanke hukunci cikin fushi a koda yaushe idan har kasan abunda zaka faɗa ba mai kyau bane, to ka yi ƙoƙarin danne zuciyarka ka yi shiru saboda faɗar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da ya ce(falyaƙul khairan auliyasmut, ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru) saboda shi baki dafi ne da shi wanda idan aka yi maka wata mummunar magana har abada ba zaka taɓa mantawa da ita ba"
Safwan ya shafo kanshi da hannunshi mai lafiya ya ce "na yi kuskure Hajiyarmu kuma Insha ALLAH bazan sake maimaita kwatankwacin hakan ba...."
Kiran wayar Safwan ce ta katse maganar da yake yi, cikin sauri ya duba mai kiran sai ga shi da kallo Hajiyar cikin sauri ya ce
"Mahaifinta ne"
Hajiyarmu ta ce
"Ka ɗauka ka ji to"
Ya ɗaga ba tare da ya ce ƙanzil ba ya saka hands free, sai ga muryar Mahaifiyar Zee cikin wayar tar! tar! tana kuka tana faɗin
"Me ke faruwa ne? Me ya sami Zainab ɗin ne? ga Daddynta nan ya faɗi rai a hannun ALLAH sai sunanta ya ke kira, me ke faruwa ne na ce?"
Ta ƙare maganar cikin kuka tare da ɗaga murya Hajiya Mama ta yi masa nuni da hannu alamun ya sanar da ita, cikin sanyin jiki ya fayyace mata abunda ya faru a dunƙule, mahaifiyarta ta fasa wata uwar ƙara tare da cewa
"Innalilahi wa'Inna ilairraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa alkhalifni khairun minha"
Sannan ta kashe wayar gaba ɗaya jikin kowa ya yi sanyi, ran Hajiyar a matuƙar ɓace cikin tagumi ta ce "ka ga abunda nike sanar da kai ko? To idan har ka yi sanadin mutuwarshi sai kasan abunda zaka faɗawa ALLAH idan kun je lahira"
Hajiyar Mama ta miƙe cikin fushi zata fita ya yi saurin shan gabanta yana bata haƙuri tare da su Aunty Ummi, Dije ta duƙa ƙasa ta riƙo leɓen zanenta cikin kuka ta ce
"Ki yi haƙuri Hajiyarmu kada ki fushi da Malam don ALLAH ki yafe masa"
Hajiyar ta duƙa ta ɗagota tare da share mata hawayen da suke ta zuba a idonta ta ce, "komi ya wuce na haƙura insha ALLAHu amman matuƙar yana son in yafe masa to sai ya furta ya mayar da Zainab a matsayin matarshi"
Dije da su Aunty Ummi da shi kanshi suka zaro ido waje saboda bugawar da zuciyoyinsu suka yi, cikin tabbatarwa ta sake ce wa "haka na ce kuma haka ni ke son ayi don hakan kawai zai rage raɗadin baƙin cikin abunda zai faru ga mahaifinta, wanda ko kaɗan bani fatar ace kai ne ka yi silar mutuwarshi da hannunka, duk da bana fatar hakan amman ka sani duk ya mutu a sanadin wautarka to baka yi wa kanka adalci ba"
Safwan da su Aunty Suka yi shiru kowa da nazarin da yake yi a zuciyarshi, Dije ta je gabanshi tare da haɗa hannuwa biyu alamun roƙo ta ce
"Don Allah Malam ka dawo da ita a matsayin matarka plss"
Cikin tsananin ɓacin rai ya ce "na dawo da ita da sauran igiya ɗayar da ta rage a tsakaninmu, amman WALLAhi bazan taɓa yafe mata abunda ta aikata man ba"
Yana ƙare faɗar hakan ya bar wajen cikin ƙunar zuciya, Hajiyar ma ta ce da su Aunty Ummi su zo su tafi gida, kasancewar isha ma ta wuce kuma ga shi wasu cikinsu ko SALLAHr magrib ma ba su yi ba, har bakin motar da ta kawosu Surayya da Dije suka rakasu, bayan sun tafi ne itama Surayya ta kira Mijinta ya zo ya ɗauketa, Dije ta nufi ɗakinta ta yi sallolinta sannan ta nufo ɗakinshi da ke sashenta, inda ta taraddashi zaune akan carpet fuskar haɗe ya yi shiru alamun ya faɗa cikin dogon nazari, ta sami gefenshi ta zauna tare da riƙo hannunshi mai yankuwa ta ɗora saman jikinta, cikin sanyin murya ta ce
"Don Allah ka daina wannan damuwar komi da ka ganshi daman cen rubuce yake mune ba mu sani ba, sai abun ya faru ne mu ke ganinshi tamkar sabon abu, don ALLAH Malam ka daina wannan damuwar WALLAhi bana son ganinta a fuskarka ni dai"
Safwan ya kallota da jajayen idonshi da suka rine saboda tsabar ɓacin rai ya ce "Ta ya bazan yi damuwa ba? Bayan Hajiyarmu ta sani mayar da wannan matar bala'i cikin rayuwarmu,yanzu ta sami damar yin haka ina ga abunda zata aikata a gaba? Hajiyarmu me yasa ta kasa gano Zainab ba alkhairi ce ga rayuwarmu ba? To Wallahi ko da ace zata dawo ɗin to ni kuma bazata taɓa jin daɗin zama da ni ba, sai ta bar gidan nan da ƙafafuwanta ba tare da ta shirya ba"
Dije ta yi saurin kwantawa saman kafaɗarshi cikin muryar kuka ta ce
"Ni dai ka yi haƙuri don ALLAH Malam saboda Hajiyarmu bazata taɓa cewa ka yi abunda bai dace ba kai ma ka sani?"
Safwan ya shafo kanta cikin tausayinta ya ce "wai waye malamin? Ni fa bana son wannan sunan na fara gajiya da shi, don bazan yarda ki mayar da ni tamkar wani tsoho ba, amman ki daina kukan nan bana sonshi"
Ya ƙare maganar tare da goge mata hawayen da ke ta kwaranya akan fuskarta, saboda zafin dawo da Zee ɗin da ya yi har cikin zuciyarta bata ji daɗin hakan ba, amman bata son ta nuna ne don kada aga rashin kyautawarta, amman ta ci alwashin duk ranar da ta dawo ita kuma a ranar zata bar gidan don bazata zauna ba ta kasheta a banza ba, Dijen ta ɗago fuskarta tare da saka hannu ta share hawayenta sannan ta ce
"Mu je mu ci abinci"
Ya bita da kallon mamaki ya ce " Ke kina jin yunwa ne?"
Ta ɗaga masa kai, ya ce "magana za ki yi" cikin siriryar murya ta ce "Eh" sannan ya miƙe suka fito ɗakin har zata cire hijabin da ke jikinta ya ce ta barshi fita za su yi, ta biyoshi a baya suka shiga Mota kai tsaye ya ja suka fice.
Basu zame ko'ina ba sai wata haɗɗaɗiyar Restaurant yasa aka yi mata odar abinci kala kala, Dije ta ƙi ci ta ce dole sai dai su ci tare, ba don ya so ba ta dinga ciyar da shi yana ci itama yana bata tana ci har suka yi ƙat! Sannan ya biya Bill suka nufi wata plazar suka sissiyo kayan tanɗe tanɗensu da maƙulashe sannan suka dawo gidan, duk da a ƙoshe su ke amman hakan bai hanasu sake cin gasashiyar kazar da suka siyo ba, tare da korawa da abun sanyaya maƙoshi, bayan sun kammale ne suka je suka yi wanka suka kwanta, duk da hannunshi da ke ciyo bai hanashi sakin jiki ya sake angwancewa da matarshi ba, saboda a yanda yake ji ko kaɗan ba zai iya haƙura da ita ba a wannan lokacin, haka suka raba dare suna farantawa juna har sai da ita kanta ta ji tausayinshi saboda yanda yake ta shan shagalinshi ba tare da ya yi duba da ciyon da ke hannunshi ba.
Ko da safiya ta waye Dukansu cikin farin ciki da ƙarin ƙaunar junansu suka ta shi, bayan sun yi break ma haka suka sake komawa cikin duniyar ma'auratan sannan dukansu bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da su.
Kiran wayar da ake ta yi masa wani bayan wani ne yasa ya yi saurin falkawa daga nannauyan baccin da ya ke yi, cikin yin wani uban tsaki tare da jin haushin da bai sakata a silent ba, ya miƙe ya ɗauko wayar ganin baƙin numbobi barkatai yasa ya yi saurin zaunawa, sai ga wani kiran ya sake shigowa da sauri ya ɗaga, sai ga wani ƙanen mahaifin Zee yana sanar da shi gasu cikin gidanshi sun zo suna son yin magana da shi.
Cikin jin haushi ya kalli Dijen da ke ta baccinta hankali kwance, ya yi wani murmushin jin daɗi saboda ni'imar da ya kwasa a jikinta, ya yi mata wani kiss a iska ya hura mata sannan ya miƙe ya je ya yi wanka ya saka doguwar jallabiya baƙa ya ja talkamanshi plat ya fice tare da janyo ƙafa a hankali don kar ta tashi.
Ganin baƙin motoci biyu tare da dattijan mutanen yasa ya shiga cikin natsuwarshi, ya isa wurinsu suka gaisa sannan ya yi masu jagora har sashenshi inda babban falon tarbar baƙinshi ya ke, bayan sun zazzauna ne aka sake gaisawa sannan suka sanar da shi sun zo akan su ji ba'asin abunda ke faruwa, don yanzu haka Mahaifin Zee yana kwance asibiti hawan jininshi ya ta shi, saboda abunda ya ji da kunnenshi da wanda ya saurara a gidan Tv..
Saboda ƙarin jawabin da su Ruma suka zo masu da shi na cewa Zee tana hannun ƴansanda, sannan da labaran da aka gabatar a gidan TV dangane da case ɗin masu ɗauke da rahotannin tabbatar da faruwar hakan daga bakin Safwan ɗin da kuma su Surayya da Ruma da sauran ƴan'uwanta duka da aka ɗauka, a daren jiya wanda kuma a ranar aka watsashi a gidan television, wanda ya watsu cikin mintuna ƙalilan tamkar tashin bom ta ko'ina labarin ake yi, sai dai ba'a nuna fuskokin kowa ba don Safwan ne da kanshi ya ce kada a bari fuskokinsu su bayyana saboda tsaro, amman duk da hakan labarin ba ƙaramin shiga zuciyar mutane ya yi ba, musamman wanda yasan ita Zee ɗin da su Safwan ɗin su ma, shiyasa mutane suke ta kiranshi don kawai su ji tabbaci wasu kuma don su jajanta masa.
Ba tare da jan wata doguwar magana ba Safwan ya bayyana masu abunda ya sani da wanda ya ji a bakin Surayya da kuma Ruma, sannan ya yi masu jagora har falonshi na ciki inda aka yi abun wanda har lokacin akwai warin fetur ɗin duk da ya bi iska sosai, cikin sanyin jiki suka dinga bashi haƙuri don sanin da suka yi tabbas Zee bata da gaskiya, sannan suka nemi alfarmar a basu Zee su koma da ita gida saboda Mahaifinta da ke unconscious, ya ce sai dai aje gun Hajiyarshi duk abunda ta ce shikenan, dole suka ɗuru mota suka nufi gidansu Hajiyarmu, bayan an gaisa ne suka fara bata haƙuri kan abunda ya faru sannan suka nemi alfarmar inda hali suna son a janye wannan case don ALLAH kada a bari ya je kotu, ganin girmansu yasa ta ce da su ba komi insha ALLAHu ba za'a je kotu ba indai har itace ta haifi Safwan, cike da jin daɗi suka baro gidan suka nufi Police station ɗin sai dai duk yanda suka so a basu belin Zee hakan bai samu ba, don shi kanshi Safwan ɗin sun nuna masa tunda aiki ya zo hannunsu ko ya janye su bazasu janye ba, don case ɗinta ba ƙaramin case bane bale har a yi gaggawar kasheshi cikin ƙanƙanin lokaci, dole suka haƙura suka koma ba tare da ko ganinta sun sami damar yi ba, don a zahirin gaskiya Zee tana cikin mawuyacin hali saboda yanzu haka tana Asibiti maƙale da oxcegyn saboda azabar da ta sha a hannu ƴansandan.
Tsawon sati biyu dangin Zee suna ta sintiri tsakanin Gombe da Yola akan su samu a kashe case ɗin, da ƙyar suka yi nasarar karɓota a hannunsu bayan uwayen miliyoyin kuɗin da suka narka saboda kawai a kashe case ɗin ba sai ya je kotu ba, don shi Safwan kallonsu kawai ya ke yi saboda shima kanshi da kalar na shi takun a ciki, don gurinshi na son ta gane kuskuren da ta aikata, don har lokacin bai cire takaicin dawo da itan da Hajiya Mama tasa aka yi ba, shiyasa ya nemi alfarmar Hajiyar akan a barta ta je gida har sai ya nemeta, haka ko aka yi sun karɓota aka kaita wurin Hajiyarmu ta bata haƙuri sannan ta baiwa Safwan da Dijen haƙuri suka kwasheta aka nufi Gombe da ita, inda ita kanta ta ji ina ma ace akwai wani garin da zata je ba cen Gomben ba, don tasan muddin ta je cen dole ne ta fuskanci ƙalubale ba kaɗan ba wajen ƴan'uwanta musamman masu goyon bayan Aminu.
To fa sai hkr Zee😊
Akafta🙌🏻
D/AUTA CE✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*
*NA HADIZA D/AUTA*
*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*
*Don Allah masu neman book ɗin Ƙarangiya daga farko ku yi haƙuri idan an kammala za ku sameshi a complete ɗinshi, plss ku yi haƙuri kunji😢saboda anyi nisa sosai kuma bana son kuna tambaya baku samu ba😆*
*Lamba 66*
Zee durƙushe ƙasa tana kukan fitar hankali gaban gadon da Mahaifinta yake kwance gorar ruwa saƙale a hannunshi, ya yi shiru yana sauraren sautin kukan nata, zuciyarshi cike fal da wata sabuwar damuwa don abunda ta aikata da saƙon da Safwan ya isar masa ba ƙaramin dukan zuciyarshi suka yi ba, duk da ko an sanar da shi cewa ya mayar da ita a matsayin matarshi, amman har wannan lokacin bai dawo cikin natsuwarshi ba, wata ƙanwar Mahaifinta ce mai suna Baabaah Asabe ta katsa mata wata uwar tsawa ta ce
"Zaki ta shi ki bar ɗakin nan ko sai kin iyar da kashe muna ɗan'uwa ne?"
Zee ta miƙe jikinta yana rawa dafe da bakinta tana toshe kukan da yake fitowa tana kallon Daddynta bata son fita, cikin wata sabuwar tsawar Baabah Asabe ta sake cewa
"Ki fita na ce ko sai na fiddaki da ƙarfi ne?"
Zee ta dinga ja da baya tana gunjin