Showing 69001 words to 71408 words out of 71408 words

Chapter 24 - MATAR GWAMNA BOOK1 COMPLETE

ya ji kayan lambu da hanta.

Lokacin da ta kawo tare suka zauna, suna ci tana bata labarin wasu 'yan ƙauye da suka zo kwanakin baya wai su dangin Matar Gwamna ne. Suka z

o su kusan takwas da tsummokaransu har da zabi da suka riƙo wai za su bawa Gwamna, da aka hanasu shiga suka ƙi tafiya suka tsaya a bakin gate, ƙarshe aka nemo Yaya Bello ya zo ya gansu yace bai ta

ɓ

a ganinsu ba. Asiya tace abinda ya fi bata dariya wai su

da Yafendon Tabawa uwa

ɗ

aya uba

ɗ

aya suke.

Umma ma sai da tayi murmushi. Asiya ta cigaba da gaya mata cewa kusan kullum sai an kirata ana ƙaryar dangi da ita. Akwai wadda tace ƙanwar Ale Faruƙ ce Asiya tace mata Ale ba shi da ƙanwa mace.

Bayan Isha Ya

Ubayd ya zo gaida Umma. Sama-sama suka gaisa da Asiya kowa da abinda yake ji a zuciyarsa.

"Asiya we have to talk" ya fa

ɗ

a yana nufin ta yiwa Umma bayani.

Umma dai ta yiwa Asiya kashedi akan ta sani ita

ɗ

in matar wani ne dan haka ta kama kanta.

A

ɗ

a

kin suka yi maganan nasu wanda ko Umma da bata jin abinda suke fa

ɗ

a zai da ta zargi akwai matsala. Da ta tambayi Asiya mi suke fa

ɗ

a Asiya ta mata ƙaryar magana suke akan bikin Faty da za ayi, tace sai anyi Kamu shi kuma yace ba za ayi ba. Umma tace mata ta

bari yai abinda ya dace domin ya fita kusa da Faty.

Ubayd dai fita yai a

ɗ

akin ransa ba da

ɗ

i.



*THE GOVERNOR'S WIFE*

...... MATAR GWAMNA....



*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat



Bismillahir Rahmanir Rahim



Book one

19



Da dare kusan ƙarfe goma COS ya je wajen Yalla

ɓ

ai, batun tsige Gwamna da ake shirin yi ya kawoshi. Ya sani Umaru Kwom ne da wannan shiri amma kuma yana da yaƙini akwai sa hannun Mr Paul a ciki.

"Yalla

ɓ

ai baka ce komai ba. Kana so a tsige Saifudde

en ne?"



Yalla

ɓ

ai yai dariya yace "Lamara kenan, kana ganin za su iya tsige shi ne?"

"Amma tunda suka fara maganar ai sun shirya wa abun ne"

" idan sun shiryawa abun ai Alhaji Sani Kachallah ma a shirye yake"



"Hakane kam, amma nayi mamaki

da kace kada na fa

ɗ

awa kowa cewa Asiya ta ha

ɗ

a hannu da Umaru Kwom"

"Wannan rikicin cikin gida ne, mu zuba musu ido kawai"



"Yarinyar fa abin tsoro ce, kada gaba ta zo tana bamu matsala"

"Ina ganin akwai rawar da Asiya zata taka a gwamnati Saifud

deen Kachallah, The girl has Charisma"

Yalla

ɓ

ai yai maganar yana shafa gemunsa.



***

Maganar tsige Gwamna da ake yi ya ja hankalin ƙasar kan siyasar jahar Congo. Ko'ina ka shiga maganar ake yi. Mutane da dama sun yarda Saifuddeen Kachallah mutum

ne adali, yayinda wasu maganar albashin 'yan fensho da ba a biyaba ya sa suke ganin ya gaza.

A

ɓ

angaren Asiya ko

ɗ

ar ba ta ji ba da Ubayd ya mata magana akan kada ta aikata abinda tayi niyya. So take ayita ta ƙare, ana tsige shi za ta nemi takardar saki

idan ya ƙi bata kuma kotu zata kai shi a musu Khul'i.

Ba abinda zai sata farinciki sama da ta ji yau ance mata an tsige Saifuddeen daga muƙaminsa na Gwamna. Ranan ƙila sai ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

A

ɓ

angaren Bilkisu kuwa ta rantse babu wanda ya isa

ya tsige mijinta. Idan aka tsige Saifuddeen tamkar an mata tsirara ne a kasuwa.

Shima Alhaji Sani Kachallah ya shiga ya fita akan maganar dan har wajen party chairman na ƙasa yaje sun bashi tabbacin indai Saifuddeen bashida laifi ba wanda zai tsigeshi.



Wannan magana yasa Alhaji Sani ya gane akwai mutane masu fiska biyu, kai har uku ma a tafiyarsu, kuma da sannu idan ƙura ta lafa zai yi maganin 'yan banza.

Sun za

ɓ

i ranan da Gwamna zai je bu

ɗ

e stadium da aka gyara a matsayin ranan da za a wallafa da

lilin daya sa za a tsige Gwamna. Lokacin da Umaru Kwom yace zai sa a jefi Gwamna Asiya tayi na'am da hakan. Duk abinda zai ƙasƙantar da Saifuddeen Kachallah to tana so.

Abinda Asiya bata sani ba shine, shirin da take da Umaru Kwom daban, shima shirin d

a yake da nasa mashawartan daban. Ita burinta ta

ɗ

au fansa akan Gwamna Saifuddeen ne shi kuma burinsa ya ham

ɓ

arar da Saifuddeen saboda ya samu ƙarfin gwiwa a za

ɓ

en da za ayi. Idan ya tsaya takara da Saifuddeen to ba makawa zai rasa kujerar amma idan da wan

i daban ne yana da yaƙinin zai ci za

ɓ

e.



***

Ranan Asabat ƙarfe tara da rabi Gwamna ya fita daga gida zai fara zuwa Kachallah house kafin ya wuce Stadium.



Asiya ta zauna a

ɗ

aki tana jiran komai ya tafi yadda aka tsara.

Ƙ

arfe goma saura kwata w

ayarta ya fara ringing, ta

ɗ

auka da sauri ganin Fou'ad Salisu ke kiranta. Bayanin da ya fara mata ne ya sata miƙewa tsaye da sauri dan ta tabbatar dai kunnenta ya ji dai dai.

"Hello kina jina? Na ce ba Gwamna ke da wannan account

ɗ

in ba. Alhaji Sani Kacha

llah ne. Account

ɗ

in Sa'ad Kachallah an bu

ɗ

eshi lokacin Gwamna yana shekara goma a duniya, bashi da masaniya akan account

ɗ

in. Na gayawa Umaru Kwom amma ina ganin kema ya kamata ki sani"

Tabbas ta ji shi a karo na farkon da yai maganar. Ɗimuwa, ki

ɗ

ima d

a gigicewa shine ya sa ta daskarewa a wajen.



Asiya ta tun

ɓ

uke

ɗ

ankwalin kanta ta yi cilli da shi lokacin da wayar da ke

ɗ

are a kunnenta ya fa

ɗ

o ƙasa.

"Na shiga uku ni Asiya" ta fa

ɗ

a tana dafa ƙirjinta

*idan labarin nan ya fita, sunana zai kafa tar

ihi a duniya. Zai kafa tarihin cewa ni ce Matar Gwamna ta farko a tarihin ƙasar nan da na yaƙi mugun Gwamna na kawo ƙarshen sa*



Abinda ta fa

ɗ

awa Ubayd kenan ranan da ya mata magana a kan abinda take shirin yi.

Kalamansa suka fara dawo mata filla fi

lla a kwanyarta.

"Asiya ki dena abinda kike yi. Babu kyau. Gwamna adalin mutum ne, shi

ɗ

an Adam ne, zai iya yin kuskure kamar kowa, ki masa uzuri. Kar ki manta fa MIJIN KI ne. Ko ban aureki ba Asiya har gobe ke ƙanwata ce, dan haka ba zan ta

ɓ

a bari kiyi

abinda zai jawo miki dana sani ba. Ki riƙe mijin ki da kyau ki dena ƙoƙarin ham

ɓ

arar dashi. Ki rungumi mijinki Asiya, we are not meant to be"



Ta durƙusa ƙasa ta

ɗ

auki wayarta da sauri. Hannunta

ɓ

ari ya ke lokacin da take ƙoƙarin kunna wayar saboda ta

mutu lokacin da ta fa

ɗ

i ƙasa.

Wayar na kunnuwa ta shiga lalubo numbar Mr Bassey, tana danna numbar ta ƙara wayar a kunnenta, ga kowanne ringing da ke fita yana dai dai da dokawar da zuciyarta ke yiwa ƙirjinta yana ƙoƙarin barin mazauninsa.

"Hello. Mr

Bassey. Kar a fitar da labarin nan. A dakatar da komai" ta fa

ɗ

a da iya ƙarfin muryarta.



"Miya faru Hajiya?" Ya fa

ɗ

a cike da mamaki bayan awa biyu da su ka wuce aka gaya mi shi cewa ya wallafa labarin.

"Dan Ubanka na ce a dakatar da komai, komai na

ce"

Ɗ

if dodon kunnenta ya buga saboda dena jin komai da ta yi na wasu daƙiƙu. Lokaci guda ta yi fatan inama kaman Umma Allah yayi ta marar ji marar magana.

Durƙusawa ta yi ƙasa, ƙafafuwanta da gwiwowinta su ka nitse cikin lallausan Italian carpet da

ke

ɗ

akin. A yanzu maimakon laushin carpet

ɗ

in kaushin sa take ji, ji ma take kamar a cikin harawan dabbobin Umma ƙafafuwanta suke.

*" Hajiya, ai kusan minti talatin kenan da wallafa labarin a website

ɗ

in mu da shafukan sada zumunta. Yanzu haka an fitar

da jaridan kasuwa"*



Bata iya cewa Mr Bassey komai ba saboda aikin gama ya gama.

Idan labarin nan ya isa ga Gwamna zai yi bincike, ba za a da

ɗ

e ba zai gano cewa itace da wannan aikin, ita ce take yiwa jaridar Climax rubutu. Idan aka jefi Gwamna ba

lallai ya san akwai hannunta a ciki ba, tunda yana da maƙiya dayawa zai ma

ɗ

auka mutanen Umaru Kwom ne da wannan aikin. Amma idan ya san ta ha

ɗ

a hannu da Umaru Kwom wajen ham

ɓ

arar da shi...

Ta sa hannu ta dafe ƙirjinta da tuntuni ya ke ta bugu da ƙarfi

. Ɗumi ta ji a kumatunta hakan ya sa ta shafa wajen da sauri.

Karo na farko kenan tun zamanta MATAR GWAMNA ta yi hawayen danasanin abubuwan data aikata.

Idan komai ya fito fili sunanta a tarihi zai koma Maƙaryaciya, Mayaudariya kuma Munafuka.

Kyakykya

wan fiskar Gwamna ta hango yana fa

ɗ

in "Asya WHY?"

T V dake

ɗ

akinta ta yi saurin kunnawa ta nemi remote ta lalumo tashar Hill TV dan ta san za su bayyana koma minene dalla dalla.

Daga wajen da ake kawo rahoton kai tsaye na bu

ɗ

e filin wasan ƙwallon ƙafa

da aka gyara suka yanke zuwa labari da

ɗ

umi-

ɗ

uminsa. An bayyana dalilin daya sa ake son tsige Gwamna Saifuddeen. Shekaru shabiyar da suka wuce ya ci zarafin wata yarinya lokacin da ya ke koyarwa a Jami'ar Congo.

Asiya ta zaro ido ganin abinda aka rubuta

da kuma abinda mai karanto labaren ke fa

ɗ

i wanda bai kama hankali ba. Ba abinda ta rubutawa jaridar Climax kenan ba. Ta yi saurin jawo wayarta ta duba website

ɗ

in jaridar Climax ta ga suma labarin cin zarafin da Prof. Saifuddeen yai wa wata

ɗ

alibarsa Lami

Ninja suka wallafa. Kanta ya kulle dan abu daban ta rubuta abu daban aka wallafa. Wacece ma Lami Ninja?.

Ta nemo numbar Umaru Kwom ta danna masa kira, ba a

ɗ

auka ba sai a bugu na uku.

"Alhaji Umaru ban gane abinda ake fa

ɗ

a ba. Na

ɗ

auka maganar ku

ɗ

i

ake"

"Ku

ɗ

in Alhaji Sani ne ba nashi ba, ba za a tuhumeshi da wannan ba shiyasa muka nemo abinda zai ham

ɓ

arar da shi cikin sauƙi"

"Miyasa ba a gaya min ba, miyasa ka barni cikin duhu?"

"Siyasar kenan Yarinya " daga haka Umaru Kwom ya sa dariya ya

kashe wayar.

Asiya tayi taga taga kamar zata fa

ɗ

i.

Kenan Ubayd yayi gaskiya da ya ce zai iya yiwuwa duk abinda ake Gwamna bai sani ba, ƙila kisan Saminu Bacchi ma bai san komai akai ba.

"Ki yiwa kanki adalci Asiya, a iya zaman da kika yi da Gwamna S

aifuddeen kinga alamar zai iya kisa saboda mulki, kinga alamar ku

ɗ

i da dukiya za su ru

ɗ

e shi?"

Tambayar da Ubayd ya mata kenan amma ta bari ƙiyayya da son zuciya suka sa ta amsa da cewa "eh, Saifuddeen Kachallah zai iya duk abubuwan daka lissafo"

"Ko k

in san saboda ya ku

ɓ

utar da ke daga hannun Umaru Kwom ya aure ki. Abba ya fa

ɗ

a min komai, kuma na yarda cewa saboda ya tseratar da rayuwarki ya aureki. He's protecting you Asiya. Umaru Kwom amfani da ke zai yi ya yar. Idan kika gama masa aiki juya miki ba

ya zai yi..."

"Tatsuniya kenan Ya Ubayd, ni yarinya ce da zai kareni, wani irin kariya ne da ba zai iya bani ba har sai ya aureni?"



Dana sani ƙeya. Da ta saurari Ubayd ranan da duk wannan bai faru ba.

A iya zaman wata biyu da sati

ɗ

aya da ta yi

a gidansa ta zalunce shi, ya mata laifi, amma ita laifin data masa ya ninka nasa sau dubu.

Ta kai dubanta ga talabejin inda aka nuna Gwamna na bu

ɗ

e Stadium daya gyara, hannunsa riƙe da Almakashi zai yanka ribbon

ɗ

in da aka sa. Ta ƙura masa ido kaman yau

ta fara ganinsa, tabon sallah da ya fito dal a saman goshinsa, dimple

ɗ

insa da ya ke lotsawa idan yana magana, sajensa da gemu da suka ƙawata fiskarsa. Bata ta

ɓ

a yarda ba idan mutane na fa

ɗ

a amma yau zuciyarta da idanunta sun amince Saifuddeen Sa'ad Kacha

llah yana da kyau.

Ta rintse idanunta lokacin da ta tuno cewa Umaru Kwom ya tsara za a jefi Gwamna da zaran ya gama hidimar bu

ɗ

e Stadium.

Ta jawo wayarta ta yi abu na ƙarshe da take ganin zai fishsheta.

"Allah Sa'id ni" ta furta a hankali, ta kwanta k

an gado ta fashe da kuka mai

ɗ

aci...

A nan na kawo ƙarshen littafi na

ɗ

aya a labarin Matar Gwamna.

*Shin za a jefi Gwamna?*

*Wani hukunci zai biyo bayan abinda Asiya ta aikata?*

*Ya maganar tsige Gwamna?.*

*Shin Hansa'u zata samu abinda ta

ke nema a wajen Bilkisu Kachallah?, wacece ma Hansa'u*

*Shin Umaru Kwom zai yi nasara akan Gwamna Saifuddeen?*

*Wacece Lami Ninja da aka ce Gwamna Saifuddeen ya ciwa zarafi lokacin da yake koyarwa?*

*Shin Gwamna zai iya yin gaban kansa kuwa? Ko dai Alha

ji Sani ne zai cigaba da juya shi*

*shin Bilkisu Kachallah zata bari tauraron Asiya ya haska kuwa?*

*Yaushe Asiya za ta gane cewa ita ce Attaruhu?*

*Akwai yiwuwar soyayya mai da

ɗ

i tsakanin Gwamna Saifuddeen da Asiya Shahidah. Kuwa?*

*ka

ɗ

an kenan daga

cikin batutuwan da za ku gani a kashi na biyu*

From 2g Hausa Novel

Compiled by Hausa Novels Online (Telegram Channel)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login